Showing 171001 words to 174000 words out of 181007 words
na zata kawai amfaninsu a shayar da ɗa, ashe mutum gori ake yi masa idan bashi da su"
Laila ta ce "Sosai makuwa, shiyasa ake son gyarawar ai, kuma gori ba iya na mata ba, har na miji, wanda ya fi kowanne takaici ba, miji yayi miki gori dan baki da su, ko kin bari sun lalace"
Ruma ta sake gyara zama ta ce "To ita ma na maman ilham ɗin zaki sai mini?"
"Eh mana, mai ze hana? Ki din ga biyayya kawai, mun gama magana da ita ma".
Cikin farinciki ta ce "Allah ya sa su fito kan papa ya dawo, kin san me? ce mini fa yake, wai nasa yafi nawa girma, wai nawa kamar girman wake, daga baya kuma wai kamar murfin jarkar faro".
Ƙyalƙyalewa da dariya laila ta yi ta ce "Rabu da shi, kan ya dawo zai sha mamaki, sai ki rama. Ai tun da akwai kunun maman Khadija, da kuma haɗin maman ilham, an wuce wurin, kin wuce gori mutuniyar".
"Allah ya sa anty laila, to zasu kai kamar na samha? Su Fauziyar nan, wai a dubi samha ta fini komai amma ya aureni, idan nawa suka fi nata, ai ba zai aureta ba ko?"
Laila ta ce "Wannan kuma effort ɗinki ne zai sanya, ya aureta ko ya fasa"
*INA MASU SON WUCE GORIN KISHIYA, DA NA MIJI, KAI HAR MA DA NA ƳAN UWANKI MATA, TO KU GARZAYA KU GWADA KUNUN SABAYAR MAMAN KHADIJAH DA KE ZAUNE A ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN ZARIYA 08033411249, KU TUNTUƁETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA*
*HAKA ZALIKA KU HAƊA DA MAGANIN MAMAN ILHAM MAI TULA-TULA, MAGANINTA INGANTACCE NE, WURIN BIYAN BUƘATUNKU, BA TARE DA CUTAR DA LAFIYARKU BA, KU TUNTUƁETA TA LAMBAR WAYARTA 0813 561 3021 TANA NAN A KAWO ROAD KADUNA*
*HAJIYATA KAR KI BARI MATA SU SHA GABANKI, SU RIGAKI MALLAKAR MAGANIN MAMAN ILHAM, DA NA MAMAN KHADIJAH, MACE SAI DA GYARA, SUNA TURA KAYANSU KO INA A FAƊIN A NIGERIA, HAR MA DA ƘASASHEN DA MUKE MAƘWABTAKA DA SU*
Bayan sallar azahar, mama ta je ta duba iman, jikin da sauƙi, amma dai tana jin jiki sosai.
Laila kuwa mama ce ta burgeta, saboda yadda take komai nata a nutse, gashi tun da tazo, rumaisa ke tsokanarta take son sakata magana, saboda kamar kakarta ta mayar da ita.
Mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ya tarar mama bata nan, abun da yafi komai ɓata masa rai kenan, dan haka ko abinci yaƙi ci, ya koma ƙofar gida ya zauna.
Ya kai awa guda da rabi sannan mama ta dawo.
Mama kamar ƴa da uba, a wajen ta fara yi masa bayani, dan ta san ba shi ba, hatta sauran ƴaƴanta, ba sa son su dawo su ga bata nan, amma na sa yafi yawa.
"Ƙanwar mijin rumaisa aka kwantar a asibiti na je dubata, daga nan na wuce mandawari na sada zumunci da ƴan uwana"
"Wacce daga ciki?"
Mama ta ce "Wadda ka ke tsoratawa mana, iman, ciwonta ne ya tashi, ban ma tarar da hajiyar ba, sai wannan yarinyar, da wata yayar mijin rumaisan".
"To ya jikin nata?"
"Jiki Alhamdilillah, amma dai har na taho bata buɗe ido ba"
Mama ta ɗan yi shiru tana nazarin mai sunan baba, sannan ta shiga gida.
Mama na shiga gida, umar ya ciro wayarsa ba tunanin komai ya kira wayar Iman.
Sai dai rumaisa ta ɗauki wayar.
"Ina me wayar?".
"Mai sunan baba muna asibiti fa, ba ta da lafiya, ba ta tashi ba haryanzu"
Ya katse wayar ya tashi, duk da yunwar da yake ji, ya shiga gida yayi alwalar magariba ya fito.
Ya gama yanke koma menene, yau sai ya je ya ga jikinta, dan gaba ɗaya hankalinsa ya tashi.
Bayan kowa ya tafi, ya rage daga iman sai nusaiba, laila ta ce za ta je gida tayi wanka ta dawo, ba sai ammi ta kwana a asibitin ba, su kwana ita da iman da Nusaiba.
Tun kan ya shigo, gabanta ya tsananta faɗuwa, ba tare da ta san dalilin hakan ba, sai dai ba tare da tayi tsammani ba, ta ji an murɗa ƙofar yayi sallama.
Da sauri iman ta fara kiciniyar neman hularta, dan kanta ko ɗan kwali babu, ba ta taɓa zaton mai sunan baba, ko da wasa.
Nusaiba ta ce masa "Ina wuni"
Ya amsa mata a taƙaice kamar yadda ya saba.
Ba tare da fargabar komai ba, ya je gaban gadon, ya zauna a kan kujerar da ke gaban gadon.
Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Yaya umar ina wuni"
"Ban ganshi ba" ya bata amsa. Kamar yadda yayi tsammanni, ta ɗago ta kalleshi, ta mayar da kai ta sunkuyar.
Ya waiwaya ya kalli nusaiba ya ce "Can you excuse us?" Ba musu Nusaiba ta tashi ta fita.
Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Meya sameki?" Yayi maganar kamar ɗan sanda na tuhumar mai laifi.
"Bani da lafiya"
Jin shiru bai ce komai ba, ya sanya ta sake ɗagowa, ya zuba mata ido, yana jiran ta bashi amsa, dan wadda ta bashi ba ta gamshe shi ba.
"Zuciyata ce take kumbura"
"Meyasa?"
"Nima ban sani ba"
Ya ce "Kin sani"
Shiru ta yi tana wasa da yatsunta.
Ya ce "Well, Allah ya sauwwaƙe, kin san condition ɗinki, bai kamata ki din ga wasa da lafiyarki ba, and na ji rumaisa ta ce You are getting engaged very soon, Allah ya sanya alkhairi"
Kawai ta fashe da kuka, yayi ƙuri da ido yana kallon ta, dan bai san me zai ce mata ba.
Tayi me isarta, sannan ya ce "Auren ne ba kya so?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Meyasa ki kai shi gidanku, idan ba kya son shi?"
Iman ba ta san ya aka yi ta tsinci kanta da yi wa mai sunan baba bayani ba "Bana son shi, mamansa ta ce ba zai auri wadda ba ta da asali ba, gashi ya riga ya kai maganar wurin wambai"
"Idan ba kya son shi, wa ki ke so?"
Ɗagowa ta yi a hankali, suka haɗa ido, jikinta yayi sanyi yayin da mai sunan baba yaji tsigar jikinsa tana tashi.
"Kuka ba ya maganin matsala, Addu'a ce magani, Allah na iya canza komai within seconds"
A sanyaye ta ce "Labarina ba zai canza ba yaya umar, yarinya ƴar tsintuwa"
Ya miƙe tsaye ya ce "Zai canza, put your trust on Allah, Allah Ya ƙara lafiya" tabi bayansa da kallo, wata irin ƙaunarsa na ratsa zuciyarta.
Yayin da shi ma yake jin matsananciyar soyayyarta da tausayinta a nasa ran, ji yake tamkar kar ya tafi, sai ta samu cikakkiyar nutsuwa ta kwantar da hankalinta.
Yana daf da kaiwa ƙofa, Jabir ya buɗe ya shigo.
Ayshercool
08081012143Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Kallon-kallo suka shiga yi, tsakanin shi da umar, sai dai babu alamar mai sunan baba zai bashi hanya, sai jabir ne ya kauce masa ya bashi hanya.
Mai sunan baba na fita, ya jiyo muryar jabir yana yi wa Iman tsawa "Wai iman waye wannan, meye alƙarki da shi, uban me ya zo yi wurinki?"
Cikin wata irin azababbiyar zuciya mai sunan baba ya koma ɗakin, motsin shigowarsa ya sanya jabir haɗiye sauran maganar sa.
Mai sunan baba ya taka, ya je gaban jabir ya tsaya, ya ce "Ni zaka tambaya waye ni, da dalilin da ya sanya na zo wurinta"
Jabir ya haɗiyi yawu cike da kishi ya ce "Na san kai yayan matar Adam ne amm....
Umar ya kaste shi ta hanyar cewa "Bani da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ku, ƙanwata ake aure a familynku, sai dai akwai mutunci da karrama juna, albarkacin ana auren ƙanwata a familynku, ni yakamata ka yi wa duk wannan tambayoyin ba mara lafiyar da ke kwance a gadon asibiti ba, ko ba ka san abun da yakamata ba".
Da ƙyar jabir ya aro jarumta, dan gani yake, da yayi kyakykyawan motsi, mai sunan baba zai iya kai masa naushi, ya ce "Amma ka san babu wata alaƙa tsakaninmu meyasa za ka zo in da take, aurenmu fa za ayi"
Mai sunan baba ya ce "Amma ba ayi ba ko?" Jabir yayi shiru.
Mai sunan baba yayi tsaki, ya nufi hanyar fita, a daidai lokacin laila suka shigo ita da Nusaiba, bai kula su ba ya fice.
Laila ta ce "Waye wannan?"
Nusaiba ta ce "Yayan rumaisa ne ya zo duba iman, shi ya korani waje ma".
"Au ya koraki waje ma, wane irin abu ne zaku din ga barin ƙarti suna kaiwa suna komowa a wurin matar da zan aura, wannan ai cin amana ne"
Laila ta ce "Nawa ka biyamu kuɗin gadin da zamu hana wasu zuwa wurin iman jabir? Kai ka isa kyakywar yarinya kamar iman, ka ce zaka hana masoya zuwa wurinta"
Jabir ya ce "Ba haka bane ba anty laila, amma ai kun san bai kamata ba".
Laila ta ce "Haba jabir, kalli fa kuka take yi, da wanne za ta ji? Kuma dai naga ai baka kai kuɗin auren ba tukuna. Kai baka san ka lallaɓata ba"
Ya ce "Haka ne, Allah ya bata lafiya, kishi ne ya sanya ni yin hakan, zan dawo da safe" ya ajiye ledar hannunsa ya fita.
Laila ta ƙarasa gaban gadon, ta zauna ta rungumo iman tana rarrashinta.
Ta samu ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ashe rumaisa tana da wa babba kamar haka"
Nusaiba ta ce "Ba ki ji ana ce mata ƘANWAR MAZA ba? Yayyenta bakwai maza, ita ta takwas"
"Masha Allah"
Nusaiba ta ce "Amma wanda ya fitan nan, shi da Hassan ɗin sa ne manya, masifaffe ne, ba shi da fara'a ko kaɗan, daga zuwansa fa wai na tashi na fita".
Halin da take ciki, bai hanata sake lafewa a jikin laila ta ce "Ba masifaffe bane ba, yana da kirki"
Laila ta shafa kanta ta ce "Ko dai ko dai? Ko akwai wata a ƙasa ne" iman tayi shiru ba ta ce komai ba.
Laila ma tayi shirun, tana cigaba da shafa kan Iman.
Mai sunan baba kuwa, yana kan babur ɗin sa ƙirar lifan, babu abun da yake tunani sai kukan iman, kuka mai taɓa rai, ga wannan mara hankalin a yanayin da take ciki, ya je yana yi mata masifa.
Laila kuwa sai da ta ga iman ta samu bacci, sannan ta kwantar da ita.
Mai sunan baba sai da ya koma gida, sannan ya samu ya ci abinci, sai dai condition ɗin iman, da kukanta ya gaza barin zuciyarsa.
Tuni laila ta yi bacci, ita da Nusaiba, iman kuwa jin wayarta tayi vibrating a ƙasan fulo, ya sanya ta buɗe ido.
"Ya jikin?" Da sauri ta sake mutstsuke idanunta, ba mafarki bane ba, mai sunan baba ne.
What's app ɗin ta ta buɗe, ta tura masa saƙo "Yaya umar ya ka je gida, Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi, bacci ne ya ɗaukeni, shiyasa ban tambayi ya ka je gida ba".
"I don't mean you should reply now, bacci yakamata ace kina yi yanzu"
Wani irin murmushi iman ta yi, a ranta ta ce 'Gane in da ka saka gaba sai Allah yaya umar'
Tayi masa reply da emojin murmushi ta ce "You are a good counsellor, na ji daɗin nasiharka, but please include me in your prayers, Allah ya bani mafita" ta haɗa da emojin kuka da na magiya a ƙarshe 😭🙏.
Ya sauke numfashi a hankali ya tura mata emojin kuka da cancel 😭❌.
"To na daina in sha Allah"
Ya tura mata alamar jinjina, sannan ya tura voice message, abun da ba ya yi, shi chatting ɗin ma ba damunsa yayi ba, amma yayi mata message "Na ga saura few weeks bikin saukar alƙur'aninki karo na uku, kamar yadda ki ka ɗora a status, wannan kawai ya isheki godiya ga Allah, babbar ni'im ce da baiwa, da ba kowa yake yi wa ba. Dan haka kar ki daina addu'a khadija, kuka baya maganin matsala kamar yadda na gaya miki ɗazu"
Subhanallah, iman taji voice ɗin babu adadi, musamman jin sunanta na asali a bakinsa, yana da very deep voice irin na cikakken namiji jarumi, wanda muryarsa kawai ta isa sanya mutum shiga hankalinsa.
"Alhamdilillah, yaya umar ashe kana ganin status ɗina, haka ne na kusa sauka a karo na uku, na gode sosai yaya umar, na yadda you are very simple, unlike before da kake bani tsoro" ai shi ma a nasa ɓangaren, ya saurari voice ɗin ta bai san iyaka ba, sassanyar muryarta wadda yake gauraye da sigar shagwaɓa, haɗi da iyayi mai matuƙar daɗin sauraro".
Tunawa yayi da Jabir ne zai aureta, gaba ɗaya ya ji wani irin haushi ya kama shi, ba tare da yayi reply ba, ya rufe datar sa ya kwanta.
Yayi shiru yana tunanin, duk wanda ya auri mace kamar iman, idan bai tausaya mata ba, sai yaushe, mai zai sanya mutum ya din ga ɗaga mata murya haka, yarinyar da gaba ɗayanta kalar tausayi ce.
***
Sai da ta kwana biyu, sannan aka sallami iman suka koma gida, sai dai ammi ta shiga saƙe-saƙe a kan batun auren nan.
Rumaisa ta zauna ta zana takawa a plane sheet, tare da calendar a ƙasa, wadda kullum take cancel ɗin kwanan wata, na lokacin dawowar takawa.
Laila ta ce "Rumaisa meye haka? Ya zaki liƙe mini hoton gunki a ɗaki"
"Papan ne gunki, wallahi ba gunki bane"
"To ni a wurina gunki ne mana, kawai ki zana ɗan alajani ki kafe mini, baga hotonsa nan a waya ba"
Ruma ta ce "Ni bana son na waya, na fi son wanda na zana shi da kaina, ba kin hanamu yin video call ba, kuma ke kullum sai kin ga mijinki ba, ki bar mini zanena"
Lailaa kawai tayi murmushi, wasu lokutan rigimar rumaisa dariya take bata.
"Kin sha kununki na yamma, da maganin maman ilham?"
"Na sha mana, ai anty laila bana wasa”
Ta ce "Good, yanzu dai je ki ɗaukko jakarki ta islamiyya, da ta makarantar boko muyi karatu, kin ga exams za ku fara"
Ruma ta tashi ta ce "Bari in ɗaukko, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi"
Tana fita falo tayi kiciɓis da Jabir, ya ɗago a yastune ya kalleta ya ce "Yauwwa dan Allah yi mini magana da iman mana"
Cikin tsiwa ta ce "Kai ka isa? Wallahi baka isa ka aikeni na je ba, ka nemi ƴar aiken ka"
Jabir ya ce "Wai ke meye haka, ka kowa ma sai ki ci masa mutunci baki da kunya?"
"Ina dai yi wa mutane marasa kirki, kuma wallahi ba zan bari ka auri iman ba in sha Allah, yayana zata aura yaya Umar ba, kuma zaka gani, idan kana da zuciya ka canza hali, ka fara zuwa ka kula da mahaifinka, kan ka yi tunanin auren iman"
Ba ƙaramin zafi maganganunta, suka yi
Ya risuna ya gaida ammi, suka gaisa yace mata wurin iman ya zo, ammi ta ce masa iman tana bacci, likita ya ce a bari ta samu hutu.
Ko da jabir ya tafi, rumaisa ta din ga ziga ammi, tare da nanata mata idan har jabir bai tausayawa mahaifinsa yayi jinyarsa ba, tayaya zai tsaya ya kula da iman da ciwonta?.
Daɗin daɗawa ga masifa da tijarar mahaifiyarsa, da take iƙirarin cewa ba za a auro mata wadda ba ta da asali ba.
Kasancewar rumaisa tayi sara a kan gaɓa, domin zuciiyar ammi ta fara kaiwa da komowa a kan batun, ya sanya ta ji ita ma ta gamsu da maganar rumaisa.
Abu kamar wasa a hankali mai sunan baba ya fara ɗan sakewa da iman, da Allahn da yayi shi ba shi da yarda ko kaɗan.
Duk safiya za ta yi message ta gaishe shi, daga nan kuma sai ya tamabayeta ya jiki, sai dai tana shan fama kan ta ɗan ja shi da hira.
Sai dai ta fuskanci yana son tayi zancen karatu, mussaman na addini, hakan ya kan riƙe mata shi, gaba ɗaya mai sunan baba mu'amala da shi sai mai haƙurin gaske, miskili ne na bugawa a jarida.
Mai sunan baba yana lura da yadda Aliyu yake gudanar da tasa soyayyar, ba kunya yake soyewa da ƴar mitsitsiyar yarinyar da a baya yake zage gwanji ya kwaɗe Saboda rumaisa.
Komai ya siyo sai ya ce tun da ba ruma wannan na sweet hibba ne.
Mai sunan baba ya fara tunanin yi wa iman kyauta, amma sai ya rasa ita da ke wannan gidan mai zai bata ma? Wani irin kallo ma za ta yi masa idan ya bata abu.
Unexpected ya ga Mahmud a online, suka gaisa mai sunan baba yake tambayarsa ya mai jiki?
Mahmud ya ce "Wace mai jikin?"
"Ƙanwarka mana, khadija" sai da Mahmud ya ɗan yi shiru sannan ya tuna sunan iman ne.
Ya ce "Ohh tana lafiya, ban ma san ba ta da lafiya ba ai".
Cikin mamaki yake tambayar sa ya aka yi bai san ba ta da lafiya ba.
Mahmud ya ce "Labarin dogo ne, amma ina da tabbacin jikinta da sauƙi, dan na ganta ɗazu tare da daughter na a garden".
Mai sunan baba ya ce "Ina so mu yi magana ne, ban taɓa shiga abun da ba ruwana ba a rayuwata, amma a wannan karon, ko sau ɗaya na ji ina son shiga, kuma ban ji zan iya maganar da kowa ba sai kai"
Mahmud ya ce "Ba damuwa, lallai na ciri tuta, bari mu yi maganar ta waya".
Mai sunan baba ya kira Mahmud da kansa, Mahmud ya ce "Ina shirin kiranka"
Ya ce "Bakomai, ni yakamata na kira dama. A kan Khadija ne, na je asibiti na duba ta, kamar yadda ta gaya mini tana da ciwon zuciya ne, amma kun san da wanda zaku aura mata ba ta son shi? And he is even mad gayen, ba shi da hankali gaba ɗaya, tayaya zai je yana mata shouting a ka a condition ɗin da take, ba tare da ya tausayawa halin da take ciki ba?. Yakamata ku ƙara bincikarta, kar zurfin cikinta ya sa ayi abun da zata cutu"
Ajiyar zuciya Mahmud yayi, shi kansa yana tausayin iman, kuma yayi dana sanin abun da ya yi wa ammi lokacin da ta roƙi ya auri iman.
Yarinya ce nutsatsiya da ba ruwanta da hayaniya, ita ma ta tashi cikin tsantsar ƙalubalen rayuwa, a wannan gaɓar kan shi ma ya san za ta cutu idan ta auri jabir, dan ya fita baki, kuma ba kirki ya cika ba, ya ji ina ma zai iya yin wani abu