Showing 180001 words to 181007 words out of 181007 words

Chapter 61 - kanwar maza 3 COMPLETE

12 Jul 2024

39247

sannan ta tashi ta bar ɗakin, ranta babu daɗi, yayin da tausayinta ya mamaye zuciyar turaki, tana da kyakywar zuciya, sai dai tana ta fuskantar ƙalubale kashi-kashi a rayuwarta da ta iyalanta.

Yanayin yadda ammin ta dawo ne ya tabbatar musu akwai damuwa, har ruma za tayi magana, amma laila ta hanata.

Yau wunin yau idon mai sunan Baba yana kan waya, ko zai ga saƙon iman, amma shiru, shikuma ya kasa yi mata magana, har dare shiru, gashi ya riga ya saba da daddare ɗan jan sa da take da hira, yana yi masa daɗi.
Haushi ne ya ishe shi, jin yadda Aliyu ya cika masa kunne da surutu shi da habiba, ya saka waya a speaker sai ƙyalƙyala dariya yake yi, habiba ta karkace murya tana yi masa waƙa, murya kamar an shaƙe kuliya.

"Kaga ka cika mini kunne, ko dai ka fita, ko kayi mini shiru.

Aliyu ya miƙe tsam da wayarsa, ya koma tsakar gida, duk da sanyin da ake zabgawa.

***
Jabir ne a zaune, hajiya Lubabatu da Mummy sun saka shi a gaba, suna ta yi masa famfo.

"Na sha gaya maka giwa ba ƙaunarka take yi ba, ka din ga nane musu, to gashi ƙiri-ƙiri ta hanaka auren ƴa, saboda azabar ƙarya ta je ta ce wai ni ce bana son auren nan, mun yi haka da kai? Da na nuna bana so ka dage, cewa nayi Allah ya sanya albarka, amma da yake mukafuka ce, ba ta yi niyyar baka auren ba, ta je ta ce nice bana so".

Mummy ta amshe ta hanyar cewa "Banda abun jabir, kai da ake yi wa fafutukar samun kujerar mahaifinka, ina kai ina wata ƴar tsintuwa, mara asali mata gata, kai ana ƙoƙarin ka samu kujera, amma ka nacewa Adam, shi ka san me suke yi ta ƙarƙashin ƙasa, dan ganin kujerar ta koma garesu, ga mata nan bila adadin a gari, ni ko ruƙayya ma sai na baka"

Hajiya Lubabatu ta ce "A'a wace irin ruƙayya kuma? A dai cigaba da neman kujerar, shima uban nasu ban taɓa tunanin zai kai haka a raye ba, kalli shi adam ɗin da kake liƙewa, yadda yayi suna a ƙasar nan, duk gaku matasa amma aka ware shi, aka tura shi wakilci, yayi aure ya haifi ɗa, ga aikinnsa ga kasuwanci, kai kana nan kana fama daga kai har jamil ɗin uwar me ku ke da shi, duk da dukiyar iyayenku ku ke taƙama"

Jabir yayi shiru tare da gazgata maganganun da tun a baya su mummy suke gaya masa bai ɗauka ba, tare da mantawa da asirin da takawa ya daɗe yana rufa masa tsawon shekaru.

Mummy kuwa ƙulattar Hajiya Lubabatu ta yi, da ta ce ya auri ruƙayya ta ce a'a, wato a tunaninta ya samu mulki, aci moriyar ganga a yada kwauronta.

Mummy a ranta ta ce 'Lubabatu baki da hankali, da ni ki ke zancen, lokaci yayi da zamu raba gari, kowa ya san in da ya kama'.

Kasa jurewa mai sunan baba yayi, ya fara tunanin ko jikin iman ne ya dawo, dan haka da kansa ya kira iman a waya.
Sallamar da yayi ta amsa cikin siriryar muryarta.

"Jikin ne dai?"

"A'a barka da safiya yaya umar"

"Meyafaru?"

"Bakomai" tayi maganar cikin sauke numfashi.

"Something is going wrong, feel free to share it with me"

"Yaya umar ba zan dameka da matsalolina ba?"

Cikin nutsuwa ya gyara zamansa ya ce "If you are free with me, let's share it together"

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi ta ce "An yi cancel ɗin engagement ɗina da za ayi".

"Ba abun da ki ke so kenan ba?"

"Ba cancel ɗin ya dameni ba, tun da Allah ya sa na buɗe ido a hannun ammi, take bani kariya da nuna mini ita ta haifeni, amma mutanen da suke kusa da ita, basu bata goyon bayan hakan ba. Saboda ni ba irin tashin hankalin da bata shiga ba, kullum cikin damuwa take, kullum cikin sintiri kaini asibiti, kullum cikin neman abun da zai sani farinciki take,. Amma ni na kasa kawo mata farinciki ko sau ɗaya.
Ban san dalilin fasa Engagement ɗin ba, mai girma wambai ya ce ko tayi mini aure nan da watanni uku, ko ta mayar da ni in ta tsinto ni, babban abunda ya dameni kukan da ammi ta sha, ta ce da ta rabu da ni, gara ta ɗauke ni mu bar gidan, ni rasa me ma zan yi, ina son ammi amma ba zan so ta bar gidanta ba".

A tsakiyar zuciyarsa ya din ga jin kukan iman, ya jingina jikinsa da bango, wata irin karaya ta kama shi.

A hankali ya ce "Khadija, kukan nan yana taɓani sosai, bana son jin kukan mace, ko ban santa ba, zamu yi waya anjima. Amma dan Allah bana son sake jin labarin kina asibiti, ya isa haka"

A hankali take sassauta kukan, ta ce "Yaya Umar, na gode da ka bani dama ka ji abun da yake damuna, na gode sosai"

"Don't mentioned, ki ci abinci ki kwanta ki yi baccinki, ki cigaba da addu'a, ba abun da zai faru sai ikon Allah khadija" shi kansa mamakin yadda ya tausasa murya sosai yake, bai taɓa zaton ya iya rarrashi haka ba.

Rumaisa kuwa Mahmud ta kira a wayar Anty laila, ta ce tana son ganinsa a in da suke haɗuwa.

Babu jimawa kuwa suka haɗu, sai dai cikin tsananin fushi ruma ta ce "Daddy anya mummy na son taga Annabi kuwa, daga ita har babar jabir fuska kamar an mari biri? Ya za ayi ta zo ta ce ba zata bari ɗanta ya auri Iman ba, ammi ta ce a fasa a janye, ta ce ita ƙarya aka yi mata ba ta faɗa ba?

Ammi sai kuka take yi, har da masu kiranta a waya, ana bata kyauta ba, ta hana jabir iman, gashi wambai ya ce idan ba ta aurar da iman ba ta mayar da ita in da ta tsinto ta, wai ya suke so baiwar Allah nan tayi ne, daga ita har Iman ɗin sai koke-koke suke yi, wai kai ba abun da zaka iya yi a kai? To ni zan je wurin wamban sai na tonawa kowa asiri da kaina, ayi wadda za ayi ta ƙare!

Ayshercool.
08081012143

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login