Showing 165001 words to 168000 words out of 181007 words
ammi ta bata ɗaki, amma ta ce a wurin iman za ta kwana.
Cikin dare iman ta tashi ta yi salloli, sannan ta zauna ta ɗauki wayarta tana dubawa, rumaisa na kallonta, a haka bacci ya kwasheta.
Da safe rumaisa na baccin safe, laila ta shigo da system a hannunta, ta tashi rumaisa.
Ruma ta buɗe ido ta kalleta, "Kin manta hau zaki fara zuwa islamiyya ne? Tashi mijinki zai yi magana da ke"
Rumaisa ta kalleta ta ce "Da computer zan yi wayar?"
Laila ta dungurarwa da ruma computer a gabanta, tana kalla ta ga fuskar takawa.
Ta ce "Laaa video call a computer"
Yayi murmushi ya ce "Hi little mimi".
"Iyee daga zuwa turai har ka koma bature, irin...." Sai kuma ta kalli laila ta yi shiru.
Yayi murmushi ya ce "Ba ki tashi ba ne? Yau zaki fara zuwa islamiyya fa, ki tashi kiyi breakfast, ki shirya a kai ki"
Ruma ta yi miƙa ta ce "Shikenan weekends ma ba zan huta ba".
"Ki yi haƙuri, ina boy, bai tashi ba ko?"
"Eh, bacci yake shi da anty iman, kai har ka karya? Waye ya dafa muku abinci?"
"Har ɗaki aka kawo mana, na karya"
"To yaushe zaku fara taron?"
"Sai Allah ya kaimu anjima" ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mimi meyasa ki ka bani abun da zai sakani kuka?"
Jiki a sanyaye ta ce "Ba dan kayi kuka na baka ba, ni ba dare ba rana, abun ci mini rai yake, amma ba na ce maka kar ka tambayeni komai a kai ba, sai anjima, bari na ɗan ƙara rage bacci".
"Mimi tsaya ki ji".
"A'a gaskiya sai anjima" ta ture system ɗin ta kwanta.
Laila ta daki ƙafar ruma ta ce "Ke wace irin mashirirciya ce ne?" Ruma ta yamutsa fuska ta kalli ruman.
"Ya tafi wata ƙasar, kuna waya ki kashe? Babu wani abu mai jan hankali, ba rausaya murya ba karairaya, wai ce miki aka yi dan kika ƙanwar maza, ki din ga abu kamar namiji, you are not romantic at all, mijinki matashi ne, kuma kema kin san yana da masu son sa, ko dai ki gyara ko ki ga abun da ba kya so. Ki tashi ki yi wanka ki zo ki karya"
Ta ɗau system ɗin ta, ta bar ɗakin, rumaisa ta zumɓura baki sannan ta tashi.
Laila kuwa komawa tayi, tana jinjinawa takawa. "Takawa i salute your effort, Wannan matar taka, zan iya saka bulala in zaneta wataran, she's very stubborn, beside she's much more than how i expect, ba ta ji ga taurin kan tsiya".
Adam ya ce "Haba madam, duk ita kaɗai, ki yi ta haƙuri kema, halinku ne ya zo ɗaya shiyasa ba kwa jituwa, da ɗaya daga cikin ku na da haƙuri, zaku zauna lafiya, idan ku ka saba shikenan".
"Anya zan iya jurewa? Ba ta ji fa"
"Tuba muke, ayi haƙuri dai".
Rumaisa ta shirya cikin dogon hijjabi, hatta jakar islamiyya da litattafai adam ya sai mata komai, sidi ya ɗauke ta suka tafi makarantar.
Ya je ya gabatar da ita, mai makarantar ta ce ta san da zuwan rumaisa, aka kai ruma aji.
Mamki ne ya cika su kansu ƴan ajin, ganinta sanye da hijjabi irin na islamiyyar, suna mamakin kar dai matar aure ce.
Mai makarantar ta gabatar da rumaisa a wurin malamar da take ajin, zungu-zungui ta wuce ta je ta zauna, tana jin haushin kallon da suke yi mata.
Ajin duk manyan mata ne, dan da yawa sun haifeta, wasu kuma sun yi ƙanwa da ita sosai da sosai.
Aka yi lesson ɗin da za ayi a ka gama, har lokacin tashi ba ta kula kowa ba, sai da aka tashi suka din ga tambayarta ko matar aure ce ita, sai dai ta din ga bin su da ido, taƙi magana.
Sidi ya zo ya ɗauketa, amma ta ce masa ita ɗorayi zai kai ta wurin mama, ya ce ai ammi ba ta sani ba, ruma ta ce ba ruwansa, idan ba zai kaita ba, ya ajiyeta ta je ta hau napep.
Haka ya juya kan motar suka tafi ɗorayi.
A ƙofar gidan yara suka tsatstsaya suna kallon uwar motar da aka kawota a ciki, har da maƙwabciyarsu shamsiyya a leƙowa, tana ɗagowa ruma hannu.
Ruma ta ce 'Lallai matar nan, saboda ta ganni a mota, har da ɗago mini hannu, nan gaba a daidaita sahu zan din ga zuwa, in ga ko za samu masu kulani'.
Ta kalli sidi ta ce "Ba sai ka dawo ɗaukata ba, zamu yi waya da uncle Mahmud" ta shige cikin gida, bakinta ɗauke da sallama.
Gidan shiru, sai Aliyu da yake girki a kitchen.
Ya amsa mata ya ce "Koma bamu san da zuwanki ba, daga tafiyar mijinki jiya, yau kin fara yawo".
Ta ce "Ai da yake ba wurinka na zo ba ehe" ta shiga ɗakin mama, mai sunan baba yana kwance a kusa da mama, yana kallon tv.
Mama ta ce "Ke daga ina?".
"Makarantar matan aure wai ya saka aka kai ni, mai sunan baba ina kwana"
"Lafiya ƙalau"
Ba ta tsammaci wata magana sama da haka ba daga gare shi ba dama, dan haka ta zauna ta ce "Mama jiya ya tafi fa".
"Haka Aliyu ya ce mini, ina mai gidan nawa, ina ƴa ta iman, ki ka zo mini ke kaɗai?"
Mai sunan baba ɗan gyarawa yayi, yana jiran jin amsar da rumaisa zata bayar, a kan iman.
"Mama, ni in koma kenan?"
"Gaskiya dai, ba iman ba mai gidana, sai ke fitinanniya"
"Ai shikenan, gara na koma wurin ammi. Sabir yana nan ƙalau, iman kuma gari ba daɗi, tsoro nake ji kar ciwonta ma ya tashi"
A fuskar mai sunan baba ta ga razana, amma saboda azabar miskilanci yayi kamar bai san me suke faɗa ba.
Mama ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka, yara ƙanana da ku, har kusa abu ya dameku a rai".
"To ammi kin san familyn na su sai a hankali, sun takura mata da yawa, kin san ba ammi ce ta haifeta ba, sau kusan huɗu ana yinƙurin aurenta, wannan muguwar Mummyn tana hanawa, tana cewa mutane ba ta da uba, wai ammi ce garin tsince-tsincenta ta tsinto ta"
Cikin rashin fahimta mama ta ce "Ke kin sani a duhu, kina nufin ba ita ta haifi iman ba?"
"Hmm mama baki san badaƙalar da ke cikin gidan nan ba" nan ruma ta warware mata komai, sannan ta ce "Yanzu kuma wannan jabir ɗin ya ce son ta yake zai aureta, ammi tana ta murna, tun da shi ya san halin da ake ciki, ita kuma iman ba ta son shi sam, akwai wani wanda take so daban, amma ba za ta iya gayawa ammi ba, saboda ammi ta amince jabir ya nemi auren ta, ba wanda ta gayawa sai ni abun tausayi, kuma tsoro take ji kar wanda take so ɗin, ya ji labarin ga a halin da take ciki ya ce baya son ta".
Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, lafiyayyiyar yarinya mai mutunci kamar wannan, babu wanda zai ce ba ita ta haifeta ba, ni cikin yaran nan, da da wanda yake da ƙwari sosai, ai da an auro mini ita, to sai dai ba matar talaka ba ce, ni dai ina ƙaunar yarinyar nan fisabilillahi".
Cikin son sai ta yi pressing ɗin mai sunan baba rumanta sake cewa "Bari kawai ammi, kuma fa baki ga uban samarinta da suke sonta a haka ba, masu kuɗi ta ce ta daina soyayya, kawai ta zo ta fara son wani, amma taƙi gaya mini waye, ba ƙaramin son sa take yi ba. Amma wannan jabir ɗin, ya biyo kai tsaye ta wurin ammi, kuma yana daf da zuwa wurin mai girma wambai, shi kuma wannan wamban ba ɗaga ƙafa, dama yana ta yi wa ammi kashedi, ta aurar da ita ko ta mayar da ita in da ta ɗaukkota, cikin dare ina jin tana ta kuka".
Tsaki mai sunan baba ya yi ya tashi ya bar ɗakin, rumaisa kuwa ta yi wani guntun murmushi, ta tura saƙon yadda yakamata.
Aliyu ya shigo da plate ɗin indomie, ya ce "Me aka yi masa na ga ya fita yana tsaki?"
Mama ta ce "Shi wannan sai an yi masa wani abu ma?".
Ruma ta ce "Za mu ci indomie"
"Ai ko mayya ce ke, sai dai ki ci kan ki"
Tashi ta yi ta koma kusa da Aliyu, ta ce "Dan Allah zan ci".
"Wai ke da mijinki yake ajiye miki komai, ki zo ki saka mini rani".
Ruma ta ce "Allah sarki mijina, ya tafi ya barni, papa saurayina"
Aliyu ya ce "Ke fa baki da kunya ko?"
Flashing aka yi wa Aliyu, ta leƙa wayar ta ga an rubuta "Baby Hibba".
"Ohhh ni ƴa su, yaya Aliyu soyayya?"
Ya harareta, ya kira wayar "Hello my haidar".
"Kuɗin wayar sun ƙare ne ake mini flashing?"
"A'a ba su ƙare ba, bana son ka ɗaga su ƙare ne, kuma ka sake saka wasu, shiyasa na yi maka flashing"
Yayi murmushi ya ce "An taso daga tahfiz ɗin ne?".
"Eh, yanzu na shigo gida ma"
"To shikenan, in ajima zan zo in sake jin haddar. Bari yanzu abinci zan ci"
"To my haidar, ka gaida mama, ka ci ka ƙoshi da yawa".
Rumaisa ta ce "A gaban maman ka ke waya da ƴan mata?"
Daƙuwa ya yi wa rumaisa, ta hau tafa hannaye.
"Yaya Aliyu, habiba ce ta koma sweet hibba?".
"Uban wa ye ya ce miki ita ce"
Rumaisa ta ce "Na rantse da Allah muryar habiba ce, munafuka, habiba take soyayya da yayana, ba tare da tana biyan subcidy ba, dole na je gidansu habiba, mama a gabanki ake soyayya?".
Mama ta ce "Ya ce zuwa za ayi ma ayi masa tambaya, nan da shekara biyu"
Ruma ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Su mai sunan baba ba su yi aure ba sai kai"
"Uban wa ye zai bari kansa ya kulle kamar su? Yaya Abubakar ma kuɗin aure za a kai masa, yana gama service. "
"Innalillahi, yaya Aliyu habiban da ka ke zanewa saboda ni"
Aliyu ya doke mata ƙeya ya ce "Ƴar rainin hankali ba, duk ke ki ka ja, na daki mata ta".
Mama ta ce "Too har an yi auren kenan" da sauri Aliyu ya ɗau plate ya fice daga ɗakin yana dariya.
Wani irin zullumi mai sunan baba ya shiga, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa gane tausayin iman yake ji, ko tashin hankali ya shiga jin wani na neman aurenta, wani irin kishi ne ya taso masa, tabbas ya fi jabir komai, sai dai jabir ya fishi kuɗi, sannan kuma wa iman take so
Yaya usy ne yayi sallama, rumaisa ta tashi da gudu ta tare shi, ta ce "Mussaman saboda kai na zo gidan nan yaya usy".
Ya ce "Ƙarya ki ke yi".
"Wallahi da gaske, zo mu zauna daga nan"
Ba tara da ta bari ya shiga ko wurin mama ba, ta ja shi kitchen ta rufe ƙofa, sannan ta ce "Yaya usy wani abu ne yake damuna, na ga kaine abokin shawarata, na ce bari na gaya maka".
Ya ce "To ina jin ki"
"Yaya usy, dama...dam..mm"
"Wai meye haka ne?"
"Kunya nake ji ne, amma shawara nake nema. Ka ga dama takawa ne kan ya tafi, yake yi mini abun da bai dace ba, kuma"
"Kuma me? Wane irin abu ne da bai dace ba".
"Yaya usy kiss yayi mini kuma, ba zan iya faɗar sauran ba dai, kuma kaga bai dace ba, bana son mama ta gane, ya ce mini wai ai ba komai, in tambaya in ji, wai tun da ihu nake idan ya taɓa ni, zai ƙara aure, kuma ni bana son ya yi mini kishiya. Dan Allah yaya usy ya zan yi, bana son ɓata tarbiyya ta, idan mama ta sani za ta yi fushi da ni, kuma bana son yayi mini kishiya"
Ayshercool.
08081012143
[12/13, 6:55 PM] overlasting: Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Usman ya yi ƙuri da ido yana kallonta.
"Yaya usy ba ka ce komai ba?"
"Ji nake kamar in kama ki in maƙure mini wuya ne".
Cikin damuwa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri"
"Ke dalla ware malama, ke yanzu duk zaman da ki ke yi, yake baki ci da sha, ya ɗauki nauyin karatunki, shirme kawai ki ke tafaka masa, zuwa ki ke kiyi masa ƙiri-ƙiri da ido, kamar gardi a cikin gida, ke kanki ba zaki taɓa waye ba, abun da aka koya miki baki san idan kin yi aure ki waye ba, sai kayan hauka da rashin hankali"
"Ni fa yaya usy ban gane me ka ke nufi ba"
Usman ya ce "Idan bai yi miki kiss ba, wata zai je ya yi wa a waje?"
"Yaya usy, ku fa ku ka ce mini haramun ne, Allah zai ƙona ni idan na yi"
"Kuma sai aka ce miki har da mijinki? Ai gara ya ƙara auren, kuma ba abun da zai hanamu raƙashewa da bikin, ki je ki yi ta shirmenki" Usman ya tashi ya bar kitchen ɗin.
Ta yi shiru tana tunani, ta yaya haka zai yiwu? Sun ce mata abu babu kyau, yanzu kuma an dawo an ce mata ya halatta ba tare da wani cikakken bayani ba. Ta basar da zancen ta cigaba da harkokinta.
Mai sunan baba kuwa rumaisa ta haɗa shi da assignment mai wahalar gaske, domin kuwa kasa sukuni yayi, maganar ta din ga damun zuciyar sa, ya din ga jin tamkar yayi tsuntuswa ya je ya ga Iman.
Da wayar mama, rumaisa ta kira Mahmud a waya, ta ce ya zo ya ɗauke ta, ta bashi adress ɗin gidan.
Yayyen ruma sun sha mamakin ganin Mahmud, basu san shi, ba sai dai wasu lokutan ta kan yi maganar sa.
Ya fi takawa sakewa da mutane wasu lokutan, dan haka nan da nan ya shiga cikin su Aliyu kamar sun saba.
Rumaisa ta ce "Daddy, ga Yasir, shi ne hacker shi ne ku ka yi waya da shi"
"Ki ka kuma ce mini hacker, ba zan sake yi miki wani abu ba"
Mahmud ya ce 'Rabu da ita, ai ni da kai muke aikinmu" ta nuna masa Abdallah ta ce "Ga masterna a wurin zane-zane, da shi nake koyi, duk da idan na taɓa masa kayan zane, wataran ranƙwashina yake, amma a hakan Alhamdilillah na koya, dan haka shi zai yi mana zane, sonake kan papa ya dawo, mun gama komai"
Ya ce "Lallai team ɗin nan an haɗa manyan ƙwari a cikin sa, Allah ya dafa mana". Mama sam ba ta san a kan me suke magana ba, bayan la'asar sosai, sannan ya ɗau ruma suka tafi gida.
Aikuwa ta sha faɗa a wurin laila, wai ta tafi gida, ba a kira takawa an tambayi izninsa ba, ruma tayi mata banza, irin kan ki ake ji ɗin nan.
Kusan sati guda, laila ta saka ruma a gaba, ta hanata sukuni, gashi ta yi ta mata magana da turanci, komai ruma ta yi sai ta ci gyaranta.
Ta hanata kwana tare da iman, tare suke kwana a ɗaki tare da ita, gashi ta kasa ta tsare ta hanata video call da takawa.
Abu ɗaya ne yake yi mata daɗi, kunun maman Khadija na sabaya da take sha safe da yamma, wannan kam tun da batu ake na ci, ruma tana jin daɗin haka.
Ban da wannan, duk wani wanke-wanke da gyaran fata rumaisa ba so take yi ba.
Rumaisa na zaune tana shan kununta, ita da sabir, dan idan suna sha, kamar ya shiga cikin kofin, ko zama ba ya yi, yana tsaye ayi ta bashi yana lashe baki.
Laila sai video call take da mijinta, ga mijin ya fara manyanta, amma ta shagwaggwaɓe, sai taɓara take, tana ce masa baby, suna wani abu mai kama da iskanci a wurin rumaisa.
Rumaisa har leƙawa take, ta sake kallon fuskar mijin, wai wannan gundumemen mutumin ne baby, 'Taɓ sukumbiya, wai baby taɓ' laila tana jin ta, taƙi kulata, su suke wayar amma ita take jin kunya.
Babu babban abun da yake bata mamaki, kullum da daddare sai sun yi video call, laila ta ɗau kwalliya kamar zata biki, ta sha ƙanan kaya, ta zauna a gaban waya ko system.
Yau kam da abun ya ishi kunnuwan rumaisa, ta saka hannu ta toshe kunnenta. Sai da laila ta gama wayar, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ba zaki iya ba ko, ni ƴar iska ce ni da mijina, shi ne ki ka toshe kunne?"
Ruma ta yi shiru. "Ban ce dole sai kin yi irin nawa ba, ni na yi shekaru a gidan aure, na saba da mijina sosai da sosai, ke nake fatan ki daina wannan shirmen, ki san me ki ke yi" ruma ba ta ji za ta iya abun da laila ke yi ba, a ganinta fitsara ce muraran, ga takura mata da take yi.
Da safe kan ta tafi makaranta, ta karɓi wayar iman, ta kira Adam voice call.
"Budurwata"
"Papa" ta kira sunansa a shagwaɓe.
"Ya aka yi?"
"Ni gaskiya wannan anty lailan ta takura mini, ta yi ta mini masifa, da na motsa ta yi mini faɗa, duk ta bi ta saka mini ido".
Adam ya ce "Haba mimi, baki kira ni kin ji lafiayata ba, sai kawo mini ƙara, ke ma ta ce mini ba kya ji, taurin kai ki ke yi mata".
"Yi haƙuri ya kake?".
"Ban sani ba, tun da baki damu da ni ba"
"In ji wa? To yau saura kwana ɗari da saba'in da biyu ka dawo, calendar ce da ni, kullim sai na yi marking kwanakin da suka rage ka dawo"
Adam ya ce "Wow, lallai kin damu da ni sosai, take care, kar ki makara"
"Ni kar ka kashe"
"So ki ke ki makara a school ko?"
"Hmm ka san me?" "A'a sai kin faɗa"
Ji tayi kamar ta gaya masa zancen kunun da take sha sai kuma ta fasa.
Jin tayi shiru ya sanya ya ce "Akwai matsala ne?".
"A'a"
"To ki shirya a kai ki school kin ji budurwata, sai mu yi waya anjima"
Ruma ta ce "Video call nake so mu yi in ganka, amma wannan anty lailan ta hana, duk abun da zai sani farinciki ba ta so".
Ya ce "nima dokar nan ta isheni gaskiya, mutum da budurwasa a hanasu sakewa"
Ruma ta yi dariya ta ce "To saurayina, sai na dawo, kun gama taron yaushe zaka wuce karatun"
Ya bata amsa da "sai Allah ya kaimu jibi".
Da ƙyar suka yi sallama, ta ajiye wayar ta