Showing 3001 words to 6000 words out of 181007 words
'Wai wannan wane irin abu ne kamar almara, Yarinyar da take wurin ƙaro karatu, yaushe ta dawo babu wanda ya sani, yaushe ta yi ciki har ta haihu, ta yaya zamu tabattar da ɗan nan nata ne, kuma kawai ka zo ka ce mana ta mutu, an ce ina gawarta ka ce babu, anya giwa akwai gaskiya a wannan al'amarin naku kuwa?"
Babu wanda ya tanka mata, ciki har da turaki.
"Magana fa nake yi, ko dan ana ganin bani na haifeta ba? Ko bani ma haifeta ba ina da hakki a kanta, tun da ni na riƙeta, dole a kawo mana gawar aisha, kuma yayi mana bayanin yadda ya yaudaremu ya ce karatu ta tafi, yanzu kuma sai gawarta, tabbas akwai lauje cikin naɗi".
Cikin ƙarfin hali turaki ya ce "Ya ishe ki haka Asama'u, na sani, ya gaya mini abun da ya faru na ɓatan aisha, ya sanar mini ni ne na ɓoye hakan ga kowa, na tsananta addu'a a kan abun, amma na gode Allah, da ya karɓi aisha sai ya kuɓutar mini da abun da ta haifa, Allah bai ƙaddara ƙarewar zuriyar fulani a gidana ba. Haƙiƙa na yi rashin 'ya ta gari mai biyayya, ina fatan Allah ya rahamsheta"
"Kana nufin ni nawa 'ya'yan ba su da biyayya kenan?"
Turaki ya kalli Adam ya kai hannunsa ya share masa hawaye ya ce "Na san mun yi rashi, a duniya bayan ni babu wanda ya nuna wa aisha ƙaunar da ka nuna mata, idan na ce zan hukuntaka ban yi maka adalci ba, kuma na san ba zaka taɓa aikata duk wani abu da zai cutar da 'ya ta ba, na yarda da kai ɗari bisa ɗari. Allah ya raya wannan jariri, sannan a sanar da mutane rasuwar 'yata za ayi mata salatul ga'ib. Sannan bana son wani ya san a yadda aisha ta rasu, kawai a bar shi ta rasu a can london wurin haihuwa"
Sosai Adam ya fashe da kuka, yana tuna abubuwan da suka gabata a baya, ya kifa kansa a kafaɗar turaki, turaki ya rungumi kan Adam da hannu ɗaya cike da sigar rarrashi, sai dai shi ma ya kasa jurewa sai da hawaye suka biyo idonsa.
Ammi ma kukan take yi, ji take tamkar a yanzu rumaisa ta faɗi saƙon mutuwar nan.
Mama kuwa ta ce "Tirƙashi nikam zan ga ƙarshen wannan rainin hankali, anya turaki ya ci ka amsa sunanka na uba kuwa, an ce 'yar ka ta tafi ƙaro karatu, kawai akawo maka jariri wai ta mutu a hannun 'yan bindiga, to can ƙetaren suka bita ko kuwa ya aka yi? Hmm to Allah ya kyauta" daga haka ta tashi a fusace ta bar ɗakin.
Turaki ya dubi ammi ya ce "Na san akwai tarin ƙalubale da zai biyo bayan wannan al'amari, amma ku yi haƙuri ku toshe kunnuwanku, komai zai wuce, ni na yarda da ƙaddara, kuma ya zo ya sanar mini ɓatan aisha, yanzu da Allah ya zartar da wannan hukuncin, mun karɓa mun gode, aje a sanar da mutane batun rasuwar.
***
Rumaisa kuwa tamkar za ta shiɗe kan su je gida, wani irin kuka ta din ga yi kamar za ta bar duniyar, mai sunan baba ya hana kowa ya rarrasheta, ya ce su rabu da ita.
Ko da suka je gida, ya san mutane zasu yi ta shigowa jaje, dan haka ya danƙi hannunta ya shiga da ita ɗakinsu, ya dangwarar da ita a kan katifarsa ya ce "Ga wuri nan, ki zauna ki yi ta yi, har ki gaji ki yi shiru, kuma kar ki kuskura na ga ƙafarki a waje, idan ba lokacin salla ne yayi zaki alwala ba.
Aikuwa rumaisa ta ji mai sunan baba ya bata cikakkiyar dama, ta bararraje a kan katifa ta cigaba da satatar da hawaye kamar ba idon bil adama ba, babu ko alamar gajiya a tare da ita, ta ƙudirce a ranta cewar, duk rintsi sai ta je gidan su Adam ta ɗauko yaronta, sai dai a kasheta.
Labarin sallamo rumaisa gida, ya zagaya unguwar su, mutane suka fara zuwa yi wa mama jaje, da sake duba rumaisa, amma sai mama ta ce musu ta samu bacci ne, ba a son a dameta.
'yan tsaigumi suka shiga tambayar ina jaririn da aka ce ga dawo da shi? Mama ta ce musu na miƙa shi ga hannun iyalansa, kuma taƙi yi musu wani cikakken bayani daga haka.
***
Senator wakili ne tare da ɗan sa Khalifa, sai matarsa a kan dining sun kamamla cin abincin dare, wakili ya dubi ɗan sa ya ce "My son, any update?"
Khalifa ya girgiza kai alamar babu, wakili ya ɗan numfasa ya ce "Haryanzu ina tunanin mai ya hana yaran nan cigaba da bincikata, ina tsoron kar wani abun yake shiryawa, na ɗau duk wani mataki da ya dace a kansa, domin a kawo mini rahoton duk wani motsinsa, amma har yanzu ba wanda ya iya gano me yake ɓoyewa".
"Yallaɓai, dan Allah ka mayar da hankalinka a kan siyasarka da future ɗin 'ya'yanmu, kun riga kun gama da ƙasar nan, meye na wani damuwa yadda ku ka dama fa haka ake sha, ko da za a sha ayi amai".
Wakili ya yi murmushi ya ce "Na sani, amma ko sunanmu ya ɓata ya cutar da siyasar mu, kuma mutanen ƙasar nan sun fara farga a kan 'yancin su, so suke a dole sai sun kifar da Gwamnatin mu, ina tsoron ya tono abun da zai hanamu rawar gaban hantsi".
Hajiya karima ta ce "Shi ɗin banza, daga shi har talakawan meye su a ƙasar nan banda bayinku?, banda shi ma ɗan wani ne a ƙasar nan da tuni an kawar da shi, sai dai taɓa shi directly ba abu ne mai sauƙi ba. Amma kome zai bankaɗo iyaka ayi hayagaga a lokacin ya wuce, su fa talakawan nan ƙuri'ar ce kawai a hannunsu, amma dumukuraɗiya babu ita, ku naɗa wanda ku ke so, ku sauke wanda ba kwa so, ku bar su da ƙuri'in su da shan ranar banza, duk wannan abubuwan bai kamata su tsaye maka ba, har ka kasa mayar da hankali a kan abun da ya dace ba".
Khalifa ya yi dariya ya ce 'Allah dai ya biya ki Munsy, akwai lissafi"
Wakili ya ce "Ai shiyasa nake yin ta nima, ko ma shiga ruɗu ita ke wanke mini zuciya fes".
Ta yi murmushi ta ce "Ai kai ne duk ka damu a kan wasu talakawa, talakawan me? Me jiya ta yi balle yau, ku mulkesu su yi muku bauta, idan kun gusa 'ya'yan su su yi wa 'ya'yanku, a hanasu duk wata dama da zasu motsa balle su cigaba"
Wakili ya miƙe yana murmushi yana duba agogon hannunsa, ya ce "To ni zan shiga in ɗan kwanta, ina da meeting in anjima"
Ta ce "Ok, a huta lafiya" ya jinjina kai ya tafi ɗakinsa.
Tamkar wutar daji haka labarin rasuwar aisha ya karaɗe unguwa, da gidan sarauta, ko ina ya rikice da koke-koke.
Su Iman da nusaiba ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, duk wani makusancin gaskiya ga Ammi, da gidansu aisha ya girgiza da mutuwar nan, kasancewar mace ce ta mutane, ga tsantsar biyayya da haƙuri, sai dai abun da ya jefa shakku a zukatan mutane bai wuce yadda aka ce ba gawarta ba, salatul ga'iba za ayi mata, a can ƙasar da ta tafi karatu ta rasu, kuma an binneta a can.
Turaki da kansa ya samu mama a ɗakinta, ya tarar da ita kamar rasuwar aisha bata daketa ba, yanayinta a yanzu ya saɓa da yadda ta nuna da farko da aka faɗi rasuwar.
"Asma'u gargaɗi na zo na ƙara jaddada miki, aisha dai 'ya ta ce, kuma Allahan da ya bani ita ya karɓeta, babu wanda ya san abun da ya faru sa ke, muddin ki ka kuskura ki ka sanar da wani a yadda aisha ta rasu, sai na saɓa miki fiye da ba kya zato"
Ta dube shi ta ce "Ni, ina ruwana tun da kai mai 'ya ma baka damu ba, ko a bola ta mutu kai ta shafa tun da dai baka ɗauke ta da muhimmanci ba balle kuma ni 'yar karere, amma ka sani wannan maganar bani kaɗai na santa ba, kuma idan sun raina maka hankali, mutane ba wawaye bane ba, suna ji kuma suna gani, dan haka kayi ƙoƙarin toshe duk in da ka san maganar zata fita, dan ka san masarauta yadda take sai haƙuri".
Girgiza kai kawai turaki yayi, ya fita wurin sallar aisha da ta samu halartar ɗaruruwan mutane. Duk wanda ya zo sai ace masa, ta rasu ne wurin haihuwa a ƙasar waje da ta je karatu.
Ko da labari ya karaɗe gidan marigayi Galadima, mummy ta shiga safa da marwa, tare da danasanin yadda aka yi ba ta matsa lamba, ta gano labarin nan ba kan a sanar da shi ba.
Ta san yanzu dole za a je a tattara a gidan turaki, domin jana'izar aisha, dan haka ta tsahirta abun da ta yi niyya, ta shirya ta tafi gidan turaki.
Gida ya cika ya batse, babu masaka tsinke ko ta ko ina al'umma ne ke ɓarkowa, domin ta'aziyyar aisha.
Daga iman har nusaiba tamakar zasu shiɗe dan kuka mussaman nusaiba, dan 'yar ɗakin aisha ce sosai da sosai.
Mummy ta din ga bin Ammi da kallo, tare da ƙoƙarin gano wani abun, amma ba ta gano komai ba sai tsantsar damuwa da tawakalli, ammi ta mayar da hankali tana ta rarrashin iman, saboda yanayin rashin lafiyar ta.
Mummy ta ɗan zakuɗa ta dubu Hajiya Asma'u ta ce "Ni kuwa ban ga Samha ba, tana ina ne?"
"Tana Abuja, ta je wani biki".
"Ta san da rasuwar ne?".
Mama ta ce "A'a an kasa samunta a waya, amma da an sameta za a sanar mata in sha Allah".
Hajiya Sa'adatu ta ce "Mhmm, ni abun ne ma ya ɗaure mini kai, yaushe aisha ta yi ciki ba wanda ya sani, na ga dai ciki baya zama a jikinta, ni ba wannan ba ma an ce ɗan da ta haifa yana nan yaushe shi ɗan ya biyo jirgi ya taho, abun da ɗaure kai fa".
Mama ta ce "Mhmm kuma dai kwa faɗa, ɗa dai yana nan an zo da shi ɗazu, na hange shi a zani, ƙarshenta shi ma anjima ace ba ɗan ta bane ba, dan wannan abu da rainin hankali a cikinsa" Ammi sam ba ta tanka ba, balle ta yi yinƙurin basu amsa, Mummy ce ga ƙiftawa hajiya Sa'adatu ido, tana mata inkiya da idan suka fita za su yi magana.
Duk yadda suka yi ta surutun su, a kan ina jaririn ammi ba ta tanka musu ba, dan kuwa sabir tuni ta kai ajiyarsa, ba tare da wani ya san in da aka kai ɗan ba.
Takawa yana waje suna karɓar gaisuwa, duk yayi wani iri, fuskarsa ta gaza ɓoye zunzurutun tashin hankalin da yake ciki, haka shi ma jamil da aisha ƙanwa ce a gare shi, jabir ma da dakewa kawai yake yi, saboda shi ma aisha ƙanwarsa ce, shi ne mai ƙwarin gwiwar da yake ta ƙoƙarin kwantar musu da hankali.
***
Rumaisa yadda aka ajiye mata abincin karyawa, haka mai sunan baba ya buɗe ya tarar da ita ba ta ci ba, da azahar ya fito da ita ta yi wanka ta yi alwala, 'yan jaje na ta yi mata sannu, amma babu wanda ta iya amsawa, idanunta sun kumbura sosai sun yi ja, tamakar taruwar jini, sai ajiyar zuciya take yi. Mai sunan baba sai kallonta yake yana sake jinjina azababbiyar kafiya irin ta rumaisa. Haka kurum ta ɗorawa ranta masifa, sai an bata ɗan da ba nata ba, ko idan an bata yaya zata yi da shi oho.
Yana zaune yana kallonta ta yi salla, ta idar ta koma gefe ta yi shiruu tana zancen zuci. Ya dubeta ya ce "Ɗauko kayan shayin can ki haɗa ki karya".
Sororo ta yi tana kallonsa kamar wata sokuwa, amma kallon da yayi mata ya sanya ta tashi cikin kasala ta ɗauki kayan shayin.
Yana ganin ɗan abun da ta zuba, ko kwatan kofi bai kai ba, ta zuba suga babu ko madara, ta kafa kai ta shanye, ta yasar da buredin a wurin, ta nemi wuri ta kwanta, wasu hawayen na kwararo mata. Ɗan girgiza kai kawai ya yi, dan yanzu ta daina ba shi haushi tausayi take bashi.
Sai da dare yayi sannan yayi mata umarnin ta koma ɗakin mama, tun da suka dawo ba ta kuma ido huɗu da maman ba sai yanzu, tana shiga ɗakin ta kwanta a jikin mama ta yi shiru, gefe guda ta ji daɗin ganinta a gida, bayan shafe dogon lokaci rabonta da gidan, amma tashin hankali da damuwar da take ciki ta kasa barinta ta ji daɗin.
A hankali take ƙarewa ɗakin kallo, mama kuwa sai lazuminta take yi, sai da ta idar, sannan ta kai hannunta jikin rumaisa, ta ji goshinta ya ɗau zafi, amma jikinta babu zazzaɓi.
"Rumaisa, kanki yana ciwo ko?" Ta jinjinawa mama kai alamar eh.
"Rumaisa ke a rayuwarki ba ki san tawakalli bane? Ina uwar yaron ki ka fara sani, yau ba ta duniyar gaba ɗaya, dan sun karɓi ɗan su kuma sai ki kasa haƙuri?"
Aikuwa kamar mama ta taɓo mata abun da yake damunta ta ce "haba mama, wallahi da na sani za a ƙwace mini shi, sai na zauna a can an kashemu gaba ɗaya kowama ya huta, bar mini shi fa ta yi, mama saboda son da nake yi wa yaron nan da son ya rayu, baki ga uwar azabar da na jire ba, mama kwana na fa biyu zuwa uku da ƙafata ina neman hanya".
Mama ta ce "Ki yi haƙuri ladanki yana wurin Allah, kar ki zobe ladanki".
"To mama na rasa anty aisha, shi ma kuma sai a ƙwace mini shi, mama da kin san abun da ta yi mini, Allah da sai kin din ga saka mata albarka".
"A yanzu ina saka mata albarka, kuma ba zan gushe ba ina yi mata Addu'a da fatan samun rahamar Ubangiji. Amma ke ma saboda tsabar tsagwaron iskanci, baiwar Allah nan ta rasu ki ka ƙi gaya musu, ki ka din ga wahalar da su? Rumaisa ke a rayuwarki duk wanda ya sanki sai kin kafa masa tarihinki na takaici ko, uban waye ya gaya miki ana ɓoye lamari irin wannan?"
Ruma ta yi ajiyar zuciya ta ce "Mama kenan, baki san abun da na gani ba, ba dan anty aisha ta taimake ni ba, da cewa mijinta zan yi Allah ya ƙara, ai gara a din ga sacewa har yan uwansu, sai su daina taimakawa masu satar mutane".
"Na kuma jin wannan maganar a bakinki sai na casaki, ke uban wa ye ya ce miki da shi ake haɗa baki da masu sace mutanen?" Usman ya tsaya a kan ruma yana yi mata faɗa , ya ɗora da cewa "Kuma ki Shiga hankalinki, kin san dole zasu cigaba da bibiyar ki, ana yi miki tambayoyi ki ka cigaba da yi musu gardama, komai suka yi miki ke ki ka saya".
"Yaya usy, kai ka ce in fuskanci abun da yake bani tsoro, to zan fuskanta ni na ga abun da na gani".
Ya ce "To me ki ka gani?"
"Mama kaina zai fashe fa, ciwo yake yi mini" tayi maganar tana sakin kuka, tare basar da wancan zancen.
Mama ta bata maganin ciwon kai, tare da gyara mata kwanciya a jikinta, kamar za a kuma ƙwace mata rumaisa.
***
Sai dare sannan su takawa suka koma gida, wunin ranar babu wanda ya sanya wani abu a cikinsa, hatta ma'aikatan gidan sun kaɗu da jin rasuwar aisha.
Mummy kuwa tun la'asar ta bi hajiya Sa'adatu gidanta, tun a falonta suka yi depot su ka hau zuba.
Mummy ta ce "Hajiy, kin ga mutuniyar ki ko? Wai ni yaushe giwa za ta daina kutungwila a rayuwarta, duk wanda ta raɓa sai masifa ta afka masa"
Hajiya Sa'adatu ta ce "Yo ba karfa ba ce ba, ke ki ga wani uban rainin hankali da goge hadda, Allah kaɗai ya san abun da suka yi wa yarunyar nan ta mutu, babu alamar gaskiya a tare da su, daga ita har ɗan nata".
Mummy ta ce "Kin san ya kai kwanaki tara da 'yar sa idona, ta gaya mini wani abu na faruwa, ban wani mayar da hankali ba, na fi mayar da hankali a kan samo maganin da suke masa amfani da shi, da malam ya ce na kai masa, da na san wannan abun ne da na bi diddigi, tun kan kowa ya sani na tsara abun yadda zan kunyata giwa"
"Yanzun ma baki makara ba, zan iya cewa wata dama ce ma ta zo miki"
"Ta zo mini ko ta zo mana? Ai ni zan gaya miki dama ta samu, ki zuba ido hajiyata, zaki ga yadda zan yi bankaɗa na tagayyarata da ɗan na ta da take taƙama da shi mahaukacin banza, ai wannan zance kawai zai fita ya gama cinye 'ya'yansa ya cinye matarsa yayi tsafi da gangar jikinta" suka ƙyaƙyace da dariya, Hajiya Sa'adatu ta ce "Ya wancan batu da ki saka aka yi? Na yinƙurin fyaɗe wa agolar can?".
Mummy ta yi murmushi ta ce "Ai na assasa wannan ne dan rama cin mutuncin da aka yi mini, aka ƙi goya mini baya a kan tafiyar aishan karatu, na fake da bata nan yana bin agola, amma yanzu ai sawun Giwa ya take na raƙumi, ki jira ki gani kan a share makoki idan bai yi wasa ba sai na kunno musu wutar da sai hukuma ta tuhume shi".
"Kai Jamila, kina wuta ina bin ki da fetur "
Ayshercool
[12/12, 7:33 PM] rahama Jos: paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*
Haka suka cigaba da ƙulla mugunta kala-kala suna dariya.
Wunin yau Samha ba ta bi ta kan wayoyinta ba, sai yanzu ta nutsu, ta ɗau wayoyinta ta kunna, ta ajiye su a kan gado, ta shiga wanka. Daga shigarta wanka zuwa fitowar ta missed calls sun fi goma sha.
Mamaki ne ya kamata, tana shirin duba missed calls ɗin, kiran Fauziyya ya shigo wayarta. Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce "Wai lafiya ake yi mini wannan kiran kamar mara gaskiya?".
Fauziyya ta ce "Ke dalla can, idan ma wani rabon ne har ya wuce ki baki ɗaga waya ba, kawai kin