Showing 15001 words to 18000 words out of 27923 words

Chapter 6 - MAFARKINA COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

94

ma sa dubu goma sha biyu dai-dai ya karɓa ta re da murna
Nvm''gobe ko zu ko karɓa ɗinkin.''

Su ka koma gida Yau kam ta re da Fadila su ka yi aikin gida komai tare
Bayan sun kammala lokacin an yi sallar magriba yah Abba ya dawo daga gurin aiki
Ta kai ma sa wayar acikin ƙwalinta ya ɓude ya kunna ya yi ma ta san barka
ta kuma cikin ɗaki ta yi ta juya wayar wai yau itace da Wannan wayar ta ji ɗadi acikin zuciyar ta yi wa Allah godiya
Fadila ta yi bacci abin ta
Sai kallan wayar ta ke yi
Saheeb ya na ta danna laptop ɗin sa

Shaheeda ta fado ma sa a rai sai ya duba time ya ga karfe 8:00 na dare da wani abu da ya ce ya bari da safe zuciyar sa ta kasa hakuri da hakan

Kawai ya ɗanna numbern da Amir ya tura ma sa ya yi save ɗin numban da my...

Ya yi dialing.....

Shaheeda ta ga kira ya shigo wayar sai da ta ji gaban ta ya faɗi ta san shi kadai ne wanda zai kira sai da ya kusa yanke wa ta ɗauka......

Babu wanda ya ce komai acikin su
Sai can Saheeb ya ɗaure dai
Cikin wata zazzakar muryar ya ce.
*************************
''Assalamu alaiki
Amincin Allah ya tabba ta agareki
Ki yi hakuri cikin dare na kira ki na ka sa ɗaurewa ne sai na ji muryar sarauniyar ta.''
''Wa alaikumussalam .''
Ina wuni
Saheeb ya ji sauti mai daɗin saurara anan ta ke ta yiwa Allah godiya na ba shi daman mallakar mai wandan daɗin muryar
"Ya kike?
Ya kuma Baba da kanne na?

Na ka sa hakuri ne yau na ce ina so inji murya ki ina fatan dai banyiwa gimbiya laifi ba kar ta sa ayi mun bulala
Shaheeda ta ji wani farin ciki aran ta wanda ba ta san dalilin da ya sa ta farin ciki ba?
''Su nan lafiyar su ƙalau ya aiki?

''Lafiya ƙalau gimbiya.''
Akwai wani abun da ki ke buƙata ne sai na sa Amir ya kawo Miki
''A'a na gode.''

'' Gimbiya kin tabbata ko?
''Eh babu da ma na ce ina ne man izinin zanje bikin ƙawa ta ranar jumma'a kuma ɗazu ina so in fita na sayo anko na fa ɗa wa Baffa.''
''kar ki damu duk inda fi ta ta ka ma ki ki je kawai na ba ki izini amma kar ki ba ri kowa ya ɗunga kallan mun kyakkyawar fuskar ki kinji gimbiya.''
''Na gode.''
''Kar na cika ki da surutu ki kwanta ki yi bacci kinji gimbiya sai da safe.''
'Sai da safe.''
Ya yi ending call ɗin
Saheeb da ko magana ba ta ha da shi da mata yau sai gashi harda hira a waya da ga gani Wannan soyayyar za ta ba da armashi
Saheeb ya ta kallan wayar sa kamar ya na ganin Shaheeda sa ɗauke da murmushe ma ra misaltawa

Shaheeda kuwa ta yi shiru kawai sai jin sautin Saheeb ta ke ji a kunnan yanda ya ke ce wa gimbiya ta yi murmushi

*Asuba ta gari*
Yau da safe Shaheeda bayan tafiyar su Fadila school ta yi aikin ta da wuri ta tafi gidan Khadija ta na zuwa
Hanna ta ce.
''sunyi fushi sai yau.''
Ta ba su hakuri aka cigaba da hidimar biki
zuwa gurin abokan ango Hanna da Shaheeda ne dan su ne manyan ƙawaye Shaheeda ta ce gaskiya a saka wani amadadin ta
Cewar Hanna.
''Shaheeda sai na ga yanzu ki na wani ja baya ko akwai wani abu ne ok dan ba Aisha ko.''
Khadijah ta ce.
''Haba Hanna wai ke yaushe za ki canza ne dukan mu ba duk ɗaya ne kuje da Hamida kawai.''
Shaheeda wa sa na ke yi mi ki kawai ba fi mu je da Hamida.''
Su ka nu fi waje
Shaheeda ta ɗauko wayar ta ta miƙawa Khadijah

''Ma sha Allah Wayarki ne Shaheeda kamar iphone Allah ya sanya alkhairi gaskiya ya yi kyau a kashe lafiya.''

Hanna da Hamida su ka yi ta yi da ƙyar aka ba su ɗubu ashirin duk masifar Hanna
Su ka shigo gida su na ta masifa
Za su tafi kasuwa Shaheeda ko za ki ne sai Khadijah ta ce.
''Ki barta anan kuje ku dawo
Su ka tafi.''
Khadijah su ka sha hirar su da Shaheeda har su ka dawo daga kasuwa
Fadila su ka dawo daga school su ka ci abinci Ummulqursum ta zo su ka sha hira
Su ka zauna su ka yi ta hira na ƙawaye
Aisha ba za ta sa mu zuwa ba dan suna tsaka da lecture ta
Ta turawa Khadijah gudun mawar ta Khadijah ta yi murna sosai
An gyara

Yamma ta yi Shaheeda ta yi mu su sallama
''gobe da asuba za ku ganni.''

Hanna ta ce mu je na raka ki sai na shiga gida nima

Da su ka fita Shaheeda ta nuna wa Hanna wayar ta
Hanna ta yi murna sosai
''ƙawa ta iphoneXR ne ki ce gobe zamu sha selfie
Suka yi dariya
Ta isa gida ta sa mu Fadila har ta kusa ga ma girki ta shiga an kira sallar magriba ta yi alwala ta shiga ciki
Bayan sallar isha Fadila ta ce
Aunty Shaheeda ba mu karɓo ɗinkin na mu ba
La na manta ki bari gobe da safe sai muje muƙarbo
*Jumma'a yau ɗaurin aure*
Da safe Shaheeda da Fadila su ka yi aikin gida su ka gama su ka wa auta wanka su ka shirya sa su ka nufi gidan su Khadijah yau ba Fadila ba su je school ba
Su ka wa Baffa sallama
Su ka je gurin Bashir tela su ka ƙarbi ɗinkin su ya yi ƙyau sosai
Suka shiga mutane sun cika
ƙawaye gefen su daman ta miƙawa Khadijah gudunmawa
Khadijah ta yi farin ''ciki sosai sosai"
Ansha biki lafiya amarya ta yi kyau ta sha gyara ba bu laifi
Shaheeda ɗinkin su kusan ya fi na kowa ƙyau mutane sai magana ɗinkin ta su ke yi ya yi kyau
An ɗaura aure Allah ya bada zaman lafiya
End
*Beautyn Jajirtattu ce ✍️*
*MAFARKINA*
By
*Nana Ummu Salmaah*
*Alkalami*✍️
*Beautyn Jajirtattu ce ✍️*

*Alhamdulillah gaskiya yau ina cikin farin ciki sosai Allah ya ɗauwamar da farin ciki acikin rayuwar mu na har abada nice dai ta ku Ma'ul hayate🥰*
https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

Page19&20
*******************
Bayan kwana biyu ranar lahadi kenan Shaheeda ta sa ka numbern Aisha a wayar ta ta yi dialing sau biyu ya na ringing ba ta ɗauka ba
Aisha ta na ganin kiran saboda ba ta fiye ɗaukar new number ba
Sai kira na uku ya shigo ta ɗauka

''Assalamu alaiki Aishatu na.''
''Wa'alaikumussalam wa na ke ji kamar Shaheeda.''
''Ni ce dai A'isha.''
''Kuma na ga ba numbern yaya Abba ba ne ai''
"Waya ta ce.
"Dan Allah Shaheeda!
"Kodai Sirikin na mu ne ya siya ma na?
''Ya kike Aisha?
''Ya mummy da Abba ya kwana biyu ya karatu?
''lafiya ƙalau ƙawa ta duk suna nan lafiyan su ƙalau karatu babu daɗi gabaɗaya ba bu hutu an yi bikin Khadijah lafiya?makaranta ya ha na ni zuwa.''
''Mun sha biki ai mun yi kewar.''
Allah ya ba su zaman lafiya
Ameen

''Na ji ki kina farin ciki Shaheeda wai nikam ya mijin naki yake har yanzu bai dawo ba?
''Ya na nan lafiya ƙalau bai dawo ba
''Tom sai yaushe?
''Nima ban sa ni ba.''
Su ka sha hira
''Aisha ta ce kinga ina da test gobe zan kira ki.''
Su ka yi ending.
________________________
Ammie kuwa ita ta ke tafiya da gidajen marayu na Nigeria da ziyartar Hospital dan taimakawa marasa lafiya
Ta na zaune agurin aka kira sallar isha ta ta shi ta yi Sallah ta idar ta yi addu'a sosai ta shafa
Ta nufi gado za ta ƙwanta
Fadila da wuri ta yi bacci dan ta na fashin sallah

Sai tunanin Saheeb ya faɗo ma ta a rai kwana biyu shiru bai ƙira ta ba har za ta yi dialing number sa dan ko save ɗin numban ba ta yi ba ta juya za ta ƙwanta kenan sai ta ji ringing ɗin wayar har cikin ranta ta ji sanyi.....


Da sauri ta ɗauka wayar
''Assalamu alaikum.
''Wa'alaikumussalam gimbiya kan fatan ban yi laifi ba.''
''Ina wuni?
''Lafiya ƙalau gimbiya.''
''Ya aiki?

''Mun gode Allah princess an yi biki lafiya.''

Lafiya ''ƙalau ƙalau''

''Na bar ki,ki huta ne dan na san kun yi biki kuma kin gaji ba na so ina takurawa princess.''

Shaheeda ba ta ce komai ba


'' ya su Baba da yaya Abba agaisu.''

''Za su ji in sha Allah.''

''Har yanzu ba ga ba ki wa ni da sa ke da niba ko?

''Idan kuna buƙatan abu ki faɗa mun ko menene shi zan yi mi ki kar ki damu kin ji ke nauyi akai na ko?


''Ba ba buƙatan.''

"Kin tabbata ta?

''Ehh na tabbata.''
''Shikenan ki ƙwanta ki huta sai da safe.''
''Allah ya ta she mu lafiya.''
Su ka yi ending..
Madinah ta na London sai karatu ake yi babu wasa.

Anan rayuwa ta ya na tafiya Hanna ta yi android ta zu ta nu na wa Shaheeda
Shaheeda ta taya ƙawar ta murna sosai
Hanna har ya bude what'sapp
''Shaheeda nikam baƙya what'sapp ne.''
''Kinga wayar nan sunan ta wa ce amma bansan komai ba sai dai su Fadila da Auta su yi ta kallo da shi ba bu mu numban kowa da ga Aisha sai Khadijah.''
''Gaskiya ki kawo na ɓude miki class mate ɗinmu duk muna shan hira a group Khadijah ta yi sabuwar waya harda ita duk na sauransu....
Ta ɗauki wayar ta ce
''bari na ɓude miki Sahheeda kudai za mu yi canje ne ina kaunar iphone a rayuwa ta amma ke jin samu ko a jikin ki.
Ta ɓude ma ta what'sapp a wayar
Shaheeda ta yi mu su girki su ka ci yau kam Hanna a gidan su Shaheeda ta wuni
Sai can yamma
Ta tafi Shaheeda ta raka ta

Amir suna ta shan soyayya da kausar coucin ɗin Saheeb yarinyar Alhaji Kabir
Saheeb ya tura ma ta numbern Sahheeda suna gaisawa suna chart sosai abun su dan sun shaƙu da ita
Abbah ba a cewa komai sai ma sha Allah dan yanzu komai na gidan shi ya ke yi mi su

Shaheeda kuwa ta kara waye wa dan kausar na sa ta akan hanya sosai ta sata a group na "girke girke" na (Maryama kitchen)
Ta na karuwa sosai a group ɗin

Hanna da Shaheeda su ka je gidan Khadija
Khadija ta yi kyau aure ya ƙarbe ta

''Shaheeda wai nikam ya rubuta novel ɗinki ne?
''Ke da kinsan komai ina ta rubutu na.''

''Ai kuwa na samu miki wa ta MARUBUCIYA Sakina Abdullahi Pretty Sk.a Facebook na gan ta na daura page ɗinta sai na ɗauki numban ta a group na ce zan baki kowa ko za ta taimaka miki.''
''Ga numbern ta.''
Da sauri Sahheeda ta ƙarba ta saka a wayarta
Hanna kuwa sai dariya ta ke mu su dan ita tunda idan ta na maganar rubuta novel dariya ta ke ba ta

Su ka tafi
Ta na kumawa gida ta yi chart ɗin ta a Whatsapp ta yi ma ta reply
Pretty sk ta yi adding ɗin Shaheeda a group ɗinta na what'sapp ta na karanta novel aciki
Suka yi chart da Pretty Sk ta faɗa ma ta ta na san itama ta fara rubuta novel ta yi ma ta hanya agurin manyan su maman Ihsan kenan
Aka ma ta interview aka sa ka ta a kungiyar su na marubuta *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*

Shaheeda ta fara rubuta littafin ya me suna *MAFARKINA*
Idan ta rubuta ayi ma ta gyara a editing room a fitar ma ta da gyara ayi man ta editing
Aka buɗe ma ta group ɗinta na *MAFARKINA FANS GROUP*
End
*Beautyn Jajirtattu ce*
*Nana Salmaah*
*MAFARKINA*
By
*NANA SALMAAH*
*Beautyn Jajirtattu ce ✍️*

https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

Page 21&22
Chapter 46&47&48
Shaheeda yanzu gabadaya ta mai da hankainita akan rubutu amma hakan bai hana ta duk wani ibadun da ta ke yi ba

Shaƙuwa mai karfi sai ƙara kulluwa ta ke yi a tsakanin su biyun *Saheeb da Shaheeda* yanzu kullum sai sunyi waya Shaheeda ta na jin wani abu aranta amma ta kasa yarda da cewa soyayya hakan ke nufi
*BAYAN WATA UKU*
Saheeb ya na shirye shiryen dawowa daga Dubai farin ciki sosai yake yi
Kwana a ta shi babu wuya Saheeb har ya kusa cika wata Shida a Dubai
Ammie ta sa a gyarawa Saheeb bangaran sa ta yi order na sababbin furniture daga Dubai ba tare da sanin Saheeb ba

Cikin ikon Allah Khadijah ta na da ciki na wata huɗu
"Mummy yaushe za mu je Abuja ne na yi missing ɗin su Aisha?

"Sai ki bari idan Abban ki ya dawo sai ki ma sa wannan tambayar?
Saheeb ya kira Shaheeda a waya.
''ya ke sanar ma ta da sauran kwanki kaɗan zai dawo ta faɗi kalar tsarabar da take so ya kawo ma ta.
Ita kuwa Shaheeda ta ce
Duk abin da ya ka wo ma ta ta na mara ba dashi
Sun daɗe su na hira da shi ka fin suka yi end
Nan ta ke wani abu ya faɗowa Shaheeda a rai yanzu idan Saheeb ya dawo shikenan za ta bar gidan kenan za ta yi nisa da su Auta kenan!
Kausar ta yi ma ta magana akan gyaran jiki tunda Saheeb ya kusa dawo wa kuma ya na dawo wa za ayi maganar tarewa
Shaheeda ba ta ce komai ba ita dan yanzu hankalinta ya na gurin rubuta novel ɗin ta

Saheeb ranar jumma'a zai bi flight ✈️ ya dawo Nigeria
Ammie sai shirye-shiryen dawowar sa ta ke yi

Yah Abba ya siya sabuwar mashin ɗin hawa me kyau ya kara kyau sosai kamar ba shi ba har wani haske ya kara

Kausar ta na zuwa ɗaukar Sahheeda har gida tare da izinin Baffa su na zuwa gurin gyaran jiki na Meerah -B Palace wusell ana ma ta gyaran jiki,Ammie ce ta sa Kausar ta yi hakan
Yau kam kusan kwana Shaheeda su ka yi su na waya da Saheeb ya na ta ɗaukin ya dawo ya ga wannan gimbiyar ta sa jirgin safe zai bi ya dawo Nigeria
**************************
Saheeb isa wanda ma'aika su ka kai sa airport sai gida Nigeria

Gidan Ammie kuwa yau yanda ka san baki da yawa ne za su zo ana shirya abinci kala kala Kausar a gidan ta kwana dan ɗauki tare suka yi ta aiki da Safna mai aikin su

Shaheeda ta bangareta
Tayi Snacks kala kala ta yi packaging ɗin su
_________________________
Ma sha Allah landed safe
Saheeb ya sauka lafiya
Amir ya je airport ta re da excort an je ɗauko mai gida

Ya na saukowa a jirgi cikin kana nun kaya wanda ya yi matukar amsar jikinsa sosai
Su ka yi hugging juna
''You are highly welcome.''
'ThankYou Aboki na.''
''Tom yanzu dai ka ga motoci ga na Company wanne za ka shiga oga sai wanda ka zaɓa?

''Ina ai mu je a motar ka ɗan daga nan sai gurin gimbiya.''

''Allah ko Abokina.''
Su ka shiga mota suka ɗau hanya
''Ni fa yanzu gida za mu tafi direct da ga dawowar ka ko hutawa ba ka yi ba ka ba ri idan ka huta zuwa da yamma sai na kaika ko.''
''Shikenan babu yanda na iya da kai Amir.''
Su na isa gida Ammie su Kausar,Safna da sauran su suna tsaye a hara bar gida.
Ya fito da sauri ya yi hugging ɗin Ammie ta kama hannunsa su ka shiga palo su na shiga sai kamshi ne kawai ke tashi a cikin palo
''Brother Saheeb you are welcome.''
''Thanks you my little sister Kausar kece haka ki ka ƙara girma.''
''Brother ka fara ko.''
Amir daga bayan Saheeb ya yi ma ta gwalo
''Tom yanzu ka shiga ka watsa ruwa sai ka zu mu ci abinci dan yau a gidan nan kuwa kai ya ke jira ayi lunch tare.''
Drivern gidan ya shigo da trolley da wasu kayan Saheeb cikin palo
Amir ya zauna a palo suka ci gaba da hira da su Ammie
Bayan wani lokaci sai ga Saheeb ya fito palo cikin wani jallabiya baƙi wanda ta yi ma sa ƙyau abin ka da farin mutum cikin baƙin abu ba ƙaramin kyau ya yi ba
Gabaɗaya su ka nufi dinning da su Kausar su ka yi lunching sun sha hira na yaushe gamo
Madina ta kira su video call
Fadila sai ɗauki ta ke yi za ta ga mijin aunty Shaheeda
Shaheeda sai bin Fadila ta ke yi da ido.....
Bayan sun kammala su ka nufi ɗakin hutu Saheeb da Amir

''Saheeb ga ka wani haske da ka ƙara kuwa harda wani jiki tun kafin a kawo ma ka amarya.''
Suka ƙwashe da dariya...
Aka kira sallar la'asar su ka je Masallaci ta gidan su ta can wani bangare acikin gidan saboda ya na da girma sosai
''Bayan sun dawo ne ya ke cewa.
''Amir ka tashi mu shirya na je na ga gimbiya.''
''Ka bari idan akayi sallar magriba sai muje ka ji kaga ai sai ya fi ko.''
''Alright Allah ya kaimu kawai na matsu na ga gimbiyya.''
''tom kwana nawa ne ya rage a kawo maka Amaryarka.''
''Bari na je palo cutie na jira.''
Ya tafi ya bar Saheeb shi kaɗai
Amir ya samu Kausar a palo ta sha riga da skirt na atampa ta yi kyau
Kausar na da kyau babu laifi amma ta na da jiki full package ce akwai hips sosai ga boobs
Shaheeda ta gama girkin dare tayi wanka ta ɗaura alwala dan an kusa kiran sallar magriba

Suna fito wa daga masallaci Saheeb ya shiga bathroom ya yi wanka ya fito ya sha shadda waterproof maron colour ya ɗaura wristwatch a hannunsa ya sha turare sai kace rana ake ɗaura aure ya yi kyau sosai ya fito sak Balarabe
Ya samu Amir a palo shi da Kausar sai shan love akeyi
Wato nan ka zo ka laɓe ko suka yi dariya
''Brother Saheeb.''
''Babu wani Brother ko kunya ta bakya ji ko.''
''Ta ta shi da gudu wai ita ta ji kunya.''
''Can we go.''
''Yeah we are free to go.''
Su ka ɗauki wata motor Saheeb mai matukar tsada Amir ya yi driving su ka ɗau hanya.......
Kausar ta kira Shaheeda a waya ta sanar ma ta da zuwan su Saheeb
Nan take Shaheeda ta ɗauko wani Arabian guy wanda Madina ta kawo ma ta peach colour da hijabi orange colour da takalmi da wasu turare mai matukar kamshi wanda su ke siya idan sun fita gyaran jiki da Kausar
Yau dai Shaheeda za ta ga wanda ta aura wanda bata san ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login