Showing 3001 words to 6000 words out of 27923 words

Chapter 2 - MAFARKINA COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

101

ta tashi ta tafi ɗakinsu ta chanja kaya ta yi salla sai tafito ta ce "Fadila ki je ki ɗauko Al-ameen a school."

Ta ce "Toom Aunty." ta ruga da gudu.


Ta koma ɗakin Umma Sai yah Abba ya miƙa mata maganin ya ce "Ga shi nan an da safe biyu da yamma biyu."

Ta amsa ta ajiye a gefen Umma Sai ta ce "Umma tashi ki ci abinci sai ki sha magani."
Umma ta ce "Na ci sauran wanda kuka bari."
Ta ce "Tom ga magani." Ta ɗan ɗago ta sai ta bata magani da ruwa sai Umma ta ce "Shaheeda ko girki ban iya yi ba, ki je ki ɗaura muko." ta ce"To Umma." ta fita ta shiga kitchen ta kunna abacha


Sai ga Sallamar Fadila ta ɗauko Al-ameen ya zo da gudu ya rungume ta ya ce "Aunty na." ta ce "Na,amm ƙanina ya karatu ?." Yq ce"lafiya." sai Fadila ɗauke shi ta canja mai kaya.

Sai ya shiga ɗakin Umma ya ce "Umma na Umma na" murya can ƙasa ta ce "Na,amm Auta ka dawo." ya ce" ehh Umma, ya jiki?." ta ce"Da sauƙi."

Sai Shaheeda ta ce "Fadila ki je jakata ta islamiyya za ki ga ɗari biyu ki siyo wa Auta biscuits da bobo kafin ya fara kukan yunwa."

Ta ce" toom."ta shiga ɗakinsu ta ɗauko sai Shaheeda ta ce "Dan Allah ki yi sauri kar ki tsaya wasa a hanya." Ta ce "Toom Aunty." Sai ta fita,ita kuma ta ɗaura paiboiling din shinkafa.



Sai ga sallamar Aisha, Shaheeda ta amsa mata ta shigo ta ce " Na zo na duba ki ne, dan wallahi yanda ɗazu muka rabu ban ji daɗin ganin ki a hakan ba."

Sai Aisha ta ce "Ina Umma?." Sai Shaheeda ta ce "Ta na ɗaki bata jin daɗi."

Sai ta ce
"shine ba ki faɗamin ba ko."
ta tashi ta shiga ɗakin Umma ta yi sallama ta shiga ta gaishe da Ummah ta amsa mata can ƙasa, ta ce "Lafiya Aisha ya maman naki."

Sai ta ce "Ta na lafiya." ta ƙara cewa"Umma ya jiki?.
Sai ta ce "Da sauƙi."
" Allah ya kara sauƙi." suka amsa duk ka da"Amin."

Ta fita ta samu Shaheeda ta na aiki sai ta ce "kawo in taya ki."
"sai ta ce a'a daga zuwan ki."
Sai Aisha ta ce "Shaheeda ba na ce miki mun ruga mun zama ɗaya ba."

Sai ta ce "toom Kar mummy ta nemeki." sai ta ce"Ai ta san ina nan ba za ta neme ni ba."
sai Fadila ta shigo ta ce "Ina wuni Aunty Aisha ta amsa da lafiya ta kaiwa Auta biscuits din a ɗaki har ya fara gyangyadi ya tashi ya ci.

Ƙarfe huɗu na yi Fadila ta yi Sallah ta ɗauki Auta suka wuce makarantar Islamiyya


Ta bangaren wanda ya kusa ya bige Shaheeda kuwa har ya isa gida wani katafaren gate ne na alfarma ya yi horn, Baba mai gadi ya zo ya buɗe mai kofa ya fito a mota ya gaishe shi "Ina wuni Baba."
ya amsa da " lafiya ƙalau Oga."
sai ya nufi ƙofar palon kakan gidan za ka yi kaso ka ga ya za ka ga cikin gidan ya buɗe kofan falon ya shiga, wata mata ce fara na hango riƙe da wata takarda a hannunta.

" Assalamu alaikum."
Ammie ta amsa da "Wa,alaikumussalam."
"Ammie ana hutawa ne haka?."
"Saheeb ka dawo."
"Na dawo Ammie y gida."
Ta amsa da "lafiya ƙalau." nufi part dinshi sai Ammie ta ce "idan ka huta ka fito mu yi lunch tun ɗazo kai nake jira har yamma ta yi."
"Ok Ammie sai na fito....."
Ammie cigaba da kalan takardan dake hannunta

******

Suka kammala abincin ta kaiwa Ummah ta tashe ta da kyar da kyar taba ta ta ci cukali biyu sai ta kai musu nasu ɗaki ita da A'isha.
Shinkafa ce jolof amma fa ta yi daɗi A'isha ta ce "ita kam a kashe take." Shaheeda ta ce "Abincin gidan mu ne ba za ki ci bako."
ta ce "Ni fa Shaheeda bana so kina kalan wannan maganar."
" toom bari in ci."
Shaheeda da yunwa ta gama cin karfin ta ci kawai ta ke yi A'isha ta yi loma ɗaya ta ce "kaikaikai Shaheeda a gaskiya kin iya girki sai kace a restaurant."
Suka kwashe da dariya


Sai ga Sallamar Baffa da Abba suka amsa musu suka fito tare suka ce sannu da dawowa ina wuni Baffa ya amsa suka ce ina wuni yah Abbah yace musu "sannunko."
Baffa kai tsaye suka nufi ɗakin Umma suka shiga Abba ya ce "Umma." Shiru
"Umma." shiru nan take hankalinsu ya tashe Shaheeda tare da A'isha da gudu suna shiga suka ga Umma koh motsi bata yi Shaheeda ta fashe da kuka ta na jijjigata Baffa ya ce "Abba maza ka je gidan malam Yusuf ka ce mai dan Allah ya taimaka da motar shi akai Ummah ko asibiti." da gudu Abba ya fita ya je ya gaya mai, da sauri malam Yusuf yadauko key suka nufi gidan sai ga Fadila da Auta sun dawo daga Islamiyya A'isha ta kama hannunsu ta nufi ɗakin su Shaheeda ta ɗauko ta ce wa Fadila "ta ɗauko musu abinci a kitchen."
ta ɗauko musu suka ci su koma Umma sun fita da ita sun nufi mota sai A'isha ta fito ta ce Shaheeda ku yi hakuri za ta Samu lafiya ni zan koma gida yanzo magriba ta kusa cikin kuka Shaheeda ta ce "Nagode A'isha." suka Shiga mota sai matar malam Yusuf Umma Shafa ya ce da ta turu Maryam su zo su zauna dasu Fadila kafin su dawo ta amsa da toom ta nufi gida sukuma suka nufi asibitin Gwari suna zuwa aka karɓesu aka basu gado likitoci suka shiga dubata


A'isha ta kuma gida jiki duk asanyaye Mummy ta ce "yayi Miki kyau daga bari in je in dubo Shaheeda."
A'isha bata ce komai ba yashiga ɗaki Mummy ta bita da kallo ta ce "komai ya faru koma bari dai in bita ɗaki."
Mummy na shiga ta ga A'isha a zaune a kofar gado ta ce "meya faru na ga duk jikinki a sanyaye."

Sanna ta ce "Mummy maman Shaheeda bata da lafiya har ankaita asibiti."
"Subhana meya sameta?."
"Mummy nima ban sani ba dazu dai da zamu dawo daga School Shaheeda mota har kusa bige ta ya yi Sanda nake gidansu tukun na ga ashe Ummah su ne bata da lafiya, Mummy Wlh Shaheeda Tabani Tausayi."
"bari Abbanki ya dawo gobe ma je Asibitin mu dubu su."
taji dadin hakan Tata tashi ta shiga bedroom tadauro alwala ta fi to




Saheeb kuma sun kammala Ammie ta ce "ya na ganka haka wani abu ya faru ne?." Saheeb yadan yi shiru tukun ya ce "Ammie na kusa buge wata yarinya ne yar makaranta a hanya ta,ta dawo wa gida."
"Innalillahi,babu abinda ya same ta ko?."
"ehh Ammie."
"to Allah ya ƙara kiyayewa." Saheeb ya ce "Amin."



Su Shaheeda kuwa har yanzu likita basu ce musu komai ba duk dunkasa Sukuni, Fadila kuwa suna gida tana ta faman aikin rarrashin Auta sai kuka ya ke yi sai an kai shi gurin Umman shi Maryam yaran malam Yusuf suka zo da kannenta suka taya su Zama. Har wajen tara na dare tukun Likita yafito ya ce su sameshi a office suka nufi office duk kansu Baffa yace Shaheeda ki jira mu anan ba ba yi musu ba ta koma ta zauna tana wa Ummantah addu'a Allah ya bata lafiya



Bangaren Saheeb kuwa duk ya rasa sukoni kawai tuna kyakkyawar Fuskar Shaheeda ya ke yi
End
Nasan masu karatu suna so suji meke damun Umman Shaheeda
Nasan kuna ta sake sake a kan Waye Saheeb??? Kuciga ba da bibiyata zakuji koma waye
NAGODE
https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


Mafarkina (My Dream)
By
Preetie Selmerh
Wannan page din na sadaukar dashi ga mahaifiya ta wacce ta fara bani ƙwarin gwiwa akan fara rubuta littafi Ina godiya Umma tah Allah ya kara Miki lafiya da nisan kwana AMEEN!****


Page4

Chapter 8and9


Bayan sun shiga office ɗin Doctor, nan ya ce waye mijinta a cikin su sai Baffah ya ce

"Ni ne.'' har bakinshi na rawa. Sai Doctor ya ce

" Alright ya aka yi kuka bari har ciwo yaci karfinta haka, tunga da ga yaushe ta fara ciwon?." sai Baffah ya ce

" Tsakanin jiya da yau ne."

"To a yanzo matakin da take da ƙyar mu shawo kanta amma ya kamata ku canza mata asibiti, saboda tana bukatar kula sosai da sosai. Cutar dake samun ta ciwon kuda ne."

"SUBHANALLAH" suka furta haka cikin jimami. Sannan suka fitar

"Yanzu dai kumar mutum ɗaya ya kwana da ita zuwa gobe sai mu fa abin da hali zai yi..."

Duk kansu suka fita jiki a sanyaye yasa Shaheeda ta tashi da sauri ta miƙe



_______ Sai malam Yusuf ya ce. "Shaheeda ki kwantar da hankalinki Ummanki za ta samu lafiya insha Allahu." ta amsa mai da " in sha Allah, Amin."

"Baba yanzu kunga dare ya yi ke Shaheed ta kwana anan gobe da wuri zamu dawo ins ha Allah."

Ta ce musu "To sai da safe." suka nufi gida.




Shaheeda ta shiga ɗakin ta tarar da Umma a ƙwance sai ajiyan zuciyar take saukewa sai ta ce.

"Umma na Allah ya baki lafiya......" sai ga hawaye sun wanke mata fuska.



Suna isa gida, Baffah ya yi wa malam Yusuf godiya sosai.


***Washe gari***

A'isha da ta tashi da wuri ita da mummy suka fadawa Abbah akan za suje gaida Umman Shaheeda. Abba ya ce su gaishe su suka hada musu break fast suka tafi da shi



________ Fadila kuwa jiya da ƙar suka yi barci sa bo da rikicin Auta ta ya musu dumamar ta lsllaɓa Al-ameen ya ci da kar.

Baffah ya ce mata takaishe school ita ma sai ta tafi babu ku musu har Baffah sanda ya ji tausayi Fadila yanda yaga ta yi so silent yau dyin ta dauke shi suka tafi


Baffah kuwa da Abbah suka nufi asibitin suna isa suka tarar da A'isha daga mahaifiyara zasu shiga suka gaisa
"Mummy."
Ta ce ya masu jiki suka Amsa tare Baffah da A'isha a tare suka shiga ciki suka nufi dake mai NO:7

Suka shiga suka ga Shaheeda a kan sallaya ganinsu yasa ta mike ta je ta gaishe A'isha ta rungume ta suka ce ya mai jiki ta amsa murya can kasa da sauƙi.

Mummy ta ce

"Shaheeda ki kwantar da hankalinki kinji." idanuwan Shaheeda duk sun kumbura dan jiya da ƙyar barci ya ɗauke ta.

A'ishah ta miƙa ma Shaheeda ledar da suka shigo da ita Shaheeda ta karɓa tare da godiya🙏

Mummy ta ce

"A'isha mu tafi kar ku yi late." badan taso ba ta sake Shaheeda suka tafi Mummy ta ajiye ta a School ta koma gida

***BANGAREN SAHEEB***

"Good morning." Mamiee Fuskar sa cike da annuri ta amsa da.

"Morning my Handsome. how was your night?."

"So wonderfull😊."

Ammie ta ce 👍

"Good haka nake son ji. tom muje mu yi breakfast."

"Ammie zan yi late fah, muna da meeting a office 10am." sai Ammie ta ce

"Son da sauran lokaci." ya ce

"To." suka nufa dining. soyayyen dankali da sause da kuma kayan tea a gefe suna ci suba hira Ammie ta ce

"Yawwa kar na manta..... wato ka shashantar da maganar mu ko?." ya ce

"Ammie wata magana kenan!." ta ce

"Wato ka manta ko, akan ka nemu mata na yi maka aure na gaji da ganinka haka." ya tashe tsaye ya ce

" Ammie kar nayi late idan na dawo zamu ci gaba da magana." Ammie ta yi murmushi ta ce

"Ko da yaushe da haka kake sha shantar da magana***




______Saheeb ya ɗauki motar shi land cruiser da ita zai fita sai fuskar yarinyar nan yake tunawa sai ya yi wani dogon nunfashi.

"Ko yanzu a ina zan ganta ohk?."



_________________
A'ishah Mummy ta ajiye ta tana zuwa samu har teacher ya shiga ta ɗauki escus ta shiga class kuwa hankalinshi ya koma gunta dan kullum an saba ganinta tare da Shaheeda "Allah Allah " Khadijah da Hanna suke malamin ya fita suje su tambaye A'isha




Har yanzo dai Umma ba ta farka ba sai likita ya ce za'a musu transfer zuwa Maitama hospital in yaso suje Reception su biya kuɗin test da na wasu abubuwan ɗin da aka matata, ya juya ya fita.

Hankalinsu gaba da ya ya kara tashe musamman Shaheeda da a zuciyarta take cewa.

"Wannan wani kalan ƙaddara ce ta take son rushemun Mafarkina gaba daya?.Dan bani da wani mafarki idan babu Ummah ta." 😢😢😢


________________malamin na fita kuwa Khadijah suka je gurin A'isha da jikin ta gaba daya asanyaye dan gaba daya da..............
https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


*Mafarkina*
(My dream)
By
*Preetie Selmerh*

*Wannan page ɗin na yi shi na musamman ne ga Aminiya ta kuma yar uwa tah Khadijah Muhammad Sani (Walida).
Wacce ke karatu a (fudma) Katsina Ita ce mai Supporting dina a koda yaushe acikin rayuwa tah. tana tare dani a kowani hali na rayuwa Allah ya barmu tare na har abada. AMEEN 🤲!!!


Page 5
Chapter 10


________ Aisha ta yi dogan nunfashi ta ce

"Suna asibiti, Ummanta babu lafiya kuma jikinta ya yi tsanani."


Suka haɗa baki suka ce
"Allah sarki Shaheeda Allah ya ba ta lafiya
Ameen!.
An sallame su
zasu fita neman mota
Baffah da Abbah basu samu mota ba.

Sai ga wani mota ta zo wucewa dai-dai lokacin da Shaheeda ta fito.
kawai sai
Saheeb ya hango Shaheeda ta Glass.
Ya sauƙe Glass ɗin motarsa sai ya fito daga ciki.

Baffa da Abba kuwa suna tsaye sun yi shiru sai suka ji horn ɗin motarsa.

Sai hankalinsu gaba ɗaya ya koma gunsa.
Ya gaishe shi ya ce "Ina wuni Baba."

Sai Baffa.
Ya amsa da ''lafiya klu.''


Sai Saheeb ya ce.
''Baba lafiya na ganka anan?
sai Baba ce.

"Mai ɗakina ne ba ta da lafiya ayi mana Transfer zuwa maitamaHospital.''
Saheeb ya ce.
"Ayya Baba to a ɗauko ta sai in aje ko a asibitin nima yanzo company zanje dama.''
Sai duk kan su suka yi ciki aka ɗauko ta.
Suka kai ta asibiti.

MAITAMA HOSPITAL
Suna zuwa Emergency aka kai ta direct
Saheeb ya je.
ya yi magana da doctor ɗin ya fito zai tafi sai Baba ya ce.
''Yaro muna godiya Allah ya saka maka da Alkhairi mun gode sosai
Saheeb ya ce.

"Babu komai Baba ai duk yiwa kaine."
**********************
An tashi a school. Su A'isha da Khadijah da kuma Hannah. suka nufi asibiti ko da suka je wata nurse ta ce musu an sallame su ba daɗewa sai su mata godiya


Saheeb kuwa.
ya tsinci kansa cikin farin ciki wanda bai shi kansa bai iya misaltawa ba. Ya shiga Company dama meeting ɗin zai fara 3:pm dai-dai yana shiga.
Duk ka suka muƙe suka gaishe shi
''Ya amsa.''



Suka ɗaura da meeting.......
_____________________
Aisha ta je gida
Jiki a sanya ye

''Mummy Mummy an canza ma Umman Shaheeda asibiti zuwa maitama hospital.''
Mummy ta ce.
'' har yanzu jikin?
A'isha ta ce.
''Ehhh Mummy.''
Allah ya ba ta lafiya.''
Suka amsa da "Ameen.''

__________________yanzo jikin Umma da sauki dan har ta dawo cikin haiyacinta

Shaheeda sunyi murna sosai
A kullum Addu'arta Ummanta tasamu lafiya ita kuma burinta na zama MARUBUCIYA ya cika!!!

BANGAREN FADILA DA AUTA
Matar malam Yusuf kullum ita ta ke akai musu abinci
Auta kuwa. Ya ƙi cin abinci sai kuka shidai yana so. Yaga Ummansa da Aunty Shaheeda.
A school Exam ya gaba to.
Islamiyya ma walimar sauƙar Al-qur'anin su Shaheeda ya kusa.
ONE WEEK LATER!
Umman Shaheeda ta samu sauƙi sosai.
A kullum Saheeb sai Saheeb ya je asibiti ya gaishe su ya tambaye su ku suna bukatar wani abu??.
Baffa kuwa. Sai sawa Saheeb albarka ya ke yi.
Shaheeda ba karamin da daɗi take ji ranta ba dan tana ganin Ummanta na samun lafiya

MAITAMA LIMPOPO STREET
Gidan su Saheeb.
'Ammie yanzu
'' ta ga farin cikin ɗan na ta ya na ta karuwa ta rasa Dalili???
TARIHIN ASALIN SAHEEB!
END.

> Ku ci gaba da bibiyata dan jin wane ne Saheeb a ina kuma yasan Baffa.
Amsar na gareni M@ul H@yatee.
NAGODE!!!
MAFARKINA
By
(NANA SALMA)
✍️Alkalami✍️
*Preetie Selmerh
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALEEN
Page6
Chapter 11&12
*TARIHIN ASALIN SAHEEB*
________________Asalin sunan sa
Muhammad Umar faruk gostorh wanda suke yi masa laƙabi da
SAHEEB(masoyi).
Sunan mahaifinsa Muhammad Hassan gostorh"
"Gostorh shine family names dinsu.
Mahaifiyarsa sunanta Hajiya Hafsah
Su Yan asalin garin Kano ne layin Ishaq Rabiu."

"Sai karamar kanwarsa Madina.
Iyayensa sunyi aure
sai bayan shekara goma sha ɗaya tukun Allah ya basu haihuwar
SAHEEB''
"Sunyi matukar murna sosai wanda suka ɗaɗe basu yi sa ba
Saboda murna ranar haihuwar Saheeb
duk wanda yaje suna ko sun san mutum ko basu sansa ba sai anbasa kyautar dubu ɗari biyu a envelope''
Saboda farin cikin da suke ciki
Saheeb ya ga soyayya matuka gurin iyayensa sosai mara misaltuwa
Tunda suka haifeshi suka kuma (saude Arabia)
Da zama a can Shaheeb ya fara karatunsa.
Allah ya azurta mahaifinsa sosai da dukiya mai yawa.
Alhaji Muhammad Hassan.''
Ya na da da gidan marayu wanda yake taimaka wa a Nigeria da koma kasashen wage.
Dan shi mutum ne mai matukar tausayi mara sa karfi sosai
Rayuwa tana ta tafiya ahaka
Sabeeb na da shekara 13
Aka yi masa kanwa wato
MADINA
An haife ta babu dade wa Allah ya yiwa mahaifinsa Rasuwa
_____________________ Shi kuma lokacin yana karatu a Egypt
Hajiya Hafsah kuma
Ta dawo Nigeria da zama a cikin Abuja(FEDERAl CAPITAL)
Ta ciga ba da tafiyar da Company Alhaji Muhammad
Ita kuma.
'' Madina tana karatu a London
Wannan shine takaitaccen tarihin Saheeb.
**MU DAWO LABARIN MU**
An sallame Umman Shaheeda da ga asibiti.
Taji sauƙi sosai
Bayan sun dawo ne
''yan islamiyya su kuka zo gaba daya suka gaishe
Da Umman Shaheeda.''
A'isha kuwa.
''Tayi murna sosai.''
Suka zo gaba daya
Da Abban ta da Mummy''
Suka gaishe su.''
Sun masu hidima sosai
_______________ Saheeb kuwa bayan an sallame su
Shi yakai su gida
Baffa kuwa.
Yasa wa Sabeeb albarka sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login