Showing 27001 words to 27923 words out of 27923 words

Chapter 10 - MAFARKINA COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

98

zama Babbar MARUBUCIYA acikin garin ABUJA ta shahara sosai gidajen rediyo gari-gari suna karanta littafinta a akwatin rediyo
MAFARKIN SHAHEEDA ya zama gaskiya
MARUBUCIYA A.S SHAHEEDA
Shaheeda ta waye sosai fiye da yanda ta ke da ta zama babban mace mai class da capacity
Soyayyar Saheeb da Shaheeda kullum sai ƙaruwa ya ke yi
MADINAH TA KAMMALA KARATU A LONDON
Ta dawo gida Nigeria
AN SA RANAR AUREN MADINA DA MUNIR
DA KUMA
AMIR DA KAUSAR

Rana kwatsam Shaheeda ta tashi babu lafiya hankalin Saheeb ya tashi ya kira Doctor Ammar
Ya yi gwaje gwaje ya tabbatar mu su da Shaheeda ta na ɗauke da juna biyu na sati tara kuma bincike ya nuna triple ta ke dauke da shi ma'ana( y'an uku)

Farin cike a gurin Saheeb a gaban su Ammie ya rungume Shaheeda yau ko kunya bai ji ba suka fita su ka ba su guri
''Saheeb ya yi hugging ɗin Shaheeda ya yi kissing ɗinta kamar zai haɗiye ta.''

A take agurin ya ba ta ƙyautar gida da motor da check ɗin million ɗari
Shaheeda ta ga gata gurin Ammie da Madina da Saheeb
Saheeb ya sa aka rushe gidan su Shaheeda aka mu su saban gini plat house
Idan ka shiga cikin gidan ba za ka so kafi ta ba tsabagen hadewa
Fadila an zama babban yarinya
Auta shima sai girma ya ke yi
Saheeb ya biyawa Baffa da malam Yusuf umrah
Baffa da malam Yusuf tsabagen murna bakin su ko rufuwa ba ya yi saboda farin ciki
Abba ya siya mota
Rufin asiri dai-dai gwargwado Allah ya yi wa Abba

Abba shi zai aure Hanna kawar Shaheeda
Shaheeda ta shiga watan haihuwar ta
Saheeb ya ɗena fita ko ina kullum suna tare dan Shaheeda ba ta iya komai sai dai ayi ma ta cikin ta ya girma sosai duk ta kumbura
''Nurulqalbe ni fa mutuwa zan yi na na bi Umma ta.''
Saheeb ya zauna kamar ƙaramin yaro Shaheeda na kuka shima yana yi
Haihuwa ta zu gadan-gadan aka kai Shaheeda National hospital Abuja
Aka shiga da ita ɗakin haihuwa
Saheeb kamar shine zai haihu sai zifa ya ke yi
Suna tare da Ammie da Madina sai kuma Amir da kausar

Likita ya sanar mu su cewa Shaheeda ba za ta iya haihuwa da kanta ba sai dai a ma ta operation

Ya je ya sa hannu aka shiga da ita ɗakin operation
Saheeb sai Addu'a ya ke yi
Baffa da su Fadila a gida sun yi nafila sai addu'a su ke yi Allah ya sauƙe ta lafiya.
Ma sha Allah An yi aiki successfully
Shaheeda ta haifi y'an uku
Biyu mata ɗaya na miji
''Saheeb ya je ya rungume Shaheeda sai kukan farin ciki ya ke yi.'
Da ƙyar Doctor ya ba shi haƙuri ya fita
Madina ta kuma gida ta kwaso duk wani abun da za'a buƙata
Kayan jarire kala-kala iri ɗaya ma su ƙyau
An gyara Shaheeda ta yi tsaf abin ta
Saheeb ya shigo ya yi hugging ɗin Shaheeda 'yar Al-jannah Allah ya ƙara miki lafiya
Saheeb ya ɗauke su Yaran kyawawa duk suna kama da Saheeb da Madina
Bayan kwana uku
Aka sallame su daga asibiti
Suka dawo gida mutane sun zo ana ta zuwa yi mu su barka
Umma Jamila du sun zo

*************************
SOCIAL MEDIA
Duk ta ɗauka Umar Farouk Gosto matar shi ta haifi y'an uku

BABBAR MARUBUCIYA
A.S SHAHEEDA
Ta haifi y'an uku
An yi Sunan da ban taɓa ganin irin sa ba
RANAR SUNA
An yi wa Umman Shaheeda takwara da Ammie da kuma Alhaji Muhammad mahaifin su Saheeb
Manyan-manyan Marubuta novel duk sun zo
Kamar Pretty Sk
Aishaexcel Maman uwais
Maman Ihsan mummyn Jajirtattu
Aunty lele
Da fans ɗinta A.S Shaheeda fans group
Duk sun zo suna
**********************
Hassan an saka me Muhammad sunan mahaifin su Saheeb
Ussaina kuma Ramlah Sunan Umman Shaheeda
Gambon su kuma Hafsah sunan Ammie aka sa ka ma ta
Muhammad Nike Name Aryan
Ramlah Nike Name Ayra
Hafsa Nike Name Noor
An yi suna Social media ta ɗauka gidan rediyo da gidan Tv da duk sunan ake ta nunawa
Rayuwa ta yi daɗi
Shaheeda an kawo ma ta ma su raino
Fadila tana zuwa jifa jifa tana taya ta raino su Aryan

Shaheeda ta yi kyau ta yi haske ta yi ƙiba
Soyayya tsakaninta Saheeb da Shaheeda ba zai misaltuba soyayya suke sha duniya ta yi mu su daɗi

Yanzu Shaheeda sanadin rubuta novel ƙasashe ƙassashe ake gayyatar ta
MAFARKIN SHAHEEDA YA CIKA
A.S SHAHEEDA
________________________________________________________________________________________________________________________________________________________
BAYAN SHEKARA HUƊU
Madina suna London ita da mijinta Munir sun haifi ɗa daya haisam can ta ke aiki ita da Munir

Kausar da Amir sai shan soyayya ake yi ta kusa haihuwa
A'isha tayi aure a Kaduna
Fadila tana University B.U.K ita da Ummuqursum sai baza capacity suke yi suna ɗaukar wanka

Ɓangaren Yaya Abba da Hanna
Suna da 'ya ɗaya jiddatul khair ta na da cikin na biyu
agurin su Al-ameen ya ke ya girma kamar ba shi ba
Saheeb sun kuma gidan su da Shaheeda acikin Apo Abuja wani katafaren gida ne me matukar kyau wanda bazai misaltu ba

Ammie kuma ta buƙaci abar ma ta Aryan ya na shan gata agurin Ammie

Ayra da Noor suna shan gata soyayya da kula komai na more rayuwar duniya su na da shi
Dad and Mom suna tarayrayar su kamar kwai
END OF MAFARKINA
ALHAMDULILLAH

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon kammala wannan littafin na wa me suna MAFARKINA
Shine novel ɗina da na fara rubutawa
Allah ka sa ya ƙarbo ya je in da ban yi tunanin zai je ba a faɗin duniya
MAFARKINA FANS GROUP NA NANA UMMU SALMA
INA GODIYA ALLAH YA BAR ZUMUNCI
SAI MUN HAƊU A LITTAFINA NA GABA
SALAM
DAGA TAKU
NANA UMMU SALMAAH
BEAUTYN JAJIRTATTU CE
BISSALAM

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login