Showing 12001 words to 15000 words out of 27923 words

Chapter 5 - MAFARKINA COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

100

bikin Khadijah ne.''
Nan ta ke suka ga Shaheeda ta yi shiru.
Khadijah ta ce
''Shaheeda kina lafiya kuwa ko har yanzu mutuwar Ummah ce?''
''Babu komai khadijah.''
Cewar Hanna.
Shaheeda duk kin rame dan Allah ki yi haƙuri kibarwa Allah ko wani lamarinki.''
Lalle fah Hanna an yi hankali
''Yawwa A'isha ta ce idan muka zo mu ma ta flashing ta kira koyi magana.''
Su ka kirata tayi ending kiran tabiyo kiran.''

Tana kira suka bawa Shaheeda.....
Cike da murna ɗauke a fuskar Shaheeda

Suka gaisa
''Shaheeda nayi missing ɗinki sosai fah ni gabaɗaya kaduna bata yi mun ɗaɗi saboda babu ke a kosa da ke , ta na samu admission A.B.U zaria
''Aisha na ta ya ki murna Allah ya sanya alkhairi.''
"Shaheeda gaba ɗaya na jiki wani iri lafiya dai ko?

''Zan karɓi numbern ki gurin Khadijah zan kira ki da wayar yaya Abba
Sai anjima ki gaishe da mummy ta kashe wayar.''
Su ka ce
''tom Shaheeda ga ankon nan kin san gurin zuwa da yawa koma mun san ke kaɗai ce babu kowa agida.''

Ai da tare zamu je Hanna abun na mune.
''Sai anjima Allah ya kiyaye hanya.''

Sai an jima Shaheeda.

A'isha ta ce wa.
mummy Shaheeda na gaishe ta.
''Amma mummy kamar wani abu na damun Shaheeda fa dana tambaye ta ta ce mun zata kirani da wayar Yaya Abba.''
Mummy ta ce
''Allah ya sa lafiya.''
Ameen!
Shaheeda ta ci gaba da karatunta sai kawai maganar da Baffa ya yi jiya ya faɗo ma ta arai wai ita matar wani ne wanda ba ta san shiba nan take hawaye su ka gangaro ma ta a Fuskarta.
*************************
11:am
Nan safe Saheeb ya gama shiryawa tsaf cikin kananun kaya ya yi matukar kyau sosai su ka fita gabaɗayan su za su ta kashi airport....

Sun isa lafiya suka juya zasu dawo gida. ''sai ta ce Saheeb ka bawa Madina address din su Shaheeda?

''yeah Ammie ya tura mun.''
Suka yi hugging Na shi suka mai fatan nasara suka juya
____________________

Suna hanyar dawowa gida
Madina ta ce.
''Ammie bari mu biya ta shoprite inyi Shopping kinsan na kusa kuma wa School.''

Ok haka ne tom muje.
Suka je Madina ta yi Shopping sosai harda sabon trolley ta siya da kaya masu tsada sosai da abaya na Egypt su nufi gida.

Suna isa mai gadi ya shiga musu da kayan ciki

Suka zauna hutawa

Safna mai aikinsu ta kawo musu Ruwan gora da lemo
''Yanzu Madina duk wannan kayan da kuma siya ina zaki kaisu.''

Ta yi murmushi
''Ammie na siyawa matar yaya Saheeb ne gobe zan je in gaishe ta.''

''Masha Allah Madina Allah ya miki albarka kud rinƙa sada zumunci koma ba matar yayan ki ba ki zama mai kyautatawa al'umma duk na nasan kina yi Allah ya ke mu ke ma lokacin na ki auren.''

Madina ta tashe wai ita ta ji kunyar ta shiga ɗakinta.
Ta kwanta akan gado sai ga kiran waya da kamar ba za ta ɗauka ba tadai ɗauka
Assalamu alaikum
Ta amsa da
Wa, alaikumussalam
Na san baki gane mai magana ba koh
Munir ne wanda ku ka haɗu dashi agurin bikin Zara
''Alright i remember you.''

''So long time how is Mom.''
''She's fine.''
Suka gama magana suka yi ending ɗin call ɗin
Yamma ta yi Shaheeda sun gama aikin gida tare Fadila

Abba ya dawo daga gurin aiki suka yi magana da Baffa su ka shiga gida.
End
Beautyn Jajirtattu ce ✍️
Nana Salmaah
*MAFARKINA*
By
*Nana Salmaah*
*Beautyn Jajirtattu ce ✍️*
https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
Page 16
Bayan sun shiga gida Shaheeda ta yi masa sannu da zuwa ta kawo mi shi abinnci.

''Ta ce yaya dan Allah ka ara mun wayar ka zan kira A'isha.''
Ya miƙa ma ta wayar.
Ta shiga ɗakinta ta saka numbern ta yi dialing har ya gama ringing ba ta ɗauka ba ta ƙara kira sai ta ɗauka
Assalamu alaikum A'isha
Shaheeda ce
Wa,alaikumussalam
''Ya gida ya su Fadila da Auta.?
''Suna nan lafiya klau Alhamdulillah
Sai Shaheeda ta yi shiru.''
''Hello hello'' Shaheeda kina jina.''
''Ehh A'isha.''
''Shine ki ka yi shiru ina fatan lafiyan ki kalau dan Allah ki fada mun akwai wani abu ne?
Shaheeda ta yi dogon numfashi.
'' kafin ta ce A'ishah an ɗaura mun aure cikin muryar kuka.''
Haba dai Shaheeda You are joking dai ko dan ni iya sani na da ke baƙya kula samari kinfi maida hankali akan karatunki da kuma rubuta novel.''
''Shaheeda wallahi dagaske na ke faɗa miki jiya aka ɗaura da ɗaɗɗare.''
''Shaheeda Please stop between me and you there is no joking like this, you funny.''
''Ta fashe da kuka A'isha am serious.''
A'isha ta fahimci Shaheeda da gaske ta ke yi fah......
Ok but Shaheeda when did you meet him?
When you start dating each other?
And why are you at home?
Not in your husband house?
''All this questions I did have there meaning am just know that am marriage to someone that all.''
Am sorry Shaheeda be patient Allah is with you always.''
Muryar Yah Abba ta ji ya na cewa ko kawo min wayar zan je inkwanta.
Ta ce ma.
'lA'isha sai da safe.''
ta yi ending call ɗin.

''Daughter why are like this what's going on?
''Mummy Shaheeda is marriage to someone that she didn't know.''

''Aisha are you serious or joking.
Mum dagaske Shaheeda kinsan bama kalar wannan maganar da ita tun ɗazo da safe na san da aƙwai abin da ke damun ta kuma ta ce mun tana gidansu yanzu haka
Mummy Allah ya ba mu tausayi.''
''Allah Sarki Shaheeda baiwar Allah
Allah ya sa hakan shine Alkhairin share ta faɗin mom.''

Ameen
**************************
Saheeb landed safe suna video call da su Madina.
Saheeb shi yanzu burinsa bai wuce ya dawo daga Dubai.
Ya kwanta cike da farin ciki aransa da kuma kewar gida da kuma tunanin ko ta ya Shaheeda za ta karɓi shi amatsayin mijinta na sunnah.

Madina kowa Allah Allah'' ta ke yi sa fi ya ta yi ta je ta ga matar ya'yan na ta da kuma farin cikin da ta tsinci kanta wanda ba ta san dalilin haka ba

Shaheeda ta yi nafilan dare kamar yanda ta saba ta yi ta addu'a yau kam kusan kwana ta yi ta na sallah

''Ammie na good morning.''
''Kin tashe lafiya.''?

''Ina Safna ta haɗa break fast da wuri dan ina so in fi ta da wuri.''
''Ammie ta ce tana kitchen.''
Ta shiga ta sameta ta fada mata ta kuma ɗaki
Ta je ta shirya cikin wata doguwar riga pink colour ta yi rolling din gyalen rigar ta yi ma ta matukar kyau sosai
Ta fito palo suka yi break fast da Ammie ta ɗauko key ɗin motar ta fita Safna ta biyo ta da akwatin akasa a booth ya ɗau hanya.........
Ta isa wuse2 in da aka kai Zara kawarta
Ta yi horn aka buɗe ma ta

Ta yi knocking Zara ta ɓude ma ta ƙofa

''Wow Madina ke ce su ka yi hugging juna shine ko kifaɗa mun tunda aka kawo ni ko ƙara zuwa ɓaki yi ba ko nayi fushi.''
''Ayyah i apologize Zara.''
Su ka shiga palo ta dauko ma ta ruwa mai sanyi da fresh milk da kofi.
''Amarya kin sha kanshi kinga yanda kika canza kuwa Zara har wani komatu ki ka yi fa''Makodai kodai.''
''Madina ba na son sharri.''
''ki tashi mu je kitchen mu daura abinci dan kinsan bazan miki girki ba ko.''
''Ni yanzu ma tafiya zanyi.''
Ina za ki je haka?
''Mpape zanje.''
''pape kuma me zaki je yi haka a pape.''
''Ki bari long story ne zamu yi chart ai.''
''Bari in kira miki shi sai ko gaisa.''
'' ki bari wani lokacin ma gaida dashi kawai next week zan koma school.''
''Gaskiya Madina ni ban ji daɗi ba daman ba gida zaki zo ba kin biyo ne kawai.''
''Ayya Idan na dawo hutu zanzo musha hira.''
''Ke kika sa ni, wa ya san yaushe zaki zo hutu.''
Ta raka ta tashiga mota ya dawo
Sai ga Sadik mijinZara
''Naji kamar kina magana tun dazu.''
''Hmm Madina ce fa ta zo ko hutawa ba ta yi ba ta wuce.''
''Baby Muje mu yi break ko.''
*************************
Madina tana hanyar zuwa pape ta shiga layin su ta samu wani yaro ya ma ta kwanta ce ta yi darling ɗin motar ta
Ta samu wani yaro ya ɗauko akwati.
''Assalamu alaikum.''
Shaheeda ta amsa
''Wa, alaikumussalam.''
Ta shiga da ita ɗakinta ta shimfiɗa ma ta ɗaɗduma ta zauna akai ta ɗebo ma ta ruwa a jug da kofi
Suka gaisa ke ce.
A zuciyar Madinah ta ce ko nan tambaya na wannan ita ce Shaheeda dan na ganta da hankali kalan mayar da yaya na ya ke ''mafarki''kenan
Shaheeda ta zauna tayi shiru......
Nasan baki gane Ni ba ko?
Ɗauke da murmushe Shaheeda ta ce
''Ehhh.''
''Alright Sunana Madina kanwar mijin ki ce.''
Nan ta ke ta ji wani dum aranta.
Zan koma school a satin nan shine na ce sai na zo na gaishe da matar yaya na tukum.
Murmushin ƙarfin hali Shaheeda ta yi
''Ya ki ka 'yan gida.''
''Sunan lafiyan su kalau,Ina Baba da ƙannen ki.''
''Baba ya fita bai dade ba su Fadila da Al-ameen suna school.''
''Ayya idan sun dawo ki gaishe da su.''
''Zasu ji in sha Allahu.''
Sai ga Sallamar Baffa
Shaheeda ta fita ta ce mishi an yi ɓakowa.
Madina ta fito ta gaishe shi.
Suka gaisa tamkar sun san juna.
'' Baba kanwar Saheeb ce.''
Sannun ki da koƙari "Allah ya miki albarka Allah ya miki"

Ameen!

Tom Baba zan wuce ta nuna akwatin da yaro ya shigo dashi Shaheeda ga wannan babu yawa
Shaheeda kam bata ce komai ba
Baffa ya ce.
''yar albarka harda ɗawainiya haka mun gode sosai ki gaishe da y'an gida.''

''Baba me ye na godiya mun zama ɗaya zasu ji in sha Allah
Ta fita Shaheeda da Baffa su ka raka ta har mota
Shaheeda ta ce Allah ya kiyaye hanya mun gode sosai
END
*Beautyn Jajirtattu ce*✍️
*Nana Salmaah Aliyu*
*MAFARKINA*
By
*Beautyn Jajirtattu*
*Nana Ummu Salmaah*

Godiya ta musamman ga ma su bani gwarin gwiwa akan rubuta novel na gode yan uwa Allah ya bar zumunci🙏🏻
Da masu cewa littafin akwai daɗi suna buƙatar update godiya fans Allah ya barmun ku.
https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
Page 17and18
Chapter37&38and39
_____________________
Bayan koma war Madina gida
Ta samu Ammie a palo ta na karatun Jarida

''Kin dawo?

"Ehh Ammie na dawo Suna gaishe ki."
''Tom Ma sha Allah.''
''Ammie gaskiya yah Saheeb ya yi dacen mata ga ta da tarbiyya ga girmama mutane ne ga hankali irin dai wacce Yah Saheeb ya ke so ta na da kyau babu laifi Baban ta ma babu laifi akwai kirki.''
''A toh Masha Allah haka ake so ai Allah dai ya basu zaman lafiya.''
Ameen!

Shaheeda ta zauna a tsakar gida ita da Baffa su na ta mamakin kalan kayan da Madina ta kawo ma ta dan ko buɗe wa ma basu yi ba.

Sai ga shigowar Fadila da Auta

''Aunty Fadila kayan wa ye na ki ne?

''Kin shigo ko sallama ba bu kin hau tambaya.''

''Ina wuni Baffa ina wuni Aunty Shaheeda.''

"Baffa ya amsa da lafiya amsa a dawo ƙalau''?

''Ehh Baffah.''

Auta ya hau jikin Baffa kamar ba shi ba ya na ta wasa

Baffa ya ce wa Fadila.
''ku shiga da akwatin nan ciki.''
Shaheeda suka ka ma da Shaheeda su ka kai ciki

**************************
Aka kira sallar la'asar Fadila da Auta suka yi shirin islamiyya

Shaheeda kuwa ciwon ciki irin na mu na mata ya ɗame ta period ɗin ta ne ya ku sa duk wata haka ta ke fama da shi tun Ummah na rai sai dai kawai a bata ayi ma ta addu'a a ruwa ta sha

Da kyar dai haka ta ta shi ta yi ta yi mu su girki har Fadila suka dawo ta ƙwashe tuwon ta sa cikin kula
Shaheeda ta shiga daki
Bayan Fadila ta gama ta yi Sallah ta samu Shaheeda
Aunty Shaheeda wannan akwatin kine?
Ba ta ce mam ta komai ba
Jiya ai ina jinki da Aisha kuna waya wai anɗaura miki aure da wanda baki sani ba
Aunty Shaheeda ki yi hakuri gaskiya na ji an ji miki babu daɗi amma hakan daga Allah ne kuma insha Allahu alkairi ne agurinmu
Sai lokacin Shaheeda ta dago kai ta kalle ta
Ɗazu ne kuna School ƙanwar wanda aka auramun ta kawomin
Gaskiya Aunty Shaheeda akwatin ya yi kyau amma suna da ƙudi sosai?
''Ba na son wani surutu

Fadila ta ɓude akwatin.''

''kai Aunty Kin ga wasu haɗaddun atamfa kuwa ga takalma da abaya ma su kyau necklace da dan kunne ga kayan ƙwalliya su gyale ma su kyau Aunty ai wannan ya fi akwatin lefen wa su ma.''
Ba ta ce ma ta komai ba
''Fadila.''
Ta ce na'amm Aunty

''Ki ɗauki duk wanda ya yi miki acikin kayan dan Sahheeda ko kallan kayan ba ta yi ba.''
''Da gaske Aunty.''
Ina wasa da ke ne.'
Fadila abun ne ma ya sa mu ta dauki abaya guda biyu da takalmi da atampa da gyale da dan kunne da necklace ma su kyau

''Aunty ni wannan sun ishe ni ai na gode sosai Allah ya sanya alkahiari.''
BAYAN WANI LOKACI
Madina za ta koma London hutu ya kare
Ranar litinin ta kuma
Amir kullum sai ya zu ya gaida Ammie idan su ka yi hira sai ya yi tafiyarsa
Saheeb ana Dubai ana kan aiki
A wani katafaren hotel ya sauka
Abba yayan Sahheeda kuwa aiki sai cigaba ake gani
Kwana a ta shi babu wiya agurin me rai
*************************
*BAYAN WATA BIYU*
Saheeb ya matsu ya dawo gida Nigeria suka yi waya da Amir
ya ce mishi ya siya waya ya yi registar sim ya kai wa Sahheeda ya na matukar son jin muryar ta!
Amir ya ce.
''Allah guy wato kasa matso ka dawo akawo maka amaryar ka koh?

''Amir ka fiye shirme ni dai kayi abun da na ce maka kaima ta ɗubu ɗari da hamsin ko za ta bukaci wani abu.''

''Lalle ne su Saheeb manya an san haƙƙin aure.''
Su ka yi end
Bangaren Su Khadijah kuwa biki saura kwana uku ranar jumma'a za adaura auren ana ta hiɗima
Amma Shaheeda ba ta je ba su ka yi ta mamaki ko ba ta da lafiya ne?
Shaheeda kuwa an barta cikin zullumi ta na so ta je gidan su Khadijah ta ra sa yanda za ta yi ko ta tambayi Baffa ne ita kuma kunyarsa ta ke ji

Da yamma sai ga yaro wai ana Sallama da Baban Shaheeda
Baffa na daki
Ya fito ya je

Bayan ya fita ne Amir suka gaida ya sheda mishi saƙo ne Saheeb ya bayar akawowa Shaheeda

Baffah ya ce.
''Bari na shiga sai naturo maka ita.''
''Ok Baba nagode.''
Ya shiga gida ya gaya ma ta
Ta saka hijabi har ƙasa ta fito
Suka gaisa da shi Yawwa ga wannan ya miƙa ma ta wa ta jaka mai kyau sako ne daga Saheeb ya ce akawo miki
Ta sa hannu biyu ta ƙarba ta yi
Ta ce ta gode ta juya ta kuma gida
wo
Amir ya shi motarsa sa ya yi gaba

Ta shiga gida ta kaiwa Baffa
Ya ce ma ta
''Allah ya alkairi Allah yawa Saheeb albarka

Ta ajeye cikin ɗaki ta cigaba da harkokin gabanta tana ta tuna sunan da ta ji Baffa ya ambata *Saheeb* a ina ta taɓa jin sunan nan?

End
*Beautyn Jajirtattu ce ✍️*
*Nana Salmaah*

*MAFARKINA*
By
*Nana Ummu Salmaah*
Alkalami
*Beautyn Jajirtattu ce ✍️*

Fatima(Masoyiya)
*Wannan page din na ki ne masoyiyya tarh kuma twincy narh wanda saboda ƙawanc e mutane da yawa sukan ce muna kama Allah ya bar mu tare*
*Ameen!*
https://chat.whatsapp.com/Lp80JY5H2uoLBZwPTVLyB3?mode=ac_t
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
Page 18
Chapter40&41&42
Bayan isar Amir gida ya shiga ya huta ya kira Saheeb video call

"Mai gida an yi abin da ka ce ga numbern sim ɗin da na yi regista na saka ma ta katin dubu hamsin aciki.''

''Alright Abokina na gode.''
''Ka ji ka fa ya so how was the work?
''So greatful alhamdulillah.''
Shaheeda bayan ta kammala aikin gida ta ɗauko jakar da Amir ya kawo ma ta ta yi ta kallo jakar kafin ta ɓude bayan ta ɓude taga wani ƙwalli an rubuta iphoneXR ta ɓude ta ga waya mai kyau
A cikin zuciyarta
''ta ce ina zan iya amfani da wayar nan ni da ko button phone ban ta ɓa riƙewa ba.''

Ta yi ta juya wayar a hannunta sai ya ga wani abu anyi wrapping ta na budewa ta ga kuɗi
Wannan Da ya ke ta yi mun hidima haka wani kalar so ya ke mun ko ma a ina yasan ni?
Ta ta shi ta nufi wa je ta samu Baffa a tsakar gida ya na jin radio

Ta nu na masa wayar da kuɗin
"Gaskiya ya kyauta irin wannan hidima haka Allah ya saka masa da alkhairi🙏
Ya miƙa ma ta
''Baffa ka rike kudin agurin ka.''
Shaheeda ki ƙarɓa ai ke ya bawa
''Tom ai ni ba ni da abin da zan yi da kuɗi ka riƙe agurinka kawai.''

''Amma ba na ji kuna maganar auren ƙawar ki Khadijah ba ina akwai ankon da za kuyi ƙawaye?

''Ehh Baffa jibi ne bikin ai lokaci ya kure.''

"A'a Shaheeda kinga baza ta ji ɗadi ba idan bakiyi ba daman yau ina da niyar na ba ki ƙudi ki siyo ankon kinga faɗuwa ta zu dai-dai da zama da ga nan sai ki siya ma ta gu dun mawar ki.''
Ya miƙa ma ta budu ashirin da biyar idan da kari sai ki faɗa mun na ba ki.''
Shaheeda ta sa hannu ta karɓa
'' ta re da yi ma sa godiya.''
Ta shiga ɗaki ta yi sallar azahar lokacin Fadila da Al-ameen su ka dawo daga school su ka ci abinci ita da auta Fadila ta yi Sallah
Ta sa mu Baffa a tsakar gida
''Yanzu Baffa za mu je da Fadila siyo ankon sai mukai ɗinki gurin Bashir tela zan iya fita ta sun kuyar da kanta ƙasa.''

''Shikenan Shaheeda zan fada masa fitar ce dole sai ke da kanki da ace na san kalar Atampar ne sai in je na siyo muka amma ban sa ni ba kuje da Fadilan Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo

Ta shiga ɗaki ta saka hijabi light blue har ƙasa ya ma ta kyau sosai suka fi ta da fadila
Su ka je wani shago a bakin kasuwa su ka duba kalar Atampar su ka samu akwai cotton da kuma mai sauƙi ta ɗauka mu su cotton ɗin ita da Fadila
Su ka shiga shagon kayan kitchen ta siya kula da plate
Su ka nufi gurin bashir tela mai ɗinki ayi mu su doguwar riga mai ƙyau
ya ce tunda su ne
''Su bayar da sha biyu ita da fadila kuma ɗinkin express ne.''
Ta miƙa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login