Showing 189001 words to 192000 words out of 220972 words
ta cika kwanaki talatin cif kamar yadda Bokan ya fad'a sai ta tashi da wani irin special attitude that has never appears since incidence d'in ya faru,Hajiya Mariya ta fito za taje d'akinta sai taji tana iface² da kiran sunan Abbah tana shek'a dariya,abun nata dai sak hauka,agurguje Hajiya Mariya ta k'arasa shiga tana kiranta,abunda ya bata mamaki sai taga Kariman tana yi mata wani irin firgitaccen kallo,da gudu kuma ta nufo inda take tana fad'in "Sai na kashe ku,duk wanda yace zai raba ni da miji na sai na kashesa" tana maganar tana yowa kanta bakinta har wani irin kunfa yake like ta sha liquid soap,Hajiya Mariya taga babu sarki sai Allah ta fita daga d'akin but sai ta manta bata rufe k'ofar ba,Hajiya Karima tana ganin k'ofa a bud'e itama ta fito ta kama hanyar fita daga parlor dake a bud'e,Hajiya Mariya tana hangen lokacin da ta fito,da gudu² ta biyo bayanta tana fad'in "na shiga uku,shi kenan za ta fita ta tona mana asiri" a gaggauce ta biyo bayan Karima d'in da tayi nisa da tafiya tana yi tana surutai wanda duk wanda ya ganta zai fahimci ba lafiyarta k'alau ba.
Sun yi tafiya mai mugun tsayi,Hajiya Mariya was in a napep suna binta duk inda tayi da son dakatar da ita,duk magiya da yaudarar da tayi mata da taga yak'i aiki a kanta sai ta hak'ure tace mai napep d'in yayi ta binta har suje inda za ta gaji ta tsaya,mai napep yace "Hajiya kud'in ki fa k'aruwa yake yi" tace "Muje kai dai ba ka da matsala" haka mai napep yayi ta binta duk inda tabi,wajen maghreb har an fara kiran sallah sannan ta dakata bakin get d'in gidan Abbah had'e da fashewa da dariya tana kwala masa kira,mai gadi ya lek'o da ya gansu sai ya bud'e musu saboda wancan ranar sun yi masa barazana za su had'a shi da Abban,kafin Hajiya Mariya ta sakko a napep ta tuni Karima ta shige gidan tana zabgawa Abbah kira,Binitta dake can kitchen ta window d'in da yake a bud'e ta jiyo ana kiran ubangidansu da sauri ta lek'o wajen,tana tsayen taji Hajiya Karima ta kece da wani irin k'ak'k'arfan dariyar da ko namiji ba lallai yayi irinta ba,and then she began to reveal everything da suka aikata,cikin hauka ta bada labarinsa,jikin Binitta yayi mugun sanyi,tsoron Hajiya Karima ya sake shiga jikinta,leaning her back on the cabinet ta fashe da kuka,ta jima sosai a kitchen d'in,da ta daina jiyo surutun Hajiya Karima ta mik'e ta fito jikinta har lokacin bai daina rawa ba ta wuce d'akinta ta fara had'a kayanta,tana kuka tana fad'in tafiya za tayi,yau kam a gurin mamanta za ta kwana,baza ta sake zaunawa ba,but kafin ta tafi she decided to call Nusrah saboda kada ta tafi kai tsayen gara ta fara sanar da su za ta ajiye aikin.
*****
A mugun firgice Annie dake bacci ta farka bakinta yana jeranta fad'in "A'uzhubillahi minashshaid'anir rajiiym.. Laa ilaaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn!" Yanayin da ta farka da shi jikinta ya had'a gumi duk uban sanyin dake cikin k'ayataccen bedroom d'in,su suka ja hankalin Abbah dake aiki kan computer,da sauri ya nufo inda take fuskarsa cike da damuwa yana tambayarta "my dear are u alright?" Ta kad'a masa kai idanuwanta a rufe,a hankali ya zauna next to her sosai kamar za su shige cikin jikin juna saboda son sanin abunda ya tayar mata hankali,ta had'iye saliva's da kyar tana kallonsa sai ta k'irk'ira murmushi tayi saboda ta ta yadda hankalinsa ya tashi,a hankali Abbah yayi ajiyar zuciya yana kallonta hannunsa rik'e da nata yace "What happened?" Tayi jim tana tunanin abunda za ta fad'a,a hankali ta lumshe idanunta tace "mafarki nayi" ya sake yin ajiyar zuciya yace "Ok! Ai kinyi addu'ah,in sha Allah nothing will happen" Annie tace "in sha Allah" daga hakan ta fara sauke k'afafunta,Abbah ya kalleta kad'an yace "Where are u going?" Ta d'aga kai tana kallonsa tace "lokaci ya k'ure ne,and ya kamata ace na fara preparing mana dinner" ya kad'a mata kai a hankali yana dawo da ita kusa da shi yace "kamar ba kya jin dad'in cikin kwanakin nan,ya kamata ki huta yanzun zan fita idan ina dawowa sai na siya mana abunda ya dace" tayi murmushi idanunta akansa but sai bata ce komai ba ta hak'ura bata sake yin maganar girkin ba,Abbah yana gama abunda zai yi ya fara shirin fita kamar yadda yace Annie ta taimaka masa,har bakin mota ta rakasa na nan cikin apartment d'in ya wuce tana d'aga masa hannu har ta daina ganinsa sosai sannan ta koma,tana shigowa direct kitchen ta wuce ta fara preparing musu healthy food as their dinner,ta gama shirya komai kafin lokacin maghreb yayi,brown rice da cabbage stew sai butter lettuce and fresh herbs,sai fruits da ta yanka different styles,duka a gaggauce tayi aikin ta kammala ta fito da komai ta jera a dining,lipton data bari kan gas d'in ta shiga saukewa saboda ya tafasa k'amshin herbs da ta sa duk ya cika parlor'n,da sauri taje ta juye a flask ta ajiye saman cabinet ta kashe gas,ta juya da niyyar d'aukan flask d'in ta fita k'aurin gas da ta shak'a,in time taji zuciyarta ta fara tashi a gurguje ta isa inda flask d'in yake tana rik'e da numfashinta,tana d'aukar flask d'in ta fita a kitchen d'in har tana had'awa da gudu,tana fitowa ta rufe kitchen d'in,sai ta lumshe idanunta a hankali tana sakin ajiyar zuciya,ta bud'e ido da nufin k'arasawa inda dining yake ta fara ganin komai yana juya mata,da sauri ta dakata tana ware idanunta sosai,a jima kad'an ta daina ganin komai duka.
Some hours left ...
Annie who was lying bayan farkawarta,ba tare da ta bud'e ido ba ta kai hannu ta dafa kanta da take jin yayi mata nauyi tana yamutse fuska,haka ma duk tana jin jikinta yayi mata babu dad'i,a hankali ta furta "Alhamdulillah alaa kulli shaii'iy" rik'e hannunta da taji anyi sai ta fara bud'e ido,Nusrah ta gani zaune kusa da ita quickly tayi yunk'urin tashi ta zauna Nusrah ta dafeta tana mata murmushi,a hankali ta waiwaya tana kalle²n wajen da suke,ganinsu a hospital ta zaro ido tana fad'in "me muke yi a hospital daughter?" Nusrah tayi mata murmushi tace "Muma fa Annie we just come and found u lying on the floor,but not knowing what was happening" Annie tayi shiru kamar tana tunani can ta d'ago ta kalleta tace "me yake damuna to muka zo hospital? Ni lafiya ta k'alau daughter" ta fad'a tana k'ok'arin sauka daga saman gadon,da sauri Nusrah ta rik'e mata hannun da ake mata k'arin ruwa saura kad'an ta cire cannular d'in,cike da mamaki Annie tabi hannun ta da kallo ta d'ago ta kalli Nusrah kafin tayi mata wani tambayar aka turo k'ofar aka shigo,Abbah ne tare da Nuraz kallo d'aya za kayi musu kasan suna cikin farin ciki,Annie ta bisu da kallo but ta kasa fahimtar yanayin su duka,suka kalleta suna yin murmushi,itama ta daure ta mayar musu,Nuraz ya zauna d'aya side d'in nata yana rik'e hannunta ya kwantar da kanta jikin shoulder d'insa,cikin sanyin murya ya furta "Annie ya jikin?" Ta tab'e baki tana kallon hannunta mai k'arin ruwa a jiki tace "Who told u i was sick?" A tare suka kalli juna,Nusrah za tayi magana Nuraz yayi gyaran murya yana nuna mata da ido,sai ta wayance ta d'auke kai kawai,Annie ta bisu da kallo su ukun but sai bata sake tambayar kowa ba cikinsu,har ruwan ya k'are tana zaune tana kallonsu,nurse tazo ta cire mata daga nan Dr Paredes ya shigo,bayan ya sale duba yanayin jikin nata yayi mata y'an tambayoyi sai yayi discharging nasu daga hospital d'in,su Abbah suka yi masa godiya then suka fara shirin barin hospital d'in,lokacin da Dr Paredes yazo fita ya mik'awa Nuraz hannu da fad'in "Allah ya inganta!" Wannan kalmar da Annie taji sai ya tsaya mata a rai but kuma sai ta kasa fahimtar abunda suke nufi,a hakan har suka fito daga Nuffield health suka nufo gida.
After they came in decideddare ya fara yi sai basu zauna ba suka yi sallama da su Annien suka tafi,ita dai Annie tun da suka baro hospital ganin duk sunk'i fad'a mata abunda yake damunta sai ta koma kamar wata dumb,maganar ta ya koma kad'an² shima sai ya zama dole,tun da su Nusrah suka bar gidan kuma sai duk ta sake yin shiru,idan Abbah yayi magana sai dai ta bashi amsa da "Uhm" ko "um'um" da yaga ba ta son magana sai ya kyale ta a tunaninsa duk jikin ne yasa ba ta son magana sosai,sai bai takurata ba har lokacin bacci yayi,a nan ta fara ganin wani sabon salon kulawa na musamman,motsi idan tayi sosai idanun Abbah suna kanta har ta fara zargin wani abu but she decided not to ask him again.
Washe gari Lolly da Hajiya suka je duba jikinta,and she was surprised at how they were treating her bcus a lokacin kuma ita tana jin lafiyarta k'alau babu inda yake mata ciwo,but idan sun yi wani abun sai tayi murmushi tana yi musu kallon they know nothing,while su ma a nasu gefen suna yi mata kallon bata san komai ba,tun daga ranar kusan kullum tsakanin su Nusrah ko Lolly sai wani ya je gidan,Annie ta gaji da yin shiru bcus har lokacin an kasa samun wanda zai mata bayanin rashin lafiyar da take yi,ranar da dare ta tsare Abbah da tambayar me yasa yanzun kullum sai Nusrah ko Lolly sun zo? Abbah yayi murmushi yana mik'ewa tsaye zai bar wajen ta rik'e shi da sauri,cikin damuwa tace "ban san mene ne kuke b'oye min ba,u should let me know,ni na san lafiyata k'alau but kullum sai ace min ya jiki na? What's wrong with me? And wancan ranar me muka je yi hospital?" Da Abbah ya kula mood d'inta had changed,here he sat down ya warware mata abunda yake faruwa,baki bud'e Annie da taji batun she was pregnant for about 12 weeks ta kafe Abbah da kallo,bcus ita da ta daina ganin period d'inta lokacin ta yi tunanin ko lokacin dainawarta yayi,so da take tana da sani a nan gefen shi yasa ma bata wani damu ba,Abbah yaga ta kasa magana yayi murmushi yayi blowing mata iska a fuska,ta kyafta idanu a hankali hawaye suna sauka kan fuskarta ta d'ora hannunta saman cikin,wani irin sanyayyar iska mai tattare da ni'imomi sai shiga jikinta suke tare da k'aunar cikin,with a crying voice kuma ta furta "Shukhraan ya k'adeer!" Kanta yana kallon sama,sai ta k'ara fashewa da kuka,da sauri Abbah ya rik'o fuskarta yana fad'in "U know there are many ways to be grateful,kuka ba shi ne abunda ya dace kiyi ba,if u want to show ur Creator that u are happy with his gift,ki nuna farin cikin ki ta wasu hanyar,but please don't cry!" Wani wawan rik'o tayi masa hawaye wasu suna korar wasu,Abbah ya rasa yadda zaiyi kawai ya rungume ta yana sakin murmushi da shafa bayanta like Annie ta koma sweet 18 lol,bayan wani lokaci tana kwance jikin Abbah sai ajiyar zuciya take yi and har lokacin hannunta yak'i rabuwa da cikin,duk sai take gani kamar ba gaske bane abunda aka sanar mata d'in,since that day maganar cikin ya bayyanar mata sai ta fara kind of anomaly attitude,duk abunda ta ci sai ya fito except lipton bak'i ko madara ba ta sawa haka take shansa,a hakan dai tun abun yana damun Abbah har ya hak'ura ganin hakan shi ne kwanciyar hankalinta,k'arshen tafiyar da basu yi ba kenan zuwa Nigeria,laulayin da take yasa aka rusa zancen tafiyar but sun tsayar da maganar after Annie ta yi giving birth.
Days went on from days to weeks to month,which is zuwa yanzun cikin Annie ya shiga about five months,and by the time cikinta ya fito sosai yayi wani irin girma na ban mamaki,ko ina a jikinta duk ya kumbura,kaya ma idan ba oversize ba basa shiga jikinta,su Lolly duk sai murna suke yi za su samu k'aruwa ta b'angaren Annie sun manta batun zuwa Nigeria,a haka lokacin haihuwar yayi ta matsowa,lokacin da cikin yayi wata tara duk wanda ya san Annie idan ya kalleta yaga uban girman da cikinta yayi sai yayi magana,while a gefe d'aya kuma tun da cikin yake ba ta wahala Abbah ya kawo mata Bareerah ta dawo wajenta da zama,though a time d'in ma da jimawa suka yi magana da Nusrah kan case da ya faru a Nigeria,so tun lokacin yaje ya taho da su tare da Binitta saboda ayyukan gidan,Annie kam baiwar Allah dukzuwa lokacin idan ta zauna a guri ko motsawa ba ta son yi saboda nauyin da cikin yayi mata,komai za ta yi sai Bareerah ta taimaka mata,while Binitta kuma ta ci gaba da aikin kulawa da gidan,in the evening ranar wata Monday Nusrah got out of school,ganin Nuraz bai zo d'aukarta da wuri ba ta gaji da zama tace su Veronica su ajiyeta gidan Annie da yake sunfi kusa da gidan akan mansion,suna yin parking arean ta sauka suka yi sallama tana d'aga musu hannu,suna wucewa then ta fara tafiya,ta tsaya bakin entrance tana yin knocking Bareerah ta bud'e mata,ta shigo ta wuce parlour,bayan sun gaisa taji shiru bata ga Annie ba,ta kasa daurewa tace "Bareerah aunty Annie fa?" Bareerah tayi sanyayyar ajiyar zuciya lookin at the way of her bedroom tace "Tun da ta shiga sallar asr she hasn't come out" Nusrah ta waro ido da sauri ta nufi hanyar bedroom d'in Annie tana fad'in "Haba Aunty kin san condition d'inta me yasa baki duba kin gani ko lafiya ba,yanzun fa maganar maghreb ake yi" maganarta ne ya katse lokacin data bud'e k'ofar d'akin,seeing Annie kneeling on her knees ta had'a zufa,da gudu Nusrah ta k'arasa tana kwala kiran Bareerah Aunty,a 180 Bareerah ta iso bedroom d'in bcus ta san kiran ba na lafiya bane,sai ga Binitta ta fito daga kitchen,su duka suka rik'e ta suna tambayar lafiyarta but duk sun kasa sanin me za suyi su taimaka mata saboda rud'ewa,ga Annie kam situation da take ciki sai ya kasance a duk motsawar second yana yi ne but kamar ana k'ara mata k'arfin ciwon,Bareerah ta kalli Nusrah da tayi firi² kamar ita take nak'udan ta langab'ar da kai tace "Ko za ki kira Abbah muje hospital?" Da sauri Nusrah ta gyad'a kai sai kuma ta koma parlor,wayarta ta d'auka a jaka kafin ta yi k'ok'arin kiran line Abbah,kiran Nuraz ya shigo da sauri ta d'auka ta kai kunne,kafin tayi magana yace "Hello Madam! Ina kika shiga na shigo skul sai nemanki nake duk inda kuke zaunawa ban gan.." Bai k'arasa ba Nusrah cikin muryar tashin hankali tace "I'm at Annie's house,please hurry and help us muje hospital" hankalinsa yaji bai kwanta da yanayin da tayi magana ba da sauri yace "okay" ya ajiye wayar seat d'in kusa dashi ko katse kiran bai yi ba,Nusrah tayi kiran Abbah and informed him they would pass to the hospital yace sai su had'u can d'in,cikin k'ank'anin lokaci Nuraz ya iso,tun da ya shigo arean kafin yayi parking ya fara yi musu horn,hijab kad'ai suka saka ma Annie suka fito da ita lokacin duk ta gama shan wahala,suka shigar da ita back seat with Nuraz's help Bareerah ta zauna tare da ita,Nusrah ta shiga front seat suka d'auki hanyar Nuffield health,aka bar Binitta to take care of the house before su dawo,kusan a tare motocin su suka shiga hospital d'in da na Abbah,but kafin su k'araso har an shirya mata bed suna k'arasowa nurses suka wuce da ita maternity ward,wasa² tun wajen maghreb har suka yi sallar isha but shiru,after sun dawo daga sallah Dr Paredes ya nemi ganin su a office,it was there he explained to them yadda za su fahimcesa kan baza ta iya haihuwa da kanta ba,take Abbah ya amince ayi mata aiki,ko isashen awanni uku ba'a yi ba aka ciro mata kids d'inta uku mace d'aya maza biyu,murna gurin Nusrah har da kuka ta samu y'an uwa,bayan an shirya kids d'in aka kawo su,tunda aka yi haihuwar suka tabbatar da lafiyarsu duk sai suka samu k'arfin guiwar yin waya suka fara sanar da y'an uwa,Nusrah ta d'auki yaran tayi musu addu'ah murnanta yak'i b'oyewa,da ta d'auki macen kuma sai ta hana kowa ya d'auketa bcus duk ciki ta fi su rashin girma and tafi sonta,ta barsu da rik'on mazan,kafin wani lokaci Hajiya da su Maimunatu sun k'araso hospital d'in bakin kowa yak'i rufewa dan murna,haka Mummy ma matar baffanta Mr Sajid da su Afaf da Hannah duk sun zo,kowa yazo yana son d'aukar baby girl d'in but Nusrah tayi kane² ta hana kowa,Hajiya tayi dariya tana kallonta tace "Anya baby za ki bari mu d'auki y'ay'anku?" Nusrah tayi dariya cike da wauta tace "Kai! Gaskiya Hajiya ni dai babu mai d'aukar min yara har sai na gansu sunji d'umi na,nima na ji na.." Da suka zuba mata ido suna dariya sai ta kasa k'arasawa saboda kunyar maganar da ta fad'a d'in quickly ta tashi za ta bar wajen,aka yi sa'a su Nuraz sun shigo cikin ward d'in sai ta koma bayansa ta b'oye,Abbah ya kalleta yayi murmushi yace "Baby! Wane mai sa'ar kika bawa aron lil sis d'in naki?" Bata yarda ta fito daga bayan Nuraz ba cikin shagwab'a tana turo baki tace "Ba Hajiya ce ta karb'eta tun d'azun ba" Abbah yayi murmushi yace "Ato! Ai gara da ta karb'eta a hannunki,tun da aka fito da su kika hana kowa d'aukarta" ta sake turo baki tana daga bayan Nuraz har time d'in tace "Ai dai naga tafiya za kuyi ma ku barmu da su" Nuraz ya waiwaya kad'an ya kalleta yace "Ke da waye za'a barki d'in?" Tace "with Bareerah aunty" ya gyad'a kai yace "I see" daga haka ya fara tafiya ya zauna kan wani empty chair dake gefe,Hajiya began to tell Abbah what had just happened babu jimawa,Abbah yayi dariya yana kallon yadda Nusran taje ta shigewa Nuraz,though ba wai suna yin magana ana jinsu ba ne,but their circumstances yasa Abbah fahimtar hankalinsu a kwance yake,he smiled softly yana kallon Lolly da ta