Showing 63001 words to 66000 words out of 220972 words

Chapter 22 - DAN MACE COMPLETED COMPLETE HAUSA NOVEL

24 Aug 2025

2177

ido ya bud'e yayi ajiyar zuciya mai nauyi yace "Mahaifana ba wasu bane,sannan na kasance ni kad'ai ne a gurin mahaifana,na taso a rayuwata ba ni da elder brother ko wasu little siblings,na rayu a wajen Big mom d'ina,duk da a cikin gidan mu bamu kasance da wani relatives namu ba,mun rayu mu kad'ai big mom d'ina da maidservant,sai Mommy na though she was unconscious bayan ta haife ni,sai kuma ni kai na kenan,dalilin da yasa na zab'i zama psychiatrist kamar yadda na fad'a a bayan saboda Mommy na ne,,sanadinta na zab'i wannan field d'in.."
A hankali cikin sanyayyar muryarsa ya fara finding out irin rayuwar da suka yi tun kafin a haifeshi,irin wahalhalun da suka sha kafin ya zo wannan matakin har ya dire a k'arshen,but abu guda ne bai yarda ya fad'a ba,sunan mahaifinsa though Jennet ta so ya fad'a,ya tsaya a nan yace "Idan har lokacin sanin ko wane ne mahaifinsa yayi zai bayyanawa duniya,though ya san ba b'oyayye bane,sunan sa kad'ai idan ya fad'a gaba d'aya duniya zata girgiza,but shi har yanzun yana doubting ne akansa,anya ya cancanta ya zama uba.!? Mahaifiyarsa ita ce komai nasa a rayuwa,,dan haka yana so al'ummar duniya su shaida hakan,kamar yadda mutumin da yayi ik'irarin shi ba mahaifinsa bane,shima ba yau zai fad'awa duniya shi d'ansa bane,saboda haka zai ci gaba da amsa sunansa na *'DAN MACE..* Kamar yadda society da k'abilar malam bahaushe take kiransa da shi.."
Yadda tattaunawar ta kasance zuwa bayyanar tarihin sa yasa al'ummah da dama kuka,Rafeek na zaune ya k'afe screen na cinema da ido yana hawaye da wani irin nadamar abunda ya aikata a zuciyarsa,he feels that time where running back,surely da there is nothing will stop him from turning it first,a hankali yayi descending daga saman chair yayi collapsed on to the ground,bakinsa na wani irin karkarwa yake fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaik.. Allah na tuba,na san ni bawanka ne mai tsananin taurin kai,na wulak'anta kyautar da kayi min a lokacin da ya kamata ace na nuna godiya ta gare ka,na tozartar da su,ya Allah ka dubi halin da nake ciki ba don hali na ba ka dawo min da su cikin rayuwata.."
A cikin wannan mawuyacin halin da yake ciki Clark ya shigo masa da report d'in binciken daya sa shi yayi masa ya riskeshi hankalinsa a tashe,ganin uban gidansa na kuka babu ji ya kira Hajiya ya sanar da ita,ita kanta hankalinta a tashe ta zo apartment d'in ta tarar da shi durk'ushe a k'asa hawaye wasu suna bin wasu a fuskarsa,idanunta sun yi wani iri saboda tausayinsa ta rik'o shi tana tambayarsa "RAFEEK kanka d'aya ka ke neman mayarwa da kanka bara ta za dawo bana.!?"
Jin muryar mahaifiyarsa yasa ya d'ago jajayen idanunsa da sauri ya kalleta yana girgiza kai,muryarsa sai rawa take da kyar yace "Hajiya ina jin tsoron abunda zai faru da ni gaba,tun a baya kunyi k'ok'arin fahimtar da ni abunda zai iya faruwa amma a lokacin sai nak'i saurarenku,na watsa muku k'asa a ido,bayan na butulcewa mahalicci na ta hanyar nuna masa kyautar da ya bani ba komai bace face k'azantacciya,al'halin ni nayi silar samar da ita ta tsarkakakkiyar hanya,,Hajiya da wane idon zan kalli d'an dana wulak'anta.!? Da wane idon zan kalli mahaifiyarsa.!? Na wulak'anta su,na tozarta su,duk da haka ban tsaya a nan ba,sai dana tozarta su a idon duniya,na yi sanadin da mahaifinta ya koreta,Hajiya me zance da ubangiji a lokacin da na ganni a gabansa.?? Me zan fad'a na wanke kaina saboda hak'k'in dana d'aukarwa kaina.!? Ina dana sani a rayuwata,ba zan tab'a daina yin nadamar abunda na aikata ba har zuwa numfashi na na k'arshe.." Hawaye ne ya gangaro mata tana rik'e dashi a jikinta,ta rungume shi tana fad'in
"Yi shiru haka nan,in sha Allah za su yafe maka,kai dai kayi k'ok'arin neman yafiyarsu,ta wannan hanyar ne kad'ai zaka samu sassauci.."

"Ba zasu yafe min ba Hajiya,na cutar da rayuwarsu da yawa,ba zasu yafe min ba.. Na sani hakan ba zai tab'a kasancewa ba"
Girgiza kai tayi ta d'ago fuskarsa ta masa whipping tears tace "in sha Allah za suyi hak'uri su yafe maka" ya girgiza kai da sauri wasu hawayen suna sauko masa zai yi magana Hajiya tayi saurin taron numfashinsa "Kada kace komai,kaci gaba da addu'ah in sha Allah babu abunda yafi k'arfin ubangiji.."
Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi,ya sake kwanciya a jikinta yana maimaita "Astagfirullah..! Astagfirullah wa'atubu ilaiik.!"
A hankali ya lumshe idanunsa yana jin wani irin yanayi a jikinsa,Hajiya tana shafa kansa sai data tabbatar ya fara samun nutsuwa sannan ta barshi ta wuce nata apartment d'in.

***
Yana gama aikin da zai yi ya fito daga asylum da yake yamma tayi sosai kai tsaye ya wuce gida,jinsa yake wani iri yau duk baya jin dad'in jikinsa,har ya k'araso harabar gidan yayi parking bai kula da mutum a gurin ba,ya fara tafiya ya jiyo sautin dariyar ta,ya juya a hankali zuwa side d'in da yake jin dariyar,zaune take saman ginannen kujerun dake lambun,su biyu ne ita tana facing d'insa shi kuma guy d'in da suke tare ya bashi baya,yadda take zuba murmushi da gani kasan abun da yake fad'a mata ne yake sata dariya,ta rufe baki da hannunta tana murmushi kad'an cikin son ta tsayar da dariyar dake taho mata,ta d'aga idanunta a hankali za tayi magana karaf suka had'a ido da shi yana tsaye ya kafeta da kallo,gabanta taji yana fad'uwa saboda yanayin kallon da yake mata,tayi sauri ta sunkuyar da kanta tana runtse ido,duk wani annurin dake shimfid'e a fuskar take ya b'ace,siririn tsaki yayi ya wuce yana tab'e baki,sai data tabbatar ya bar gurin kafin ta iya d'agowa ta kalli guy d'in da suke tare,ya kafeta da manyan idanunsa cikin nuna damuwa yace "What happen dear.?"
Ta d'anyi murmushin yak'e tana kad'a kanta tace "Babu komai" da yake Aatif shima d'an 9ja ne aiki ya kai mahaifinsa can,sai suke zaune a k'asar kamar su,yawan shiga skul d'insu da yake yi ya sauke k'anwarsa suka had'u da jimawa sai dai bata yarda ta bashi fuska ba sai yanzun shima dalilin irin nacin da yake mata ne,tun ba ta saurarensa har ta fara sab'awa da shi,yau shi ne zuwansa na farko gidan shima ba'a son ranta ta yarda yazo ba,,a hankali yana marairaicewa cikin shagwab'a yace "Kin san bazan yarda babu komai ba ko.!?"
Ta d'ago manyan idanunta ta d'an kalleshi kad'an ta tab'e baki tace "Saboda me.!?" Yace "Bcos that's not ur face before" tace "Uhn.!" Bata sake magana ba,ya kalleta yace "Me yasa ba zaki fad'a min ba.!? Ko har yanzun baki gama sab'awa da ni ba.!?" Ta d'ago ta kalleshi ta kawar da kanta gefe,yace "please Nusrah,ya kamata idan da wani matsalar da kika gani a tare da ni ki sanar da ni,,na fad'a miki ina sonki kuma kin san hakan,me yasa ba zaki aminta da ni ba.!?"
Tayi shiru tana tunani ya sake kallon mood d'inta daya canja lokaci guda yace "talk to me,ina son sanin matsayina a gurin ki,lokaci yana tafiya amma har yanzun baki tab'a furta kina so na ba,,me yasa ba za ki bani goyon baya ba.!? Ina sonki sosai kin sani,I love u with all my heart,ki yarda muyi aure shi ne burina.."
Saurin kallonsa tayi ya gyad'a mata kai da sauri,ta tsaya kallonsa ko k'iftawa babu tana mamakinsa,tashi yayi daga inda yake yayi kneeling a gabanta ya rik'o hannunta yana murzawa,tayi saurin kallonsa jin abunda yake mata tana k'ok'arin kwace hannunta ya damk'e su sosai,da wani shegen voice mai kashe jiki yace "Baby will u marry me.!?" Yana kashe ido,bata san lokacin da ta gyad'a masa kai ba,yayi mata sanyayyan murmushi yace "Thank u baby,, I love u.." Tayi ajiyar zuciya tace "I love u too" wani irin ihun jin dad'i yayi hannunta dake rik'e a nasa ya d'ago ya kai saitin bakinsa,sanyayyan kiss ya shiga jera mata,bata yi k'ok'arin hanashi ba,tana kallo ya bud'e tafin hannunta ya shiga jera mata ruwan kisses yana mata murmushi da zuba mata mahaukatan kalamai masu tsuma zuciya,tayi kasak'e tana sauraronsa,a hankali ya gyara zama yayi flexing legs hannayensa a saman cinyarta kamar zai shige jikinta ya fara bata labarin Mom d'insa da junior siblings d'insa,wasu tayi murmushi wasu kuma tayi yak'e cos tun d'azun ita dai irin kallon da yayi mata ya kashe mata jiki,fiye da rabin abunda Aatif d'in yake fad'a bata jiba hankalinta yayi gaba,ya gaji da mata surutu yana matse hannunta a nasa yace "Baby saura naki labarin nake son ji" ta kalleshi a tsorace tace "Ni.!?" Ya gyad'a mata kai yana kallon idanunta,ta had'iye saliva's da kyar ta fara kame²,yayi murmushi yace "No baby.. Speak well" ta kalleshi ta gyad'a kai a hankali,ta fara magana muryarta tana rawa,ya sake rik'e hannunta da kyau yace "Baby.!" Ta d'aga idonta tana kallonsa,a hankali yayi ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa yace "Na ga alamun baki shirya fad'a ba,mu barshi zuwa wani lokacin" ajiyar zuciya tayi tana lumshe ido,daga haka bata sake magana ba,Aatif yana kallon yadda tayi yace "baby na san kin gaji,ki shiga gida kawai sai mu yi waya" ta gyad'a masa kai a hankali yayi mata sallama yace idan ya je gida zai bata Mom suyi magana,ta kalleshi tace "Da wuri haka.!?" Yace "Ehh! Me zan jira.? Ko so kike nayi sake wani ya riga ni.!?" Ta girgiza masa kai kawai,suka yi sallama ya shiga motarsa ya tafi,ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi,tana juyawa kamar ance ta kallo balcony d'in d'akinsa ta hango shi zaune gefen pool k'afafunsa a cikin ruwan,sanye yake sa towel robe da cup a hannunsa yana sipping,kasa tafiya tayi ta tsaya tana kallon yadda yake komai nasa cikin nutsuwa,kusan mintuna biyar tana ta tsaye a gurin taga ya ajiye cup d'in saman mini table ya mik'e tsaye,threads d'in da yayi bundling ya fara warwarewa,tana nan a tsaye kamar an sassak'a ta ta kasa d'aga k'afa ta bar wajen kamar ance da shi ya d'ago,yana waiwayowa idonsa ya sauka akanta,bai fasa abunda yayi niyya ba duk da irin kallon da take masa ya ajiye rigar a saman madaidaicin gadon dake gurin,daga shi sai nickers ya silale yabi cikin ruwan,wani irin siririyar ajiyar zuciya tayi a hankali tayi blinking idanunta tana kallon wayarta data dawo da ita cikin hayyacinta,dai² kiran ya kusa katsewa sannan ta d'auka ta kai kunnenta tana fad'in
"Assalamu alaikum..!"
Aka amsa daga d'ayan side d'in,jin muryar mace ce ta sake nutsuwa ta gaisheta dan muryar ta nuna babba ce,cikin barkwanci matar ta tambayeta ta san Aatif.!? Tayi murmushi matar tace "Ni ce Mammansa" Nusrah ta sake yin murmushi ba tace komai ba,matar tayi ta mata tambayoyi,da kyar Nusrah ta aro jarumta tayi ta amsa mata,tambayar ta Maman Aatif tayi "Aatif yace min tare kuke da iyayenki a nan k'asar,shin haka ne.!?" Nusrah tace "Ehh Mommy tare muke da familyna" tayi murmushi tace "Hakan tayi kyau sosai,in sha idan Daddy'nsu ya dawo zan sanar da shi komai,za muzo muyi magana da parent d'inki a san da mu,kada wani yayi mana shigar wuri",gaban Nusrah ya fad'i ta daure tace "Toh Mommy,Allah ya kawo ku lafiya",ta amsa sannan suka yi sallama ta bawa Aatif dake kwance a cinyarta waya tace "Son karb'i waya" yayi murmushi yana bud'e lumsassun idanunsa,ya fara kai wayar kunnensa yace "Hello baby.!"
Daga side d'in Nusrah tace "Shi ne kawai sai ka bari Mommy ta fara magana,maimakon kace min zaka bata waya" yayi murmushi yace "No.! Kawai ina son yin surprising naki shi yasa banyi magana ba first" ta tab'e baki kamar yana gabanta tace "Hope ka isa gida lafiya,ya mutanen gida,da Mommy.!?" Yace "Alhamdulillah..! Kowa yana lafiya",tace " Masha Allah",yayi murmushi yace "Kefa.!? Kin shiga gida lafiya.!?" Tayi murmushi tace "Ni ai banyi tafiya ba" yace "kin yi mana,from garden to parlor na san zaifi twenty footstep" tayi y'ar dariya tace "Amma dai ban hau mota ba" yayi mata murmushi yace "duk da haka kin yi baby,ki yarda kawai" tace "Na yarda" yace "Yawwa! Sai anjima za muyi waya.!?" Yayi maganar da sigar tambaya,tace "Allah ya kaimu" yace "Ameen,take cake of ur self for me please" tayi ajiyar zuciya tace "I will in sha Allah" ya mata blowing kiss through phone d'in,tayi dariya mai sauti tace "Baka jin kunyar Mummy ne.!?" Yayi dariya baice komai ba ya katse wayar,murmushi tayi ta lumshe ido ta bud'e hak'oranta a bayyane tana murmushi ta juya ta kallo balcony,zaune ta hango shi a gefen pool jikinsa sai tsiyayar da ruwa yake,ya sunkuya yana ci gaba da d'iban ruwan yana watsawa a jikinsa,wani irin fad'uwa gabanta ya sake da ta kalle shi sosai fuskarsa babu annuri,a hankali k'irjinta yana ci gaba da bugawa kwakwalwarta ta tuno mata abunda Aatif ya fad'a yanzun kafin ya tafi,fargaba da tsoro suka sake kama zuciyarta a hankali ta furta "ta yaya ne zan iya fad'a maka labarina.!? Ta yaya ne zan iya sanar maka wad'annan mutanen ba sune asalin family na ba.!? Da wane bakin zan sanar da kai gaskiyar al'amarina.!?"
Hawaye taji sun fara gangaro mata tunawa da conversation daya faru tsakanin mahaifinta da Nuraz ranar da suka je gidansu,take muryar mahaifinta ta bayyana a kunnenta kamar yanzun ne suke maganar
_"What joy would a father have after his daughter had humiliated him.!? Yarinyar da ta sa k'afa ta fice tsayin wattani biyar ba ta gida,uban daya haifeta bai san ina ta shiga ba,bata tab'a waiwayar gida ba sai yau.. In ur own speculation nake so ka fad'a min,every woman who has been leave their home for a period of time,and u know she's not married,ba kuma ziyara taje gidan yan uwa ba,she has escaped from her home and her destination is unknown,,Then one day sai aka ce maka ta dawo,tsakanin ka da Allah what kind of name community will they call her.!? So i've already decided idan har ni na haifi Nusrah,daga yau na hak'ura da ita a matsayin y'a,thank God i was not alone,da tuni ciwon zuciya ya kama ni"_

Muryar Nuraz ta ji yana bawa Abba'nta amsa _"But Alh i think u know the best of ur daughter's character,,u should not make decisions without investigation,don't ever use what people say's.. Sure sharri suka yi mata,u have to study it carefully,,but now tunda ka yi furucin ka hak'ura da ita i'll go back with her,whenever wants ur daughter come back to u,u can contact us.."_

_"I will never be able to track what already happened."_

_"Of course if u investigate definitely u will find the truth,and u will make sure ur daughter doesn't do what u are talking about,,u know her best,if she does and if she doesn't,u all know by ur self.."_

Maganar Mommy taji a kunnenta cikin wannan hayaniyar nata _"To yace baya buk'atarta shin dole ne sai ya dawo da ita gidan nan.!? Ta bayyana cewa itan fasik'a ce,and we said we removed it from our house.!? Malam ka ga tun da wuri ku tattara ku fita mana a gida,mun yafewa duniya ita,idan ka ji baka iya rik'onta kaima daka d'aukawa kanka wahala kana iya sallamarta tayi gaba,duniya da fad'i duk inda take so zata iya zuwa ta rayu.. Wa ya sani ma ko garin yawon ta kwaso wani mugun ciwon shi yasa ta lallab'a ta dawo gida,shi kenan bamu sani ba tazo d'aya bayan d'aya ta goga mana.! Na tabbatar ruwa baya tsami banza,dole akwai sharrin data k'ullo shi yasa ta dawo.. An yi gadon bak'in hali.."_

_"Ni naga damar cire ta daga jikina babu ruwan Hajiya,saboda haka idan iya wannan maganar ta kawo ku,heard my words,,,wish u could go and leave my house.."_

_"Alh ya kamata kayi tunani dai gudun wata rana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata.!"_

_"There is no thought to waste my time on it,it is a final decision banga dalilin da zaisa nayi nadama ba kuma."_

Maganganun ne suka had'e mata a guri d'aya cikin wani irin yanayi suna sake yi mata amsa kuwwa da k'arfi a cikin kanta,hawaye sun gama wanke mata fuska cikin tsananin damuwa ta kama kanta ta rik'e,ji take kamar zai fashe saboda yadda maganganun mutane ukun suke repeating mata kansu babu sassauci,durk'usawa tayi saurin yi tayi kneeling saman k'afarta cikin tsananin damuwar da bata san mene ne zai iya faruwa a gaba ba ta fasa k'ara mai ban tsoro.....


*#thank u my people,u don't worry about it,as u express ur concerns in sha Allah i'll not be ashamed of u,it has already passed,so let by gone be by gone.. I love u all.♥*


#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

  
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

 
Pᴀɢᴇ 21.
#Mɪɴᴅꜱᴇᴛ

       Bayan fitar Hajiyarsa a apartment d'in tunani yayi ta yi yana jin yadda zuciyarsa tayi masa nauyi saboda damuwa,yayi shiru shi kad'ai kamar wanda aka tsikara ya kira Clark,ya shigo cikin girmamawa ya ce "Here i am sir" RAFEEK ya kalleshi idanunsa sun k'ank'ance sun canja launi yace "Ina report na binciken dana sa kayi min.!?" Clark yayi ajiyar zuciya yayi tunanin wani abune daban yasa boss d'in kiransa,yace "Sir ana nan ana binciken,but kamar yadda ka buk'ata,duk binciken mu ya tabbatar mana babu wani namiji a gidan sai wannan likitan mahaukatan" Rafeek ya kalleshi cike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login