Showing 3001 words to 6000 words out of 26231 words
dashi wanda bazaka ta'ba iya tantance kona menene ba,lokaci guda tsanar yarinyar da kiyayyarta ya'kara samun gindin zama a zuciyarta
Kama hannun anee tayi tazaunar akan 1seater, ranta matuka ajagule yake.aneesa dai aneesa tata y'ar gatanta da batasan kwa'baba bare kyara itace yarinya karama tama wannan lahani?
Taso kwarae awajen ta lakad'awa zahra dan karen duka.Amma kuma data tuno insun bugeta zasu tonawa Kansu asiri yasakata yin murmushin takaici ta bayan gida ya kaamata ta'bulloma yarinyar nan.don taga alamar lallai wankin hula yanason kai y'an maza dare.
Aneesa kuwa ganin mum batace komai ba yasakata sake hasala tamike tana kundume-kundumen zagin saitaga bayan zahra,Dr.aysherh tana hanata amma inaaa kitchen tanufa tararumo wu'ka tayo kan zahra dake tsaye gefe ko gezau batayi ba saima sake kunburi datakeyi kamar kububuwa.
Da gudu Dr.aysheeh ta rike anee tasoma mata fad'a"au kinason tona mana asirine aneesa? Kilumama y'ar mutane wu'ka kibarmu da tsugunne tashi da alkalai? To banason raahin hankali kin gannin nan."
"Shige muje..."
Tafad'a tana kama hannun aneen da idanunta ke fitar da ruwan hawaye.
Bedroom suka shige har saida Dr.aysherh ta maida kofar ta murza key kafin tace"zauna inbaki extra care kafin muga abinyi".
Y'an gwaje-gwaje tayima anee tasamata magani a Inda zahra ta cijeta sannan taja hannunta suka zauna tasoma tambayar abunda yahadata da zahran.
Anee bata rufa mata komi ba ta sanar da'ita yanda sukayi.
Murmushi Dr.tayi kafin tace"lallai aneesa ada ina tunanin nahaifi jaruma jajurtatta dazata tsaya da kafafunta ko bayan babuni,amma ayau na tabbatar haryau *igiyar 'kuruciya* tana jani injaka dake.har yaushene zaki biyema yarinyar da batada hankali ki hada jiki da ita? Kada kimanta itaafa renon tuwon dawa miyar kuka ce,kekuwa renon cake da ice-cream ce bazaki taba hada jikinki danata a mazauni d'aya ba.kina ganinta yarunya wannan me zubin 'kartan koni sainayi da gaske in cimmata
Sannan shi zama da kishiya Aida hila da munafurci akeyin galaba,zaunawa zakiyi kisiye zuciyar kowa a gidannan da kyautatawa shi kanshi isha'q din ki zame masa chewing gum kitakura duk wata hanya dazata sadashi da had'uwa da wannan akuyar yarinyar itakuma a gaban kowa kijata a jikinki tayanda duk me kikace tayi baza'a karyata ba.
Amma daga karkashin kasa zataci ubanta,saita bar gidannan da kafafunta.
Ajiyar zuciya anee ta sauke itafa duk tama manta da makaman yakin data tanada don d'ana bom dinta azuciyar isha'q tazauna yarinya karama na shirin dasamata hawan jini.
Kwafa tayi da shu'umin murmushi lokaci guda ta tuno shawarar nafee kawarta batasan lokacin data fashe da dariya ba.
"Don't worry mum I will hndle this prblms with my hand"
Murmushi Dr.tayi "yh I know, I will thrust you my dear."
Cafewa sukayi kamar kawaye,
Sai alokacin anee tasamu natsuwar zuciya.
Da taimakon mum dunta suka gyara gidan saika rantse wani Abu na 'barna bai faruba,wanka tasoma fesawa duk kuwa da azabar da kan nonon yake mata lokacin da ruwa ya ta'bashi aranta tana ayyana miyagun aguguwan da zata aikatama zahra ada batasan ta tsani yarinyar ba amma yazuwa yanzu tariga da ta hakikancema kanta lallai kiyayyar Zarah me karfi ce aranta.
Doguwar riga ta shadda ta zuba ta kashe d'auri abunta tayi kyau kwarai dinkin yadace da yanayin jikinta mara kiba sosai.
Sai kusan 4:pm mum din tata tawuce bayan ta'ajiyemata maganin mata kala-kala nasha dana shafawa da gargadin tadena wasa dasu don dasune ake juya kan nimiji dan ubanshi ko wanene.
Anee aranta cewa take"inako zanyi wasa da damata ai damara yanzu na daura shege ka fasa.
Kitchen takoma tasake shirya tuwon semovita da miyar egusi,Wanda tasan gwaggo rabi tana matukar so da tsimakon inna delu.
Don dai on her own idea bazata iya girki mai ma'ana haka ba.
Gefe guda ferfesun naman sane dayaji albasa da spices yana tashin kamshi sai macaroni data sake gyarawa ta hada lemon kwakwa da dabino tagama komai with tym.
Zaunawa tayi tasake tsular uwar kwalliya cikin very cotton na lallausan gown din material, tana mutsuka humra a hannayenta tajiyo horn din Dr.rukayya saida ta bankama kofar harara tamike da azama kallabi a hannu tanufi get din.
Alokacin tuni tagama parking a parking loat,anee kam tana zuwa hanan tacafe sama tana juyawa tana dariya da lakatar hancinta"y'ar mumy yau ina kika 'boye kikamun wayo baki dawo da wuri ba?"
Tafad'a tana dariya da satar kallon fuskar Dr.Rukayya don ganin yanayin karbuwar sabon salon nata.
Kamar yanda ko ta zatan hakance ta tabbata don murmuahi mumyn tayi tana bada amsa"office tasaka driver yakaita wai yau wajena zata wuni."
Anee tasake dariya tarike hannun hanan tahad'a da hand bag din mummyn suka jero atare kamar 'kawaye,duk da mummy tana korafin anee tabata jakar kada kaya sumata yawa,kiyawa tayi saima sake tsokano hanan take da zance"autar mummy gobe kada kibi mum asibiti zamuje saloon mugyara kanmu da farcenmu and amaki wani hadadden style na kitso yana a wayata muje kigani yanada kyau Sosai."
Dad'i yakashe hanan don akwaita dason kwalliya tasoma murna Dr.ru'kayyama farin ciki yagama cikata.
Saida taraka mum har part dinta data sake gyarawa ta feshe da air freshener takama hannun hanan sukabar d'akin bayan ta dauki kayan dazata canja acewarta subar Mummy tahuta takwaso gajiyar office.
Dr.ru'kayya tayita samata albarka,sam tama manta da wata zahra agidan abunda bata ta'ba yiba kuwa,don ka'ida kullum tadawo saita tambayi ina zshran amma yau rana d'aya kissar anee tasaka tama manta da 'kurar data kwaso wata wai ita zahra.
Hmm....
Anee kam jin har tabar part din mum bata tambayi zahra ba ranta'kal tafara d'ana makaminta na farko kenan.
Dakanta tahad'ama hanan ruwa a toilet d'inta tayi mata wanka duk da hanan tana no'kewa itafa tafara zama ammata🤪.
Anee kam baki ta ta'be yanda kirjin hanan yake kamar shafen siminti bata raba d'aya biyu haaka na zahra yake,kai namiji barshi da jaraba yo inba jarababa anan har kace kayi aure?
Tsakin dabatasan yafito ba taja"mtsww"
Dasauri hanan tace"Anty lfy?"
Shafa kanta tayi"zuciya ke tashi kanwata.'
"Eyya sorry anti let me tell mum"
"No!"
Am ok now"
Anee tabata amsa tana gyara mata zaman top din jikinta.
Fira tadinga jan hanan wanda haakan ya d'aukemata kewar zahra batamako tambayi ina zahra dinba.
Sai ana sallar magrib muryar gwaggo rabi tasoma karad"e gidan da sallama.
Jin shiru yasa tasoma tijarar tata"wai halan mutan gidan kuramene,ko kafurci ya motsane Baku amsa sallama ".
Dr.Rukayya dake sallah har kosawa tayi ta'idar don tsoron jarabar gwaggo akanta zata 'kare.
Typing is not easy wlh.
To be continue✍🏽
[3/15, 8:40 AM] 0mmer Farouk: [12/20, 8:22 AM] Real Mum Meenat😍: *MIJIN 'KWAILA....2*🤦🏽♀
*chapter 5*
*by Maman meenat*
*Inayinku over y'an gaban goshin mum meenat do or die we are 2gether for ever insha Allah.always ur part of me ..*
*my die fans...hajara ghandi,sweet mum janar...my miss Ayush...jamila Muhammad...Mr's hamza....kai kunada yawafa nasan yawanku yawuce lissafin Alawee😍*
*My Qawa ta Amana,kawar arziki kawar Albarka farin wata shakallo ta Maman meenat me taqama da ayar Allah. .kinyi naki kinyi na raggo yanda kika ziyarci gidan mum meenat saboda 'Kauna Allah yabani ikon zuwa kano nakwaso shockie na 'kannin shaheed😜FATIMA ABUBAKAR MAMAN SHAHEED (KUSKURE)writer,mum meenat love you and respect to you over wlh so much luv u..*❤.
Jin maganar gwaggo rabi ya tilasta fito da aneesa tasaki murmushin ganin gwaggon,itama gwaggo rabin murmushi tasaki tana tambayar "y'ar nan kina ciki dama?"
Anee tasake sakin karamar dariya,"ina ciki Granny kwalliya nakeyi."
Tafad'a da jujjuya idanuwa.
Baki gwaggo rabi ta mere dacewa"oh sabon salo wai miya d'uwawu 'kunshi,wata kazar ce kuma gurani?(Granny) "
Anee ta fashe da Dariya sosai tace "kai don Allah gwaggo I mean kaka fa kenan."
Tsaki gwaggo rabi taja tayi gaba tana fad'in "yau dai nalura wani sabon kad'afiri kika tsiro dashi,ninan kar nake kallon kowa."
Tayi 'bangarenta abunta bayan tazabgama gefen zahra harara.
Oganniya zahra wacce taci kukanta tabama uku lada bayan shigewar Anee daki koda wasa takaici baibarta sake tunanin komawa kitchen din karo abunci ba,itama dakinta tanufa kangado tafad"a tasaki kuka sosai kewar ummanta da baba kai harma da kawayenta su ummilolo da uwande tagama cika ranta.
Idan har a taata haukar takurata Anee zataci gaba dayi toko lallai bazata jureba,gida zata koma ita dama bawani dad'in zaman gidan takeji ba.
Yaushe rabonta dazuwa tonon fad'a satar kifi da tusa wa me awara?
Tsaki taja,shikenan su ummilolo sunmata wayo sunata zuwa yawonsu itako anmata Katanga bata fita ko ina.
Yau kam alwashi tasha gida zata kwana,sam dad'in benen ma tayafe bataso.wurin umma zata koma.
Jakarta tafito tasoma yayimar kaya tana watsawa ciki,saida ta tabbata tagama cika jakar ta'ajiye agefe guda yau kam sai gida!take fada aranta.
Daga zaman shiru kuma saita bude wardrobe kukar 'bahe ta d'ebo ta hada da sikari a kofi ta kad'a tasoma zuqa tana y'an wakokinta hawaye duk sun bushe a fuska.
Tunin duniya ta manta dawata wai ita Anee.
Da kofin korbebe a hannu bacci yayi a won gaba da ita.
Kamar koda yaushe yauma d'in sai wajen 7:30pm yashigo gidan da brief case a hannunsa agajiye kwarae yake sosai.
Sallama yayi falon tsit! Babu kowa sai kamshin turare da karar A.C,ahankali yake takawa har ya karaso inda tafkeken hoton nata yamamaye gefen kusurwar da aka makalashin.
Hannunta na dama sa'kale cikin nashi,saina hagun tad'aga wani card da alama na shedar kammala karatune don gown din dake jikinta ta shaida hakan.
Tayi matu'kar kyau har dai ko yaushe bakinta da murmushi kumatunnan a lo'be rolling daya zame mata jiki yana akanta.
Gabanshi yaci gaba da fad'uwa,sai yake ganin kamar tana rayene.wai sai yaushe zaidena kewar zahransa ne?
Sai yaushe ne zuciyarahi zata dena bugawa a duk second na kallonshi da ita?
Shafa gefen fuskarta yayi,yanasonta yanason komai nata kai! Yasaalam!
Tabbas soyayya ba karya bace.
Jingina yayi a jikin bangon idanunshi a numshe baisan yanda zai kwatanta meyakeji a ranshi ba.
Kamshin turaren Anee me fisgar hankali ya bud'e kafofin hancinshi,kamar kada ya kalleta amma bazai iyaba.
A kasalance ya bud'e idanun yazube akan fuskarta takuwa haskeshi da murmushinta.
Ta juyar dakai,kawai.
"Wlcm back," tafada da sigar yaudara dik da har a ranta taji kishin hoton zahra datakama yana kallo,tarasa jarabar daya nacenawa a wannan bakar matar me d'agggen hanci.
Bai iya bata amsaba sai sake lafewa dayayi ajikin bangon dakin.
Ta danne takaicinta,tahanyar sa'ka yatsunta a cikin nashi.
"Damuwa..damuwa bata haifar dakomai sai nadama my sheyq,Allah daya amsa zahra yayi replacing dinta da biyu fa.bai kamata kayima Allah butulci ba,kasaki ranka ka amshi jarabawar Allah ko late zahra tasamu takwanta makwancinta a cikin salama.domin lallai tasan ruhin masoyinta yana acikin walwala."
Yanda take maganar acikin kunnenshi da salonta yasakashi sauraronta,kuma tabbas tayi nasarar tankwaro zuciyarshi cikin ruwan sanyi.
Duk da be tankamata ba amma baimata shamaki daga jagorar datayi mashi tazuwa dakin taba.
Dakanta ta temakamishi wajen rage kayan jikinshi,duk da aranta tana ayyana anya zata iya wannan aikin data fara kuwa? Tun ba'aje ko'inaba duk jikinta ciwo yake.
Ganin tana niyyar rakoahi toilet yasakashi bata umarnin fito mashi da kayan dazai saka
Bahka taso ba,amma baamatsala.
[12/20, 8:46 AM] Real Mum Meenat😍: Kaya marasa nauyi ta fitar mashi,takoma tagyara dining.
Saida yagama shirinsa tsaf suka fito atare,sunyi kyau dukansu kyawawane na kwatance.
Kusan duka gidan sun hallara a dining dinne inka dauke zahra wacce take d'aki tana buga game din Mario.
Sam batamasan tym yatafi haka ba,don tun farkawarta wanka kawai tayi da sallah tasoma game dinta.
Cike da kissa Anee tasoma serving mummy abincin abunda bata tabayiba a tsawon zamanta gidan,kai ba ishaq mummy da gwaggo rabi ba hatta hanan tana mamakin canjawar Anee a lokaci guda haka.
Isha'q ne yami'ke da sauri, bayan ajiye spoon din dayake kokarin kaiwa baki.
Duka da idanu suka bishi sai gwaggo rabi datayi kokarin watsamar tambayar"oh ni rabi! Ina kuma zakaje daga fara cin abincinka sai kace me cutar d'an kanoma?"
Batare daya juyo ba yabata amsa"banga zahra ba tunda nadawo."
Aneesa ta had'e rai sosai,tare da ajiye spoon din dayake hannunta.tana sonjin me wani zai furta a cikinsu.
Gwaggo rabi ta'be baki tayi taci gaba da cin abincinta.
Yayinda mummy tace"lallai nima yau banji duriyarta ba tun dawowata."
Takaici yadad'a 'kule Anee.
Tana bisa gado tajuyama kofa baya,ita kadai ke surutunta da game tana dariya.
Sweet cotton gown ce ajikinta talafe a lukutin jikinta sosai,kannan marason kallabi yatashi fiiiiya abayanta.
Fuskarta tayi haske,kila hakan yanada nasaba da ynda batayi kwalliyar taba yau tatsaya iyakar Vaseline kawai.
Jitayi an rufe mata idanu tabaya,kyalkyalewa tayi da dariya dacewa"nasan hanan ce,wooyi na ganota."
Jin shiru yasaka tasoma fad'in"dallah bud'eni,ainasan kece."
Numfashin mutum taji yana sauka a saitin wuyanta da sauri-da sauri.
Tuni cikinta yabada "quuuuilulii"
Yage baki tayi iyakar karfinta daniyyar zubduma ihu taji ya rufe mata baki yana dariya.
.
Bude idanuwa tayi ganin isha'q yasakata mi'kewa da fashewa da kukan takaici ta rarumo pillon dake kan gado ta jefa mashi.
Kaucewa yayi yana dariya dayimata gwalo.
Tasake hassala wannan karon d'auko filon tayi tabishi aguje tana kuka,"wlh Sena rama yaro ban yarda."
Shiko dariya yake dacewa"cab! Asheko zaki rame😜yana mata gwalo."
Binsa tayi a guje suka nufi falon kasa yana dariya tana kuka.
Anee dake zaune sai juya cokali takeyi tama gaza gane a duniyar datake ayanzu.
Kusan 5mns daga kiran zahra ba zahra ba isha'q?
Badon kada tabata rawarta da tsalle ba dataje anyi duka mai yuwuwa Sam bamazata jura ba.
Zuciyarta na ayyana mata wama yasan mesukeyi a d'akin kai namiji munafuki tafada aranta zuciyarta na suya.
Kamar daga sama suka ganshi ya runtumo a guje yana haki da dariya ga zahra da katon filo a hannu tana biye dashi.
To be continued✍🏽
[3/15, 8:40 AM] 0mmer Farouk: *MIJIN 'KWAILA...2*
*Chapter 6*
*by Maman Meenat*
*Maman Shaheed tawa,baki baya iya furta girman matsayinki gareni.Ana'uhubbukki fisabilillah*👌🏼
*One luv hajara ghandy❤*
*Kuyi hakurin jina shiru kwana 2,matsaloline sukasha 'karfina.Adaitaman Afuwa filis*👌🏼
Runtse idanuwa anee tayi zuciyarta na suya kamar zata tsaga kirjinta ta fito.
Dasauri Dr.rukayya ta kauda kanta kamar bataga mesuke aikatawa ba.
Gwaggo rabi madai a wannan gabar kawar da nata kan tayi,don ba shirginta bane.
Oganniya anee dai itace tami'ke fuuuu tanufi part dinta ranta yana mata zafi tare da suya.
Babuma wanda yakula da tashinta,ishaq dayayi masauki da dining chair yana sauke numfashi tare da d'aga hannu alamar sallamawa yana dariya.
Itama zahran dariya take sosai,tayasar da filon 'kasa tana cewa "matsoraci kawai"
Dariya sukasa duka hada hanan suka had'a hannayensu waje guda a dunqule(boxer). Haka sukeyi idan sukai abun gwaninta insunajin nishad'i.
Agurguje dai😍
Yanayi yakan canja tattare da abubuwa masu damar gaske wasu mukan gansu a zahirance yayinda wasu a badini sukan faru
Irin wannan wulkitawar yanayin da sannu -sannu wanda hausawa sukance jariri angone, ahakanne rayuwa kaf tasauya a wannan babin.
Wasu y'an mata ne zaune bisa wani dutse karkashin bishiyar mangwaro da inuwarta ta rinjayi girmanta.
Cake ne da lemon Cway a hannun kowaccensu ahankali suke ci da alama kuma magana me muhimmanci suke tattaunawa a tsakaninsu.
Farar wadda tadire lemon hannunta tadubi y'ar bakar me lukutin jiki tace"nadai gayamaki haba lokaci yayi dazaki gane kin girma yanzu fa ba daba bane ba."
Murmushi d'ayar tayi dacewa"nifa sweety kingaza fahimtanane Allah kunya nakeji haba! Wai kawai sai awani ganni da breziya.taafada tana kulle idanuwa.
Tsaki deeja tayi"mtsww kada agakki da breziya,akama ganki da nono bare breziya,ni wlh kinaban mamaki kwarae zahra saikace baki waye ba.ke gaki da afkin nashanu amma kice bazakisa bra ba haba wannan ma aibada kaine."
Ta'kare maganar tana hararar zahra dake dariya kasa-kasa don tasan takai aminiyar tata bango .
Jaka deeja tazuge tafiddo braziers masu kyau guda uku tace"gasunan da ummi taje Dubai tasawoman su guda 6 nazabo maki uku aciki kuma Allah inbaki sakaba kinemi wata kawar baniba,kinasa kowanne banza yana hadiye maki yawu haka kawai."
Murmushi zahra tayi dajin rigimar kawarta,amsa tayi tana godiya itakanta tayaba kyan kayan sun mugun haduwa.
Turasu tayi ajaka tana duba agogon hannunta"yakamata mushiga class kada musake wani laifin.
Tafada tana mikewa.
Deejama tami'ke tana fadin "bawaninan ainagano auncle bashir sonki yakeyi zahra."
Idanu zahra ta fiddo aranta tace"da Auren nawa?"
Amma sanin bawanda yasan tanada aure yasata dariya tace"yanada aiki,donni sainayi digiri harda digirgir.
."
Deeja tace"cab!aahakan"?
"Ahakan fa" zahra tabata ansa tana murgud'a mata baki.
Tsaye suke bakin get din makarantar students ne mafi yawanci daukarsu ake a mota kasancewar makarantar ta y'ayan masu dashine.
Zahra da deeja suma agefe jefi-jefi suna taba fira mafi yawanci akan karatunsu ne.
Zahra dake kange fuskarta don yanda rana ta gallabeta tadubi deeja dacewa"sweety Allah zanhau adaidaita nasoma gajiya da ranarnan tana gasani dayawa fa".
Yanda tayi maganar a shagwabe yasaka deeja harararta tace"to aysaiki bari saurayinki yazo kyamashi wannan shagwa'bar amma bani ba."
Zahra tayi tsaki"matsala gareki kamar gidan haya ...."
Duk suka dara atare,tsayuwar wata zilleliyar mota agabansu tasaka zahra had'iye miyau jikake mu'kut
Deeja kam cewa tayi"sweety anacewa end of discussion, yau kuma ga never discussion wagga car taci uwar haduwa...haduwama dakanta dataganta saida tazagi uwarta.."
Dariyar da zahra ke dannewa ta kufce,tace"shegiya naira!rabbi kabamu ko'a kiyama."
Kokarin kawar dakai sukayi saidai agefe santin motar sukeyi,bama su kadai ba hatta y'an mata da samari students dabasu gama watsewa ba idanun kowa yana akan motar ne.
Burin kowa yaga waye mamallakin motar wakuma akazo d'auka.
Kusan 3mins ba alamar nacikin motar zaifuto hakan yasaka zahra Jan tsaki,tasoma tsaida adai-daita tana mitar"mungode at last dai munkashe kwarkwatar idanu dama nunamana mota kazoyi.."
Taci gaba da sama adai-daita hannu abunta.
"Wooow nice looking, mamallakin motar uazarta motar haduwa....zahra...zhhhh"
Sauran maganar ta makale abakinta ganin yasoma doso inda suke, saita kanta tasomayi tana gyara zaman sight bag dinta.
Zahra kam hankalinta baya wajen,har saida ya karaso gab dasu.kanshim turaren dabazata iya mantawa dashi ba tsawon rayuwarta ya bugi hancinta.
Ahankali tajuyo da fuskarta,jitayi kafafunta suna kokarin gaza daukarta,kasa furta komai tayi sai zuba mashi idanuwa datayi takasa koda kyakyawan motsi.
Shima kallonta yakeyi,zahranshi haka? For 3years zahranshi tagirma har haka ya'elahe....
Ganin sun zubama juna ido yasa deeja cewa"yadai besty kinsanshi ne?"
Tambayar tazoma zahra abazata,tasoma sosa kai"amm..yaaa...yaaa.....
Isha'q nefa besty"
Ita kanta tayi mamakin yanda tayi furucin.
Murmushi deeja tayi tasoma gaidashi,ya'amsa da tambayarta ya karatu yanayi yana kallon zahra da mamakin girmanta da canjawarta.
Itama satar kallonshi takeyi aranta tana ayyana lallai turai ta amshi yaa isha'q yasake zama wani giant dashi hutu ya ratsa ko'ina na jikinshi.
Aranta tace koya Anty anee takoma yanzu?
Dasauri takauda tunanin aranta don haka kawai taji ranta ya sosu.
Mota yanuna mata,alokacin har anzo daukar deeja tamasu sallama da shelantama zahra saita kirata awaya.
Kamar wadda kwai ya fashewa take takawa jitake kamar bakasa take takawa ba.
Tun daga inda suke taga motar tana bud'e kanta awani irin a slow dinnan.
Caiii. ..Zahra kam bata kara sakankancewa da iya shegen nasara ba saida tajita luntsum akan sitter yasalam!
Idanba kauyanci taso yiba jitayi motar harwani shillata takeyi,bayaga laushi da kamshi da sanyin Ac dayaso zautata😜 .
*2be continue✍🏽*
[3/15, 8:40 AM] 0mmer Farouk: *MIJIN 'KWAILA..2*
*Chapter 7*
*By Maman Meenat*
Zagayowa yayi yazauna mazaunin direba,yayinda zahra tasake takurewa gefe guda itakanta tagaza tantance dalili kokuma hujjar dayasaka tsananin kunyar yaa isha'q takeyi har haka.
"Maa princess, wanann kunyar duk tawace?"tura baki tayi gaba tana kauda kai gefe.
Sake kallonta yayi yana dad'a mamakin wai zahranshi ce tagirma haka acikin abunda baigaza shekaru uku ba,haka kawai yakejin zallar nishad'i yana zagaye dukkanin gabobin jikinshi.
Dan rausayar dakai