Showing 24001 words to 26231 words out of 26231 words

Chapter 9 - Mijin Kwaila book 2

28 Aug 2024

10052

zurarar da hawayen tausayin Zahra gefe guda na zuciyarshi yama rasa yanda zai iya fasalta kiyayyar dayake yiwa Anee.

''Meya jaza hakan?''
Shine tambayar da mummy ta watsa mashi batare data kalli kwayar idanunshi ba,kanta yana akan paper din datake rubutu akai.

''She trying to kill her.''
Yabata amsa shima idanuwan nashi agefe yana hasaso irin rashin mutuncin dazai shukama Anee.

''Who?''mummy tasake tambaya awannan lokacin tamayar da hankalinta kacokan kanshi ne.

''Anee,tadade tana ambata kisan yarinyar nan,Amma yaukam tasamu dama akanta.''

Ajiyar zuciya mummy tasaki Ahankali cike da natsuwa da kamala ta'ajiye Alkalamin rubutun dake hannunta tahade duka hannayen nata waje guda akan teburin dake gabanta tasoma fadin''Ta inda akahau tanan ake sauka ishaq,wannan magana za'ayitane agaban mahaifinka,gwaggo rabi wacce itace ta kulla komai sannan da ita mahaifiyar Aneesan dama yayanka wanda yake tafe ayau dinnan shida iyalanshi.

Dasauri ya kalleta duk da yana cikin tashin hankali saida yace''but he surprising me mum.''

Murmushin dole tasaki.
Kafin tace''Bana bukatar kacema Anee komai amma zuwa gobe da ikon Allah kowa zai hallara sai ayita takare.
Gyada kai yayi kawai.
Daga haka yamike don zuwa duba jikin Zahran tana ayanda take baccin da aka sakata nadole ke dawainiya da ita dagani kasan a wahalce take baccin.

★★★★★★★★★
Anee na ganin ficewar ishaq itama bata tsayaba don duk anata zaton Zahra ta mutu,dan haka agurguje ta hada yanata-yanata,motarta tafada tafice aguje hankalinta amatukar tashe yake.

Gidan mahaifiyarta tafara zuwa takumayi sa'a morning tayi dan haka tana gida.
Kwance ta isketa tana amsa waya da alama tanajin dadin firar Anee tashigo aguje tana waige-waige kamar wacce aka biyo aguje.Dr aysherh tamike bayan datse kiran tariketa tana fadin''Ke lafiya,keda waye haka kika shigomun gida kamar wacce aka biyo.Lfiya meyake faruwa.''

Kuka Anee tasaki tanafadin''Nashiga uku na mum namutu nabani yazanyu ina zansaka rayuwata''
''Ke banason shashanci kinji kiman bayanin abinda yake faruwa kin tsaya kina kirama kanki masifa da bala'i haka kawai.''
Dr Ayaherh tayi furucin kanta amatukar daure yake.

''Na kasheta mummy nakashe ta.

''Wakika kashe,ban fahimceki ba.''
Ayshern tafada hankali amatukar tashe.

''Zahra mummy,zuciya da Sharrin kawa yakaini yabaroni,gashi tun ba'aje ko inaba nadama tasoma bibiyar aikina.''

Tafada tana sake fashe da matsanancin kuka.

jabar dr.Aysherh tazauna hannu bisa kai tace '' Shine babban *kuskuren* dakika tafka arayuwa wanda ninan ban isa inhana ayanke hukunci akan kinba.meya aikkeki aikata danyen hukunci haka na shiga uku ni A'isha nayi nadamar gurbata tarbiyyarki danayi Aneesa ban taba cutar dawata raiba gashi ke kinada hakkin rai akanki meya kaiki.''

Cikin hawaye Anee tace''mummy sharrin Nafee ne itace takaini tabaro.''

''Nafee?''mummy ta mbata bayan sharatawa Anee wani Azababben mari.

manage🤒.

_*ROMANTIC WRITER'S ASSO*_💥

_We are d stars,keep shining Always_💥


*MIJIN 'KWAILA...2*



Chapter 27.

by maman meenat.


Kuka sosai Anee takeyi sai ayanzu ne takejin zazzafar soyayyar ishaq tana sake ninkaya acikin zuciyarta.

cikin hawaye take magana''Dan Allah mummy kiyafeni,abaya kinyi iya naki yin akan narabu da nafee ban gane cewar itadin makiyiyata bace sai yau nayi matukar da nasanin ta arayuwata.

kallon uku saura kwata Aysherh tamata tajuya ranta ajagule yake.

Bata kai ga shiga bedroom data nufaba wayarta tasoma tsuwa juyowa tayi ahankali takai hannu ta dauki wayar saikuma ta tsurama screen din wayar idanuwa ganin sunan dr.rukayya ajiki baro baro.
Kasa tsaida shawarar dauka ko akasin hakan tayi da zurfin tunani har wayar ta tsinke wani kiran yasake shigowa.

Dakyar ta'iya kangata akunne muryarta a sanyaye bazaka taba cewa tatan bace tayi sallama,ganata mamakin a tausashen dr.rukayya ta amsa tdora da neman zuwa gidanta ga dt.Aysherh inda hali harma da Aneen suzo tare.

Batare da dogon nazari ba dr.Aysherh ta amsa da cewar suna tafen zuwa dare kamar yanda mumnyn ta bukata.

Anee dai duk jikinta yagama sanyi kalau.
Ajikinta takejin lallai ranar rabuwarsu da ishaq ce tazo.
Hawaye sunki su yanke mata acikin idanuwanta tayi matukar danasani mara amfani.

★★★★★★★★
'Karfe takwas dai-dai falon yagama daukar duk wani mai ruwa da tsaki akan issue din zahra da anee kama daga mahaifanna Zahra zuwa na anee gwaggo rabi mummy dady saikuma uban gayya ishaq wanda yake kasa durkushe saidai kallo guda zakamashi ka tabbatar da bacin ran dayake ciki yanda idanunsa suka gama rinewa jiniyar kanshi duk ta mimmike.
Anee ma adurkushen take tana zubar da hawaye.

Gwaggo rabi dake hakimce bisa 1seater tanama Anee kallon uku kwata tagaza hakuri tasoma yadama anee bakaken maganganu''Yo aidama nidaga ganin dangin jaraba nasan bazasukai labari ba,inba haka baace mace shekara shida ko kashi mai nauyi bata tabayiba ballantana nishin nakuda.sai tsabar jaraba da masifa dakika dorawa kanki,yar yarinya wato kinga zata haifamun jikoki kike bakin ciki da ita,to ta Allah ba taki ba.mun rigaku munce Allah.


Babane yace''ni hjy inaga duka wannan bata tasoba,kaddara duka bata wuce lokacinta kuma Alhamdulilah zahra tana cikin koshin lafiya muna murna da hakan sai fatan Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba kawai,sannan kee anisa yajuya da akalar maganar tashi akanta.

''Amatsayin wanda ya haifi y'a kamarki koma wacce tafiki nake baki shawara bawai amatsayin uban kishiya ba,Abunda nakeson sanar maki shine itafa rayuwa gaba dayanta ana ginatane akan tubalin hakuri tattare da nasara,dukkan matan duniya da'ace zasu fahimci menene aure yake nufi toda ansamu saukin zafafa kishi,kishiya yar'uwar rufin asiri ce ba abar kyama ko tsangwama ba.bazaki taba gane hakan ba sai tamaki rana.Kodon gaba ki kyautata mu'amalarki da jama'a tofa kowa zai soki .''

Murya cike da nadama Anee tace''wlh Abba nayi nadama nayi danasani,bana fatan sharrin kawa dana shaidan su sake tasiri akaina.
Inamai rokon mijina da zahra dasu yafemun su yafeni nayi nadama.


Gwaggo ta amshe''Bakimayi nadama ba ai sai an hadaki da hukuma kuma isiyaku ya ambatamaki saki uku ananne zakiyi nadama.

Anee takuma fashewa da kuka ta rarrafa da niyyar rike kafar gwaggon saidai cak ta janye kafafunta''kada ki jazamun masifa,ki tabani kisamu hanyar hallakani.


Dakyar Daddy da Abba suka taushi gwaggo rabi tadena jifar Anee da mugayen kalamai.

Nasiha sosai Abba yayima Aneen dakuma Zahra wacce aka kawo a lokacin,tamurmure dama matsalar sarkewar numfashi ce,saidai rashin kwarin jiki.
Nasihar Abba tasa kusan jikin kowa awajen yayi sanyi tunma ba Anee da dr.Aysherh ba.
Daga karshe Umma da kanta tayita rokon Alfarmar Ishaq daya yafema anee kuskurenta ya janye saki dayan daya ambata agareta.

Duk yanda Ishaq yakejin nauyin Umma kasa amincewa da bukatar da tazo da ita yayi.

Mummy tasaka baki tana cewa''Nifa anawa ganin yakamata ka yafemata son kagane Allah baya barin zalunci da Azzalumai,Nasan wacece Ayshar nasan nufinsu akanmu Amma Allah yagama maka gata yabaka zahra ya mallaka maka ita sannan yakara maka kyautar da babu mahalukin daya isa yabaka inba kaiba.kasani a lokacin da mukaima zahra scaining dan tantance babu sauran matsala a tattare da ita alokacin naci karo da Abunda ya gogemun duk wata damuwata aduniya wato zahra tana dauke da gudan jininka ishaq....''Daga Zahra har ishaq mutuwar zaune sukayi yayinda ishaq yakasa dauke idanunsa akan zahra wacce tsabar kunya yasakata kwasawa aguje,gwaggo rabi ta rangada guda tana fadin Ahayye kwaila tayi abun mata.

Hawaye suka cika idanuwan dr.rukayya tace ''Adaidai wannan gabar zan bankada wani sirri wanda naboye tsawon shekaru goma.
Dangane da late Zahra,wacce tarasu saura kwana shidda bikinsu da ishaq...Gaba daya su anee suka zuba mata idanuwa cike da tashin hankali.

mummy tasoma da aranar da Zahra ta tashi da ciwon ciki a tsakiyar dare,nagagara samun natsuwa wannan tasakani debo kayan aiki batare da sanin kowa ba nasoma mata gwaje-gwaje gwajin farko yanuna anmata allurar gubane wanda zai hallakata cikin awannin dabasu shige uku ba.

Hakan yasakani iyakar kokarina wajen ceto ratuwarta kuma falillahil hamdu,nasamu nasarar cetowar saidai nagza samun natsuwa tun zahra bata gama watsakewa ba nasoma tambayar wanda yamata wannan aika aikar.
Nasha tsantsar mamakin jin cewar dr.Aysherh kece kika saka akayima diyata zahra wannan muggun abun.



Gaba daya falon suka dauki salati.
mummy taci gaba.''Mun tattauna da Zahra sosai akan yuwuwar aurenta da ishaq duk da yanda suke son juna,nunawa tayi zata hakura dashi saboda tsaron rayuwarta.
Hakan yasaka namata allurar dogon suma,amatsayin ta mace wanda bayan awanni nasaka aka tonota.

Screat waje na ajiyeta harta gama jinyarta daga karshe na turata can wajen yayanta a amurka inda acan tayi aure harda yaranta guda biyu.

Ishaq kasa dauke idanuwanshi yayi akan Anee wadda gumi yagama jiketa sharkaf itada uwarta.

Kira mummy ta kwalawa zahra,saikuwa ga little zahra da late Zahra tare kowa tafito daga daki na daban.
Zubama juna idanuwa sukayi yayinda suka nunama juna yatsa a tare.''kece Zahra?''
Suka sake ambata ataren.


Kowa afalon mikewa yayi yana ta'ajjibin wannan bakon Al'amari,ananne kuma yayah Aliyu yafito Shima sabe da kyawawan yarah.

Wadanda suka dauko fuskar Zahra sak suka kuma dauko farin yaa Ali.

Mummy tasoma murmushi tayi aure da yayanka Aliyu ne bayan Allah ya baka little zahra amatsayin mata.

Rungume yaa Aliyu ishaq yayi yana hawaye.





Loading.....3pages remaining ....Never forget🥰
*MIJIN 'KWAILA...2*



Mman meenat


*Chapter 28...Second to the last post..*


*Zakui kewar Zahra? Shin nace zakui kewa? ingani A'kasa....lol i so much luv u guy's.*


*Wannan shafin nakine ke kadai,deejah(maman Zahra) kina kaunar wannan labari kamar yanda nake 'kaunarki.*🥰


What to say when leaving the home

*Arabic: بِسْمِ اللهِ ، تَوَكَّلْـتُ عَلى اللهِ وَلا حَوْلَ وَلا قُـوَّةَ إِلاّ بِالله*

*Pronunciation: Bismi l-lâhi, tawakkaltu 'alâ l-lâhi, wa lâ hawla wa lâ quwwata illâ bi-l-lâhi.*

*Arabic: In the Name of Allah, I have placed my trust in Allah, there is no might and no power except by Allah.*


Duka wajen kabbara suka d'auka,yayinda Anee da uwarta sukayi tsuru-tsuru kunya kawai ayau idan aka barsu da ita ta'ishesu suyi danasanin mugun hali irinnasu.
Cike da takun kasaita irinna manyan yarannan late Zahra(Ada bah.🚶🏽‍♀🤨) tatako zuwa inda anee take,akwai murmushin who are u akan saman fuskarta.
'Dan dukawa tayi kusa da Anen tarage murya kafin tace''kina zaton kisan innocent soul abune mai sauki Anee? shin taki kalar zumuntar kenan?Na rikeki matsayin kawata kuma aminiya agareni,ashe kece makashina.Lallai mutum ba abun yarjemawa bane,ayau kadai Allah yanuna maki cewar kedin baki isa ki canja rubutun kaddara ba.Ishaq dakike fafutuka akanshi gashi kankanuwar yarinya tahanaki zaman lumana wanda idannice bazan hakan ba.
Kamo hannayen Zahra tayi ta hade dana ishaq''Gatanan,amanarta nabaka idan harka ci amanar namcy bazan yafeka ba.'' wasu siraran hawaye ta goge yayinda taci gaba dafadin.
''Aneesa tayi kokarin cusa soyayyarta acikin zuciyata tayanda nakasa banbance illar datake shirin yimani.Nakasa tantance cewa itadin makiyiyace agareni.
Sun yaudareni itada uwarta tahanyar yimun kyautar Apple wanda aka sakama sinadarin Allurar kisa,bankawo komai acikin rainaba naci apple din gaf da lokacin dazan kwanta bacci,hakika wannan shine ya canja kaddarata tazama matar ishaq nakoma matar Aliyu.Madallah da wannan taimako naki agaremu Aneesa.''

Kuka Anee take tana rokon gafarar duka jama'ar wajen,saidai babu wanda tabama tausayi,kasancewar mugun aikinta itada uwarta.
ishaq ne yakare wasan ta hanyar sake zabga mata saki guda akan nabaya.Bayan rokon dayayi dasu umma suyi hakuri kada suce yayafe mata don bazai iya ba.

A'karshe aka rufe taro da Addu'oi dafatan zaman lafiya mai dorewa acikin zuri'ar gabaki daya.



★★★★★★★★★★★★

Akwana atashi ba wuya awajen Allah,cikin Zahra yashiga watanni shidda cif soyayya da 'kauna tsakaninta da ishaq ba'ama magana.
Hakanan dangin mijinta musamman ma gwaggo rabi,mummy,Hanan...ba karamar soyayya suke nunawa zahran ba.
Kowa yadau burin duniya yadora akan cikinna zahra wanda bashine jika na farko acikin zuri'ar ba.

Akuma wannan datsinne ummilolo ta Amarce da angonta yahuza,wanda yakasance babban sepetor na y'an sanda.

Ba karamar rawa Zahra tataka akan bikinba, kusan ita tayi uwa tayi makarbiya akan komai.Hakan yakara mata kima a idanun mahaifan ummilolo harma dasu Abbalo wanda ayanzu yazama saurayi abunsa.

Tsakanin auren ummilolo dana uwande watanni biyu ne rak.Nan ma ba karamar rawa zahra tataka ba.Yaya murja itama adai-dai lokacin ta haihu,sai Zahra tasake zama busy yanda yakamata.

Kusan kullum saitaje gidan aikin bakwai,saidai inta dawo tadosama ishaq rigimar kafafunta ciwo.Baynta dadai sauransu.Karshe sai yayi aikin yimata tausa kafin ta sassauta kukan kissan data tsira na babu gaira babu dalili.


Acikin wannan lokacin zahra ta kile tazama y'argayu ta kwatance,abunka dama damaison gayun.
fatarta tasake yin wani kyau na musamman.
Shi kanshi ishaq din kallo daya zakamasa kagane cewar kwanciyar hankali da wadata sun 'kara samun gindin zama awajen shi.

Duk wannan baisa zahra tafasa karatunta ba,dukkuwa da yanda ake korafi akan girman cikinta da nauyin dayayi.

mates dinta da malamanta sunsha Zallar mamakin jin wai ashe tanada aure.

Ayanzu kullum da ni'kab dinta take shiga skul saboda (y'an holi.)sa'idinawa.Acewarta.


Soyayya da 'kauna wajenta da ishaq kace romio ne tare da juliet.Sam ishaq baya duban kankantar Zahran yayinda itama bata duba girmanshi.Rayuwa sukeyi mai ban sha'awa cike da sanin girma dakuma darajar junansu.

Sun mugun 'kullewa tsakaninta da Zahra matar yaa Aliyu,kullum yaran suna gidan Anty Zahran Auncle ishaq,kamar yanda suke fada.

Haka zahra zata biyemasu da tsohon cikinta,sune buga ball wajen 'buya.Kai wasanni kala-kala.
Yaran sun mugun shakuwa da zahra inka gansu saika rantse itace ta haifesu saboda kamarsu dansuma fuskar uwarsu suka dauko.




Cikin Zahra yanada watanni tara da kwana goma cif,tatashi da matsananciyar ciwon mara wanda yagama gigita tunaninta.
Duk yanda taso daurewa abun gagararta yayi tasoma tashin ishaq tana kukan ya taemaka mata mutuwa zatayi.

Hankali atashe ya kamata yana shafa bayanta,inda tafi korafin yana mata ciwo.

Cike da dabara da hikima yariketa da hannunsa na dama ya jinginata akan kafadarshi.

Hannunshi na hagu yana bisa qugunta yana murzawa.

Zagaye gidan suka somayi.
Intagaji saiya tsaya sun huta tukunna.

Ahakan bakaramin dad'i takeji ba,kusan Awa biyu suna hakan.Har saida ta fashe mashi da kukan mararta zata fashe.

Ya d'auke abarsa cak!ita da cikinnata ya shimfidar a bedroom dinshi yasoma kiran mummy.

Batawani jimaba sai gata,kasancrwar bawata tazara ce mai nisa ba atsakaninsu.

Alokacin zahra babu abunda take illa salati dakuma mai-maita wannan Addu'ar...''Allahumma lasahla'illa ma ja'altahu salhan wa'anta taja'alul hazna iza shi'ita sahlan,La'illaha illa antassubhanaka inni kuntu minnazalimin.Lahaula wala quwata illa billah.Rbbi sallim-sallim...Summassabila yassara...''dadae sauransu.

Ahaka mummy ta sameta,ita kanta tayaba jarumta irinta zahra bbu ihu baretane kwaratsi.Addu'a kawai take mai-maitawa tana sharce zufa.

Isowar mummy da Gwaggo Rabi yayi dai-dai da turowar kan jariri..wata kalmar Shahadar zahra ta furta da karfi,saikuwa ga sunkucecen yaro ahannun gwaggo rabi ya canyara kuka.

Hamdala duka suka d'auka gwago tana kai bude idonta kaga innarkarabi gata nan.



2pages remaining🤪

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login