Showing 1 words to 3000 words out of 26231 words
Compiled By Umar Dalha Funtua.
*MIJIN 'KWAILA....2🤦🏽♀*
*chapter one*
*written by Maman meenat*
*Editing A'isha Abdullahi T. Fulani*
*HAPPY SALLAH....🤝🏽*
....... *KOTU* tayankema zahra d'aurin shekaru tamanin agidan yari....itace Kalmar dataci gaba da amsa kuwwa acikin kunnuwan isha'q wsnda yafarka firgigit kamar wanda aka tsikara da allura,ahankali yasoma bin dakin dayake ciki da kallo.Tabbas dakinsune ba kotu ba,musamman dayakai dubanshi akan fuskar gimbiya anee daketa kwasar baccinta hankalinta kwance abinta.
Ahankali kuma dukkan abunda yafaru acikin mafarki yasoma dawo masa aka tamkar dai magijine aka kunna masa dake nuna mashi hoton komai din yanda yafaru"yasalam"Kalmar
Daya furta lokaci guda yasoma sharar zufar data tsatsafo akan goshinsa,
'Wai meke shirin faruwane dashi dakuma Amanarshi *zahra* wai zahra in prison, kaii! It will never happened"Abunda yake maimaita wa kenan saika dauka shida wanine yake maganar.
Durowa yayi daga bisa gadon dayake kwance bayan yasake tulama anee katon blanket dasuka rufa dashi,takuwa juya gami da sake ruqunqume bargon abinta.
Yajuya yanufi wardrobe bayan zura fara kal ta jallabiyya daya biyo baya,ficewa yayi adakin baiko dubi hanyar toilet ba baretane yasaka ran wanka,a tym din zahra kawai yake burin yayi tozali da kyakyawar fuskar ta me debemashi damuwa.
Dakinta yanufa wayam bata ciki sai dai ga tulin kayan wardrobe dinta nan data fidda gaba daya tawatso atsakar dakin.Saikuma gefe guda tarin yayan magarya ne datasha tajuye yayan a plate da alama shanya abinta tayi.
Yagirgirzakai zahra badai rigima ba,abunda ya raya acikin zuciyarshi.yanufi part din mummy sai dai bai karasaba yahango zahran kofar kitchen da y'ar roba a hannunta,ranshi yabashi da'akwai abunda takeson aikatawa....Saikuma mafarkinshi yadawo fess akan idanunshi yanufeta dasaurin gaske tana hangoshi tasoma dashe bakimta duka,karasawa yayi kusa da ita yarage tsawonshi tahanyar durkuwasa yakasance tsayinsu yazamo dayane yakama hannayenta dake rike da robar yana juyawa"menene wannan" shine tambayar daya watsa mata.
Tsurama ruwan ciki idanuwa tayi,saikuma tarage murya sosai tace"inka yarda amana idanna fada maka bazaka fadama kowa ba?"
Tayi maganar tana kafeshi da idanunta masu shagaltar dashi.
Numshe nashi idanuwan yayi ahankali yace"nayarda"
Zahra datayi kasa'ke saikuma tace"Amanatun...Amana..wa'azabatun azaba,yaro gwaggo rabi zan zubamawa ahanya daga tataho tana masifa saita fad'i mukuwa musha dariya,"tafada tana dariyar tun kafin abun yafaru.
Gaban isha'q yasoma bugawa da sauri-sauri yarike robar hade da yan yatsunta yatsura idanuwanshi cikinnata har saida ta kauda nata idanun tanacewa"nidai kadena kallona haka idanunka sai ingansu kamar na mage🐱😜
"Mage kuwa?" Isha'q ya tambaya yana murmushi kasa-kasa,zahra data murguda baki tace"eh mana,jinake kamar inta kallonka fa..."
Yasaki dariya akan saikuma yace"bani wannan robar kada kisake attempting yima wani mugunta hakan babu kyau, halin yn wutane kekuwa nasan yar aljannah ce koba haka bane?"
Zahra tasoma murmushi sosai tana gyada kai,bakuma tayi kokarin hanashi robar hannun nataba.
Isha'q amsa yayi yaje yazubar harya dawo tana inda take atsaye,kama hannayenta yayi "oya muje kiyi wanka..Ina jamee(me aikinsu) tazo tagyara dakinki.
Zahra wadda tamakale kafa tace" nidai yaya saikayiman goyon kura"
"Goyon kura kuma zahra"
Isha'q ya tambaya donshi baimasan wani goyon kura ba,tace"eh kokuma kayiman makawuya ba"
"Yasalam! Nikam duka wadannan ban sansu baamafa,"
Bude idanuwa tayi saikuma Amana asaki kukan shagwabar data tsiro dashi kwanannan na babu gaira babu dalili.
Tuni isha'q ya sunkuceta sama yasoma shillawa yana juyawa da'ita dukansu dariya suke kyalkyalawa yayinda zahra tamakale wuyanshi
Tamau tana sheka dariya abinta..
"Yau nashiga ukuna ni rabi'atu mezan gani da namata..."
Gwaggo rabi tafada lokacin datake karasowa wajen rike da casbaha a hannunta.
Bama Susan da zuwanta ba baretane abunda dake fad'i.
Hakan yasake 'kona mata rai,tadage iyakar karfinta ya caulama isha'q carbin abayanshi abunda yazo mashi a bazata yasaki zahra dasauri.
Tasulmiyo batakai kasaba yasaka duka hannayenshi ya tareta,suka fad'i atare yayinda zahra tafada akan ruwan cikinshi...
Idanunta suka nitse cikin nashi,suna hada idanuwa tamashi gwalo,shikuwa ya lakace hancinta duk suka sheke da dariya...
Abinda yadada tunzura gwaggo rabi tace"au dariya nabaku tabbatattu,shikenan isiyaku kazama sallamamme akan wannan 'kwailar yarinyar dababu ibanda ta'iya sai jaraba..gotai gotai dakai kadauki yar cikinka kana wannan hauka da ita..."
Sauran maganar tata tatsaya cik! Hango anee dake labe jikin kofar dazata sadaka da kitchen din tana hawaye...
Loading.... *Anty Alawee*😍
[3/15, 8:39 AM] 0mmer Farouk: *MIJIN 'KWAILA.....2🤦🏽♀*
*written by Maman meenat*
*Editing Aysha Abdullahi T. Fulani*
*chapter 2*
Dasauri gwaggo rabi takarasa kusa da anee saida takare mata kallo kamar bazata tankataba saikuma tamere baki tace"kekuwa lafiya kika tasa jama'a kina zubar da ruwan hawaye saikace wadda akama albishir din mutuwar kishiyar gyatumarta.."
Anee takauda kai ranta amatukar jagule,saikuma tajuya fuuuu tanufi part dinta.
Gwaggo rabi tabita da idanuwa kamar yanda zahra da isha'q suka bita danasu idanun.
Yayinda gwaggo rabi ta tabe baki dacewa"kyaji dashi med'an Karan kishin tsiya,"
Tajuya taci taga da surutanta"yoni inma banda kee dakika rako mata duniya har wannan *kwailar* ce zatasaki zubar da hawaye yanda Allah yagama tsara halittarki tako Ina "takuma Jan tsaki" bokonki sam be amfana maki komiba."
Tajuya tana kwafa gami da lekawa kitchen din da inna delu keta hikirkirin had'a tuwo a warmer kallo daya tamata tajuya abinta.
Ahankali isha'q yasauke ajiyar zuciya,yasabi zahra akan kafadarshi harzuwa dakinta da already angama gyarashi kai tsaye toilet ya direta yace"oya kiyi wanka maza banason dattinan"
Zahra data sake shagwabewa tace"tonidai kazo ka cud'ani ai hannuna baya kaiwa bayana"
Isha'q ya fidda idanu yanacewa"idan bananan wayene yake cud'akin?"
"Hanan mana",
Zahra wadda ke kokarin shigewa bayin tabashi amsa.
Ido isha'q yaware,kai ,ahra tana kwamacala yanda yakamata.
Dakanshi yashiga bandakin harta tu'be kayan jikinta tasoma tara hannayenta jikin shower tana wasa dashi,tana ganin isha'q tasaki murmushi hade da dukawa tana dauko soson wankan.
Wani masifaffen shock ya ziyarci isha'q tundaga kan babban yatsan kafarshi har yazuwa tsakiyar kanshi yaruntse idanu dasauri komai zai iya faruwa kallonnan dayakema yarinyar nan ahaka.
Sam zahra bata fahimci komai ba saima tambayar data watsomashi" wai me akai naga kana runtse idanu?"
Bai iya bata amsa ba sai dai hannu daya mika ya'amshi soson already tasaka sabulu hakan yasa yasoma gurzawa abayanta cikin wani yanayi daya kasa tantance koma namenene..
Akalla ba akasar ba yadau kusan 5mins yana juya soson akan lallausan gadon bayan zahra wadda tagaji da zuqunawa tamike tana cewa"kainifa bahaka ummana da hanan suke cud'ani ba,waikai saikayita gogawa bakasa ruwa kuma baka denawa."
Sai alokacin isha'q yafarga da abunda yakeyi,dsauri ya sakemata ruwan agadon baya yafice toilet din cikin mawuyacin hali.
Kai tsaye part din anee yanufa har lokacin tana cika tana batsewa,suna hada idanu tasake shan mur tana aikamashi sakon harara yayinda yasakar mata murmushi gami da sharce mata ruwan hannunshi akan fuskar ta.
Takauda kai ranta a dagule,matsowa yayi inda take zaune abakin gado hade da dora hannayenshi akan kafadarta.
Tasoma kiciniyar ture hannun nashi takasa,yayinda yasoma zagaye dukkan jikinta da hannayennashi.
Kasa jurewa tayi tamike tsaye tana harararshi saikuma tasoma "mezanmaka isha'q? Aibanan yakamata kazoba wajen waccen kwailar yakamata kakoma tunda harzaka iya bata dukkanin tym dinka abinda kagaza bani.kagoyata akan gadon bayanka kana dariya da ita abunda baka taba kwatantawa agareni ba.saikaje kagama lagujeta sannan kadawomun nan kana zaton zan kawarma da kishin ruwanka ko?"
Saikuma tasoma kuka tanacewa"don Allah isha'q meyasa baka sona,meyasa ka tsaneni why...isha'q why...u hate me"
Baibari taqarasa ba yahade bakinshi danata yasoma bata darasi mai zafin dayasakata manta awacce duniya take,dayake er hannu ce sannan kwarai isha'q yakaranci lagonta adan zaman dayayi da ita .
Saida ya tabbatar tagama shiga hannu sannan yarabu da ita yadauketa cak ya aza bisa cinyarahi ahankali yasoma magana"kidena cewa banasonki anee kisani ke babbace bazai yiwu duk abunda nayima zahra yazama lallai saina aikata agarekiba kamar yanda itama bata samu 100%na abunda nake baki,itafa goyon kadai kikesha kekuwa megoyonma sha kikeyi ba?...."
Yakare maganar yana daga mata gira.
Ta kyalkyale da dariya kamar ba itace maiyin kukaba,fadawa tayi jikinshi suka haura babban filin jirgin Aminu kano...bansani ba killa jidda suka nufa😜.
Zahra kam tana gama wankanta fitowa tayi abinta daga ita sai pant data saka tun a toilet, batako dubi inda kayan shafa sukeba takutsa karkashin gadonta tajawo wata yar bakar leda tulin gorubane da magarya aciki saikuma taura.
Qirgawa tayi taware wasu agefe,takulle ledar tamayar kasan gado tadauki goruba guda tadage dai-dai karfinta tana gwaguya tana wasa wakokinta wanda rabi duk shirmene take jabga abinta.
Wardrobe tabude saikuma taruntse ido tace"yasin duk Wanda na cafko shizan saka..."
Tadora hannunta cikin wardrobe din tasoma lalube,asa'a kuwa talalabo bakar jallabiyya tabude idanu taganta rigar bakace doguwa har kasa sai-dai hade take da hularta Wanda akama ado da kunnen zomo..
Bata damuba tazura rigar tazauna gaban dressing mirror tana taunar goruba tanama madubi gwalo da malgwada baki tana fiddo harshe da idanuwa.
Ahaka tagama cin gorubar tajefar tsakiyar Chinese carpet dake malale adakin tasoma fesa kwalliyarta wanda tasoma da foundation tace"hmm ainaga bidiyon make over na wayar Anty hafsa....yama take cewa...tadauko foundation tafara wannan shine foundation tadai fara acting like professional make over din.
Sai daifa tun awajen saka foundation takauce hanya don saida tagama zazzage akwatinta tas babu brush na shafa foundation hakan yasaka daukar zanin data cire tajabgashi akai tasoma danbarama fuskar abunka da liquid yakuwa daddanqare mata.
Bata damuba tasoma jagira"ummmm cinko ma zanyi"
Tafada lokacin datasoma durza eye pen akan girarta ganin kamar baya fitowa yasata cillar dashi dafadin"shege kadama kayibaga kwalli ba"😏
Tafada da murguda baki bayan tasoma jagiran da kwallin matsayar jagirar agefen kunne bashine yafi 'kayata zahra ba a'a yanda tad'ora jagirar asaman ainahin natural gira da Allah yabata.saiya kasance giranta daban jagiran daban.
Takuwa bishi ta zagaye da foundation maimakon concealer dabata gani acikin kayan shafar nataba.
Wannan yabama girar tata damar cakulewa tazama tamkar ta gwaggon biri,duk da haka zahra saida ta danqara powder akan goshinta kasan habarta cheeks nata amatsayin highlight kai ranar zahra sam bata hango na biyunta wajen kyauba.
Musamman yanda tajabga janbaki meruwan ganye akan lebennata takuma tattakura tazagaye abinta da bakin kwalli,
Tasoma sakin murmushi tana tsuke baki kamar yanda taga masu nuna make up din sunayi bata raba d'aya biyu wajen gwanancewarta akan kwalliya kota amare tayi..
*Nace ba mr's hamza...mizz Ayushh...hajara ghandi ko zakuzone zahra tamaku ranar sallah*😝🤪
Daga wannan tsakar gida tanufa,gidan tsit bakowa kasancewar rana tatake sosai wannan yabata damar nufar get wajen maigadi..saidai bata hangoshiba taja tsaki afili tace"wajen gwabama zanje inhaye bishiya insha shagalina"
Kai tsaye garden tanufa,wata ringijejiyar bishiyar gwaba tahanga yayanta sun nuna kwarae hakan yasakata hadiye yawu ta takarkare tamakale bishiyar tasoma tsinka tana gatsawa intaji zaqi ta cinye,intaji bauri tajeho kasa....
Tana sama gwaggo rabi takaraso wajen daya kasance wajen hutawarta saboda rana,acewarta batason rabar esay tana bugunta ga ni'ima daga Allah.
Karkashin bishiyar gwabar ta shimfida dardumarta da casbaha a hannunta tadan kishigid'a tana lazumi.
Zahra hankalinta yana akan gwaba sam bataga zuwan gwaggo rabiba wannan yabata damar cilli dawata rusheshiyar gwaba Mara dadi afili tace"katuwar banza saigirma ba dad'i"
Gwaggo rabi datadan saurara jin siririyar murya bisa bishiya yasata sake natsuwa😆sai dai fa batayi auneba taji jifaaa tuiiii! Gefen kafarta tajanye dasauri tana fadin"kai jarababbun tsuntsaye basason barina insha Inuwa"
Takai dubanta akan gwabar da niyyar dauka sai kuma tajefar dasauri ganin shacin hankoran mutum fici-fici...jikinta yabata ba lafiyaba,
Ahankali cikin fatgaba tad'aga kanta mezata gani....
Zahrace tawatso idanunnan nata amatukar tsorace don harga Allah batasan dazuwan gwaggo rabiba face sambatu datajiyo daga kasa...
Wata razananniyar kara gwaggon tasaki dayasaka zahra durowa wa....
Loading......
*Anty Alaweeen dai😍*
[3/15, 8:39 AM] 0mmer Farouk: [6/22, 6:50 PM] Anty Alaweey🌹: *MIJIN 'KWAILA....2🤦🏽♀*
*chapter 3*
*written by Maman meenat*
*Godiya tattare da jinjina gareku ma'abota hankuri juriya tattare da jajircewa akan bibiyar wannan labarin dakusan zan'iya cewa yana daga cikin novel mafi jinkiri da'akeyi a kafar sadarwa.hakanan bakina bazai gaza wajen godiya mai tarin yawaba agurin mutanen dani kaina idan zanyi rantsuwa ban'isa in TA tantance adadin y'awansu ba,nasha kira inakan shan kira duk maganar dayace"mum meenat ki taimaka kikaimana karshen labarinnan..bayin kaina bane wlh DAGA ALLAH NE*.
*Tabbas kuna tare da Maman meenat akoda yaushe kamar yanda nake tare daku fatar ubangijin rahma yasada mu amafificin waje"Aljananah Ameen..*
*Matsayinku yawuce Maman meenat tayi wancakali da bakatunku dayawa masu rokon nasakasu group dina Allah baibani ikoba sakamakon matsalar datasha kaina..wannan yasa zan'ajiye no.gamasu bukata mata saikuyimata tagana zata saku inda zakuci gaba dasamun wannan novel insha Allahu*
*0701117618..*
*Thank you for the love and care*😘
Zahra nadurowa saitin gwaggo rabi ta dira,tasake gigicewa ganin gwaggo rabi tayi suman zaune,tafice a lambun da gudunta dakinta tanufa tasoma haki aranta tana ambayar Komenene ya firgita gwaggon haka?
Gwaggo rabi kam tana samun kanta waje tayo a tamanin tasoma haki tana kwalama mai gadi kira,yakaraso aguje tazube agabanta yanacewa "gani hajiya"
Ran gwaggo rabi yasake baci tace"Menene aikinka agidannan har d'an biri 🐒 yashigo baka sani ba?"
Takare maganar tana mazurai idanunta fal da masifa.
"Biri kuma" maigadin ya mai-maita cike da mamaki dakuma kokonto.
"Zanmaka karyane," gwaggo rabin taci gaba da fad'i,"ninan da idanuwana yanda Allah yanunaman birinnan yanunaman Annabin rahama haka.ba'ki wulik dashi da doguwar wutsiyatai🤥(su gwagg banda qari mana☺)
Maigadi yasake cika da mamaki da alhini "shikuwa wannan buri ta'ina yaratso jama'a yashigo gidannan"?
Gwaggo rabi tayi cikinshi da tijara" karkaman iya shege,kadaije maza kafitar dashi tunkafin Alhaji yadawo insakashi sallamarka sullutu dabesan aikinshi ba."
Jiki a sanyaye megadi yanufi dakinshi danufi dauko sanda,karar horn din motar dr.Ru'kayya yakarade kunnuwanshi yanufi get din dasauri yataleshi yanamata sannu da zuwa.
Dafara'arta ta amsa tafaka motar a'inda yadace tafito hankalinta yana akan gwaggo gaba d'aya.
Tasoma tambayar bahasin tsayuwar ta gwaggo awajen,
Cikin takaici gwaggo rabi ta zayyanewa mummy komai daya faru shigarta lambu.
Shiru mummy tayi tana nazarin maganar to inabiri yaga hanyar ratso jama'a yashigo gidanta...tambayar data soma nanatama zuciyarta kenan,
Saikuma tabiye rajin gwaggon tahanyar umartar baba yusha'u daya gaggauta bincike lambun yafidoo birin.
Baba yusha'u yanufi lambun da katuwar sanda yayinda Dr.rukayya ta rufa mashi baya,inda gwaggo rabi tamakure gefe guda kamar kace arr! Tatsera...
Duk iyakar binkicen baba yusha'u babu abinda yagani face gwabobi da'aka gwaigwaya aka yarda ya tsintosu yana nunama Dr.Ru'kayya wacce tayi shiru tana juya gwaibar tana murmushi.
Daga can waje suka soma jiyo salatin gwaggo hakan yasa suka bazama dasauri suma tozalin dasukayi da zahra yabasu mamaki,baba yusha'u dayasoma sosa keya yana dariya ahankali yadubi mummy cikin ladabi yace"mummy wannan ai amaryar megidana ce,Allah dai yasa ba'ita gwaggo ta ambata da biri ba."
Ita kanta mummy wannan kwliya ta zahra saida tasakata darawa sosai,yayinda gwaggo rabi taci gaba da ruwan bala'i tana cewa yau ko'ita ko zahra agidannan taga alamar zahran sotake ta kasheta tun bataga jikokinta dake jikin isha'q ba.
Mummy dai hakuri tayita bama gwaggo yayinda taci gaba dafadin"ai tsaf na hakalci wannan makirar yarinyar babu abinda tasani face munafurci.To ta Allah bataki ba yanda naga auren isha'q haka zanga yayanshi."
Kama hannun zahra mummy tayi sukabar wajen.
*BAYAN KWANA BIYU*
Tundaga wannan rana kiyayya tsakanin gwaggo da zahra ke 'kara ruruwa tamkar *wutar Kara* yayinda anee itama anata 'bangaren sam abin badad'i sai gidan yahad'e yazamewa zahra tamkar *prison* idandai isha'q mummy dakuma hanan kowa yakama gabanshi tofa wulakanci dacin zarafi babu kalar da zahra bata gani daga anee da gwaggo rabi
Sa'arta dayane batada wayon saka damuwa acikin zuciyarta gakuma baba yusha'u datake zuwa susha firarsu su more,wannan yake rage kewarta dakuma matsin lambar datake samu.
Yauma kamar sauran ranakun,mummy isha'q da hanan kowa yakama gabanshi yayinda gwaggo rabi tafita zuwa gidan kawarta innaru nan makwabta yakasance daga zahra sai anee.
Zahra datayi wankanta gado tahaye tashaqi baccinta bata farkaba sai gab da azahar yunwace tasakata mikewa babu shiri tafito daga dakinta kanta babu kallabi tanufi kitchen inda take jiyo kamshin sanwa bata raba d'aya biyu anee ce tad'orashi.
Batare da fargaba ko kokonto ba tanufi kitchen din jallop na macaroni yasha hadin vegetables tayi tozali dashi ayayin data bud'e tukunyar dake girke bisa gas,zahra tahadiye yawu saikuma tajuya dasauri tajawo plate tasoma loda abincin son cikinta.
Bude Fridge tayi tadauki lemon exotic tafito dashi niki-niki daniyyar shiga dakinta,saurin rugugin anee yasakata tsayawa cik!
Anee tamatso tana mata matsiyacin kallo tace"ke bakar ja'ba me warin baki,bayan bakar fatar jiki ashe kinhad'a hada ta zuciya 'barauniyar banza munafuka bisa umarnin wa kika satarmun abinci?"
Zahra tatsaya sororo tana karema anee kallo kafin tace"nidai baniba"tana murgud'a baki.
Idanu sosai anee tafiddo tana karema zahra kallo saikuma tasoma mumushin mugunta tadad'e tana tanadin wannan ranar don haka tace"ohhhh rashin kunyar da'akace kina tashe itace zaki nunaman? Aiko idan kin gagari tsohuwar uwarnan taki tzahranki gagareni ba domin babu gagararre sai bararre.."
Zahra tuni idonta yakawo ruwa tatsani a ta'ba mata ummanta ko abbanta,yanzu y'an rashin mutuncinta sa motsa..
Tasake Murgud'awa anee baki tace "wlh badai ummata ce tsohuwaba sai dai taki😏"
Ran anee yagama 'baci tad'aga hannu ta shararawa zahra mari,marin daya gigitata takuwa kambad'ama anee plate d'in dake hannunta da abincin gaba d'aya.
Tsananin azaba yasaka anee kukan kura tamakure zahra iyakar karfinta takayar tasoma duka kota Ina "yarinya duka iskancin dakike zubawa barinki akayi tunda kika shigo gonata kuwa yau saina ciremaki iskancin dakike takama dashi."
Anee kenan take tijara bayan ruburbudar datakema zahra..wacce tsananin azaba baisa bakimta yamace daga ruwan zagin datake aunama aneesa,agefe guda anee tasaka hannu tamatse bakin zaginna zahra har saida zahran taji kamar zatayi fitsari awando.
Wannan yasakata dagewa iyakar karfinta ta danqarama anee matsiyacin cizo ababban d'an yatsa abunda yasaka anee d'agata dasauri tana yarfe hannunta dake zubar jini,ganin jinin yasake tunzurata tayi kukan kura akan zahra aranta tanajin gara takashe zahra sai dai kome zaifaru yafarun.
Zahra ta ma'kale anee ta cukuikuye tahanata kata'bus,cikin dai sa'a anee tasake kayar da zahra danufin ma'kureta zahra azaba yasata kama wuyan rigar anee taja'kiiiiii....!!! Saiga wuyan rigar gaba d'aya ahannun zahran.
Wohoho..kai ranar anee
taga tashin hankalin da tunda uwarta ta haifeta bataga koda makamancin shiba.
Don dai anee d'iyar hutuce ita batama iya fad'aba yau gashi tatsokalo *zahra balbali zahra bala'i ta'ba d'aya kaga zuga....zahra'u mala'ikar yara kota mutu ba ruwan Allah walakiri ya jibigi kayanshi...* kirarin zahra kenan dana tuna🤥
Rigima dai kamar wasa tazama gaske duk dacewar zahra keshan jibga hannun anee hakan baihana zahra tagaza ta'buka don kuwa anee har saida tagaji da kulawa tasoma haki zahra batayi ko gezau ba tamakale anee makatam tana kuka tana"Allah ya'isa muguwa azzaluma wlh saina Rama..."
Kuka sosai zahran keyi,ganin wankin hula yana neman kai anee dare yasata kukan kura danufin jefar da zahran tasamu ta arce daki😂
Zahra tace batasan wannan ba,tofa rikici yai rikici anee tasake kayar da zahra tasoma nausar bakin dake zaginta bakin zahra yafara fesar da jini abunda yasaka zahra rikicewa tagallama anee cizo akan nono🤣😆
Anee ta kwantsama uban ihu tad'aga zahra tana duba nonon harda jini🤦🏽♀
Kuka anee tafashe dashi tanacewa"wlh yau sainaga bayanki acikin gidannan...
Sauran maganarta tamakale lokacin da Dr.Aysherh ta banko labulen falon,tayo kan anee ta tallafe tana kallon yanda kan nonon anee yake d'igar jini d'is-d'is..bala'i da rayuwa *tsarki da ruwan ganda me had'e da barkono*😆
*muje zuwa mutanena anjima akwai new post faaa💃🏽👯🏼♀*
*Anty Alaween dai🌹*
[3/15, 8:39 AM] 0mmer Farouk: *MIJIN 'KWAILA...2*
*Chapter 04*
*by Maman Meenat*
Wani mayataccen kallo takebin zahra