Showing 21001 words to 24000 words out of 26231 words
karyata,tana ihu da hayagagar saita illata zahra.
Abunda ya dakatar da ishaq barin abinda yakeyi yazura jallabiya yafito rai abace.
Anee ta'batamashi bajat.
Idanunshi yasauke akan anee wacce tayi wuji-wuji da ita,tatuje d'an cibbirin gashin kanta yatashi sama kamar anjika kan mage.
taci dammara da kallabin kannata ga wuka ahannu idanunta sungama kumbura sunyi suntum dagani kasan taci kuka hartaba uku lada.
Suna had'a idanuwa jikinta yayi sanyi kalau,wani san ishaq kishinsa suka dira aranta lokaci guda.
yarda wukar tayi tafashe da kuka sosai da gaske.
Shima wata matsananciyar tausayinta yakamashi kishi bala'i ne.
Hannayenshi ya bud'emata ahankali tataka saikuma tafad'a kirjinshi dasauri.
Atake tasake fashewa da kuka cikin muryar kukan tace'' i wish in mutu ishaq,nadena jindadin rayuwata daga jiya zuwa yau.jinake duniya tamun kunci raina zafi zuciyata kuna take dan Allah kamun adfu'a kozan samu sassauci pls.''
Tafad'a tana kuma fashewa da kukanta mai sauti.
Tayar dakanta yayi yazubama fuskarta idanuwa dukta wani jeme saikace ba anee gwanar kwalliya da iya kisisina ba.
Seyaji takara bashi tausayi.
rungume ajikinshi yanufi bangarenta da ita.
Batare daya tankataba,ruwa mai sanyi yadauka ya tsiyaya mata a glass cup.Aikuwa nan take tashanyeshi saitaji ranta yaimata sanyi kadan.
Kafafunta yasoma matsawa cikin tausasa murya yace''Aneesah....''
yanda yakira sunanta yasakata d'aga idanuwa tana kallonshi daduk natsuwarta.
Sake tattara natsuwarshi yai fuska babu alamar wasa yace''nakira sunanki sau uku kada kiyarda nakira nahudu dan bazan kirashi da alkairi ba.kisani zahra dakike hauka akanta batataki takeyi ba.Kidena tada hankalinki akanta inkika kwantar da hankalinki zata baki girma yanda yakamata.Kada kimanta itafa amatsayin uwargida take amma bata taba tayar da hankalinta akanki ba.Shekara nawa ina tare dake bata taba nuna damuwarta akaiba saike don nawuni kawai adakinta kika dauko wuka zaki kashe ta? tokiji dakyau koda wasa,duk abinda yasamu zahra inami baki tabbacin saikinyi nadama.Kishi ba hauka bane tunda ba'akanki akafata ba bare aqare akanki.''
Don haka kikiyayi kanki.Bazan dauki shashanshi komai kankantarsa ba.
daga haka yamike yafice yabarta tana matsar kwalla dakuma sake jin tsanar zahra aranta.
**
Washe garin ranar zahra bata samu damar fitowa da wuri ba kasancewar arna sittin dasukaita kisa.
wannan yasakasu makara daga ita har ishaq din,saukintama weekend ne da ansamu matsala.
sai 12suka tashi yunwa fal cikinta.laluben abinda zataci tasoma cake tadauka tahada da yoghurt tasha dan batajin zatayi wani girki a tym dinnan.
Tana azaunen nafee tashigo falon dawata kafurar shiga,rigace gown tamugun tieting jikinta kannan yasha gashin doki kunba zaqo-zaqo kamar ta diyan arna.
gyalenma tsabar wayewa riqe yake ahannu guda.
takalma tuntud'i wada ko ince acikari duniya.
Babu sallama tashigo tana d'aga hanci ta dibar iska daga gabas ta watsar yamma.
Dakallo zahra tabita saikuma tasaki murmushi ''iska na wahal damai kayan kara.''
tafurta murya can kasa.
Nafee dama jiran zahra take tamatso da takunta na kasaita tanamata kallon uku kwabo tace''ke kwaila kanwar 'bera harkinkai macen dazataman kallon banza,toni bazanyi dake ba saidai inyi da gyatumarki.jikike kinkai mace jiya d'aya kin kwana da namiji ko? saikuma tasaki dariyar shakiyanci tana maimaita kalmar zahra da ishaq ''wayyo yaa nidai banaso kadena,akwai zafi.''
''Haka kika fad'a ajiyanko,toshi amsar me yabaki.''
Afusace zahra tamike danufin zabgawa nafee mari amma saitaji anrike hannunta tabaya''shine kuskuren da idan kika aikata hatta uwarki bazata yafemaki ba,dan zaki sata a matsala.yenye yar matsiyata kawai.''
Anee tafad'a bayan ta dangware hannun zahra wacce tsabar mamaki yasata kasa magana.
jan hannun nafee anee tayi sukayi gaba suna dariya,zahra na'iya jiyo muryar anee tana fad'in ''matukar nacika mace saina fidda waccan tsinanniyar yarinyar a gidannan koda karfi koda yaji.''
da'bas zahra tazauna rana tafarko data zubar da hawayen takaicin abinda anee tamata.takuma kuduri aniyar nunamata ruwa ba sa'an kwando bane.
it's by ibraheem tnx for sharing my novel.
*ROMANTICS WRITER'S ASSO...*💥
*MIJIN 'KWAILA..2*
Chapter 24
By maman meenat.
Jikinta yayi sanyi ahankali tamike tanufi daki ranta ajagule matu'ka.
ganin isha'q tayi harya tashi ya fesa wankanshi cikin lallausan farin yadi mai shara-shara yana zuba amshin anguna.
kallo daya tamashi ta kawar da kai tanufi gado takwanta kawai.
saida yagama fesa turaren yajuyo yana tambayarta''yaaa nayi kyau kuwa.''
duk yanda taso ta boye damuwarta kasawa tayi saidai ajiyar zuciya datake saukewa lokaci zuwa lokaci.
gefen gadon ya karasa yakamo hannunta nadama yahada cikin nashi ahankali yasoma matsawa,idanuwanshi akan fuskarta.
Ajiyar zuciya tasoma saukewa ahankali.Hakan yabashi damar jawota ya rungume ajikinshi gaba daya yasoma murza yatsun kafarta ...
lakwas tayi a jikinshi,ahaka saida ya tabbatar yagama gusar da damuwarta yamike yana jifarta da murmushi yace''oya kiyi wanka before na dawo,zanyo mana oder breakfast inyaso saimu fita muje gidan mummy da umma ko?''
jin haka aikam aguje tamike tasoma tsalle yariketa yana cewa''kadafa kimun wasa da baby na dake tare dake.
idanuwa tafitar ''kai yaa ishaq wanne babe kuma..
cikinta yashafa yana kanga kunne yadago yana kallonta da smile akan face dinshi yace''its my babe here...yesterday baby.
idanuwa ta kulle tana fadin''Haba ainayi kankanta da daukar baby.
hakama zakice yafada yana kokarin kamota dafadin barin chaking inji dagaskene.
toilet tanufa aguje tana dariya.
Sakai yayi yafice daga gidan.
agaggauce zahra tayo wanka tajima tana tsara kwalliya kaya kam tasaka yafi akirga tana cirewa saitaga duk wanda tasaka baiba.
Ahaka taqare zabenta akan wani leshi sky blue sararin samaniya leshin sassauakne mai manyan fulawoyi yanada yarfin siraran touch ajiki masu kyalli da daukar idanu.
rigar dai-dai jikinta ce,half gown sai plain zani .Daurin hauwa waraka tayi yazo gaban goshi jelar kallabin kowacce ta kalli nata bangaren.
tafesa turare yakai kala biyar saisuka bada kamshi na daban.
jin ishaq shiru yasakata nufo main falo dan duk tagama kosawa ya'iso sutafi yunwa da damuwarta nemansu tayi tarasa gaba daya.
light blue high hill ne a kafarta tana takawa yana kara kwas-kwas sai alewar iklas datake guda biyu a hannunta idanuwanta sukayi tozali da nafee da anee wadanda suka baje a 2syter sunacin chips.
kallon uku kwata zahra ta watsa musu lokaci guda tanemi kujera 1syter ta zauna kafa daya akan daya yayinda tajanyo remote tasoma canja tasha daga wacce suke kallo zuwa bollywood.
Anee tamike a fusace tayo kanta tana fadin''yar marasa mutunci,waton har kinada damar kicanjamun tasha ina kallo waye wai ubanki a garinnan ne.''
saida zahran ta mi'ke a nutse tabare alewar hannunta tajefa baki hadi da numshe idanuwa ahankali saikuma tabude tana kallon anee cikin idanuwa''kamfanin ikhlas sun iya sarrafa alewa mai nagarta.gatadai y'ar charas da ita yar karama sai zaqi da d'andano sabanin wasu kattan alewoyin dasai girman amma salaf zakajisu.
salati nafee ta d'auka tana fadin''kajimun shegiyar yarinya,kina nufin anee salaf take.
zahra tasake numshe idanuwa da karya wuya tana kallon anee tace''ohhh calm down babe,ai ba'aji abakina ba.''
Anee tasake hayyayakowa tana kumfar baki.
tsayuwa zahra tagyara tana juya idanuwa kafin tace''kinyi tambayar mahaifina,bamafa boyayye bane.talaka mai wadatar zuci.malam Adamu ishaqa yake.
shin zan iya jin sunan naki mahaifin?inkuma babu to akoma atambayi tsohuwa inda tasamoki.
nikike kira shegiya zahra,ni!
Anee ta fada a harzuke lokaci guda tacukumo wuyan zahra.
kaima zahran nushi tayi cikin sa'a taduke dazafin nama ta wasgama anee mari lokaci guda tananunata da yatsan hannunta ''dukan zahra abune mafi wahala musamman akan ballagazaye irinku kwancen bariki.''
daga hakan takoma tazauna,yayinda anee tanufi kitchen ta yayumo wuka tana zage-zage,saidai sallamar ishaq yasakata rike wukar tagaza katabus.
zahra tamike da tafiyar nan tata kalar catwalk ahankali ta isa gareshi ta zagaya hannayenta akan kafadarshi tana murmushi da fadin wlcm backhme dear...
kama hannun nata yayi yana smiling..
kallon anee yayi yana tambayar metake da wuka ahannu.
kafin tayi magana zahra ta amshe''zamu yanka lemune fa dear kasan yaa anee akwaisan lemu.
tafada tana kallon aneen yayinda nafee tarike baki dan mamaki.
murmushin dole anee tayi tanafadin yeh lemu zamusha gayena.
Anan kasan capet zahra tabaje abincin tasoma saving anee sannan ishaq saikuma ita kanta.
Anee takalli zahra wacce tayi basmala tasoma bama ishaq abaki.Tace inana nafee kum.
kai zahra tadan dafe saikuma tasaki smile tana hararan nafeentace kinga sam nama manta da ita,amma bakomai tadauki na warmers din taje dakinki taci inbai isaba takawo inqara mata anawa dama bazan iya cinyeshi ba.
Ayi manage🐧
*ROMANTIC WRITER'S ASSO...💥*
_We are d stars,keep shining Always_💥
*MIJIN 'KWAILA...2*
Chapter 25
by maman meenat.
*Hmmmm i don't know how i describe my feelings...happiness,smile or what?*
*I ask my self...*
*Arayuwata tunda nake rubuta labarin mijin kwaila nakanji wai-wai akan yawan fans na wannan novel amma nakan dauka kawai anyine domin kambamani ko sakawa nasake jajircewa saidai kuma me? nagani da idanuwana.*
*Tayama zan bayyana farin cikina? sama da mata ashirin suna dakon ganin fuskar maman meenat makaranta da yawa zasuji mamakin hakan amma nikam banida bakin dazan iya cewa wani abu farin cikin dayake araina yazarta ko wacce kalma dazan iya furtawa.*
*Wannan shafin dana gaba dashi duka mallakin wadannan bayin Allah ne wanda banma samu damar tsayawa tambayar sunansu ba.narasa shin zanyi hawayene kokuma zanyi dariya ayayinda babbar mace dazata ninka shekaruna uku take kirana da anti agaban* *idanun dinbin jama'a.*
*Lallai ko ayau ni Alawiyya sani na ajiye rubutun novel hakika naga tarin masoya wallahil azeem ayayinda naga wadannan mata ataron gidan biki* ana *nunani anacewa itace maman meenat mai rubuta mijin kwaila.*
*Yanayin fuskokinsu yanuna zallar soyayya da kauna,ayanda nataho tasigar raha ina dariya dacewa ''tomm suwaye masu nemana dafatan jakata zasu cika da kudi''*
*Amsarsu tafi komai sakani acikin wani yanayi ''ko nawa zamu baki bazasukai tasirin kaunar damuke makiba antinmu...Ashe da rabon muganiki,Ashe gari daya muke.*
*hawaye naji yana niyyar subucewa acikin idanuwana Allah kaine ka haskaka tauraruwar maman meenat kakai haskenta acan kololuwar sararin subhana batare da neman shawara daga maman meenat ba.Allah kaine mai mayarda jinjiri yazamo ango,Allah kasaka soyyayyar yar kankanuwar yarinya azukatan da bata taba zato ko tsammanin soyayyar su ba.banmasan adadin masoyan nawa ba.bansan sunana yakai haka zagayawa ba.*
*Towaima me.zancene...?ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN.*
*Nagode-nagode da 'kauna masoya wlh da'ace fuskokinmu zasu gauraya awajeguda watakila da bazan iya boye hawayen farin cikina ba.Amma koma meenene kalma mafi girma agareni itace zan baku..INA 'KAUNARKU FISABILILLAH.*🤝🏼
*Wannan shafi yana daga cikin shafukan da nake rubutawa tattare da murmushi akan fuskata...zanso duk wanda ya karanta shima muyi sharing murmushin atare.dama nace Ana tare🤝🏼Ana tare🤝🏼Ana manne da junan dai*😊.
*Godiya gareku zaratan marubutan qungiyata waton romantic writer's Association ina matukar sonku har cikin raina😍*
Awulakance Nafee ta kalleta saikuma tasaki gajeren murmushi na saman kan lebe kafin tace''Ah kinga karma kisamu matsala dani,qawata bani naki kinga saikici da ishaq ko''
tafada tana kallon Anee awani kaikaice tana dan kashe mata ido daya yayinda take tsuke baki da dan cizon lebenta na 'kasa.
Atake Anee ta hasko inda zancen yadosa danhaka taja plate din agaban nafee tana murmushi.
saikuma ta jingina bobbs dinta akan shoulder din ishaq din tanad'an murya kasa-kasa''dear bari mi sharing naka mana kasan ance bakonka annabinka,so yaxama wajibi mu girmama bakonmu.''
Tafada dai-dai lokacin datakai lomar farkon bakinta bayan tadebi na gaban ishaq din.
Wannan yasaka Aneen har Nafee kallon juna suka sakarma juna murmushi da alamar jinjina.
Wani dan karamin juya idanuwa da zahra tayi mai kama dana Ashwariya ray ne yasakasu kallonta duka.
saikuma tadan matsa jikinta kadan dana ishaq din cikin muryar salo da kissa adan ahagwabe kadan bada yawaba tace''Babe kaga nifa kabani abaki da hannunka,spoon nauyi yakemun ahannu nah..''tafada tana yarfe hannaye kamar wacce ta ta'ba wuta.
kallonta ishaq yake take ya d'ago plane din kowacce,shi harma mamakin wannan kishin kissar dasuke gasa yakeyi waton ita yanzu zahra tadena yarda ashata basilla kenan.
madamar suka nuna mata bariki saita rama.
bai kai karshen tunanin nashi ba tasaki yar kara da rukunkumeshi.Bashiba hatta su nafee tsayawa sukai kallonta tasoma jaa da baya tana yarfa hannu awannan lokacin hawayene kwance akan fuskar tata.
''Wayyo yaya na kone wayyo ummana...zafi.''
tafada tana yarfe hannaye tanakuma sake shigewa jikinshi.
Kama hannun nata yayi yana kokarin duba inda ta konen har lokacin takidena yarfa hannayen tana kuka.
''Kinje garin shirmenki da shirirta zaki lahantamun kanki ko,yanzu menene amfanin wannan sabida Allah kinazuba abinci hankalinki baya tare dake ''.
yafada adan tsawace.
Maimakon taji haushi saima sake cusa kanta datayi acikin jikinshi tana hawaye''nidai kayimun addu'a,kakaini wajen mummy tasamun magani.Wayyo yatsayana zai cire.''
taci gaba da fadin harlau tana yarfar hannu.
hannun yakama Ahankali yasoma hura mata iskar bakinshi akan yatsan nata idanuwanshi suna akan fuskarta.
hawayen taci gaba dayi tana sake cije lebe saika rantse da Allah acikin kaskon mai tasaka hannun nata.
Ganin abin bana 'kare bane yasakashi tura yatsan datake ikirarin ta konen abakinshi aduk kokarinshi na ganin tasamu sassaucin zugin da hannun yakemata.
Idanunta masu kama da shanyayyu ta daga ahankali ta sauke acikin nashi, zubama juna idanusukayi tamkar aranar suka soma ganin fuskokin juna.
Akalla mintuna uku gam suka dauka batare da d'ayansu yasamu tagomashin janye nashi idanunba.
Ahankali zahran tajanye nata idanun da suke zirarar da hawayen so da kaunar mijinta.
wani yanayi takeji tamkarma su dawwama a halin dasuke aciki.
kanta ta kwantas,akan kirjinshi ahankali tasaka hannayenta duka biyun ta zagaye 'kugunshi dasu tana sauke ajiyar zuciya asannu-sannu.
Hannu yasaka yasoma dibar abincin yana nufar bakinta dashi bayan basmala daya furta.
noke kafada tayi da salon nata shagwabar tana nuna bakinshi ma'ana saiya fara ci tukun.
Murmushi yasaki yana kokarin kaiwa anashi bakin suka hada idanuwa da anee.Zalla masifa da bala'i ke balbali acikin kwayar idanuwanta.
Yanda nafee kemata signal yasakata kasa magana saima ture plate din datayi tamike afusace ta shige nata sashen batare datako nemi abokiyar gayyar tata nafee ba.
''Dan Allah kayi hakuri ranka shi dade,kawar tawace batada hakuri danna tabbata zahra ba karamar hakuri takeyi da Anee ba.Baya ga haka yaushe zaka takahakkin yarinya kuma wai kace kanason ganin daidai.
''
Nafee ke maganar cike da kisaa tana kashe idanuwa.
Zahra tadan dago kanta tana murmuahi wa nafee''Ba laifi bane dan mace tayi kishi akanabinda takeso nafee,dan haka komi yaya anee tayi soyayyace tajata.Aikishin kyautatama miji shine kishi ba wasan yarburun burun ba.
promise next page 2morrow insha Allah.👏🏽
*MIJIN 'KWAILA..2*
*Romantic Writer Association*💥
_We are d stars,keep shining Always_💥
Chapter 26.
by maman meenat.
*Agurguje mu'karkare before ramadana.Insha ALLAH Zan kammala wannan Labarin a shafi na talatin ciff.Nagode da bibiyar mijin kwaila so much luv u*👏🏽
Sum-sum nafee ta mike tana mirmushin yaqe dafadin''hakane kam Abunda kakeso shi kake kishi.''
Zahra tasaki murmushi''yayi kyau dakika fahimci hakan.''
Rai abace Nafee tajuya tanufi bangaren Anee,Arigingine ta isketa kan gado tana durzar kukanta mai cimata zuciya.
Tallafota Nafee tayi tana share hawayen idanunta''Saifa kin jajirce kawata sai kinyi kamar kinayi,Ishaq baya sonki baya 'kaunarki inbaya ga haka agaban idanuwana yake gayama Zahra cewar don dole yake zaune dake badan yana 'kaunarki ba.Harma yana ikirarin rabuwa dake akoda yaushe.''
Cikin zubar hawaye Anee take kallon Nafee''Nadade da fahimtar haka nafee,nadade da sanin ishaq baya kaunata saidai har zuwa yanzunnan damuke magana dake nakasa kankare koda d'igo guda daga soyayyar danake masa,ina sonshi tamkar jinin jikina son danake masa ya zarta tunanin duk mai tunanin.''
Gajeren murmushi nafee tayi tana d'an dukan kafadar Anee''Ranar biyan bukata rai ba'a bakin komai takeba 'kawata.Kije kiyi hauka ke ban hanaki ba koda wu'kace burmama yar tusa inyaso ayi wacce za'ayi,bazai yiwu kina zaune yarinya karama tana jan ragamar Akalar mijinki ba zai sabu ba.''
Sake fusata Anee tayi takuwa hau fanfon Nafee takwasa fuu tanufi falon tsakiya.Zahra takai kwanoni kitchen tafito danufin gyara inda suka bata taji an shaqota tabaya.Duk yanda take kokarin kwacewa hakan ya faskara saboda Anee ta cukuikuyeta ne da wuyan rigarta.
Iyakar kokari Zahra tayi amma ina Anee ta mameta.Hakan yasa tagaza kata'bus baki ta bud'e da zummar kwarara ihu Nafee ta dam'ke bakin gami da sharara mata mari.
Ajuyen Anee tasamu galabar kayar da zahra tasake shaqe wuyanta iyakar karfinta tuni idanuwan Zahra sun canja tasoma jan numfashi tana kakari tamkar wacce ake zarewa numfashi.
Ganin haka yasaka Anee soma nausar fuskar zahra iyakar 'karfinta,sosai Zahra tafita daga hayyacinta sai idanunta dasuke rufewa suna budewa.
Ganin hakan yasaka Nafee kwasawa aguje tana salati tanufi bangaren Zahra ishaq da alokacin yafito wanka yazura vakar jallabiyya yaba tsane gashin kansa,Nafee ta fado dakin lokaci guda tafashe da mahaukacin kuka tana fadin''Shikenan Ishaq kayo agaji..burin Anee yacika takashe maka Zahra takashe maka farin cikinka wayyo nashiga uku.....!''
Ishaq kam baima tsaya idasa sauraron abinda take fadiba yayo waje aguje.Saikuma yatsaya cik! Ganin Anee murkushe da Zahra wacce gaba d'aya hannayenta suke asake bakinta yana fidda dafara.
''Shegiya tsinanniya burinki yacika,yanda kika kashe Zahra haka kema za'a kasheki.Kishi ba hauka bane Anee .''
Nafee ke maganar cikin 'karaji,sai alokacin ishaq yadawo daga suman tsayen dayayi.Ayayinda Anee ta dubi Zahra da sauri itama ba karamar razana tayi ba,soma jaa baya take tana girgiza kai tamkar wacce take gudun ishaq ya cafketa.
Baimako bi takanta ba ya sunkuci zahra wacce take wani irin kakari tamkar na fitar rai tana shure-shure.
Duk shakiyanci irinna Anee lokaci guda ta fashe da kuka shikenan zuciya takaita ta barota.
Nafee kam itace kan gaba ita tabude mota tasoma driving Zahra tana kan cinyar ishaq dan takwana dasanin bazai.iya driving ayanayin dayake ciki ba.
ita kadai ke sambatun dama Anee sam bata cancanta da ishaq ba.
Shi baimasan tanayi ba.
Dr.rukayya hospital suka nufa ,sanin nanne inda za'a karbi Zahra da gaggawa.
Aiko tana parking tafito aguje tana kwalama nurses,kira akan sukawo agajin gado akwai patient.Ishaq baima jira zuwan gadon ba ya sunkuci zahra yanufi cikin Asibitin da'ita aguje.
Nurses din ganin Ishaq sunsan kowaye shi,dan haka suka rufa mashi baya,yayinda daya daga ciki takwasa aguje tayi office din dr.Ru'kayya.
Tana zaune as usual tana duba wata patient dake fama da matsalar hawan jini,dr.rukayya tana mata bayanin yanda zata kula dakanta cikin natsuwa.
Nurse din batako jira neman iznin Shiga office din ba tafada tana fadin''Hajiya,ishaq yakawo zahra ba lafiya am sorry tosay ithink she's died....''
Dr.Rukayya bata tsaya saurarenta ba bakuma tajira saka takalma ba takwasa aguje anan tabar patient din kowa yaganta yasan tana cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa.
Tun kafin ta'karasa sauran likitocin sun soma jagula z
Zahra sunkuma cika inda take dankam da kayan aiki.
Dr.Rukayya tana shiga bata tsaya sauraren komai ba ta durfafi Zahra hankali atashe.
''Oxygen tasoma kokarin sakamata,duk ishaq yana tsaye tamkar batunbatumi gaba daya kwakwalwarshi tadena aiki na wucin gadi.
Sosai suka rufu akanta d'auko wancan miko wancan saka allura acan jona mata ruwa shine kawai umarnin da mummy take bayarwa.
Kusan awa guda cur suka d'auka kafin susamu nasarar ceto numfashin Zahra wanda yake fita da taimakon iskar bututun shakar iska din.
Saida ta tabbatar komai yazama normal sannan tasauke ajiyar zuciya tana godiya ga Allah,dabata kasance likita ba batamasan mezai faru da yar mutane a wannan lokacin ba.
Allah.yanufa Akwai sauran kwanan gaba.
Nafee duk abinda akeyi tana kofar dakin tana addu'ar Allah yasa Zahra tamace da hakane kawai zata cika muradinta na auren ishaq cikin sauki.
Ganin fitowarsu yasakata saurin durkusawa gaban mummy tana zubar da hawaye''Allah dae yasa tana raye in yarinyar nan tamutu bansan dame zan iya kiran Aneesa ta amsa ba.''
Duk da yanda kan mummy ya daure bata aminta da tarbiyyar Nafee ba sam.Fuska babu walwala tace Zahra tana fine.''
Daga haka tawuce tabar Nafee idanu awaje.
Office dinta suka nufa,Zaunawa tayi tazuba tagumi da duka hannayenta,yayinda idanuwan ishaq suke