Showing 30001 words to 30903 words out of 30903 words

Chapter 11 - MIJIN TA CE BOOK 3

20 Aug 2024

4868

cikin

155

wannan daren wanda nasan da wuya kwarai ace
akwai wani cikin mutanen gidan nan da bai ji kiran
da take yi min din ba, tunda dare ne, dare kuwa ba
raina motsi yake yi ba.
Ado ya yi maza ya dora tafin hannun shi akan
bakin nawa ya rufe da iyakacin karfinsh1, don hana
sautin maganar tawa fitowa sosai.
Ganin hakan ya sanya ni kokarin kwatar kaina
a hannunshi, tunda shi da kanshi ya ji kiran da ake
yi min daga inda muke din kuma muna jin muryar
Umahmah da ke ta faman canyara kuka.
Amma hakan bai sanya shi ya hakura ba, sai da
ya natsa don kan shi sannan ya kalie ni cikin wani
yanayi da yafi kama da na tsananin gajiya.
A hankali ya bude baki yana yi min magana, ke
ba ki da wayo ai shiru za ki yi abin ki sai ta gaji ta
koma daki sai kiyi fitowarki, na ce mishi to.
Amma duk da haka jikina ya kai matuka wajen
tsorata sai bari nake yi, ya zuba min ido yana
kallona ke menene haka? Na fa zunubi muka yi ba
ni mijinki ne ke matata ce.
Na ce mishi uhun, ai ni babu abin da yafi
damuna da tsayuwar min a rai irin bazuwar
maganara cikin gidannan da yanda za'ayi ta yadata
ana cancanzata, cikin sauri ya ce min ke kar ki

156
nemi ki maida mutane wadansu iri mana. Goggo
Ayallen da girman shekarunta ne ki ke cewa za ta
yada wannan maganar?
Kina so ki ce ita din bata san girma da lalurar
aure ba ne? nayi kamar in ce to ai a sanin girma da
lalurar auren nata ne taja ta tsaya a tsakar gida a
cikin tsohon daren nan ten wage balkinta tana
kwalawa sunana kira tanfar wata yarinya yar
Karama.
Bayan kuma tasan karamin mnotsi ma dare bai
raina shi ba, balle wannan ihun da ta rinka yi
wanda ba mutanen da ke cikin gidan nan ne kadai
za su jiwo ta ba, har makwabta sai sun ji.
Sai kuma na ce uhun, bari dai ma kawai in
kama bakina in yi shiru, kar in jawowa kaina wata
magana tsakanina da shi a wannan lokacin da na
san ba karamin abu zan fuskanta a cikin gida ba, in
fadi wata magana ya ce na yi wa matar Baban shi
rashin kunya.
Rako ni yayi nayi wanka yana tsaye yana jiran
fitowata sannan ya tasa ni a gaba ya kai ni har
kofar dakin Goggo Ayalle. Ya kalle ni cikin
natsuwa da murya mai sanyi ya ce min shiga kiyı
kwanciyarki na sake daga ido na kalle shi.
Fuskata ta bayyanar da alamar tsoro yayin da

157

zuciyata ke ta faman harbawa da sauri ya sake
kallona fuskarshi ta bayyanar da murmushi mai
yawa daina jin tsoro Humairah.
Ai ni mijinki ne ba wurin wani kika je ba kin
amsa umarnina ne na kuma gode miki iyakar
abinda Goggo zata yi in ma ranta ya baci ta ce ki
koma dakinki gobe shi kenan, amma ba za ta je
tana yáda wannan maganar ba.
Ai ita babbs ce, in kuwa haka zata yi to ai ai
yafi min na riga na gaji da wankan naki, lin gane?
Na gyada kai nuna alamar eh, don ni kam ko bude
bakin nawa in yi magana bana iyawa, saboda
kaduwar da nake yi.
To shiga mana, na kaile shi cikin natsuwa a
hankali cikin muryar da tafi kama da rada na ce
mishi, to jeka ka kwanta zan shiga.
Ya ce uh'uh ai ba zan bar ki cikin daren nan a
waje ba in haka yasa na tura kofar a hankali na
shiga. Cikin sa'a gaba daya dakin a duhu yake nayi
matukar jin dadin hakan don haka na lallaba a
hankali na dale kan gadona, ina shirin kwanciya
kenan sai kawai naga Goggo ta hasko ni da
tochlight dinta.
Ashe wai duk abin nan da ake yi duk da
dadewar da nayi ban baro wurin Ado ba, duk da ita

158

yarinyar tuni ta hakura da kukan nata ta koma
baccinta.
Ita Goggo bata hakura ta kwanta ba, tana nann
zaune dingir a tsakar dakinta bata ma yarda ta hau
gado ba, don kar tayi gyan-gyadi da bacci zai
dauke ta har in shiga bata sani ba.
Don haka tayi zaman dirshan a tsakar daki tana
Jiran sai taga zuwana wai ita nan a dole sai taga
KWALUWAR DAKA'.
"Ina ki ka fito? Ruwan me ke diga a jikinki?
Jegon kenan? Dama damuwarki kenan yasa kika yi
ta tasa yaron nan a gaba da koke-koke? Haba ni
fa...kuka na soma yi wa Goggo kuka kuma mai
tsanani, saboda tambayoyin nata sun yi min tsanani
da yawa.
Kukanki din banza da na woff? Ina...daga waje
Ado yayi gyaran murya mai karfi, wai dai don
Goggo tasan shi din bai yi nisa ba yana wurin ko
zata yi hakuri ta bar maganar tata.
Ban sani ba ko bata gane abinda gyaran muryar
tashi ke nufi ba ne ya hana ta saurarawa ta ci gaba
da fadin ina amfanin ace mace ita ce fitinanniya?
Namiji bai damu ba sai kece...
Uh'uh Goggo, uh'uh Goggo, abinda ya ci gaba
da fadi kenan don kara yi wa.Goggo Ayalle

159

kashedin maganar tata, yayin da ni kuma gabana ke
ta faman harbawa saboda tsoron kar ya ce zai tanka
mata.
Gaba daya fatana da burina bai wuce ya bar
wwrin tsayuwar tashi yayi tafiyarshi wurinshi, ba
Care da ya bude baki ya ce mata komai ba.
Saboda nasan yin maganan nashi ba zai taba
haifar mana da da mai ido ba, fin barin maganar da
Goggon tayi shi ne ya hassalar da Ado har yayi
dalilin da ya toro kanshi cikin dakin ya ce mata ba
ita na ce Gogggo ni ne, ba ita ba ce kyale ta kawia
ni ne.
Abinda kawai naji Ado ya gayawa Goggo
Ayalle kenan sai kawai naga ta fashe da kuka tare
da salati mai tsananin karfi.
Mu tafi littafi na hudu don jin yanda za'a kare
tare suke'.

Fatan alheri gare ku dukanku taku,
Hafsat Chindo Sodangi
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
24 ga watan uku 2013
07035586299


160



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login