Showing 18001 words to 21000 words out of 30903 words
matan suka
same ni muka yi hira da su, sai da ya gama ya aika a
kira ni.
95
A hanya muna dawowa Ado yana bani labari, kai
biyan bashi da dadi Humaira, kai da ka biya ka ji
dadi shima wanda ka baiwa ya ji dadi.
Balle shi Mallam Haruna ma bai dauka zan
maida mishi da kudin ba. Nayi maza na ce don me?
Ado ya ce mutanen yanzu fa ba wani damuwa da
biyan bashi suka yi ba.
Na ce, hu'un, ai kuwa dai suna daukarwa kansu
jidali.
"Kinga iyalin Haruna ko? Ga gidanshi ga
ya' yanshi gashi yana noman nan, yana kuma taba
kasuwanci. Komai nashi gwanin sha'awa ko? Na ce
ni ban sani ba, na dai san kawai bai fika komai ba.
In dai ba yawan matan nashi ba ne yake ba ka
sha'awa, to, to shi kenan mu bar maganar, na ce eh
gara mu bari.
Ana cikin haka rannan girki yazo kaina, kafin
zuwan ranar kuwa babu abin da Ado bai tanada ba na
kayan amfani, tunda ga bokitaye, robobi, kwanuka,
kore, ludaya, cokala suna kammale.
Ina tashi da safe na kammala ayyukan wurina,
nayi duk abin da zan yi na jira Ado ya dawo kamar
yanda yayi min umarni, gabana sai faduwa yake yi,
ina dai ta faman addu'a.
Kar fa ki ce za kije kiyi wahala mai yawa ga
buhun shinkafa can na kawo, in kinga ba za su
96
taimake ki ba sai ki juye ta kawai gaba daya, ki juye
mata abin hadinta akai in ta nuna za'a ci.
Nayi murmushi na ce mishi, to na fita. Ina fike
da tsintsiyar zabori a hannuna don share wurin yin
girkin, da kuzarina na fita sai dai ina dosar wurin na
susuce.
Tun daga nesa dai na hango buhun shinkafar da
Ado ya kawo a kwance a kasa, ga kwandon tumatur,
attaruhu, albasa da tattasai, ga galan din man gyada
da ledar maggi da su kori da sauran kayan hadin da
ya san ina amfani da su.
Ina dosar wurin naji matan gidan suna shewa
suna fadin "Lalle yau za'ayi sha'ani shinkafa? Matar
so zata yi girki, Ruwaila kuwa sai cewa tayi mutanen
birni ne yaushe za su je suna taba dawa? Ai sai mu.
Nayi kamar ban ji su ba, na gaishe su suka amsa
na wuce naje na kawar dá buhun naja shi na jingine
shi, na kama sharan wurin na share shi tas na kwashe
tokar da take murhu.
Naje na debo itace na kawo wurin, ban ankara ba
sai kawai naga gaba daya sun sulale sun watse sun
barni ni kadai a wurin ko wanda zan yi wa tambaya
in wani abu ya daure min kai babu.
Na leka tukwanen da zan yi amfani da su babu
wanda aka wanke gaba daya kayan wanke-wanken
yana tare a bakin rijiya, randunan da ake tara ruwan
97
girkin ma babu komai a ciki.
Don haka na tafi wurin Ruwailah tunda ita ce ta
riga kowa karbana a gidan sannan kusancin da ke
tsakanina da ita ma yafi yawa.
Cikin natsuwa na kalle ta na ce mata babu ruwa a'
randunan kuma ina so ki hada min itacen murhun
don wutar ta kama sosai.
Sai kawai naga ta zuba min ido tana kallona cikin
wani yanayi "Dama kin mike kin yi aikinki tunda
kema ba taimakon wasu kike yi ba.
Al Da zai yiwu kema kice sai an taimake ki ba, in
zaman jikin miji ne babu mijin da baya so á zauna
mishi sai dai in bai samu ba ya hakura.
Don babu wata matar da mijinta ba ya sonta,
tunda duk daya muke amfanin da ki ke yi wa mijinki
shi nake yiwa nawa mijin, shi ko wace mace ma take
yi wa nata kin gane?
Na ce mata eh, na juya na tafi, na nufi bakin
rijiya tana fadin au, tafiya ki ka yi tun ban gama yi
miki bayanin ba? Ban sake sauraronta ba.
Na dauki guga na jefa cikin rijiya da nufin debo
ruwan da zan yi aikin da shi, sai ga Ado ya shigo
wurin, abin da ban ta6a ganin yayi ba tun zuwanmu,
tun da yasan wurin zaman mata ne.
"Ke me ki ke yi a wurin nan? tambayar da ya
soma yi min kenan, ban iya amsawa ba saboda in na
98
ce zan y1 magana zan yi kuka.
Ajiye gugar ki tashi a wurin, na ci gaba da jawo
gugar, tunda na riga na cikota da ruwa ga nauyi.
Ajiyeta kuma yana nufin ta koma cikin rijiyar.
Ganin da yayi ban ajiyeta ba ya sanya shi
Rarasowa wurin yasa hannu ya karbeta daga gare ni,
wannan rijiyar da ba a ganin cikinta ne za ki zo kina
jan ruwa a ciki?"
Ya dangwarar da gugan a kasa ruwan da na jawoo
din ya kife, ya wuce ya fita. Ina tsaye ina tunanin
abinda zan yi sai naji wata a cikin matan da şuke
dakin Ruwailah tana ce mata wai fa matan so zasu yi
girki a gidan nan maza sai zirga-zirga'suke yi.
Ta ce, ai zai ga tsiya ai sai dai ya cire rigarshi
yayi mata girkin, haba ina amfanin namiji ya susuce
ya zama 'MIJIN TACE' kamar Ado ya laface akan
wannan yarinyar ya záma sai yanda tayi dashi, wai
har yana cewa suna aka tara.
To da me tafi wata? Gaba daya suka kwashe da
dariya suna fadin to shi ba tashin ya sani ba.
Taja wani mummunan tsaki da ke kara baiyanar
da tsananin bacin ranta, ai ni da su ne a gidannan
zasu ga tsiya, zan ga yanda za'ayi sujr dadin zaman,
sai dai in zasu tattara su koma in da suka fito, ko da
yake dai can din ma koro su ita Hajjyar tayi.
Tana tayin maganganun bata san Ado ya shigo
99
ba, yaran Almajirai ya kirawo ya kirawo guda biyu
wadanda dama sanannu ne a gidan Hamza da Bala,
ya nuna musu tarin wanke-wanken da.aka tara vace
musu su wanke su kuma debi ruwa su cika randuna
suka ce mishi to.
Daga muryar da yayi ya kira Furera, shi ya
fahimtar da Ruwailah mai rantsuwar Ado zai ga
tsiyar da zata yi mishi tasan yana wurin nan.da nan
tayi tsit.
Furera ta fito tana gyara daurin dan kwalinta
tana murmushi lafiya yau maigidan yake yawo a
wurin da mata suke girki? Ko ba ya koshi ne?"
Bai saki fuska ba balle ya rama mata wasan da
tri nishi, sai ya ce mata taimakona nake so kiyi ki
hadawa Humaira wuta ki kuma tsaya ki kula da
girkin ko ba za ki iya ba?
Da sauri ta ce, to me zai hana? Ya ce to na gode.
Yajuya zai tafi tayi maza ta sake ce mishi in dama ba
kana so ta zauna a wurin don ta ga aikin ba ne ai da
tayi tafiyarta.ma za'ayi.
Ya sake cewa to na gode, ya wuce ya tafi, na
tsaya zan taya Furerah aikin da ta unguma da hannu
bibiyu zata yi, sai kawai ta kalle ni cikin murmushi ta
ce ke tafi ki je wurin mijinki kin ji?
Kiran da Ado ya yi wa Furera ya danka mata
aikina a hannunta ba karamin abu ba ne wurin
100
Ruwailah, don a zahiri ne kawai suke abokan juna na
kut-da-kut, amma a 6oye abokan adawa ne.
Don ita Furerah ma ita ce uwar dakin amaryar
Ruwaila ban da haka kuma ita din bata yi zaton zai
iya yin hakan ba, don ganin ba sasansu daya da
Furare ba.
Sannan ita Ruwailah ban da zumuncin ita mata
wanshi ne na sasa daya akwai kuma zumunci na jini,
don haka ta dauka dole dai ita zai nema.
Ina tare da Ado a daki da daddare nayi mishi
kwalliya da sabuwar rigar baccin da ya zo min da ita
daga Zaria, sai kamshi nake yi, yayin da shi kuma
yake zaune daga shi sai dogon wandonshi na Track
Suit.
Yana tashe da laptob din shi Intenet ya shiga
yana bincike kan noma irin na zamani, ni kuma ina
kwance a gefenshi nayi filo da gefen cinyarshi ina
kallon abin da yake yi.
Yana kuma kara yi min bayani kan abin da na
tambaye shi, sai kawai Furera tayi sallama a bakin
kofa, ya amsa ya ce mata shigo mana. Nayi maza na
tashi na zauna na jawo dankwali ina daure kaina.
Suka gama gaisawa, sauran kayannan ne na
kawo, ga shinkafa mudu zai kai bakwai nayi amfani
da mudu ashirin da biyar ne ga... ya katse ta, je ki da
su Furerah da rana sai ki girkawa yaran wurinki, tayii
101
ta godiya ta tashi ta tafi.
Tana fita ya ture laptop din nashi gefe yasa
hannu biyu ya jawo ni jikinshi, kin san yau kuwa yau
wata uku daidai tun da ki ka yi rashin lafiyar nan."
Dan langabe nuna yana yin zolaya na ce mishi
bana lissafi, ya dan rage fara'ar shi ya ce to ni ina yi
wani lokaci kuma nakan tambayi kaina, to ko dai
nayi kuskuren ne.
Kamar yadda Goggo ta ce, nayin da na bari aka
yi miki wankin cikin? Nayi maza nace mishi baka yi
ba ban yi ba? Na ce mishi eh, baka yi ba, lokaci ne
kawai bai yi ba,
Kankame ni yayi da iyakacin karfinshi yana
tambayata, to yaushe ne lokacin? Kin kuwa san
haihuwar da aka yi wa Malla Haruna ta shekaranjiya,
ita ce ta sha bakwai?
Na ce, uhun! To sai me? ya zuba min ido yana
kallona, ina sonki Humaira, ko ace dandani-haukaci
ki ka yi min ko ace wani abu aka wanke aba ni nasha,
ni na gode da hannuma ma in aka bani zan iya kaiwa
bakina insha kin ji?
Ban tanka mishi ba, kiri-kiri a gidan nan
Ruwailah tayi dalilin da aka radawa Ado sunan
'MIJIN-TACE' wai shi din ta ce, ne wai bai da
katabus sai yanda aka yi dashi.
Ado da nake ganinshi jarumi in na ce jarumi ina
102
nufin akan komai ma shi din jarumin ne. wajen
neman halal din shi wajen tsayuwa kan ra'ayinshi a
gida ne kuwa ko a waje musamman ace ra'ayin nashi
akan gidanshi ne.
Tunda nasan kullum nai ce nake bin umarninshi
nake kuma barin ra'ayina in koma nashi don mu
zauna lafiya amma wai shi ne MIJIN-TACE da
zuciyata tayi kunci na tsunduma cikin tunani mai
tsanani, saboda bakin cikin kira min jarumin mijina
MJIN-TACE.
Da tunani ya tsananta gare ni, sai na tunano
Babana, na tuna marasa mutuncin unguwarmu har
nuna mana gidanmu da dan yatsa suke yi suna fadin
wai gidan mijin tace kenan, nace to ko dai shima ba
mijin tacen ba ne sharri kawai ta kama ni a dalilin
tausayin shi da yafi matukar kamani.
A hankali cikin zuciyata na shiga fita da addu'ar
ina ma dai ya huce ya daina fushi dani, don wata rana
in samu damar zuwa gabanshi don in roke shi gafara
kan laifin da nayi mishi?
Tunda Furera ta karbe ni hidimar girkin abincin
gida sai take ta kokarin sanya ni cikin al'amuranta
misali haihuwa ko baki da suka dangance ta zata
gaya min ta ce in gayawa maigida in ya bar ni sai
muje tare don mu saba da jama'a tunda shi mutum
shi ne babban arziki in bai bari ba babu damuwa in ce
103
mata to.
Rannan kanwarta da suke ciki daya ta haihu tazo
har dakina ta gaya min nace mata wanan kam dani
za'aje tayi murna sosai.
Ado yana dawowa na bashi labari, ya ce to in
lokacin ya matso sai ki tuna min, na ce to. In ka samu
sarari sai ka saya min rigar yanmata in bata don
mace aka haifa.
Ya ce min to, yana fita kuwa sai ga shi yazo min
da riga mai kyau na kai mata tayi ta murna.
Tun ana jibi suna na tuna mishi ya ce to, ina ta
murna nima zan fita unguwa tare da matan gida
abinda ban taba yi ba ana gobe sunan ma na tuna
mishi bai yi magana ba.
Washegarin suna ina gama aikina nayi wanka na
zauna nayi shafa na gyara jikina, yayi tsaf sai kamshi
nake yi na dako sabbin-under wears dina na sanya
tunda su kam ban taba rashinsu ba.
Duk rashin kudin Ado ba taba fashin sayen under
wears rigunan bacci da man shafawa ba, ko turare.
Ina tashe da atanfata dana ciro don daurawa,
cikin zuciyata ina tunanin Ado, tunda ya fita da safe
bai dawo ba, gashi har rana ta fito, mutan gida kuma
duk sunyi shirin tafiya baya nan, zuciyata ta raya min
in har aka ce in fito ba dawo ba, tafiyata zan yi tunda
ya san da maganar sanda na gaya mishin, kuma ba
104
musu yayi ba.
Ina cikin wannan tunanin sa gashi ya shigo rike
da leda mai dauke da robar yourgout da kuma fura a
ciki.
Ungo dama in na kalle shi cikin natsuwa na ce
mishi, ko za kayi hakuri ne kawu duk sun riga sun
gama shiri, ni kadai suke jira ka kuma san matan
gidannan kara ce dasu, in hidimar mutum daya ta
tashi sai kaga duk an dunguma an rufa mishi baya.
Ya ce, eh ai kirki ne da su, na ce eh, sai kawai
naji ya ce min, amma ba da wadannan sabbin under
wears din za ki ba ko? Wadannan ai kin san don
kaina na saye su me yasa za ki bude su bananan'?
Na daga ido na kalle shi ya bata rai sosai ji kuma
irin kamshin da. kike yi a haka ki ke shirin tafiya
gidan sunan? Wannan ma ai rainin hankali ne cikin
natsuwa da sanyin murya na ce kayi hakuri ka barni
in tafi na yau, tunda nasa mata rai, in yaso na gobe ka
hana ni."
Ya ce, a haka a kamshin da kike yi? Ai alhaki ma
sai yayi miki yawa, gara kawai ki sake wankan, na ce
to. Ina cewa to din ya matso jikina, to zaki yi wanka
mara dalili ne. Humaira bayan kin yi shafan nan mai
kyau ai bari ki ga hikimar da za'ayi ai gara kawai a yi
mai dalili sai kiyi kawai gaba daya kan nan ma kowa
ya gama shirinshi maimakon kije kiyi ta jiransu.
105
Babu halin in ce zan yi musu dashi kan bukatar
tashi sai ya ce kan tafiyar zan sabawa umarnin da
yayi min, saboda haka nayi hanzarin sallama mishi
kaina ban tsaya ja mishi rai 'ba, don nima yayi saurin
sallamata.
Sai dai abin takaicin shi ne, ina shiga hannun
Ado na mance da komai, ya sanya ni ciki wani hali
da ya kidimar dani, ya hanani tunani balle jin wani
motsi.
Ban sake tunawa da komai ba balle in tuna a
cikin sauri nake don kar in yarda in biye mishi, sai
bayan da na ganshi kwance a gefena kokarin ne na
tuna abin da ke gabana.
Zunbur nayi na mike cikin sauri na mufi ban daki
nayi wanka da ruwan sanyi aazo ina shiri hankalina a
tashe saboda shirun da gidan yayi min yayi yawa da
sauri.
Na sanya kayana ba tare da na tsaya shafa ba na'
fita naje don in gani ko sun gaman suna jiraa nawwa
babu kowa a gidan gaba daya sasan babu kowa sai
yar gidan Fureran budurwa Hasiya.
Na ce ke Hasiya tafiya suka yi basu gaya min ba?
Ta ce sun gaya miki baki ji ba ne? Na ce sun gaya
min wa ya gaya min? Ta ce ni ta aika sau biyu ina yi
miki magana ba ki ba.
Na dawo daki raina a bace gululun bakin ciki sai
1O6
yawo yake yi tsakanin wuyana da makogorona, na
dawo daki har lokacin Ado yana nan a yanda na bar
shi barci ma yake shirin yi bakin ciki da takaicinshi
suka kama ni har ban san lokacin da na soma kuka
ba.
Cikin sauri ya bude ido yana tambayata menene?
Ban kula shi ba, balle in tsaya yi mishi magana ba ki
da lafiya ne? Ban kula shi ba, menene ya same ki? Na
ki yin magana har ya gaji ya dawo kan hanya sunyi
gajin hakuri ne.
Haka suka tafi suka bar ki? Ban amsa ba yayi
maza ya mike bari in yi wanka in zo in kai ki ke da ki
ke da babur ma menene abin 6acin rai a ciki?
Nayi shiri Ado ma ya shirya muka fita ya burga
mashin na hau bayan shi muka kama hanya a yanda
duk suke fada kauyen Tukunya kusa kwarai take da
Dabai. Muna tafiya naga bamu je da wuri yanda nayi
zato ba, na ce mishi har yanzu ba mu zo Tukunyar
ba?
Yayi maza ya ce min Tukunya dama ki ka ce
zamu? Nayi maza na ce, to da ina ka ji na ce? Ya ce
Randa na ce, a'a ban da Tukunya akwai wani kauyen
ma Randa ne a nan kusa?
Ya ce min eh, na ce to ai Tukunya na ce maka ya
ce, to ai Tukunya na ce maka ya ce to ai babu
damuwa bari mu gaida wadannan sai muje Tukunyar
107
na ce to.
Ya tsaida mashin din shi gaban wani gida mai
tsananin tsabta ga ko'ina an dabe shi an kuma share
shi gwanin sha'awa.
Wani farin Dattijo mai wadatar farin gashi a
fuskarshi yana zaune kan farin buzunshi a gindin
wata katuwar bishiya mai yawan gaske.
Yana rike da carbinshi a hannunshi yana ja, cikin
natsuwa Ado ya kalle ni ya ce min, "Gidan Kawo'
kenan wannan da ki ke hange shi ne Baba Sambo.
Sanda mahaifina yake raye bai da wani Aminin
da ya fi shi, kin kuma san an ce mu sadar da
zumuncin iyayenmu ko bayan ba sa raye ko? Nayi
maza na ce eh, haka ne.
Muka karasa gaban dattijon nan cikin yanayi na
giramawa yana gane Ado ya gyara zamanshi cikin
fara'a da murmushi, ya amsa sallamar da Adon yayi
mishi, ya kuma shiga yi mana sannu da zuwa, Ado
yana amsawa.
Can kusa dashi yaje ya tsuguna yayin da ni kuma
na tsuguna daga baya, amma yana hangena tafin
hannunshi ya dora akan Ado tanfar wani dan yaro a
hakan ya ke yi mnishi magana, da alamar dai akwai
shakuwa da kulawa a tsakaninsu.
Wannan ita ce iyalintaka? Ya dago ido yana
kallona cikin nuna alamar jin dadi, sannu kin ji
108
yarinya, sannu Aishatu, sannu kin ji sannunku
Ubangiji yayi muku albarka, ya kuma jikan Mallamn
Sulaimanu."
Ado yayi maza ya ce, "Amin Baba." Ya ce, "Kar
ayi wasa da yi mishi addu'a, amfanin barin da a
duniya kenan, ka kuma san kai kadai ya bari." Ado
ya ce, haka ne Baba.
Muka dan yi hira, Ado ya ciro kudi ya bashi, ban
san nawa ne ba, yayi tasa mishi albarka har nima
yazo ya burga mashin din shi muka hau muka tafi.
Wata hanya ya biyo da ni da bangane ba, wasu
gine-gine nake gani da ban taba ganinsu ba, nan
kuma ina ne? nayi mishi tambayar cikin natsuwa ya
ce min "Dabai mana Humaira, ban biyo da ke ta inda
ki ka saba bi ba ne."
Tuni na shagala ina kallon gidaje da layuka har
da su kwalta a shimfide cikin unguwanni, ga
rijiyoyin burtsatse a ko ina, na ce kai Kawu, Dabai
din nan ma fa ba wani kauye ba ne, ai ban san haka
take ba sai yau.
Dubi gidaje har da tunkunan ruwansu, ga titina
ga fanfunan burtsatse birjik, ga lantarki har mutane
da yawa sun sanya a gidajensu, mas'alar dai kawai ba
ku da babbar kasuwa.
Wani irin lallausan murmushi Ado ya saki cikin
natsuwa naji ya ce min, sannu. A hankali dai in nayi
109
sa'a Dabai zata yi miki halin nata ta dabaibaye min
ke, ta maida ke 'yar gida har ki mance garinku.
Kin ga shi kenan sai muyi zamanmu mun huta da
kowa sai in kuta jin ana cewa an yi mafarkin anje
gida an ga an canza kofar gidan ko anje gida anga
Sa'adatu balle kuma aje ana mafarkin anje gida Baba
yayi kora da sanda.
Tsuke fuska nayi na ce, ai ni ba zan taba
mancewa da garinmu ba, kuma ma ai ta nan wurin ne
in da ba kauyen ba ne ta can wurinku ku kauye nel?
kan mu karasa gida muka yi fada da Ado, don haka
nan da na ganshi ya kafe