Showing 24001 words to 27000 words out of 30903 words
magana ba ne yasa shi yi min
hukuncin da yayi min, to na daina yi mishi magana
124
VAvi min abin da yafi wannan tsanani.
Har aka yi Sallar La'asar bai ji na bude bakina
na ce wa weai wani abuba, balle yasa ran zan yi
mishi na kuma ki yarda da cewar da yayi in tashi
muje asibiti,
Ina kallonshi ya jawo wayarshi, kalaman shi
suka fahintar da ni da Innata yake yin maganar
gaskiyar abinda ya faru tsakanina dashi, ya gaya
mata abin da nayi mishi da wanda shima yayi bai
rage komai ba.
Haka nan bai kuma fara ba, da kuma halin da
ake ciki a yanzu duik sai de ya gaya ata.
Ban ji ita abin da take gaya mishi ba amma na
ji shi yana amsa mata da to Inna sai kuma neji shi
ya ce mata to gata, nayi kamar in ki kar6ar wayar
sai kuma naga to in ranta ya baci fa?
Alhalin bacin ran Babana shi kadai shi ne ya yi
min wannan sanadin, to in ya hada har da nata fa?
Ya ya zan yi? Nasa hannu na karbi wayar ina jin ta
soma yi min magana naji muryarta.
Sai kawai na soma kuka, kuka kuma mai
tsanani ina jin itama ta gane ina cikin bacin rai mai
sanani ne yasa ta talkaita maganar tata da cewar
tunde dai ya zabe ni ya kawo maganar gabana ina
ganin ya kamata ta kare don girmarma ni yayi.
125
Ga manya nan a gidan naku bai kai maganar
gabansu ba saboda yana ganin in na gaya miki zaki
ii, in kuma kin ga ba za kiyi min wannan alfarmar
ba duk matar da ki ka gani a dakinta tana zaune, to
hakuri talke yi.
Ba kuma zai yiwu ace kina zaune da miji amma
ba za ki girmama shi ba, in yaja sai kema ki ja
saboda lina ganin kin isa. Wannan ba tsarin aure ba
ne na Shari' a ya zama auren 'yan iska.
In kuma kin ga irin shi ki ka fi sha'awa sai kiyi,
sannan zan yi miki kashedin ki daina fada da shi a
gaban yan uwanshi. Ki rike sirrin da ke tsakaninki
da mijinki, ki gamsu da alherinshi tun ba ki kure
hakurinshi ba.
Inda za ki daina jin jita-jita kuma kina amfani
da zato to da zai fiye miki amfani, in kin yarda da
abinda na gaya miki ki bashi hakuri, na ce mata to.
Tana kashe wayar na sunkuyar da kaina kasa
na ce mishi, kayi hakuri, bai taba tsammanin abin
da zan gaya mishi kenan ba, wata Kila jira yake yi
mu gama maganar shi ya bani hakurin.
Dadi ne yayi matukar kama shi yesan in na ce
ta sani ba shi hakurin, dawowa kan katifar ds nake
kwancem yayi ya dago ni ya kwantar a jikinshi inna
tana sona Humaira, in ma dai ke ce ki ka fahimce ni
126
irin fahimtar da tayi min?
Sau dava nake fadin gaskiyata ta yarda da ita,
amma ke baki yarda da ni ba, yaya za'ace miki na
ajiye wata mata a wani wuri ki yarda? Sannan in
ban da Inna tayi miki magana ta saki ki bani hakuri
ke kina shirin muyi tashin hankali ne.
Ni kuma ba ki sani ba tausayinki nake ji na
rabo ki da iyayenki da danginki na kawo ki cikin
nawa na ajiye ki ni da ki ke ganina ban cika son
muna samun matsala da ke ba.
Iyaka dai ba zan yarda da wasu halayen da ki
ke fito min da su ba ne don ko da ki ke jin ana ce
min 'MIJIN TACE' in ma dashi ki ke lura to na
rantse miki ni ba shi ba ne.
Sannan masu kawo miki bayanin abinda nake
yin dama ko menene? Da yake zama sanadin fada a
tsakanina da ke in na nemi aure a danginsu fa za su
jagoranci a bani in kuma kina ganin karya ne to.
Na daure fuska na ce to a baka mana sai me?
Rannan haka muka kwana da Ado maganganu
masu kwantar min da hankali yake tayi min na
yanda zamu fahimci juna mu zauna lafiya, ban
tanka mishi ba muka yi kwanciyarmnu yana
kankame dani a jikinshi bai kuma nemi komai ba
daga gare ni.
127
Washegari tun daga fitowarshi Masallaci Sallar
Asuba ya yi shiri ya ce min zai tafi Danja, na ceto
sai ya dawo, nayi mishi addu'ar da ta dace in yi
mishi, ya kama hanya ya tafi.
Wunin rannan ma ban fito ba ina dakina, ina
kwance kan katifata tunanin al'amura kawai nake
yi a zuciyata. Hasiya tazo tayi min duk abinda ya
kamata tayi min ta tafi ta bar ni ni kadai.
Tuni na kudurawa zuciyata bin hanyar da zan
zauna lafiya da mijina, in daina daukan zancen
wani ko bin shawararshi tunda na gane hakan ba
zai amfane ni da komai ba.
Sai dai yayi min sanadin wahala da 6acin rai
mai tsanani, babu kuma wanda zai agaza in da wani
abu sai dai ma in an gane halin da nake ciki ayi ta
zundena ana yi min dariya.
Don haka na yanke wa kaina shawarar ajiye
makaman fada in bi hanyar lallama da rarrashi da
bin umarninshi akan komai in dai baya sabawa
Shari'a ba ne shima kuma nasan da wuya yasa na
saba shari'ar.
Don kuwa mai kokari ne akan kiyaye dokoki
tunda na gane abin da ake yi wa wasu mazan a
kwashe kalau shi kam ba zai lamunta ba dama
kuma Hausawa suna da karin maganar da suke
128
cewa, wai in da wani yayi rawa aka yi mishi kari,
in wani yayi to dukan tsiya yake sha.
Nayi sallar La'asar nasa ruwa nayi wanka irin
wanda na dade ban yi ba, don kuwa rabona da in yi
wanka har na manta, tun da bakin cikin Ado ya
kwantar da ni. Ni da kaina tsamin jikina nake ji.
Na fito nayi alwala don yin sallar magarib da
Isha'i, sannan na zauna nayi shafa mai kyau na
gyara jikina sosai tun daga gashin kaina har farcena
babu abin da ban gyara ba.
Sanyi ya sauka min har cikin zuciyata saboda
ni' imar tsabta da na sau, kai kazanta dai musiba ce,
ni da kaina na gayawa kaina hakan.
Nan da nan na mike na canza zanin gadon da
ke shinfide kan katifar na shimfida, wankakke,
gogagge, na fesa freshner mai sanyin kamshi na
kuma kunna turaren tsinke a bayan gida na jawo
dan kofan tsaki gina na koma dakina na zauna ina
jiran lokacin Sallar magrib tayi.
Cikin zuciyata dai bani da wata matsala illa
jiran in gabatar da sallolina insha tea in kwanta
tunda nasan ni da ganin Ado watakila sai gobe da
yamma ko kuma ma ranar Allhamis.
Na idar da Sallar Isha'i na kulle kofata na dawo
ina hada tean da zan sha kafin in kwanta tunda ban
129
yi girki ba ban kuma aika an karbo min abincin
gida ba sai naji ana taba kofa nayi maza naje na
bude don ganin ko waye?
Sai naga Ado na kauce daga kofar ya shiga
nayi mishi sannu da zuwa ya amsa da har kin rufe
kofar ne? na ce mishi eh, yana cire kayan jikinshi
alamar wanka yake shirin yi yana tabayata me ki kaa
girka ne?
Cikin natsuwa na ce mishi ban yi giki ba
saboda ban san zaka dawo ba, in ba zan dawo ba ba
za ki girka abin da za ki ci ba? Kin ga irin ramar da
ki ka yi kuwa? Ya maida rigarshi ya fita.
Tunda Ado ya dawo ranar Talata da yamma bai
sake tafiya Danja ba yana gida bai kuma fita ko'ina
in ba sallama aka yi dashi ba.
Zuwa nayi na gayawa Princepla da yake akwai
fahinta a tsakanin na ce mishi akwai matsala a
gidana, ya ce to in je ya bani wannan satin sai na
roki wani Malami ya taimaka min da darussan
nawa don kar yara su cutu.
Ya dago idanuwanshi ya kalle ni doon a kwance
yake sanda yake maganar. Sai dai kuma gashi na
dawon tun ba aje ko'ina ba har na gundure ki kin
gaji dani ban tanka mishi ba don nasan me yake
nufi.
130
Tun daga wannan lokacin mu'amallar Inna da
Ado tayi matukar karuwa, na kuwa gane hakan ne
daga yawan kiranta da nake ganin yanayi, ba zai
yiwu sai rikici ya taso min a gida in rinka kiranta
tana kwantar min da fitinar ba.
Abinda ya gaya min kenan rannan da na ji su
suna magana ban kula shi ba, na dai san kawai yana
ganin girmanta da darajarta yana kuma girmamata
da iyakacin gaskiyar shi.
A wannan lokacin ne na gane gaba daya mataan
gidan bakin su daya ne haduwa suke yi suyi
maganganinsu kan abinda ya shafe ni ni da Ado.
Illa iyaka kawai ita Furerah ta ki yarda ta daina
karbar girkina tana yi saboda tana matukar amfana
dashi. A zahiri kuma tana nuna ita babu ruwanta ni
tata ce saboda alherin da nake yawan yi wa
ya'yanta.
Don haka sai na hada su gaba daya nayi musu
jumiah guda daya dukansu ina girmama su bana
kuma jin zafinsu tunda na gane damuwarsu bata
wuce ta kulawar da mijina yake da ni ba.
Ado bai daina zuwa Danja ya kwana ba na
kuma cire raina a kan hakan randa yake gida ma
mafi yawancin lokaci yakan raba dare ne biyu yana
waje bai dawo ba.
131
Ban kuma damu ba duk da 'yan maganganun
da ake yi in an ganni, nasan yana wurin lambunshi
yana lura da yanda ake ban ruwanshi.
Wani lokaci ya dawo ya samu ina zaman
jiranshi, wani lokaci yazo ya samu nayi bacci,
randa yaga zai tashen ya tashe ni in yi mishi abinda
yake so in yi mishi.
Randa yaga zai hakura ya bar ni in yi barcina,
shi yasa ma mafi yawancin lokaci in naji yana tayi
min kashedin kar fa kiyi bacci ki jira ni ce mishi
nake yi gara dai in ka dawo ka tashen, don ba zan
iya wannan dogon hirar ba a wannan duhun ni
kadai.
Yawan itar da nake yi wa Ado akan duhu ya
sanya shi yana fara diban labun nashi ya kashe
kudi mai yawa ya sanya wutar lantarki a gidan
gaba daya.
Ya kuma gyara katangar gidan yayi mata kofa
daya, yayi wa zauren gidan kyakkyawan gyara,
soronshi ya zauna daidai maimakon da da yake
barazanar zubowa, amma bai yi musu gwaninta ba.
Su Ruwaila wai cewa suke yi aikin banza, tun
lantarki yana sabo a Dabai ba a sanya mana shi ba
sai yanzu da ya zama gidan kowa da shi, kuma dubi
hanyoyin nan da muke samu muna shiga makwabta
132
hankali a kwance wai don fitina yasa an toshe.
Yanzu babu halin ka fita sai ka nemi izini, kai
zama da fitinannen mutu dai wuya ne dashi, sai
kayi hakuri.
. Ni kam tunda na gane mijina na kuma gane
halinshi na gane yana sona yana girmama min
mahaifiyata yana tattalin yan kannena sai na.
kudurawa kaina yin hakuri da shi da duk wani abin
da ya shafe shi.
Ban ganin yayi wani abu in ce mishi don me?
balle in je ina tambayarshi dalilin da yasa yayi har
akai ga jallin da zan ce ban yarda ba na daina.
Shi kuma in ya ga nayi mishi ba daidai ba ya
kama zai yi fada tunda shi baya iya ganin an yi bai
tanka ba sai in ba da hakuri ko da kuwa ina sane
nayi don ya ji in da dadi.
Don haka yan uwanshi başa bata min rai
komai suka yi min ban tankawa saboda na san
fitinata da su ba za ta saman mishi farin ciki da
kwanciyar hankali ba ni kuma abinda son ganin ya
samu kenan.
Rannan na dauki wayar Ado na kira Inna don
mu gaisa, tunda zaman jiran fitowarshi daga wanka
nake yi muna cikin hira Innar take bani labarin anyi
ruwan saman farko a Bauchi jiya.
133
Nayi kabbara cikin farin ciki tare da addu'ar
Ubangiji ya sanya damunar ta zamo mai albarka, ta
ce min to amin. Na ce shi kenan Inna za ku dan
samu saukin zafin nan da ake ta fama dashi ko ina.
Don mu ma nan din zafin ne, Inna tayi
murmushi ta ce to mu tun yaushe kuma muka huta
da zafi? Nayi maza na ce, Inna bana ba ayi zafin ba
ne sosai a Bauchi? Ta sake wani murmushin kafin
ta ce min.
"Hala ba ki san mijinki ya aikowa Umar mai
shagon dinkishi kudi ba? Wai azo a sanyawa mai
sunanshi (A.C), ai mu tun nan muka daina jin zafi.
Na ce bai gaya min ba Inna, cikin zuciyata
kuwa tunawa nayi da ranar da naji hirar Ado da
Sa'adatu yana tambayarta mai sunanshi, tana bashi
labarin ai tunda zafin nan yazo baya baccin daree
kwana yake yana kuka wai shi nan ma baya son
zafi.
Ado yana jin anyi ruwan saman farko a Bauchi
ya fitar da hatsinshi da ya noma gaba daya ya kai
kasuwa ya sayar, sai dan kadan ya bari. Dama
tunda' aka yi girbi ya fidda Zakka tun a gona na
baiwa makwabta da 'yan uwa nasu hakkin.
Ya tattara saura ya adana da niyyar sai damuna
ta gabato zai kai hatsinshi kasuwa, don yayi amfani
134
da kudin wajen yin noman wannan damunar.
Ado yana ta shirye-shiryen noma bana na
wannan damunar da muke addu'ar zuwanta lafiya
nima ina nawa shirye-shiryen na rubuta jarrabawata
ta gama Secondary a lokacin nan kuwa ina da ciki
wata hudu.
Sai dai babu wanda ya sani don babu alamar
shi ga ni kuma lafiyata kalau yan matsalolin da
nake dasu ba wasu masu yawa ba ne.
A wannan lokacin babu abin da nake so irin
Ado ya yarda ya barni in je gida in ga iyayena da
yan uwana. Amma sai in yi tayi mishi maganar
yana jna baya ma amsawa sai in ya ji na matsa
mishi da zancen sai ya ce min io wai me za ki jie ki
yiwo ne?
Da Aliya ta dawo daga aikin Hajji sun zo gidan
nan ita da Atika da Sa'a har da Baba karami suka
kawo miki tsarabarki suka yi miki bakunta ta
kwana uku. A wannan dan tsukakken dakin naki
baile ko in ce tsarabarki kike son karbowa.
Inna kuwa kina jin maganarta a waya mai
babban allo in yana son ganinki shi da matanshi
sun san in da kike tunda yazo Hajiya 'yar dubu ma
tazo to wa yai saura? Kullum yayi min irin wannan
maganar bata rai nake yi in daure fuskata in ce
135
mishi su kadai ne yan uwana da dangina?
Babana fa? Sai in hado da Mama don in yi
mishi kara tunda na gane har yanzu yana sonta
yana kuma girmamata, sauran 'yan uwana fa? Sai
ce to ba yanzu ba sai ya duba yaga lokacin da ya
dace.
Rannan muna tare da Ado a dakinmu bayani
yake yi min kan kudin hatsinshi da ya noma bara
wanda sai à wannan lokacin ya sayar da kuma na
lambunshi da ya sayar shima ya adana yana harin
damunar bana da gonakin da yake shirin nomawa.
Bana duk gonakina na gado zan noma
Humairah ki taya ni da addu'a, nayi murmushi nayi
mishi addu'o'in tun a gabanshi wanda kuma dama
ka'ida ne sai dai in ban yi sallah ba.
Haka kawai ma na kan shi da irin koKarin- shi
da wahalarshi in roki Ubangiji ya sanya mishi
albarka mai yawa a ciki.
Muna cikin hirar ya daga ido ya kalle ni, amma
a anya Humairah ba zan kure hakùrinki, in sa ki
gundura da halayena da dabi'una ba kuwa?
Nayi kamar ban ji shi ba, saboda tunda muka yi
fadan da nace halayenshi da dabiu'unshi ne suka
gunduren ya.maida maganar ta żama ka idar nenman
magana a wurinshi.
136
Ban taba ganin mutum nmai son kai irina ba
Humairah alherin da na samu a noman banan kawai
ya ishe ni in yi miki ginin da za ki zauna a ciki ki
yalwata.
Amma ban yi ba, wai so nake in juya kudin in
sake maida su gona wai da a irin nawa son kan so
nake duk abin da ya fito daga gona in maida shi
gonar a aikin da nake yi in yi tattalin da zan rinka
yi mana hidimominmu.
Ban kula zancen nashi ba, wucewa kawa' nayi
na kwanta a bayanshi.
A warnan noman da Ado ya yi na wannan
damunar ne na gane talaka dai ba karamar wahala
yake sha ba a kasar nan duk abin da zai yi karfin
shi kadai yake yi mishi bai da wani mataimaki
ba dai na Ubangijinshi ba.
An riga an sani sarai babu yanda za'ayi a hada
noman wanda yayi amfani da karfi yayi da na
wanda yayi amfani da hanyoyin noma irin na
zamani wanda bai yiwuwa sai ana da wani abu a
hannu.
Amma an ki a yi wa manomanmu na asali
taimakon da ya dace da su wanda za su sau su
bunkasa aikin nomansu sai kullum ayi ta bayani a
baki a gidajen Radiyo da Jaridu, amma wasu yan
137
tsirarun mutane suke tsare komai su amfana da shi
a bira ne ba tare da ya kai ga manoman na asali ba.
Kullum irin korafi da maganganun da nakeyi
wa Ado kenan a duk lokacin da ya zauna yayi min
bayanin mai dadin ji kan aikin da ake yi mishi a
gonakin nashi in ganshi kuma garau babu wata
alama ta wahalar da zata tayar da hankali a tare da
shi.
Hannu babu bororo balle kanta, bal;e aje ga
jallin yin fason kafa ga ciwon baya da na kugu,
gashi kuma ya tabbatar min da cewar noman nashi
na bana zai nika na bara sau goma ko a fiye da
haka.
Sannan a hakan duk dan wani dama da ya samu
na zama zaka gan shi yana tashe da laptop din shi
bincike yake kara yi kan hanyoyin noma irin na
zamani a kasashe daban-dabarn da suka ci gaba, wai
ya kara koyo da sanin sabbin dabarun noma don ya
kara samun sauki.
A wannan damuwar ta bana sau biyu ina kaiwa
gonakin Ado ziyara sabanin na bara da na ki zuwa
saboda aikin ya wahalar min da mijina da yawa ya
fitar min dashi daga hayyacinshi, don ma shi din
namiji ne.
A duk lokacin da na kaiwa gonakin nan ziyara
138
kuwa tsayawa nake yi in yi ta kallon yabanya,
yanda ta mike fetal ta tafi tayi nisa cikin jeji ban
iya hango karshenta. Gashi ta yi kore shar.
Wani irin dadi ne yake kama ni wani irin sanyi
ya sauka cikin zuciyata, in ji ba ni da wani sauran
nauyi ko kunci da ya addabi zuciyata in ji babu
abin da yafi dacewa da ni irin in kara tsarkake
Ubangijina.
In kara kadaita shi da bauta, in kara jin
tsoronshi saboda ko daga kallon baiyanannun
ayyukanshi na zahiri a kawai wadanda su ba sai
mai hankali da ura ne kawai zai gansu ba.
Misali halittar sama da kasa canzawar yanayi
daga rani zuwa damuna, yanda dan Adam ke shuka
kwaya guda daya ya fitar da daruruwa kasa guda
daya ruwa iri daya ya fitar da nau'o'in tsirrai
daban-daban ya ishe mu zamowa abin lura.
Bin bayan Ado nayi can cikin gonar saboda
hangenshi da nake yi yana ciccire kananan ciyayin
da ke son fitowa da tsirran da bai son gani don in
gaya mishi tunanin da ke damun zuciyata.
A duk lokacin da na kalli yanayin sama ko
yanayin shuka a lokacin da tayi shar a jeji in ji ko
shima tashi zuciyar tana raya mishi irin wadannan
al' amuran,
139
Ban san yanda aka yi ba, ban san ina na
tsunduma wajen aikin ciccire mishi kananan
ciyayin ba sai da na ji shi yana cewa "Ke Humaira
ba fa abin da na kawo ki gonar nan kiyi kenan ba.
Kawo ki kawai nayi ki ganta kiji dadi ki taya ni
yi mata addu'a na rokon Ubangiji ya sanya mata
albarka mai yawa." Na ce mishi amin Kawu.
Taso ni yayi a gaba muka fito daga cikin gonar
muka dawo in da ya ajiye babur dinshi da muka zo
akai, cikin natsuwa ya kalle ni bayan ya burga
mashin din.
"Hau mu tafi mana." Na kalle shi na ce, "uh'uh
yi gaba zan tako da kafa