Showing 1 words to 3000 words out of 30903 words
MIJIN TACE
3
NA
HAJ. HAFSAT C. SODANGI
(Mrs. Abdullahi Yunus Dabai)
HAKKIN MALLAKA
Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat Chindo
Sodangi ne.
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
17/1/2013
07035586299
GODIYA
Godiyar ga Allah take, Subhanahu wata'ala,
Masanin yau da gobe, Gwani Mai Hikima, wanda yayi
halitta tasa duka bibiyu, mace da namiji, ya kuma
halicci mutum da aljan don su bauta mishi.
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga
cikamakin Annabawa Shugaban Manzanni, Annabin
tsira, Annabin karshe Muhammad (S.A.w), da
Alayensa da Sahabbansa, da wadanda suka bi ma
tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe Alkiyama.
Bayan haka, ina mika godiyata ga Makaranta
littattafaina, wadanda kullum sakonninsu basu
yankewa a gare ni, suke ma kara min hima wajen ganin
na fiddo musu da sabbin takardu.
Na gode da hakurinku a kaina, na kuma gode da
kulawarku kan rubutuna. Ubangiji ya saka muku da
mafificin sakamako.
Na gode.
Hafsat Chindo Sodangi
17/1/2013
2
SADAUKARWA
Sadaukarwar kullum ta Iyayena ne saboda kulawarsu
da tarbiyarsu a gare ni.
Alhaji Chindo Muhammad Sodangi, da Hajiya Fatima
C. Sodangi, Allah ya saka muku da mafific
sakamakonsa, amin.
TUKUICI
Tukuicin littafin na wana ne.
Mallam Lawal Chindo Sodangi
(N.S.I.T.F. Abuja) da Amaryarsa
Zuhuriyya Ibrahim Usman
Ubangiji ya baku zaman alfiya da kwanciyar hankali,
amin.
YABO
Babayo Yusuf Dabai
Ahmad Bello Sodangi
Na gode
FATAN ALHERI GA
Hajiya Aisha Garba Mai Kwano
Hajiya Lubabatu Illelah
Hajiya Fatima Usman Muhammad (Nigerian Defence
Academic Kaduna)
Na gode.
3
JINJINA
Jinjinar taka ce Abba.
Aliyu Chindo Sodangi da Amaryarsa
Saliha Yusuf (Ardo).
Ubangiji ya zaunar da ku lafiya, ya kuma rufa muku
asiri, amin summa ámin.
KUNA RAINA
Hajiya Maryam Dan Hassan (Mami)
Hajiya Aisha Balarabe (Jazan)
Hajiya Hafsat Mustapha
Fatiman Hamzą Isah (Batulu)
Hujiya Mariya Saleh Tsafe
Hajiya Fatima Abbas Salmanduna
Na gode.
GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA
Hajiya Sameerah Gambo Dage-dage
Na gode.
INA SONKI
Asma'u Bello Nazir
Allah ya raya ki da Imani.
INA SANE DA KU
Na'ima Nura Bashir Galadanci (A.K.T.H. Kano)
Fatimah Yusuf Hashidu (Mrs Hon. Jibrin)
4
Sumayya Ibrahim
Sumayya Baba Idris
Fatima Ibrahim Zaria
Alawiyya Ado Unguwar Dorayi, Kano
Na gode
BAN MANCE DA KE BA
Hajiya Atti Manzo, Marubuciyar littafin nan
na(Sarauniyar Zuciya)
Allah ya kara basira.
GAISUWAR BAN GIRMA
Hajiya Bilkisu Ibrahim Na-Bature
(Mrs Salisu Ahmad Funtua)
Allah ya kara lafiya, amin.
MANUFA
Bana nufin habaici ko yi da wani cikin lamarin
rubutuna, yi kawai nake yi don isar da wani sako. Na
roki masu ganin kamar an yi da su, don Allah suyi
hakuri.
Na gode.
5
Littattafan SODANGI:
- Uwar Miji
- Naga Ta Kaina
- Wayyo Duniya
- Rabon Kwado...
- Cikar Alkawari
Tabbataccen Al'amari
Yi wa Wani...
- Abu Naka...
- Nufin Allah
- Garin Banza...
Gani Gare Ka
- Me Za Mu Ce Da Maza?
- Biyan Bukatar Rai
Kifi Na Ganinka...
- Da Kamar Wuya...
- Daga Kin Gaskiya...
- Shamaki
- Mai Uwa...
- Hattara
Mata Da Kicin Dinsu
- Mata Masu Duniya
- Duk Daya
Kyautata
- Ayi Dai Mu Gani..
- Wacece Ni?
Wata Fuskar...
- Mijin-Tace
6
MIJIN-TACE. 3
Tuni zuciyata ta tsayar min da cewar ba zan
bi Ado ba, don kuwa na gane zabin da zai
fi dacewa da ni shi ne zabi na zama da Mahaifiyata
da dangina, ba zai yiwu in tafi in bar innata cikin
bacin rai da bakin ciki da damuwa da kewa mara
misaltuwa ba.
Kowa yasan Innata, yasan babu abinda take so
irina. Shi da kanshi Ado ya tabbatar min da cewar
tsananin son da Innan take yi min ne ya sanyata
saurin yafe mishi laifukan da yayi mata a baya,
kafin auren namu.
Ta kuma yi gaggawan maida shi da a wurinta,
ta hanyar kyautata mu'amalla a tsakaninsu, ta
girmama al'amarinshi ta hanyar bani umarni na in
kyautata mishi.
To in kuwa har haka ne shi da kanshi yasan
wannan, to ai shima bai kamata ya zartar min da
hukuncin tafiya kauye ba, in dai ba hakan yana
cikin ajandar su ba ne shi da Mama. Tunda dama
da gayya Marnan ta zabe shi ta ce a ba shi ni.
Don haka ban yarda da su yarda na dari bisa
dari ba, don haka ba zan bishi ba, zan zabi zaman
gidanmu ne in rabu da shi yayi tafiyarshi, in rabu
dashi in rabu da fitinar Mama, ba zan taba yarda
7
soyayyarshi ta wata uku da yaudare ni ba in rabu da
Innata, in rabu da ita cikin &unci da bakin ciki
bayan nasan soyayyar da take yi min ita ce ta
gaskiya, ita ce ta asali, ita ce wacce bata karewa
saboda babu algus ko wani magudi a cikin ta, don
ba yi min ita take yi don taga wani abin sha'awa a
gare ni ba.
Ado kuwa fa? In ma har da gasken ne yana
sona, to ya fara son nawa ne a daidai lokacin da
watan amfanina ya kama a wurinshi, ya fara sona
ne a daidai lokacin da aka bashi shawarar karbar
aurena tunda tun zuwana gidanshi sau daya ban ga
wata alamma da ta nuna yana nufin nuna min tsana
ko kiyayya ba.
Tun zuwana a cikin kokarin shawo kaina yake,
don ya samu zaman lafiya da kyakkyawar
mu'amallah a tare da ni, amma kafin wannan
lokacin babu irin wannan mu'amallar a tsakaninmu,
in kuwa haka ne to zan iya cewa da wata lagwada
da ya hango wacce ya gane in yayi wasa ya rasata
kanshi ya yi wa asara.
Ta hanyar tsiya da nuna fin karfi kuma yasan
ba zai taba samunta ba, tunda ni da shi ai kar-ta-
san-kar ne, ya sanni na san shi, don haka yayi
gaggawar watsar da makaman fada ya nemi hanya
8
ta rarrashi da kyautatawa ba gare ni ni kadai ba, har
da ita me haifiyata da kuma sauran dangina.
In kuma har nace Ado ya canza ra'ayin shi ne a
kaina ya janye daga taimakon 'yar uwarshi kishi ta
hanyar wulakantata don su kara sanya mahaifiyata
cikin karin bakin ciki kan wanda suka saba sanya
ta? To ba sakarci yayi ba, don kuwa nasan maza da
yawa za su iya yin irin nashin a kaina, tunda ko da
ban taba daukan kaina na jefa cikin kyawawan
matan da kyansu ya kai ya kawo ba, saboda ganin
kyawawan yan uwana da nake tare da Su, su Aliya
da Atika, wadanda su din dukkansu farare ne so, ga
su kuma da dogon gashi tunda su kama da Innata
suka yi.
Na sani tun ina yarinya 'yar karama nasha jin
Innar tawa tana gaya min cewar ba fin ki komai
suka yi ba, ai bakar fata ba muni ba ne, Babanku ai
kyakkyawan mutum ne, ban kara yarda da hakan
ba sai da na girma na zama cikakkiyar budurwa, na
ganni a tsaye sanbal har ban bukatar sanya dogayen
takalma, saboda tsayin nawa ya ishe ni.
Sai dai kawai in yi hakan wani lokaci don
nishadi, ga ni da kyawawan idanuwa masu tsananin
fari da wadatacciyar girar ido da gashin idon,
sannan ni din ba 'yar siririya ba ce, ina kuma da
9
cikakken kirji gami da damammen ciki da ya sanya
kudurina ya samu damar fitowa, gashin kaina ba
mai tsayi ba ne, amma a cike yake gashi kuma da
laushi.
Ga shi bakar fatar tawa tasha gyara saboda Inna
bata yarda in shafa wani mai ba tare da ta zauna
tayi mishi hadi na musamman ba, ba wai don fatar
ta canza daga launinta na bakin ba, a'a sai dai don
ta kara laushi tayi kyau.
Sannan kuma ga ni ma'abeciyar tsabta da
kamshi a kowane lokaci, sai nake ganin tamfar
wadannan dalilai su ne suka janye Ado suka yi
dalilin da suka hana shi jarumtakar ci gaba da
taimakon 'yar uwar tashi fadan kishin kamar yanda
ya saba, sai yaga maimakon yayi hakan a karshe ya
rasa ni, gara mishi ya rike auren shi in yaso ko ma
menene zai biyo baya bai damu ba.
To in kuwa haka ne, ai son nashi yana da dalili,
sabanin na Inna da shi makaho ne, yin shi kawai
take yi sona kawai take yi a kowane hali nake kuma
ba za ta daina ba, don haka ba zan bar ta in bi wani
Ado ba.
Haka nan don nace ba zan bishin ba, ba wani
laifi nayi ba, zai je ya samu wata a gaba. Sannan
cikin dangin shi zai koma ban da haka ma juna biyu
10
ne da ni, zan haifan mishi da ko 'ya yazo ya dauka,
wannan ba karamar riba ba ce a wurinshi.
Sannan zai tafi ne tare da iliminshi da yayi
arnfani da dukiyar ubana ya nema, ai ko da ya
dawo mishi da abubuwan shi da ke wurinshi bai
dawo mishi da ilimin ba, ya rike wannan balle ace
shima ya ajiye Babana ya samu ya rabawa nashi
ya'yan da sakarci ya hana su yin karatu.
Don haka ba zan bishi ba, ko don in dandana
mishi bakin cikin rasa ni bayan ya soni ba zan bishi
ba, tunda bai so ni a lokacin da ya dace ya sonin ba,
ya so ni ne bayan ya taimaki 'yar uwarshi sun
gallawa Inna, sun gana mata azaba ita da 'ya'yanta.
Ya so ni ne bayan na gama wahala a hannun
Mama, na gama azabtuwa da azabar dukanta, bai so
ni a lokacin da nake bukatar taimako ya taimake ni
ba, don haka ba zan bishi ba. Sannan na riga ia
sani ko ban bishi ba ba zai sake zama tare da Mama
ba har yayi mata irin biyayyar da yayi mata ba a
baya, don kuwa ya riga ya kamu da sona
matsanancin son da ya ba shi dama da kuzarin iya
yin fito-na-fito da ita kaina. Don haka ko don in
dandana musu wannan takaicin dukan su ba zan bi
shi ba.
Ina cikin wannan zancen zucin, kalaman Mama
11
suka katse ni, suka dawo da natsuwata ga kallo da
sauraron ainda ke faruwa a tsakar gidan namu.
Daga ido nayi na kalli Ado a dalilin jin irin
kalaman da Mama ke yi mishi.
A durkushe yake irin durkuson da yafi kama da
ace dan kiris mutum yake jira ya ruga a guje,
makwal wuyanshi sai kai kawo yake yi a tsakanin
wuyanshi, yayin da idanuwanshi suke kaina ko
Rifta su baya yi.
"Dama ka hakura ka fidda ranka a kanta, ka
kwantar da hankalinka ka samu natsuwa da yafi
maka, don kuwa ba za ta bi ka kauye ba, uwarta ma
ba za ta yarda ka daukan mata ita ka kaita kauye
ba.
Sun dai cuce ka ne kawai suka yi maka irin
surkulle-surkullensu da tsatsube-tsatsuben su suka
mallake ka suka yi maka dandani-haukaci, saboda
sun san baka taba sanin mace ba sai akan yarsu,
don haka suka kidimaka, to ba ita kadai ba ce a
haka. Kar kaga kanmar ba za ka sake samun irinta
ba, dubu suna nan kamarta wasu ma sun fita da
yawa ma kuwa."
Bata Yahya ya kalli Mama cikin wani irin
yanayi da yafi kama da na jin kunyar kalaman nata,
ya ce "Ke madajan wadanne irin kalamai ne
12
wadannan ki ke furtawa a cikin mutane na rashin
mutunci da rashin ganin girman mutane?"
Ta ce, "Ah'ah, bar ni kawai in gaya mishi
gaskiya, in ya hadiyi zuciyata a kanta ya mutu ma
to shi kadai ya yi wa kanshi asara, tunda uwarshi
kam ai ta riga ta dade da mutuwa, ni kuma ya riga
ya nuna min iyakata a kanta, ya watsa min kasa a
ido, ya kunyata ni ya tozarta ni a gaban makiya
kuma abokan gaba yasa su sun yi min dariya, to ai
babu wani abu a tsakanina da shi a yanzu tunda an
yi mishi ingiza mai kantu ruwa ya yarda.
Wai har ni ka ke dawowa da kayayyakina da
suke wurinka akan wannan ja'irar yarinyar,
shu'uma, yarinyar da kwanannan ta gama yi maka
gori a kan kauyancinka, tana fadin ta godewa
Ubangiji ita gidan ubanta gida ne mai albarka,
kowa yazo cikinshi zai ci arziki ya koshi ya murje,
ya goge, yasa sutura ya fita daga kauyancinshi.
In ba wanda ya san shi ba babu mai kallon shi
ya gane ina ne asalin shi yake? Shi yasa ita ko
bakunta bata barin gidan ubanta taje yi a na wasu.
Ba Humaira ba ce ta furta maka wadannan
kalaman?" Ta zuba mishi ido tana kallonshi, sanin
da nayi cewar gaskiya ne daga bakina maganganun
suka fito yasa nima na zuba mata nawa idanuwan
13
ina kallonta.
Tsana ne karara ya bayyana a idon Mama, zai
yi wuya a yau in har da akwai sauran wani abu
naso ko tausayi a tsakaninta da shi, to me yayi
mata? Ko kuwa don kawai ta ce ya saki aurena ya
ce a'a?
To in har haka ne yasa a yau Mama ta tsane shi
to anya Mama tana yin so kuwa? Ko kuwa dai ita
din takan so mutum ne kawai a gwargwadon irin
amfanin da take yi da shi? Ai baka tozarta ni ba
kanka ka tozarta ka tsiyata kanka don ka burgeta, ta
cc zata bi ka ba kuma zata bi kan ba kai ne ka zabe
ta ka bar ni amma ita ni ba za ta zabe ka ta bar
uwarta ba, ko kuwa Humaira?
Ta juyo da kallonta gare ni, za ki iya yin rashin
hankalin zaben namijin da ba shi da tabbas ki bar
iyayenki uwa da uba tunda kin san su ba sa son
tafiyar taki? Ado ai dan kauye ne, kauyen kuma
babu wanda bai san shi ba, a nan sai ko ke din
sussuka ne da surfe gami da nika kafin aci abinci
gidan su Ado kuma wani irin gida ne da giran shi
ya hana shi yin fasali.
Don ko katangar arziki basu samu arzikin yi
mishi ba, gasu da wani irin yawa mara sha'awa,
sannan wai don rashin adalci duk mutanen gidan
14
nan suna ci ne a tukunya guda daya mace daya
kuma ke tuka shi, ko karya nayi nuku?
Ta zuba mishi ido tana kallonshi, ya girgiza kai
a hankali cikin natsuwa nuna alamar ba karya tayi
ba, gaskiya ta fada, ta gyada kai nuna alamar
gamsuwa da amsar da ya ba yar tare da fadin kin ji
ba? Shina ya ce ya karya nayi bà.
Kalaman batanci da tozartawa da Mama ke'ta
faman furtawa a kan Ado, anyi-anyi da ita koama ta
daina ta ki, sai suka sanya ni canza ra'ayina naga ko
ba zan bishi ba to ba a gaban Mama kuma zan faii
hakan ba, tunda na gane abinda take son ji daga
gare ni keren, don taji dadin tozarta shi ta yanda
zai kunyata yayi bakin ciki.
Ke Hajiya da kin bar yarinyar nan ta zabi
abinda ta zaba, don musan abinda muke ciki." Bai
sauraronta shirun nata ba balle ya gane tabi
umarnin nashi ko bata bi ba? Ya dawo da zancen
nashi gare ni.
"Ke Aisha wanne ki ka ga za ki yi? Za ki bi
mijin naki ne ko ba za ki bishi ba?" Na daga ido
cikin natsuwana kalli Mallam Harisu
makwabcinmu da yayi min wannan tambayar, na
ce mishi "Zan bishi Baba."
Ina fadin hakaa dakin ya dauki kabbara mai
15
karfi tare da hamdala, daga wurin Ado da Liman,
Mama kuwa kurma ihu tayi da iya kacin karfinta,
tamfar wacce wani mugun abu ya samu, tana fadin
ita kam ta shiganga, to bara kada ta mutu ta bar rai
a duniya, wayyo!! ita magadan an kwace mata dan
uwanta an shiga tsakaninsu an rabata dashi, ina ma
dai ace taji kashedin da wannan yarinyar tayi mata?
Baba Yahya ya ce, "Kaltume ba? Ni da kina ji
da mugun nufi iri-iri da ba ki aiwatar da shi ba,
amma ga ki nan ga irin abinda ki ke shukawa."
Babana ya yi maza ya mike a fusace a'a Alhaji,
kar ka ce zaka yi wa Mama baki, in dai akan
wannan ja'irar yarinyar ne, ai gata nan ga wanda ta
zaba din, ba dai a kanshi ta wulakanta ni ba? Na ce
kar ta zabe shi ta zabe shi?
To in ta bi shi suka tafi ta tafi kenan har abada
ba za ta sake tako min cikin gidana ba, kuma ma in
naga dama inyi mata baki ta lalace tabi duniya,
kowa ya huta, tunda ban ga amfaninta ba, tunda
tasa Mama take irin wannan kukan.
Nima da iyakacin karfina na soma kuka ina
birgima ina shure-shure, Babana zai yi min baki ina
zan shiga ni 'yasu? Hankalina yayi matukar tashi,
na rasa in da zan sa kaina in ji dadi, na rasa wanda
zan matsa kusa da shi in rada mishi cewar ni fa ba
16
da gaske nake yi ba, zabin da nayi na cewar zan bi
Ado nayi hakan ne kawai don in sanya Mama bacin
rai, amma babu wanda zan iya fuskanta da maganar
tawa ya saurareta."
Gaba daya wuri ya hargitse, hankula sun kai
matuka wajen tashi, Baba Yahya da Babana sai
faman rirrike su ake yi saboda Babana ya koma
taya Mama zagin Inna da danginta da take yi, yana
tayata kiransu munafukai masu raba dan uwa da
dan uwa, shi kuma Baba Yabya yana rama musu
To ma na fasa tunda akan wannan..
Cikina ya bada wani irin sauti na kulułulu!!!
saboda tsoron kalmar da zai karasa zancen nashi da
ita, sai naji ya katse zancen nashi ya ce, na fasa ba
in da zata zabin da tayi zabin banza ne, ban yarda
ba, ba za ta bishi ba, a zuciyata nace tafi nono fari,
Baba da haka kayi tun farko ma da ba a tsaya
wannan kace-nacen din ba, tunda dai ni din ai
mallakinka ce.
Zancen Baba Yahya ya katse ni da na ji yana
fadin, wannan ai shi ne karya ba za ta zabi mijinta
ka hana ta bibn shi ka kashe mata aure ba, saboda
kawai matarka tana son ganin hakan, in zaurawa ka
ke son gani a gidanka ai gasu nan ka samu."
Mama ta sake kurma wani uban ihun, wai Baba
17
Yahya ya yi wa 'ya'yanta gori, bai saurare ta ba
balle Babana, ganin shi kawai naga yayi ya damko
hannuna yana jana zuwa inda Ado ke makure a
jikin bango.
"Yau ka ce kana son tafiya da matarka?"
Da sauri Ado ya ce mishi "Eh." Baba yana jin
haka yayi maza ya danka mishi ni a hannunshi, tare
da fadin "Gata nan Ado na baka ita ku tafi, ka ike
min ita amana ka sani iyayenta ma hakuri da su
muke yi, to balle kuma ita yarinya ce yar karama."
Ado yayi maza ya kama hannun nawa ya rike
da iyakacin karfinshi, tanfar yana tsoron kar a
kwace mishi ni.
"Wuce ku tafi." Ya bani umarni mai karfi,
daidai lokacin da Babana yake ta sakin wasu
maganganu masu tsanani su Mallam Harisu suna ta
faman bashi hakuri, na kalli Baba Yahya ina kuka,
na ce mishi "Ba zan bi shi ba Baba, ba zan bishi ba,
ni dama ba da gaske nake yi zan bi shi..."
Wani irin gigitaccen mari ya dauke ni dashi, sai
da naga waikiya ta haske ni gaba daya, Ado yayi
maza ya kankame ni a jikinshi da sauri yana baiwa
Baba Yahya hakuri.
"Kayi hakuri Baba, kayi hakuri." Yana kuma
tattare ni da fadinshi don gudun kur hannun Baba
18
Yahyan ya sake kawowa gare ni, gigitaccen marin
da Baba Yahya ya kifa min ya katse min komai,
hatta kukan da na dade ina yi, na daina shi na koma
zare ido saboda ban taba jin mari mai tsananin
wannan ba.
Ado ya tasa ni a gaba, muna fita daga gida ina
jin Baba Yahya yana fadin, "Ai ko za ki shide ba
shure-shure ba sai ya tafi da ita, ai ba zai zabe ta ya
bar ki ke da mijinki da duk abinda ki ke ganin kun
mishi ya ce ita kadai yake so sannan ku hana shi ita
ba, yana sonta tana son shi ke ki ka kulla auren da
nufin sharri don ki cutar da ita, kisa shi ya
wulakantata.
Amma' abin mamaki sai gashi zaman da yayi da
ita na kwanaki tamanin da bakwai kacala sun sa shi
ya zabe ta ita kadai ya barku ke da mijinki da duk
abin da ku ke ganin kuna dashi.
A kofar gida Ado yana kokarin shigar da ni
cikin motar da ke tsaye tana faman jiranshi wadda
shatarta ya dauko, sai ga su Liman da Mallam
Harisu, har da Baba Yahya sun fito. Mallam Harisu
da Limar suka wuce, Baba Yahya yana yi musu
godiya.
Shi kuwa Baba Yahya yazo ya tsaya jikin
motar hannayenshi duka biyu ya saka cikin
19
aljifayen shi ya fito da duk abinda ke ciki ya
mikowa Ado tare da fadin sai kayi hakuri da
wannan baka ba da lokacin