Showing 12001 words to 15000 words out of 30903 words
bata aiko ba shi kenan. Don abin da ya ce
kenan, sai ko yaran gida da na gama suna wurina.
Yarda da bin ka'idojin Ado da nayi sai suka yi
dalilin da na samu wata irin rayuwa a tare dashi
wacce ta fahintar dani cewar ita mace ba wai tarin
dukiya ko wani kyale-kyale ne yake samar mata
farin ciki da kwanciyar har kalin rayuwarta ba, a'a
mijinta kawai.
Kullum ni da Ado a cikin tarairayar juna muke,
yana gudun bacin raina ina gudun nashi, yana
65
tattalin farin cikina kamar yanda nima nake tattalin
nashi, duk da matsanancin aikin da yake fama da
shi a gonakin shi ramar shi tayi matukar raguwa,
saboda yana da kwanciyar hankali a gida ina kuma
tarairayarshi da abinci mai kyau.
Rannan muna daki da daddare ni da shi, hadari
ne ya taso a gari ganga-ganga, tuni na fara sabawa
da irin wannan hadarin mai yawan iska da rugugi
gami da tsawa, shafa maina nake yi ban fasa ba, na
ce mishi kai-kawo hadarin nan ba irin namu ba ne
na can.
Idon shi yana lumshe ba tare da ya yarda ya
bude su ba, ya ce min eh ai ko ruwan ma ba daya
ba ne, in kin lura ai mun baro can ne damuna ta
riga ta kankama sai muka zo nan muka tarar
lokacin ake shuka.
Na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi idon
naka yana ciwo ne? Bai yarda ya bude suba ya ce
min to ko ba sa ciwo Humairah tunda ki ka zauna
kika bar kirji a waje ai dole in yi maza in rufe su in
dai ba so ki ke in kasa cika alkawarin da nayi miki
na cewar shekaran jiya waccan da wacce ta wuce
da jiya da yau da gobe duk za su zamo ranakun
hutu ne a gare ki ba, don ki san in aka yi min alheri
nima na iya irin nawa alherin.
66
Nayi murmushi na ce eh, gaskiya ne kar ka
bude kai dai to dan bani hannunka in sa shi yayi
min wani aiki.
Ba tare da ya bude ba yayi maza ya miko
hannun yana laluben in da nake tare da fadin ungo
shi Humairah ungo hannun nawa karbe shi ki sanya
shi hidimar da ki ke ganin ta dace da shi ina kama
hannun nashi na ji Ado ya yi wani irin ajiyar zuciya
mai sanyi ban sake ganin yanda aka yi ba sai
ganina nayi a gefen shi a kwance ya zagaye ni da
hannayen shi duka biyu tare da yi min tambayar.
"Kin san wani abu ne Humaira?" Bai jira na ba
shi amsar na sani ko ban sani ba, sai ya soma
rattabo min bayaninshi, ke din mai alheri ce,
alherinki kuma yawa ne da shi saboda kina da kirki
ga ki da abin arziki iri-irni, in ki ka ga dama sai ki sa
mutum ya rinka ganin tanfar babu ma wanda ya kai
ki abin arziki, balle ya iya fin ki.
Ban kula zancen na Ado ba, iya ka dai nasan in
dai barin shi ya yi yanda yake so shi ne kirki, ko
alheri to na yi mishi.
Muna cikin irin wannan zaman mai dadi ni da
shi wara magana ta taso a cikin gida, Ruwaila ce
take yawan yi min magana akan kankane ni da Ado
yake yi, yana hana ni mu'amalla da kowa cutata
67
yake so yayi dama haka tsofaffin maza suke yi ma
matansu, don su hana su fahimtar komai.
Shi Adamu ai ba yaro bane ga sa'o'inshi ne da
ke garin nan suna shirin yin surukai, ko ma daukan
jika kwanannan, don haka ga adashe nan na kafa ki
zo ki shiga, na ce ai ba zai bar ni ba, ta gallà min
harara "Ke ko iya zama da miji baki yi ba? Ai
kamewa za ki yi daga gare shi ba a sakan mishi jiki
haka sakakaka ba, in ki ka ga ya matsa sai kema ki
bijiro mishi da taki bukatar.
u da muke da shashun kishiyoyi ma muke yin
hakan muci nasara balle ke ke kadai? In ki ka saban
mishi da yanda ku ke din nan ai wahala za ki sha
tunda in ke kin yarda da hakan wata ba za ta yarda
ba, kin kuma san ana yin kaka in ya saida amfanin
gonarshi kishiya zai yiwo miki."
Kirjina ya bada sautin rugugugu! ban sani ba
ko itama ta gane tsananin tsoratar da nayi ne yasa ta
yin murmushi, ta ce "Lah, to wannan ai ba wani
abu ba ne, mu nan ai haka ake yi kaka tana yi in
aka cika runbuna da hatsi, to abinda yai saura sai
akai kasuwa a sayar sai ki ga an kawo miki wacce
zaku ci hatsin tare shi kenan."
Ta sake kallona ta ce min, to balle ko mijinki
da wahalar damunar nan bata hana shi manne miki
68
ba, ai kuwa kin san ya huta da kaka akwai magana,
na kuma ji Yayanshi yana cewa yayi noma ba
kadan ba, in kaga irin aikin da yake yi ma sai ka ga
tanfar da gayya yake yi.
Sammako yake yi ya riga kowa tafiya, sannan
duk a can ake baro shi, na ce mishi babu wata
gayya so yake yi yayi gini ya kuma kara wani
auren, ai kuwa dolen shi yayi aiki tukuru." Na zuba
mata ido kawai ina kallonta don kuwa ban taba jin
maganar da ta dame ni ta daki zuciyata ba irin
cewar wai Ado zai yi min kishiya, to ni kuwa
kenan ribar me naci a biyo shin da nayi?
Ta salke kallona cikin natsuwa ta ce, yarinya
kamar ki ya kyale ki kina yawo cikin wasu
zulunbun dogayen riguna da tun suna baiwa
mutane sha'awaa har sun daina sun maida ke kin
zama tanfar wata tsohuwar Babarbariya."
Kalaman na Ruwailah sun yi matukar yin tasiri
a zuciyata, musamman da ta tabbatar min da cewar
su al'adar mazansu ne ma in sun cika runbu da
hatsi, to abinda ya saura in an kai shi kasuwa aure
ake yi.
Don haka nan na kame sosai daga yawan
sakewa Ado fuska, al'amura suka yi matukar
sauyawa a tsakaninmu, da yazo zai taba ni sai in ce
69
mishi cikina na ciwo, sai yayi maza ya kyale ni.
Rannan dai ta kure, mun kai wajen sati uku a
haka tunda safe Ado yake yi min magana,
rarrashina yake yi a dalilin bai son tilasta ni saboda
abin da ya taba faruwa a tsakaninmu, ganin da nayi
ya matsu kwarai mu fahirnci juna ya sani bijiro
mishi da maganar adashen da ake yi a gidan, wanda
ni kadai ce bana yi.
Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, "To kina da
sana'a ne Humairah? Adashe ai na mutane masu
sana'a ne, ke ba ki da sana'a ni ba wani abu nake yi
ba in ban da maganar gonar nan, gona kuna ci mun
kudi take yi bata fara bani ba, yanzu ne nake
neman aikin koyarwa tunda na gaya miki na mika
takarduna ba kuma zan yi wani aiki de va wiice
koyarwa ba a yanzu, saboda ina son in jarraba yin
noma sosai.
Ni yanzu fatana da addu'a ta bai wuce mukai
lokacin da za a yi girbi asirinmu bai tonu ba. Na
rantse miki Humairah rutin asirin Ubangiji ne
kawai yake tafiyar mana da al'amuran sai ma ganin
kamar zata kure sai kuma in ga wata hanyar tazo ai,
wani lokacin ma ba da gangan nake kwashe miki
kudinki ina bar miki nera hamsin ba, Kurewa take
yi.
70
Kiyi hakuri kin gane? Nasan kina hakuri dani,
amma ki kara maimakon in ji wannan rarrashi da
bayanin da yayi min, na riga naji zuga zugan da aka
yi min cewar su din ma'ana, 'maza' ba ayi musu
sassauci mai yawa sai su raina mutum.
Don haka sai na kara daure fuska na kara 6ata
rai na ce, to sai muyi hakuri duka, na kawar da
fuskata gefe.
Abin da kawai na fada kenan, sai ya fahici abin
da nake nufi, muyi hakuri duka? Na ce, eh, me
kenan hakan yake nufi? Na sake bata rai na ce, ko
ma menene? Ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa
ya ce, waye ya koya miki wannan iskancin ?
Nayi kamar ban ji shi ba, ya ce to ai da sai ki
gaya mata naki mijin ba irin nata ba ne. na ce uhn,
na mike da nufin fita in bar mishi dakin, sai kawai
naji ya kamo hannuna ya murde da karfi, sai da na
kwallara kara mai tsanani, amma bai sake ni ba.
Ai babu in da za ki tafi sai kin gaya min
wacece take koya miki wannan iya shegen?
Ruwailah ko? Sai naci abu kazanta, in bata yi
hankali da ni ba, ha'a me tayi maka zaka zage ta?
Kau na ji, ya wanke ni da wani irin wawan mari,
nayi maza nasa daya hannun na dafe wurin, ai in ba
ki gaya min wacce tasa ki kiyi min wannan
71
wulakancin ba, za kiyi mamakin abin da zai faru
yau."
Na soma mutsu-mutsun kwatar hannuna naga
hakan ba zai yiwu ba wahala kawai nake karawa
kaina bai kuma kula kukan da nake yi ba, balle ya
damu da cewar rana ce mutanen gida zasu iya jin
abin da muke ciki.
Wulakanci irin wanda Ado yayi min rannan bai
kwatantuwa, murde ni yayi ya yi abin da yaga ya yi
mishi daidai sannan yasa kai ya fita ya bar gidan da
azahar tayi ma ya sake dawowa, babu kuma wata
mu'amulla ta rarrashi ko sassauci a tsakani na rasa
in da sa kaina in ji dadi, ga shi kuma bsbu halin in
kai kara in maganar ta fto ban san me Zai faru ba.
Ba kuma zan iya gayawa Inna ba in ce tayi
mishi magana, nasan zai iya gaya mata abin da ya
hada mu, na kuma san zata yi fushi mai yawa don
na saba jin ta tana cewa dabi'ar matsiyatan mata
kenan su ne wadanda ba za su gaya wa mazansu
bukatunsu ba, sai a lokacin da suka ga sun matsu
da su.
Don haka na lallaba na samu Ado ina kuka na
ce mishi kayi hakuri Kawu ka daina irin wannan
mu'amullar dani.
Ya dago ido ya kalle ni ban san yenda aka yi
72
ba, tausayina ya kama shi cikin natsuwa ya ce min
ya wuce amma ki gaya mata tayi hankali da ni ko
wacece? In ita bata sani ba ke kin sani cewar Mama
ita ce mafi darajar mutum yau a wurina tunda bani
da uwa ba ni da uba su Baba Tanimu ne iyayena.
Ita ta rike tayi min gatan da nayi karatu na koyi
al'amura masu yawa na rayuwa, amma sa nayi
jaruntakar rabuwa da ita don in zauna dake ya sake
zuba min ido yana yi min kallo mai tsanani, shi ne
za'a saki kiyi min abinda ki ka san zanyi bakin
ciki?
In ana son cutar da ni sai a hada kai da ke?
Yanzu in an san ina sonki sai ayi amfani dake? Ni
in ina da hali sai kinyi adashe? Me zan yi da kudin?
Hankalina yayi matukar tashi jin kalaman Ado
nayi matukar jin kunya da Nadama na abin da nayi
mishin kuka sosai na soma yi ina bashi hakuri don
kuwa na san ba karamar wauta nayi ba dana ji irin
wannan zugan na kuma yarda nayi amfani da ita.
Na dade sosai ban iya sakin jikina sosai da Ado
ba saboda naji kunyar abinda nayi mishin ba kadan
ba duk dai shi din bai sake yi min wata magana ba
ko kuma nuna min wani abu.
Ana cikcin haka rannan ya dawo da rana, wasu
takardu ya ciro a aljihunshi ya miko min, nasa
73
hannu biyu na karba ina dubawa tun kafin in kai ga
gama karantawa ya ce min naje nan Government
Day Secondary School Dabai nayi magana da
Princepal din ya yarda za ki soa zuwa satin nan.
Kije kiyi karatu ki samu takardar ki yafi min
wunin da za ki rinka yi a gida bana nan ana koya
miki abin da ba zai min daidai ba, da na bari ne sai
badi don in ga na soma yin wani abu, to amma sai
na tuna kuma ai 'Though Times Never Last but
though people do."
A haka na soma zuwa makarantar (S.S. 2) aka
sanya ni, babu kuma abin da Adon bai saya min ba
na karatuna, tun daga uniform, sandal, safa, har
zuwa littattafai na karatu. In nayi shiri Zan ta in
sanya dogon hijabina akan uniform din sai na shiga
cikin makaranta in cire in shiga aji in mun taso ma
in mayar.
Tunda na shiga makaranta na soma koyon
jarumtaka kan al'amura masu yawa nayi matukar
rage baccina, kullum na kan tashi ne da wuri in yi
mana abin karyawa da abincin da zamu dawo muci
da rana, in zuba a cikin food flask kafin in yi
wanke-wanke, in yi wanki in yi shara in yi wanka.
Karfe bakwai nayi kuma zan sanya kayana in
dora hijabina in je in gaida su Baba da su Goggo,
74
da sauran mutanen gida, in fita waje in samu Ado
yana jiran fitowata bayan ya rurrufe mana wurinmu
mu jera mu tafi sai yaga shigata makaranta sai ya
wuce gonarshi.
Yana kuma daidaitan lokacin tashin mu ne ya
taso daga gonarshi ya biyo min ta makaranta mu
dawo gida tare, da daddare in mun gama abinda
muke yi kuma yana duba takarduna yaga aikin da
aka yi mana ya yi min gyara kan abin da ban gane
ba.
Zaman lafiyan da aka lura aka ga ya samu
tsakaninà da mijina ne ya bayyana a cikin gida,
wanda ban samu hakan ba sai da na yarda ni ce a
kasa shi ne sama da ni, sai da na yarda da barin son
raina na koma bin nashi, na koma karbar umarnin
komai daga gare shi, na koma rayuwar yi nayi bari
na bari ko da kuwa ina son barin ko kuma ina kin
yin da aka ce in yin.
Misali, ko a cikin gida ina son shiga cikin mata
'yan uwana in dan yi mu'amalla da su in dan ji dadi
a raina, amma tunda yake min ya hana ni žaman
gindin bishiya don hira, na ce mishi, to na kuma
bari ko baya nan bana zuwa.
Tunda ya hana ni bin dakunan mutane matukar
ba wani dalili mai kwari ne ya kai ni ba, na hakura
75
na daina sai ko dakin Goggo Ayalle.
sKullum ni kadai ce a wurina, in ba shi din yana
gida bane kowane lokaci a cikin hidimarshi nake,
tunda daga wankin yan suturunshi da adana su da
tattalin abin da zai ci hakan kuma bai hana ni ba shi
lokacina a duk lokacin da ya bukaci hakan.
Ana cikin hakanne kawai na soma jin
maganganu suna yawa a cikin gida, wai ni din fin
karfin shi nayi, bai da wani katabus bai iya yin
komai sai abin da nasa shi, ko kuma na hana shi,
wai ai tunda na iya raba shi da Hajiya Majadan duk
alherin da tayi mishi, to babu wani wanda ba zan
iya raba shi da shi ba.
Ina jin maganganun na gane daga inda suka
fara fitowa, cikin zuciyata na ce don ta gane na
daina daukan shawarwarinta ne, gara ita, nata mijin
yana da irin wannan juriyar ni nawa in na ce zan yi
mishi haka ba kwashewa kalau zan yi ba.
Na dai kudiri aniyar zama lafiya da kowa ba na
son fitina, don kuwa nasan babu alheri a cikinta,
tashin hankalin Mama kawai da ta tasa mu a gaba
shi ne yayi dalilin barowarmau gida muka taho nan,
to ta wadannan bataliya fa?
A wannan lokacin aka sake fito min da wata
dabi'a, duk wacce zata yi wanka ko zata yi taya bahaya
76
sai tazo wurina ta ce wai a nan zata yi.
Wuni suke yi suna layin shiga bayan gida,
kuma duk yanda na kai da wanke shi sai sun 6ata
shi yayi ta wari, wani lokaci har cikin daki, don
tuni da nayi hakuri da su akan sabon halin nasa.
To Ado ya ce bai yarda in hana su, in gaya
musu cewar shi din ya hana su shiga wannan bayan
gidan ya ce in gaya musu su rinka wanke hasu,
suna gyarawa don su rinka jin dadin shiga ko ni din
da irin barin wannan din da kazanta da ba su zo sun
shiga ba.
Ni kam ban iya gaya musu ba, ina jin kunya
don mafi yawancinsu sun girme ni nesa ba kusa ba,
shi kuma yana ganin wata tazo ta shiga ni yake
balbalewa da fada, sai da nayi sa'a maganar ta kai
ga Baba Tanimu.
Shi ne yayi kashedi mai kari kar ya sake ganin
wata taje ta zaga a wurina baya son iya shege da
neman magana.
A wannan lokacin har a gabana a kuma kan
idona za a rinka tsaki ana cewa a hau, to namiji
kuma, wacce bata san shi ba ai ita ce bata san sh
ba, mu kan ai sun shamu un warke, muna nan da ke
za ki zo kina zubar mana da hawaye sanda zai yi
miki halin nasu mu ce muma bamu sanki ba
77
amarya muka sdni.
Kusan kullum sai an ce min an ga Ado gidan
Mallam Korau yaje tadi, rannan dai na daure na
samu Adon na tambaye shi cikin natsuwa na ce
mishi ni da gaske ne wai kana neman yar gidan
Mallam Korau?
Bai wani kalle ni sosai ba ya ce min Menene
in ina neman nata? Na ce a'a na dai tabaya ne
kawai don in sani ya ce ba uwardakinki ce ta gaya
miki ba, ai ba zata yi miki karya ba, watakila dai
kina ganin ne tanfar gonar tawa ba, za ta rike min
ku ku biyun ba ko?
Ban sake ce wa Ado komai ba, amma wani irin
al'amari ne naji ya taso min ya tokare ni a kirji,
wani irin nauyi ya saukar min a kirjin, zuciyata tayi
matukar kunzi, karo na farko da naj! in wannan
abin a tare da ni.
Kishi mai tsanani ne ya kama ni, na tabbatar wa
kaina da cewar aiki ne babba a kaina, in har ya
tabbata Ado auren nan zai yi tun daga. wannan
lokacin na soma sa ido akan lokutan fitanshi da
kuma na dawowanshi tare da tunann io a wane
lokacin yake zuwa wurin nata?
Zuciyata ta soma raya min cewar wata kila
daga yin sallar Isha'i ne tunda kullum bai dawowa
78
gida bayan Isha in sai yayi zama na awa daya da
minti goma sha biyar ko kuma da minti talatin.
A farko ya ce min yana zaman yin karatu ne
wurin Limamin Masallacin unguwar, na kuma
yarda. To yanzu kam na gane ba gaskiya ba ne,
loba ni kawai yake yi, tadin shi yake zuwa.
Don haka rannan da zai fita Masallaci don
sallar Isha'i; na ce mishi in an yi sallar Isha'i ka
shigo gida don ban yarda da wannan munafukar
makarantar taka ba, babu kowa a ciki sai kai kadai.
In ban da munafurci wane karatu ne ba za ayi
shi ido na ganin ido ba, kullum sai dare yayi?
Zuba min ido yayi yana kallona, a hankali ya
bude baki ya ce min, makarantar tawa ce kuma
munafuka yau Humaira? Nayi maza na ce mishi,
eh, kana nema ne ka maida ni wata yarinya 'yar
kankanuwa.
Ka shanya ni a gida da sunan kana wurin
Mallam alhalin kai kana can ne wurin tadin ka.
Ya ce, To shi kenan, ke ba yarinya
Rankanuwa ba ce, tunda kin yi kokari kin gano ni,
to amma ai kuma ina jin ban taba yi miki karyar
zan zauna da ke ke kadai ba, balle ki ce na 6oye
miki.
A kullum kuma ina kokarin gaya miki cewar ni
79
din namiji ne, shi kuma namiji ai kin san imijin
mata hudu ne.
Kalaman nashi suka kara fusata ni, na soma
sake mishi maganganu masu zati, musamman ma
da na tuna eh, gaskiya ne shi din kullum a cikin
alkawarin zai nuna min shi namiji ne, wato dama
abin da yake nufi kenan?
Ba. mu gama fita daga cikin wannan