Showing 15001 words to 18000 words out of 30903 words

Chapter 6 - MIJIN TA CE BOOK 3

20 Aug 2024

4867

maganar
ba tunda bai yarda zai daina zaman waje bayan
Sallar Isha'i ba, sai kawai na dauki wayar Ado ina
bincike a cikinta.
Text din yanata na soma gani, yayi maza ya
fige wayar daga hannuna, nan take kuma ya kama
yi min fada ""Kina fa nemana da fitina, kina nema
sai kin takura min, yaya ne haka?
Ya ya za ki tsananta min bincike bayan kin san
an hana? Na soma yi mishi kuka saboda a wannan
lokacin na riga na gane gaskiya ne yana neman
aure?
Kenan gaskiya ne duk wahalar gonar nan da
yayi da juriya da taimakon da nayi tayi mishi kudin
a dawainiyar aurenshi zasu tafi?
Hannu biyu na dora a kaina nayi kuka har na
gaji bai yarda ya sake shigowa dakin ba.
Washegari tun safe na tatt a na bar mishi

80


wurin, na koma dakin Gogori Ayalle nayi
kwanciyata, zuwanshi uku in dawo wurinmu zai
zauna muyi magana ta gaskiya, ni da shi ban yarda
ba.
Har kusan yamma ban koma ba, anyi sallar
La'asar ya shigo ya zo ya same ni, "Zo muje kiyi
mana girkin abinda zanmu ci mana Humaira, na ce
mishi kaje ka kawo yar gidan Mallam Korau ta
girka maka.
Ya zuba min ido yana kallona cikin natsuwa,
kiyi hakuri mana Humairah na ba ki hakuri na
kara ina ce ni duk girman laifin da ki ka yi min
hakuri daya ki ke bani in ce na hakura?
Na daga ido na kalle shi, kayi min wulakanci
akan wata 'yar iska? Yayi murmushi, "To ai na ce
kiyi hakuri." Ban tanka mishi ba sai ya juya ya fita,
Bai wani dade ba ya sake juyowa zai dawo, sai
kawai naji Ruwaila tana ce mishi, ai kai kuma yau
taka ta sae ka tunda ka yarda ka bata mata rai, baka
da šauran zama lafiya tsugune ta kare maka tunda
ka bari aka yi fushi da kai.
A zuciyata na ce, kai wasu da rashin zuciya
suke, tanfar dai bata gane irin sharewar da Ado
yayi mata ba kusan kowane lokacin a cikin
nemanshi da magana take.

81
Sai kawai naji ya ce mata, eh ai ta isa ne kin
san ni din a hannunta nake, wata matar don ta yi wa
miji fushi ai shirme tayi, tunwa wanda tayi domin
shin ba zai kula ba, balle ya bi baya.
Abin da kawai ya fada kenan, tayi matukar
fusata da maganar tashi ta shiga sakin maganganu,
ai kai ma ba haka kawai ka ke wannan zaryar ba.
Ka ke ganin a kanta zaka iya batawa da kowa,
ai rashin imani suke gwadawa tunda abin da ba a
sha suke wankewa suna ba ku.
Maimakon yayi shiru tunda ya ji inda ta maida
zancen nata, sai naji ya ce, ni na yafe mata, ba
kuma rashin Imani aka yi min ba, da bakina sai in
yi yanda ake so tunda ai nawa ne.
A mafi yawancin lokaci, nakan hakura da
abubuwa masu yawa sosai inyi ta hakuri dasu
saboda sanin da nayi cewar gaba daya matan gidan
nan idonsu a bude yake akan al'amarin zamanmu
ni da mijina.
Tunda Ado da Ruwaila suka yi wadannan
maganganun gashi dai a zahiri wàsa suka yi irin na
matar wa da kuma kanin miji, amma can cikin
al amarin nasu sun kulle wani abu Ruwaila dai 1a
nanata maganar yafi a kirga.
Ana cikin haka, raninan na amsa kiran da

82

Goggo Ayalle tayi min da sassafe, Ado bai fita ba
ya jira in je in dawo don ya ji kiran akan menene?
Me ta ce miki? Yayi min tambayar tare da bina
da kallo zuwa in da na zauna.
A hankali cikin natsuwa don kar ya dauki
maganar da tsanani nace mishi kan maganar girkin
ne.
Wani lalataccen ashar ya wulwulo ya antakawva
Ruwailah, zan sa kafar wando daya da matar nan,
wai ita tana son takurá min ne ko?
Nayi maza na fara bashi hakuri, ba fa ita ba ce.
Da sauri ya ce ke matsa can, ke me ki ka sani? Tlo
ka gani ma dai kawai ni kam kayi hakuri na
gayawa Goggo zan karbi girkin.
Da sauri ya tanbaye ni mene? Za ki karbi girki
ki ka ce musu? To kje ki karba ta kuma kisan
yanda zaki yi dasu ni babu ruwana.
Tunda na gane kin fi jin tsoronsu da ni, kin
kuma fi jin maganarsu da tawa.
Kuka na soma yi mishi sosai da sosai, to ya ya
zan yi? Iyayenmu ne in naji maganarsu ko naji
tsoronsu nayi hakan ne saboda girma da darajarka a
wurina ba zan 1ya jayaiya da su.
Goggo ta ce, "Ci gaba da kin shiga girkin nawa
zai zamo sanadin da kowa zai 1ya warewa ya ce

83

baya ciki, in nayi haka kuma ban kyauta musu ba,
don wannan girkin nasu yana cikin alamomin hadin
kan gidansu.
Gaba daya suna ci daga tukunya guda, to sai
kuma in ce mata ba zan yi ba?
Shiru Ado yayi cikin nazari da tunani kafin
jimawa can ya dago ido ya kalle ni ba za ki iya
aikin ba Humaira ba, kuma zasu taya ki ba don
wannan haduwar da ki ke ganin suna yi kowadanne
suna taya 'yan group din su ne.
Ke kuma ba kya cikin na kowa, sannan cefanen
gidan nan ba karamin abu ba ne, ni kuma a halin
yanzu ba zan iya ba saboda a halin da nake ciki
kina gani sarai kullum kara maneji nake yi.
Ban yi miki bayani ba ne, don,ba ki yi magana
ba, ba ki kuma nuna min damuwar ki ba duk wani
abin da nake kashewa yanzu ba nawa ba ne,
rancensu nayi.
Hannu biyu na dora a kaina na ce rance? Bai
kula ni ba sai yaci gaba, to zan rinka cin bashi ne
ina yin cefanen da bai zaa min wajibi ba?
In suka yi hakuri ma ai nima ba zan bar abin
haka kawai ba, tunda duk masu cin abincin nawa ne
ba sai an ce min in yi ba.
Ni kam kuka na rinka yi saboda na tsani bashi,

84

gai nake tankar shi ne karshen fitina tunda naji
Malla mai babban Allo yana yawan neman yin
magans kan Hadisan da suka yi mini da gaggauta
biyanshi in har mutu ya cilka ana bin shi, kai ni kam
ban son bashi.
Kukan da nake tayi yasa Ado tsayawa yi min
bayani Ke bashin fa ba wanda za'a matsa min ba
ne wurin Haruna naje na karba wannan abokin
nawa da nace miki tare muka yi Secondary School.
Yana gamawa shi ayayenshi suka yi mishi aure,
har na ce miki yanzu matanshi uku da 'ya'ya birjik
yana kuma ta hidimarshi.
Duk da Ado yasha bani labarin abokinshi
Haruna na rowan bargo ban ji dadin bashin da yace
min yaje ya karba a wurinshi ba da nayi tunani
sosai ma sai na gane har 'yan atamfofin Nicharm
din da ya sayo min guda biyu yazo min dasu a
dinke, wai in dan sabunta a kudin da ya rantan ya
sayo min su.
Ke ba fa ni kadai ne nake cin bashi ba utane da
yawa ana bin su bashin da bai dadi shi ne wanda ka
karba bayan kasan baka da hanyar biya, ni kuwa
ina da shi.
Damuwar da ya gani a tare da ni ce tasa shi yi
min wannan bayanin, tabbacin da Ado ya bani na

85


bashi da halin da zai yi cefanen gidan nan in girkin
yazo kaina yayi matukar tayar min da hankali.
Duk da ni din ba mai yawan yin addu'a ba ce,
sai na dukufa nayi ta karanta wata addu'a da mai
babban allo ya bani ita, ya ce min addu'ar Nana
Aisha' ce (R.A) a kowanne lokaci.
Wani lokaci ma in na zauna ina yi na rinka
kenan sai Ado ya gaji da ganina a zaune ya sure
ya dora a katifa yana daiyar cewar da nayi mishi
mai babban allo ya ce min mai yawan karanta
addu'ar baya talauci.
Shi kuwa Ado sai ya ce nin, in ya kama sana'a
ko? Ko kuwa haka kavwai za su Zubo mishi? Ban
kula shi ba, iyaka dai ban daina ba.
Rannan mun tafi Makaranta da safe shi kuma
ya wuce gonarshi kan hanyar tatiyar tamu dai ya
bani tabbbacin a satin nan zai fara dibar masararshi
ya sayar ko da bata gama karasawa ba, tunda ba zai
sake zuwa wurin wani neman wani rancen ba.
Na ce mishi, to in dai ba ya zama dole ba kar
ya yi hakan, ya kara hakuri kawai
Na shiga aji ya wuce ya tati, ina aji ina tunanin
Ado, irin wahalar da ya yi wa gonarshi ya sonmna
diban masararshi a yanzu ba karamin asara ba ne
tunda ba duka ne tayi ba wacce tayin ma bata yi

86

wani kwari ba.
Ana tashinmu na fito ban ganshi a inda yake
jirana ba, na dan tsaya kadan ko zai karaso ban gan
shi ba naga za'a watse a bar ni ni kadai nia na biyo
hanya na dawo.
Ina bullowa lungun gidan mu naga wata
lafiyayyar mota a tsaye a kusa da Masallaci mai
lambar Abuja, ban sake kallonta ba, na wuco na
nufi cikin zauren gidanmu muka yi kaci6is da shi
Na daga ido na kalle shi har ya dawo yayi
wanka yasa T-shirt da wandon shi masu kyau
wadanda ma ba kasafai yake sanya su bayana kuma
kamshin turarenshi.
Ban san dalili ba sai naji haushinshi ya kama ni
nan take na soma yi mishi kuka, shi ne baka biyo
min ba ka dawo gida?
Ina kukan ina tambayarshi, to kiyi hakuri mana
Humaira, ki tsaya mana kiji abinda yasa nayi hakan
in ban da uzuri ba ki gamsu ba sai kiyi hakan ki.
Daga cikin dakin zauren nan na jiwo wata
murya tana tambayar Ado to kai tsoron kukan nata
ka ke yi ne?
Da gudu na fada dakin jikin mai babban allo na
kwanta shi da Baba Yahaya ne a ciki.
Mai babban allo ya ture ni yana fadin "Ke

87
matsa can ja'ira, shagwababbiyar wofi, kar ya baro
ki a makaranta ya dawo shi kadai akan me?
Duk tsiyarki da wayonki mata hudiu zai yi ba
da ke kadai zai zauna ba, nayi murmusha na cee
oho, ni dai nayi gaba, Baba Yahya ya taya ni
murmushin tare da fadin gaskiyarki Aishatu.
Na gyara zama na gaida Baba Yahya cikin
ladabi da girmamawa, yana kallona sai murmushi
yake yi alamar dadi ya kama shi.
"Karatu ki ke yi?" Na ce mishi "Eh Baba." Ya
sake wani murmushin ya kalli Ado Ubengiji ya yi
muku albarka ya rufa muku asiri ko in e ya kara
don ya riga ya rufa sai neman kari. Ado ya ce amnin
Baba.
Na kalli mai babban allo ina murrmushi "Ina su
Hajiyoyinki?" Ya taya ni murmushin tare da fadin
kalau din su, ba su ma san zamu zo ba."
Na sake kallon Baba Yahya na ce "Baba ba ku
gaya wa kowa ba ne? Baba Yahya ya ce, ai babu
wanda ya sani jiya da daddare ma da Yayanku yazo
nan gidan shi da Atika nayi kamar in gaya musu sai
kawai na fasa.
Nayi murmushi na ce dukansu lafiyarsu kalau
Baba? Ya ce kalau dinsu Aliya dai zata tai aikin
Hajji ita kuma Atika cikin dake gare ta yasa ba a yi

88

maganar tafiyar tata ba. Dadi ya kama ni jin alherin
da 'yan uwana suke ciki.
Na sake kallon Baba Yahya cikin natsuwa na
ce mishi oh Baba, ashe zaku zo dubani da sauri ya
ce zamu zo mana Humairah, zamu zo mana mu gan
ki.
Na kuma ji dadin zuwan da nayin ba kadan ba
nazo na same ki kina karatu, mijinki ya maida ke
makaranta don kiyi ilimi shi kuma naje gonarshi na
gani wannan noma da wannan yaro yayi ya wuce
abin mamaki sai abin tsoro.
Zuciya dai ita ce mutum, shi yasa Manzon
Rahma (S.A.W) ya ce, in ta gyaru dukkan jiki ya
gyaru, in kuma ta Baci to dukkan jikin ne ya baci.
Na dan yi murmushi saboda jin dadin
gamsuwwar da ya ce sunyi na ganinmu cikin natsuwa
na ce mishi Baba har kun je gonar ne?.
Mai babban allo ya ce ai mu ta can muka fara
don da muka yi tambaya gonar tashi aka kaimu, ai
mijinki ya zama sarkin noma.
Na sake wani murmushin daidai Ado ya sake
shigowa da wani kwanon a hannunshi.
Baba Yahya ya kalle shi cikin natsuwa daidai
yana ajiye kwanon ya ce mishi kai mu fa mun riga
mun koshi, wannan gaudan da ka kawo mana ba

89
cin wasa muka yi mishi ba.
Ai rabon ma da in ci gauda mai dadin na yau
har na manta matanmu na can ba su iya irin wannan
girke-girken ba.
Ina jin sun tsunduma hira da Ado akan maganar
gonar tashi nayi maza na nemi izininsu na shiga
gida naje na tube uniform dina na daura sabuwar
atamfata.
Na gyara nayi tsaf, na yafa sabon gyalena na
dauko abincin da na tanadan mana muci, in mun
dawo. Na hada da abin shan da nayi na ajiye cikin
randar kasa na dora a tire na hada dasu plate
cokali da kofuna, na dawo nayi sallaa a bakin kofar
suka amsa.
Na shiga na tsuguna na ajiye tiren mai babban
allo yana kallona yana cewa, amma ai kina jin
Babanki yana cewa sarkin noma mun koshi ko?
Ban asa mishi ba, na kalli Baba Yahya cikin
yanayin da zai tausaya min, na ce mishi Baba
wannan abincina ne da nayi da hannuna, kuci ko ba
yawa.
Nan da nan ya ce, zuba mana muci Aisha, nayi
maza na jawo plate-plate zan fara zubawa, mai
babban allo yana fadin "Ka ji wai tana jaddada da
hannunta tayi kamar hannun nata ya wani iya ko

90
kuma dabanne.
Ado yana murmushi yana fadin, kai dai bari ka ji
kawai Mallam.
Ina zuba musu abincin, Baba Yahya yana
kallona. Burabuskon gero ne da miyar taushen da taji
busasshen kifi da tantakwashi, sai kamshi suke yi
daga shi har miyar.
Na zuba musu a plate na zuba musu miyar sosai
na mika musu, Baba Yahya ya kai lomar farko ya
tsaya ya sosa kunnenshi da dan makullin motarshi
kafin yaci gaba da kai loma bakinahi.
Jimawa can, sai naji yana tambayata Ke da ki ke
sammakon zuwa makaranta Aishatu, da wanne lookaci
ki ke wannan girkin?"
Kan in yi magana Ado ya soma yi mishi bayani
har yana ce mishi ban cika gane ina wahala mai yawa
ba Baba, saboda Humairah wata irin yarinya ce mai
hakuri da juriya.
Duk abin da zata ji ta taimaki abokin zamanta shi
take yi, babu yanda za'ayi in dawo gida bata gamsar
de i ba, tana kuma tsusayin wahalata.
Matsalarta daya ce, Baba kullum a kanta muke
fada da ita, Baba Yahya yayi murmushi saboda ganin
rin kallon da Adon yayi min yasan zolayata yake so
yayi.
Ya ce, kishi ne da ita Baba kishin ma na rashi

91
hankali, in ba haka ba.... Mai babban Allo ya karbe
maganar, don haka Adon yayi shiru shia yana
sauraron shi.
Yayin da Baba Yahya yake ta faman murmushi,
ni kam tsuke fuska nayi na sunkuyar da kaina kasa, ai
duk tsiyarta sai kayi hudun nan don kayi biyu ma'ai
ba wani kokari kayi ba.
Kana girbe amfanin nan naka, ka samu wata
santaleliyar fara ka hada, kaga sai ya zama kana da
baka ga kuma fara ka kawo.
Baba Yahya yayi dariya ya ce rabu da su kin ji
Humairah ke dai ki kara kokari akan wanda mijinki
yake bada labari kin ji ko? Na ce, to Baba.
Na kwashe kwanuka na fita dasu na dawo don
yin sallama da su, ina durkushe Baba Yahya sai
faman sanya mana albarka yake yi, zan je in baiwa
uwarki labarinlku.
Na sake wani murmushin, kudi ya miko bandir
din Naira hamsin-bamsin guda biyu sababbi, "Rike
wannan ki rinka zuwa makaranta da su."
Nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya,
suka fita suka tafi ina leke ina ganinsu tsaye tare da
su Baba Tanimu da sauran mutanen unguwa.
Na koma na shiga gida ina ta murnar kudin da
Baba Yahya ya bani cikin zuciyata, ina fadin shi
kenan ajiye su zan yi in girkin ya zo kaina Ado ya

92
samu abin da zai yi cefane dashi.
Jimawa can sai ga Ado ya shigo murmushi yake
tayi, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi sun tafi?
Ya sake wani murmushin ya ce sun tafi Humairah, ni
a rayuwata ko me zan cewa Baba Yahya? Oho! Nayi
murmushi na ce mutumin kirki ne amma Baba Yahya
kadai mai babban allo fa?
Yayi murmushi ya ce, dukansu Humairah, amma
Mallam ai kin san ganinki yazo yi, na ce ai haka
kace? To bari sai na gaya mishi.
Yayi dariya ya ce, "Yi hakuri." Na mika mishi
kudin da Baba Yahya ya bani, ina murmushi ""Ga shi
nan ka samu kudin cefane in girkin ya zo kaina.
Wani irin lallausan murmushi ya sake kafin ya
daga gefen katifa ya rinka fiddo min bandir din dari
bibiyu sai da ya ajiye guda biyar,
Zubawa kudin ido sosai nayi ina kallonsu, a ina
ka same su? Ya ce a ina na samne su kuma? Ban da
wurin Baba Yahya. Sannan ko mai babban allo bai ga
lokacin da ya bani ba.
Baba wani irin mutum ne mai iya martaba
mutum ya sake kallona cikin murmushi mashin zan
je in sayo mana don in hutar da ke tafiyar kafan da
kike yi zuwa makaranta kullum da dawowa.
Asabar da Lahadi kuma in dan rinka daukanki
muna fita kina ganin kauyuka da kasuwanni.

93

Na kalle shi cikin natsuwa na ce, ni na yafe kaje
ka biya bashin da ka karba in sun ragu ka rike don
cefanen abincin gida.
In gonarka takai kayi girbi in ka gama biyan
sadakin aurarrakin da zaka yi in wani abu ya ragu ka
sayi mashin din.
Yayi dariya ya ce, wai wa ya ce miki zan yi aure
ne? Na galla mishi harara na ce, uhun ba ina jin mai
babban allo yana ce maka kar ka yarda in tsufar da
kai ni kadai ba? Yayi dariya mai karfi ya ce, kai
Humairah! Ke kam ban san iyakacin kishinki ba.
Don haka yau bari in yi miki wani alheri tukuicin
zuwa mai babban allo gidana, in hutar da ke in
kwantar miki da hankali, don ki sakata ki wala kiyi
abin da ki ke so, aure ko?
Ya zuba min ido yana kallona cikin natsuwa da
walwala kafin ya ce a yanzu a wannan halin da muke
ciki ba zan yi shi ba, ban ce miki kwata-kwata ne ba
zan yi ba, a'a a wannan lokacin ne ba zan yi ba.
Don haka kar wata ta sake ce miki an ganni wani
wuri bani ba ne, in kuma lokaci yayi na in yin to ni
da kaina ne zan gaya miki.
Don ina fatan in yi ne a lokacin da ke da kanki za
ki gamsu da cewar eh, ya dace in yi in ba, wannan
halin na samu ba, ba zan yi miki kishiya ba Humairah
to me zan yi da ita?

94



Duk da cewar da nayi wa Ado kar ya sayi mashin
sai daya saya don irin na matasa, yana kawo mashin
din gida su Baba da su Goggo suka sa albarka ya
shigo ya ce min ki shirya in rana tayi sanyi za ki raka
ni Ruwan bago muje in kaiwa Mallam Haruna
kudinshi.
Daga nan kuma tunda yau ranar Lahadi ne sai mu
tsaya a kasuwar "Sundu' muyi sayayyar abin da ba
mu dashi na kayan abinci, na ce mishi to.
Da yamma na shirya nayi kwalliya da daya
atanfar tawa itama Nicharm ce amma nayi kyau
sosai, na yi wa mutanen gida sallama naje na dale
bayan mashin din Ado, wanda tunda na gan shi nake
ta faman murmushi.
"Ke ba ki san yanda tafiyar kafan nan da ki ke yi
yake ci min rai ba ne." Abin da yake gaya min kenan,
lokacin da na sa hannu biyu na kankame shi kamar
yanda ya yi min umarni.
Muka fara tafiya, sai da muka tsaya a Sundu
muka yi sayaiya muka ajiye a wata runfa muka wuce
zuwa Ruwan Bago.
Gidan Mallam Haruna, ni na shiga wurin
iyalinshi na shiga wurin uwargidan Hannatu, don
Ado ya ce min ita yafi sani, nan sauran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login