Showing 6001 words to 9000 words out of 30903 words

Chapter 3 - MIJIN TA CE BOOK 3

20 Aug 2024

4865

yawan zuwa wurina, na
gyada kai nuna alamar na gane shi, ya ce to shi ne
babban wanmu a nan sasan shi ne dan Baba
Tanimu na farko wanda yaje ya karbar min aurenki
amma ai kin san ni ni kadai ne wurin mahafina ko?
Na girgiza kai a hankali, nuna alamar ban sani
ba, ya ce to ni kadai ne. Ya ci gaba da abinda yake
yi na kaye-kaye da gyare-gyare tanfar dai ba a cikin
dare muka shiga dakin ba.
Ruwailah ta dawo da ruwan zafi a bokiti da
wani kuma a flaks dinta da ta dauka a dakin, ga
kuma wani kunshi cikin leda da ta ajiye a gefe, wai
yana yi muku sannu da zuwa.
Ado ya yi tsaki ya ce, kai ke kan ba ki da kirki,
yanzunnan sai da ki ka tashi bawan Allahn nan a
cikin tsohon daren nan ki ka yi sanadin fitarshi
waje? Ta ce, oh oh, ba ma a wurina yake ba, to
amma da bai fitan ba da wa ya sauke maka

35
mutumin da kazo dashi din?
Ado ya rike baki nuna'alamar mantuwa, ya ce
na shagala ina kallon Humaira, kin san ni in ina
tare da ita to sunana ne kadai ban iya mancewa da
shi.
Ruwaila ta kyalkyale da dariya ta ce, ai kuwa
dai ma kayi kokari tunda ba ka mancewa da sunan
naka a nan sanu.
Sabon soso da sabulu da brush da abin wanke
baki da sabon tawul ya fiddo daga cikin jakar tashi
ya miko min na karba nabi bayan Ruwailah da ta
daukan min ruwam muka je ta nuna min ban dakin.
Na dawo daga wankan na samu kwanukan
abinci iri-iri, ya kalle ni ya ce min wannan kunshin
na gasasshen nama ne Yaya Jafaru ya sayo miki, ga
furar da Baba ya bayar da nono Ruwailah ta dama
miki, ga kuma tuwon dawa miyar kuka shima mai
dumi ne ta dumamo da wanne za ki fara?
Na ce kowanne, ya kalli Ruwailah da ke ta
faman bubbude min kowanne in gani ya ce mata ba
kin gama naki ba, to kije mana kuma sai da safe, ta
ce am wai jira nake yi ta gama mu tafi can wurina
ta kwanta.
Yayi maza ya ce, wasa kenan, tabar dakin
mijinta da mijin nata a ciki taje ta kwana a wannan

36
tsohon dakin naki? Ta ce, to ai shi kenan sai da safe
Amarya. Nayi murmushi na ce mata to ki huta
gajiya.
Tana fita Ado ya kalle ni ya ce wannan
atishawan da kike tayi fa don kin yi wanka a bayan
gidan da babu rufi ne baki saba ba, ban amsa mishi
ba amma cikin zuciyata nima na yarda hakanne don
maimakon in ji dadin wankan da nayi sai naji
kamar sanyi ya kama ni.
Naci tuwo sosai don yayi min dadi laushinshi
da dankonshi yayi banban da irin tuwon da na saba,
nasha ruwan tea mai cçitta naci nama kadan na
gyara na kwanta bayan na shafa mai nasa rigar
baccina wanda itama shi yazo da ita.
Na kalle shi cikin natsuwa nayi mishi magana
wanda tun fitowarmu ban yi mishi ba saboda na
gane babu komai cikin jakar tashi in ban da
kayayyakin amfanin da ya saya saboda ni na ce to
da ban biyo ka ba fa yaya zaka yi da kayan nan?
Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, ban taba
daukar za ki iya kin bina ba, na dauka ke ma kina
sona.
Muna kwance ni da Ado akan katifar yana
gefenshi ina nawa sai dai mu dukanmu babu wanda
ya samu yayi bacci, ya daga ido cikin natsuwa ya

37
ce min Humairah ba ki ga kamar kasa yin baccin
nan da muka yi alama ne na muna jin marmarin
juna ba?
Nayi maza nace mishi, a'a bana ji ya sake daga
ido ya kalle ni ya ce, to ai ni ina ji, nayi maza na
tsuke fuska na ce mishi ba fa na zabi biyo ka da
nufin in biyo ka ba ne.
Cikin natsuwa ya ce min ai na sani, na sake
tsuke fuska na ce, to ko da na biyo ka akan
kuskuren ba zaa zan yi ba, komawa zan yi. Ya sake
cewa na sani, ya sake saurarawa ko zai ji zan sake
fadin wata magana, sai yaga nayi shiru.
Sai naga yayi murmushi kafin ya ce min to
amma ai ko za ki koman tunda ba ki kai ga tafiyar
ba ai ina ganin ba zai hana in nace nayi marmarinki
kiyi min yanda ki ka saba yi min bä ko kuwa. Nayi
maza na kara tsuke fuska, kafin na ce mishi a'a, ya
ce to shi kenan sai da safe.
Washegari tun safe Goggo Ayalle ta dawo
gidan a dalilin aiken da Baba Tanimu yayi na a
dauko ta, tana dawowa kuwa ta maida ni dakinta,
wunin ranar har dare ban gane na gama gaisawa da
mutanen gidan nan ba saboda yawansu.
Don haka kowa na gani kawai sabuwar
gaisuwa nake yi mishi, sai in shi ne ya ce min ai

38
dazu mun gaisa in ce mishi to.
Karba sosai Goggo Ayalle tayi min, ta yi ta ina
taka saka dani, komai hannunta ya kai kan shi in
dai ta daga taga naci ne miko min shi take yi, ungo
ki ci, sai in ni ce naga zan kwari kaina in ce mata
na koshi.
Sau goma kuma in ta kalle ni zata yi murmushi
ta ce, oh haka rabo yake har da rabon aurenki cikin
al'amuran da suka kai Adamu garin nan suka
zaunar dashi, kin san shi rabo ba karamin al'amari
ba ne.
Sai kawai nima in taya ta murmushin da take
yin sai dai ban ce mata komai, can anjima kuma sai
ka ji tana sake tambayata in ce ko dai manyan duka
lafiya? In sake cewa lafiyarsu kalau, tamfar dazu
bata tambayí lafiyar tasu ba.
A haka muka wuni har dare ina idar da Sallar
Isha'i ta kalle ni ta sake nuna min gadon da na wuni
akai ta ce min hau kiyi barcinki ki huta gajiya, kar
yan hiraa suce zasu dame ki, na ce to. Na sake
dalewa gadon nayi kwanciyata, zuwa can naji Ado
yana kirana, nayi kamar ban ji shi ba, ya matso
kusa da kofar Goggo yana tambayarta.
"Goggo Humaira tana kusa ne?"
Goggon tayi maza ta sauka daga nata gadon ta

39

leka tana tambayarshi wani abu ka ke so ne
Adamu? Ya ce a'a Goggo, sai da safe. Abin da
kawai ya fada kenan sai na jiwo Baba Tanimu daga
dakinshi yana fadin "Yau ga wani al'amari, wannan
fa shi ne girman kwabo.
An gira ba ayi hankali ba, yaro yana kwalawa
matarshi kira kina ji tayi shiru ba kiyi mata magana
ba, ya taso yazo har kofar dakinki yana tanbayarki
ita kin ce wai in wani abu yake so ya gaya miki, to
in ita yake so fa?
Na ce in yana da bukatarta ne ma ya gaya
miki? Goggo tayi maza ta ce au, to ai bangane ba
ne. Ke Aisha tashi-tashi je ki maza mijinki yana
kiranki."
A kan dole ta fito da ni daga dikin na shiga
dakinmu na samu Ado yana zaran jiran shigowan
nawa, gasasshiyar kaza ne a gabanshi, a gefenta
kuma flaks ne na ruwan zafi, ban kalle shi ba na
wuce na hau katifa nayi kwanciyata, ya biyo ni da
kallo fuskarshi ta bayyanar da rashin jin dadin shi
kan yanda nayi.
Yayi karfin hali ya hadiye fushinshi tashi mana
Humairaa nayi kamar ban ji ba, yayi tayi min
magana nayi shiru kamar ba dani yake yi ba, ke ni
fa kin san bana son irin wannau wulakancin na ayi

40

tayi miki magana kina yin banza da mutane, ban
tanka mishi ba, ban san yanda aka yi ba sai kawai
naji ya cafko hannuna ya murde.
A firgice na kwallara kara saboda zafin da naji,
na kuma yi maza na kame bakina nayi shiru saboda
funawar da nayi cewar a bakon wuri muke ko kuma
ni din ni bakuwa ce.
Daga cikin dakin Baba Tanimu da ke
makwabtaka da namun naji an yi gyaran murya
alamar dai yin kashedi.
Ado ya hakura ya gyara ya kwanta, ni kuwa
naci gaba da zama a kan katifar ina kukan sharbe
tare da shisshika a hankali sai dai shi Ado shiruu
kawai yayi amma yana ji na.
Ana cikin haka wani irin hadari ya taso mai
matsanancin iska da guguwa da rugugi mai
tsananinn firgitarwa har wani bai iya cin motsin
wanda suke tare, sai in yayi motsi ne da karfi nayi
maza na gyara na kwanta da nufin yin shiru kamar
yanda shima Adon yayi, sai kawai naga ya juyo
gare ni.
"Kin fasa kukanne?" Nayi kamar ban ji shi ba,
Ni fa yau ba zan iya irin kwanan da muka yi jiya
ba." Ya miko hannu zai taba ni, nayi maza na ce
mishi "Gaskiya ni fa ba zama nazo.yi ba, ko yau

41

dinnan da ina da kudin mota da tafiyata nayi."
Ina gama fadin hakan ya cafke ni, bai saurari
ihun da nake yi mishi ba saboda yasan ba zai kai ga
kunnen Baba Tanimu ba. Sabuwar iskar da ke
kadawa ga tsawa da rugugi, watakila ma ya dade
yana baccin shi, gane hakanne yasa ni barin ihun na
koma yi mishi bayani.
"Ni gaskiya tun da muka zo fa cikina yana
ciwo, ban gaya maka ba ne kawai." Bai saurara ba.
Na kwana da matsanancin ciWon cikin da yay
dalilin da na kwana ina murkususu daga kan katita
in koma kasa, na rasa in da zan sa kaina in ji dadi,
nayi kuka har na hakura nayi shiru.
Ado yayi nadamar abin da ya faru tsakanina
dashi, yayi nadamar tilasta min da yayi a haka
muka kwana daga ni har shi babau wanda ya samu
runtsawa.
Ana fitowa daga sallar Asuba muka kama
hanya zuwa asibiti da ni dashi da Yaya Jafaru da
Ruwailah, saboda tun dare ya shaidawa Baba
Tanin halin da nake ciki, tun daren kuma Yaya
Jafarun yayiwo aron mota wurin wani abokinshi
don ma Baba Tanimu ya hana tafiyar daren ne yaa
ce a hakura ayi sallah tukunna.
Asibitin Malunfashi ya kai mu, shi ne wai yafi

42

girma a nan kusa, gwajin farko da Likitan tayi min
tayi bayanin ciki ne ya lalace ya fita daga cikin
mahaifa, sai dai bai shiga ya fadi ba, saboda haka
zasu wanke shi ya fita don in ba haka zan yi ta
wahala da shi kafin ya kai ga fita.
To amma me ya kawo haka Likita? Ado ya
bukaci sani, tayi ta lissafo dalilai ciki har da tafiya
mai tsanani ko kuma bacin rai ko aiki mai wahala
shi yasa yawanci muke hana mata masu karamin
ciki ko kuma cikin da ya riga ya kai watanni
bakwai yin irin wadannan abubuwan, ku kuma
maza muke rokonku da ku rinka tausaya musu.
Daga Ado har Yaya Jafaru da Ruwailah sun
gamsu da jawabin nata.
Aka yi min wankin ciki aka sallamo mu bayan
La'asar, duk da Ado yaso a bar ni in kwana wai a
kara kulawa dani sosai aka ce babu gado.
Mun iso gida gab da magriba, kai tsaye dakin
Goggo Ayalle aka kai ni, wacce ta yi fada mai
tsanani akan wankin cikin da taji an yi min, ina
dalili yarinya ko haihuwar fari bata yi ba za aje ana
kakaba mata karfen nasara a ciki? Da da ni akaje ai
da ban bari anyi hakan ba.
Gaba daya hankalin Ado yayi matukar tashi da
abin da ya farun, ina jin Baba Tanimu da daddare

43

yana ta ba shi hakuri, ita rayuwa fa haka take, a
kullum mutumin kirki ba ya zama ba tare da ana
jarraba shi ba, ba ka fita daga cikin wannan ba ga
kuma wannan ya sake zuwa.
To kayi hakuri kar kuma ka ee zaka yi saurin
gayawa iyayenta tunda ga irin rabuwar da ka ce
kun yi dasu.
Naji Ado ya ce, "A'a Baba, ba zan iya boyewa
mahaifiyarta halin da take ciki ba, tun muna asibiti
nayi waya na gaya mata, ban dai sake gayawa kowa
ba; amma ita kam na gaya mata, ya ce to shi kenan
tunda kaga hakan yafi.
Kwanana bakwai a dakin Goggo Ayalle tana ta
faman tarairayata, Baba Tanimu kuma da su Baba
ubangida suka yi ta bayar da kaji ana yankawa ana
yi min farfesu, har ma cikin kajin Goggo ta cire
wata yar budurwa da ta bata sha'awa ta ce ba za ta
yankata ba, bar min ita zata yi in yi iri.
A zuciyata na ce, uhun ni kam ai ba.zama nazo
yi ba.
A wadannan kwanakin babu wata mu'aallar
arziki tsakanina da Ado, ko gaisuwarshi ban cika
amsawa ba. A cikin kwanakin ne kuma na lura ya
daina zama a gida tun bayan fitan da suka yi da
Baba Tanimu ba a sake wayar gari na ganshi a

44

gidan da safe ba sai gab da Azahar, ana yi sallar
La'asar kuma zai sake fita sai kusan faduwar rana
ya dawo.
Ban san ina yake zuwa ba, ban kuma tambaye
shi ba don a yanzu ko kallon shi bana yi, fatana da
tattalina bai wuce in samu kudin mota ba in kama
hanya in yi tafiyata.
31Rannan ya dawo kusan Azahar ya shigo dakin
na Goggo, duk da yana ganin naji sauki har ma
nayi kyan gani, sai ya tambaye ni ya ya jikin naki
dai Humaira? A lalace na ce mishi da sauki, ya
kalle ni cikin natsuwa.
"Amma kin ga yayi miki daidai a hakan da ki
ke yi Humaira? kina mu'amallah da kowa lafiya
amma ni da na kawo ki babu?" Na kalle shi a
sakarce na ce mishi, "To ka maida ni mana in da ka
dauko nin." Ya ce, to babu laifi ya wuce ya fita.
Ran da na cika kwana goma rannan Baba
Tanimu yasa Goggo ta sani na koma dakin namu,
ita kam taso ne a bar ni in yi arba'in.
Zaman da na yi a dakin Goggo ya sani fahintar
gidan sosai da kuma mutanen gidan.
Sassa guda hudu da ke gidan suna karkashin
dattawa hudu ne wadanda su ne asalin yayan
maigidan su kuma dukan su uba daya ne ya haife

45

su, amma uwa daban-daban, babban cikinsu shine
Baba ubangida sai Baba Halliru sai Baba Tanimu
kafin Baba Tukur shi ne karaminsu..
A duka sassan nan guda hudu akwai iyalai
musu yawa su dattawan gidan kuma suma suna da
nasu matan, Baba Ubangida shi ne mai mata Goggo
Turai wacce take sana'ar kokon safe, Baba Halliru
shi ne mai Goggo Jaku ita kuma tana furar sayarwa
mai dadi Baba Tanimu Goggo Ayalle ita kosai take
yi itama da safe.
Sai Baba Tukur, shi kuma tashi matar ita ce
Goggo 'yar neto ita kuma tana gaudan sayarwa. A
kowane sassa na gidan akwai yaran mata masu
yawa saboda kusan duk 'ya'yan gidan maza masu
aure ne wadan da basu yi ba 'yan kadan ne mafi
yawancin masu auren kuma mata bibiyu ke gare su
masu dai-dai din basu da yawa, kamar ma ba su
dade da yin nasu auren sosai ba.
Yanda duk tsofaffin gidan ke da sana'o'insu
haka suma yaran matan gidan suke da hasu
sana'o'in tun daga mangyada, manja, gyadar miya,
maggi, gishiri, Alala, dan wake, gasu nan dai birjik
Wasu har dinki wasu kuma har aikatau da su wanki
amma dai kowa da abin da yake yi gwargwadon
karin injin shi.

46
Kiwo kuwa a gidan ba a magana duk yawan
Tumaki da Awaki da Kajin kuma abin mamakin shi
ne kowa yána shaida nashi.
Gaba daya sassan nan guda hudu kuma akwai
mace guda da take kamar ita ce shugabarsu a
sassan Baba Tanimu dai Ruwailah ce matar Yaya
Jafaru ta farko, a sasan Baba ubangida da kuma
akwai Furera matar Yaya Baidu itama uwargida ce.
Sasan Baba Halliru akwai Gaje matar Yaya
Jumare, itama uwargida sai sasan Baba Tukur nan
kuma Tanbai matar Yaya Amiru akwai Uwale,
itama uwargida, gaba daya wadannan matan hudu
sun zo gidanne a kusan lokaci daya, ma'ana babu
bambancin lokaci mai yawa a tsakanin aurarrakin
nasu dukansu kuma suna da amare da kuma matan
kannen miji.
Haka nan gaskiyar Mama ne gaba daya gidan
tukunyar abincinsu na dare gaba daya ne da rana ne
dai kowa zai yi abin da zai ci shi da iyalinshi a
wurinshi amma na dare a hade yake duk kumna
wanda ke da girkin ranar to shi ne mai ba da hatsin
da za ayi amfani dashi dama duk abinda za a nema
Goggo Ayalle kuma ta shaida min cewar in mace
tayi girki sau daya to kwana ashirin da biyar take yi
bata sake ba.

47

Ai kuwa kin ga dole suyi ta neman kudinsu
tunda basu da wani aiki na ce haka ne, a zuciyata
kuwa cewa nayi yaran mata ashirin da biyar kenan
a gidan.
Muna nan zaune a dakinmu ni da Ado, zaman
babu wani dadi. Kallon shi bana yi balle in san me
yake ciki, shima baya takura min akan komai zuba
min ido kawai yake yi babu abin da nake fata irin
nera talatin-talatin din da Baba Tanimu yake bani
kullum safiya, ya ce wai in sai abin da nake so in
karya da shi da kuma ashirin-ashirin din kokon da
Baba ubangida yake bani.
Ita kuma Goggo Turai ta ce kai haba, bakin.
wannan yarinyar dai ita kadai ace sai na amshi
kudinta? Je ki ki rike kudinki kin ji? Don haka
kunu da kosai ba saye nake yi ba, sai nake tara
hamsin-hamsin din ina fata su ishe ni kudin motar
tafiya gida in sulale in yi tafiyata.
Rannan na wuni ina murna na kirga kudina sun
kai dubu daya har da dari daya ina lissafin
kwanakin da suka saura kudina su gama cika sai
kawai nazo zan ajiye wata nera hamsin din naga
babu komai sai wata tsohuwar nera hamsin itama
wata kila bai ganta ba ne sanda ya kwashe su. Nayi
kuka rannan har na gaji ban kuma iya cin komai ba

48
saboda tsananin bacin rai.
Ado ya dawo gab da Azahar ya same ni a haka,
ya juya ya fita bai zauna ba, bayan Sallar Isha'i mna
ya shigo dakin da niyyar kwanciya ya same ni ina
ta faman kuka, wuri ya nema ya zauna bayan yaje
yayi wankanshi ya dawo.
Ban kalle shi ba balle in san me yake yi, sai
naji yana magana alamar waya yake yi, gaisuwa ta
ladabi da natsuwa naji shi yana yi, don haka na
kasa kunne ko zan gane da wa yake maganar, sai
naji yana cewa.
"Gaskiya Inna na gaji da karyar da nake yi miki
ne, cewar muna nan lafiya, a gaskiya ba hakan ba
ne, ina jin salatin da Inna ta soma yi, ban san me ta
ce ishi ba, sai naji ya ce mata gata, nayi kamar ba
zan karba ba sai naga to ni kuma a wa?
Inna ta ce, a bani waya in ki karba? Ina karbar
wayar na kaita kunnena naji muryar Innata gaba ya
yanke ya fadi nan take na soma yi mata kuka bata
yi min fada ba kamar yanda nayi zaton zata yi
magana ta soma yi min cikin natsuwa da kwanciyar
hankali.
Ban ji dadin yanda ki ke yi wa mijinki ba to da
wanne zai ji? Da halin da yake ciki ko da rashin
lafiyarki da yayi ta fama da ita? Ko da bacin ran

49
abin da ki ke yi mishi? Matar kirki kuwa ai bata
haka, ita takan taimaki mijinta ne a duk lokacin da
tasan yana bukatar taimakonta, ta rufa mishi asiri a
inda tasan yana bukatar rufin asirinta.
In ta san yana cikin tashin hankali kuma ta
kwantar mishi da hankalinshi, sannan in ba ki sani
ba wannan abin da kike yi ba shi kadai ki ke
tozártawa ba har da ni, don kuwa kina kokarin
nunawa wadanda basu sanni ba ne su san yanda
nake tunda ai ita 'ya wakiliya ce ta uwarta.
In kiyi halin kwarai ace kin samu tarbiyaa a
gidan ku in baki yi ba a gane uwarki ba mutuniyar
kirki ba ce kar in sake jin an ce min baki kyauta
ba, in dai ba kina so raina ya baci da ke ba ne, tana
fadin hakan ta kashe wayar.
Sunkuyar da kaina kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login