Showing 24001 words to 27000 words out of 106967 words

Chapter 9 - NOOR ALBI COMPLETE BY MAMUGEE

Unknown   

28 Jun 2024

25448

da ita din aka bada datayi farin ciki Amma Kuma bazata iya auren Wanda ba ita din aka basa aurenba Kamar haramci take kallon kanta a auren shiyasa ta Kori shedan ta danne komai ta fada gskia.

Wasu manya manyan Ajiyar zuciya Kawu saidu ya ringa jerowa a boye Yana Dan goge zufan daya tsatsafo Masa a goshi cikin dubara
Dan duk yagama katsewa da bijrewa auren Sa'adah zatai ta wulaqanta zumuncin da mutunci da Anne ke gani
Shi Turakin ba'a maganarsa sbd yasan ko ahaka Matar da auren ba lallai suna gabansaba.

Anne kuwa wani irin kyakkwan murmushi Mai sanyi tasaki tana kallon Sa'adah din cikin tsananin burgewa da yabawa da hankalinta datai saima taji Sa'adah din tashiga ranta itama Dan Haka ta kalli Sa'adah din a natse tace"

Meyasa zasu sauya Laylah bayan da ita din Dake duk Abu dayane?

Shiru Sa'adah tayi Bata iya cewa komaiba sbd a bayyane yake basai anfadaba ansan Laylah batada gata batada Wanda ya tsaya Mata sai Allah.

Wani murmushin Anne takuma saki kafin ta kalli Kawu saidu tace"

Malam saidu kaji abindayake faruwa.

Cikin takaici da baqin cikin Hali irin na zuriarsu umma Jamila yace"

Tabbas dama Zainab da danginta bazasu taba Bari Laylah tayi rayuwarda kowane 'da mai yanci zaiyiba,
So suke yanda ta taso a wahala ta qare a wahala shiyasa gashinan masifarsu da rashin imaninsu ya haukatar da ita kwakwalwarta Bata cikakkiyar lafiya
Yarinya Takoma Kamar mutum mutumi
To gwara danaji wannan zancen Dan kuwa wallahi ita Zan daurawa aure dukkaninsu sun Dade kwadayi Bai Gama kashesuba Dan nasan manufarsu ta auren
Kema nafasa tafiyar bazan tafiba saina aurar Dake ga duk Wanda nasamu zanga uban dayafini iko akanku cikinsu.

Daga fada da maganganun Kawun Anne tafahimci abindayake faruwa a rayuwar iyalin Mahmoud din take taji wani irin rashin Jin Dadi da tsananin qauna da tausayin Laylah
Yarinyar data taso cikin maraicin uwa da uba duk da Yana Raye,
Tabbas kuwa Kamar yanda Kawun Yafada aure Kam da Laylah Kamar ba fashi saidai Kuma fushinsa na aurarda Sa'adah din daketa kuka Mai tsima Rai bataga DACEWA da adalci a hakan ba Dan kuwa itama Sa'adah ta cancanta rayuwa Mai kyau tunda har tanada kyakkwan zuciya Dan Haka Kai tsaye tace"

Malam saidu kayi hkr karka yanke hukunci cikin fushi akan Sa'adah da Babu ruwanta a wanna al'amarin
Idan har batada wani tsayayyan mijin Zan tafi da ita kodan Yanayi na rayuwar Laylah daba lafiya isashiyaba
Tunda harkace ta mental health Dole zaaje da Wanda tasaba dashi harta warware tafito daga depression din datake ciki kafin ma ayi maganar sanar da ita auren Dake kanta daga
Kuma best solution anan shine tafiya da Sa'adah,
Dan karatu da komai na rayuwar Sa'adah na dauka Inshallah Dan dama tuni yakamata muyi hakan mu dauki 'yayan Mahmoud Dan inganta rayuwarsu da ilimi Mai kyau da tarbiya
Amma tunda yanzu komai yazo da hakan Inshallah idan ka amince Zan daukesu duka su biyun
Laylah Amatsayin Matar Turaki Sa'adah Amatsayin Amanata Inshallah.

Sosai ran Kawu yake quna da Daci sbd har kunyar kansa yaringa ji daya biyewasu Alhaji Atiku Ashe yaudararsa akeyi Dan ya cutatar da 'yar marainiyar 'yar Dan uwansa duk da Sa'adah dinma daya suke agunsa Amma ita tanada gata tako Ina tunda gashi sunso cin amanarsa su tura tasu Yar gurin arzki,
To kuwa zasusan yanda asalin mugunta da yaudara take Dan yanda sukai Masa Haka zai musu bazai fada musu gskiyarba shima shiru zaiyi sai ranarda Allah ya nufa susani.

Sanin daga Laylah din har Sa'adah suna buqatar rayuwar da Anne ke fatar Basu yasa ya amince da tafiya dasu duka biyun tunda koba komai Abba ma wata qasar za'a kaisa dan Haka zamansu cikin zuriar Zainab da basuda Imanin na sanin komai bayan kudi akwai matsala gwara su tafi gurin Annen har Allah yabawa Abban nasu lfy.

Bayan ya amince rokon Anne yayi akan abar zancen auren ayanda yake abar dangin Zainab da sanin da Sa'adah za'a daura sbd karsu cutatar da Laylah.
Momy kuwa dayake da ita za'a tafi qasar daza'akai Abban itama yace abari sai bayan daurin auren zai sanar Mata a sirrance ko zatai hankali tabar rakiyar danginta taje tayi jinyar mijinta tasamu lada ko zunubanta na shekaru sa kakkabe.

Da wannan Ya tafi yabar Sa'adah din wadda Anne keyiwa nasiha cikin hikima da tambayayi akan Laylah datake iya amsa wasu
Wasu Kam bazata iya amsawa sbd basuda dadin saurare Kuma hakan tamkar zubarda mutuncin mahaifiyarta ne zatai.

Anne da kanta da Yan bayanin data samu daga Sa'adah din tasake fahimtar rayuwarda Laylah ta taso aciki Dan Haka ta yanke shawarar hadawa har Laylah din ta riqesu da Sa'adah bazatai saurin sakata a rayuwar aureba sai Laylan tadawo kamar kowane 'da mai walwala da rayuwar yanci,
Bama za'a nuna Mata tanada aurenba a yanzu tana buqatar Abubuwan sauyin rayuwa harma da ilimi duk bayan tadawo cikakkiyar lafiyayyarta kenan idan depression yabarta Dan Haka zata barta Akan riqo ta daukosu kokuma akan biyo Sa'adah datai gidan Aurenta.



Tafiyar Kawu ba jimawa Haj Karima tadawo tareda Laylah dake bayanta kamar Mara lafiya tana tafiya a sulale
Kallon qauna Mai girma Anne ke Mata tana Jero adduar samun tsaftatacciyar zuria daga gareta.

Kasa boye kulawarta tayi tasa aka dauko kyauta ta musamman na kayan Alfarma da aka dinko masu tsadar gske da sunan Amaryar Turakin tabawa Laylah tace"

Gashinan kema gobe ranar daurin auren kiyi ado.

Saida takalli anty Sa'adah kafin tasaka hannu biyu ta karba tana godiya kanta aqasa.

A hanya ba kalar fada da masifar zuwa da ita da Sa'adah tasa sukai Wanda Haj Karima din bataiba kamar ta rufe laylan da duka duk da yau Sa'adah dinma tafi qular da ita Haka suka koma gida masu gyaranta na jiranta ayi za'ai Mata qunshi.

umma Jamila taso karbar kayan ta sauyawa Laylah da wasu Momy ta Hana da cewan Kar ayi abunda zai zubarda mutuncin ko wani kallon daban daga Anne.
Hakan yasa ta hakura ta barwa laylan Amma Kam mugun kallo Babu kalar Wanda ba'a bita dashiba ta sulale tashige daki ta zaunawarta anata hidima da hayaniya sbd gidan acike yake tap da dankin Momy anata bidiri cikinma an hanasu bikin komai da Allah kadai yasan irin shagalin dazasuyi.

Qunshi akaiwa Sa'adah sai bayan magriba aka kammala tasamu ta wanke tayi wanka tayi sallah har lokacin Laylah na daki Bata fitoba dan yau fitowa daki tafi qarfinta a gidan sbd dangin Momy duk Babu Wanda yake qaunar ganin ko giftawarta.

Duk yanda taso janta da zance akan ta sake kasa sakewa Laylah tayi dan itadai matuqar dangin momyn na gidan batada sauran nutsuwa ko sukuni.

Haka Sa'adah ta qyaleta har lokacin kwanciya yayi Laylan tayi bacci tabar Sa'adah na binta da kallon gobe Kamar wannan lokacin ra igiyoyin Turaki uku cif na Aure akan Laylahn,
Wannan shine babbar nasara sbd batada masaniya,
Lokacinda zatasan da aurensa akanta kilama lokaci yaja lokacin zatafi Jin zancen auren Al'amari Mai girma.
##MAMUH#



Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*




09166221261



*_Mamuhgee 14_*
Washe gari gidan da wata irin hidima aka tashi Duk da kusan fiyeda Rabin hidimar a gidan umma Jamila ake yinta Dan ba qaramin Jin auren Nan takeyiba cikin tsakiyar ranta sbd dukkanin burikanta da mafarkantane zasu cika
Duk arzikin dasuke dashi batajin kammaluwar zuciya Kamar yanda take Shirin jinta daga lokacinda ta zama sirika ga AB TURAKI Dan Kamar itace uwa ga momyn kanta bare Sa'adah Dan Haka Bata dauki wannan auren da wasaba ko kadan
Danma anrage musu armashin komai dasu Anne suka nema aure a sirrance kawai batareda anyi hayaniyaba da Allah kadai yasan irin shiri da dukiyar dasuka so bajewa su zubar dan sunsan wannan yanzu ba matsala bane tunda sunsan inda 'yarsu zataje.

Tunda safe Aka fito da Sa'adah tsakar gidan aka Kuma darje koina jikinta da lalle tareda wasu ruwan qamshi kafin aka Bata ruwa tashiga wanka a toilet din dakinta tana fitowa tasaka Laylah tashiga tayo wanka da sauran ruwan lallen.

Koda qarfe goma ta safiya tayi angama shirya Sa'adah din cikin Alfarma ta manyan kayan mutunci dasukaji asalin dukiya Wanda Anne ce ta Aiko dasu da safiyar tace abawa Sa'adah din tasaka
Dan haka taci adonta tana daukan ido tamkar a ace aurentane za'a daura
Ga mamakinsu Umma Jamila da farin cikinsu ba kamar yanda sukaga tana walwala da farin ciki dauke a fuskarta hakan na musu nunin auren dai ta karba hannu bibbiyu itama Dan Haka suka sake sakin jiki Ana hidima.

Momy kuwa sai bin "yarta take da kallo cikin farin ciki tana qarawa
Fuskarta daukeda murmushi Dan tama kasa gane irin kewar 'yarta da zatai idan ta tafi itama gashi gobe da ita din za'a tafi da Abban qasar Germany.

Kamar yanda ake cewa _Rabo sai mai shi_ hakama Matar mutum kabarinsa
Andaura Auren *_MUHAMMAD ABUTURAB TURAKI_* da *_ZAINAB MAHMOUD LAYLAH_* Akan sadaki naira dubu dari cif Wanda Kawu ne ya karba laqadan ba ajalan ba
Hakama babbar Sa'ar da Kawun yasamu akan qudiri da niyarsa na hanawa dangin Zainab sanin komai kamar yanda suka so cin Amana
Kafin su Alhaji Atikun su qaraso yasa aka daura auren batareda anjirasuba Dan dama a masallaci ne Kuma ba wani babban masallaci bane daga shi sai Abdullahi sune dangin Laylah sai Turakin da amintaccen yaronsa A Abdoul sai jamaar Dake masallacin wainda basusan waye angonba bare Amaryar Dan kuwa ko labarin duniya basabi bare su shaida Turakin Dan Haka aure dai andaura yakuma samu jama'a daidai gwargwado dasuka ringa bi da adduar Allah ya sanyawa aure Albarka
Dan Haka Koda su Alhaji Atiku dasu Alhaji Qarami suka iso da manyan motocinsu
Suna fakin Ana Gama shafa addu'ar daurin auren saidai Suka ringa bi da Amin na adduoin da jama'a keyi suna ficewa,

Ransu yayi mummunan baci da hukuncin Kawun na daurin batareda anjirasu ba Amma Turaki agurin sai Basu bayyanarba harda qarin sanin Kar abar Turakin da zaman jira yasa aka daura auren ba Kira badan hakan ba da Kawun sai sun nuna Masa rashin mutunta su day yayi
Dan hakan Kamar tazartawane agaresu.

Washe bakuna Suka hau Yi suna gaggaisawa da Turaki Ana Masa adduar Allah ya sanyawa aure Albarka manyan shaddodinsu sai daukan ido sukeyi Dan kuwa ba laifi kowannensu yanada nasa abun duniyar Amma dogon buri da kwadayi yasa Babu abinda suke gani da hange sai Tarin girma da matsayin Turakin Wanda su connection suke dubawa kafin dukiyar tasa.

Daga gurin daurin auren Kai tsaye gida ya wuce batareda jiran Anne ba wadda zata taho dasu Laylan ya wuce airport ya komawarsa Dan yanada baqin Dake jiransa a Abujan.


Fes Laylah take zaune daki cikin adon Dan lace dinta da aka Bata jiyan saidai batai gangancin fitowaba sbd biki sukeyi gidan sosai har dare tukuna aka Kira Sa'adah din akaita mata nasihu da waazin da sirrikan Kama miji musamman Miji irin nata Wanda aqalla kafin yafara Mata kallon mace ma kila saita kusa hade shekaru nawa a gidan kafin yafara Mata kallon Mata Amma dai sun Yarda da sirrinkansu na kayan gyara dasukai Mata Dan Haka suna jiran kyakkwan labari.

Shiru tayi ta a sauraronsu jikinta duk a mace kukanma takasayi sbd batasan ta Yaya zasuji zancen waye auren yake kansaba
Saidai tasan ko tana hauka bazatai gigin fadar komaiba sbd a yanda tsanar Laylah take cikin jininsu komai zasu iya aikatawa akanta
Shiyasa ta sake roqar Anne da Kawu akan Kar afadawa ko Momy sai lokacinda aka tabbatarda zasu wuce da Abba Germany yanda batada lokaci ko damar sanarwa dangi bare wani mummanan al'amarin ya biyo baya tunda Suma a goben zasu wuce.

Daki Takoma inda ta tararda Laylah tayi sallah tana daga zaune gurin datai sallar
Ta dago ta kalla Sa'adah cikin yanayi na Dan bayyanarda tayata murna tace"

Anty Sa'adah duk ranarda Abba yatashi zaiyi farin cikin ganinki da aure,
Allah ya Sanya alkhairi Anty Sa'adah.

Wani irin murmushi Mai Dan ciwo Sa'adah tasaki tana cewa"

Amin ya Allah qanwata.,
Kuma kinsan kece Zaki ringa yimun dawainiyar kulawa dashi tunda Kinga kin fini iya aikin musamman abinci.

Fararen idanuwanta ta zubawa Anty Sa'adah din cikin jinjina Kai tace"

Eh Zan Miki komaima na aikin gidan Anty Sa'adah Inshallah.

Dafa kanta Sa'adah tayi kawai tana sake murmusawa
Aranta tace"

Tabbas wannan shine bahaguwar sauyin qaddara,
Anmiki aure batareda kinsan kece matarba,
Zakije gidanki da sunan 'yar riqon 'yayarki da kikewa kallon nice Matar,
Nikuma daga aure naqare a zuman riqo gidan Auren qanwa
Wannan badan akwai zumunci ba da dawane suna zasu Kira wannan sauyin lamarin.?.

Gidan umma Jamila ta kwana sbd goben da safe su Momy zasu fara wucewa kafin suma su wuce
Dan Haka duk wani saura ragamar rayuwar Sa'adah umma Jamilan tagama karbarsa daga yau din tunda momyn dai zatabi Abban bayan irin hanatan dasu umma Jamilan da Haj Karima basuyiba har fushi sukaso Yi da ita akan zata kassara sauran rayuwarta gurin jinyar Wanda gurin Cin Amanarta da son zuciyarsa ya hadu da hukuncin dasuke ganin Allah yayimasa akan abinda yayiwa momyn
Amma sbd zamtowarta sirikar Turaki yasa Suka danne fushinsu Dan yanzu Kam zata wuce rainin kowa duk da sunsan har abada sune masu juya momyn sai abinda sukace Mata takeyi.

A Daren Momy tasake jaddadawa Sa'adah komai nata yanzu su umma Jamila ne
Tunda batanan yanzu sune iyaye Kuma gatanta Dan Haka karta ringa komai batareda shawararsu ba
Itadai Sa'adah to kawai take cewa sai alokacin nema tasamu ta rungeme Momy tasaki kukan data keta dannewa aranta tun jiyan ga Kuma kewar mahaifiyarta dazatai dama mahaifin nasu da Babu tabbacin zasu sake haduwa dashi tunda ciwone Babu Wanda yasan yanda Allah zaiyi dashi,
Wani irin nauyi takeji aranta shiyasa ta qanqame momyn tana sake kuka siriri Mai tsananin tsima zuciya Amma su umma Jamila Kam Babu wani Abu dasukaji a zuciyarsu saima rarrashin dasuke Mata akan ai aure bautar Mata ne taje ta Kama uwar mijinta da kyau Dan kuwa mace ce Mai tsananin iko da kaida,
Sam Bata daukan Wasa ko shirme
Komai nata Kai tsaye take yinsa.

Sai datai kuka sosai har idanuwanta sukai nauyi ajikin momyn kafin ta saketa tanajin wasai a zuciyarta
Duk nauyi da radadin datake ji ya sauka gabaki daya tasauke Ajiyar zuciya tareda miqewa ta nufi dakinta tana Jin komai ya Kau akanta sai Kuma fuskantar sabuwar rayuwar Dake jiransu a Gidan riqonsu
Dan kuwa tasan Laylah ma dai kamar riqo ne za'ai Mata Dan maganar auren Anne tace ba yanzu zaaita ba lafiya da ilimi zasu kutsar da ita ciki.
Da wannan tayi adduarta ta kwanta ranta ba wata doguwar damuwa Dan kuwa tasan kyakkyawar rayuwarda mahaifinsu ke musu buri da fata zasuyi ta samun ilimi Mai inganci da zurfi.



Qarfe goma na safe su Momy jirginsu zai tashi Dan Haka tun qarfe Takwas na safe akazo da lafiyayyar mota motar Lexus aka dauki Amarya Laylah da 'yar uwarta kokuma dai ace Amarya Sa'adah da qanwarta zuwa gidan Turakin Dake Nan,
Sosai Anne ta nuna yabawarta tareda karban Amanar yaran da zuciya Mai kyau
Nan akaiwa su umma Jamila yanda suke so wato kyautar girma data kusan sakata zubewa gaban Anne din Haka suka ringa zuba godiya suna qarawa da iyayi kala kala har suka tafi
Dan take daga umma Jamilan har Haj Karima da Matar Alhaji Qarami sukaji buqatar fita gidan Dan sanin yanda wannan kyautar tasu zata jujjuya a hannuwansu Dan kuwa dalolin Amurka ne Anne ta Basu wainda idan suka canjasu ba qananun kudade bane shiyasa ba kunya kowaccensu ta gifta uzurin rashin damar rakiyar Sa'adah din yanzu zadai suzo daga baya Idan sungama sallamar baqin nesa dasukazo biki
Illa kuwa canjin dalilinsu sukeson tsayawa suyi su kammala Kan dukiyar kowa yasan abinda yayi da tasa daga baya sunbi sahun su Sa'adah din Dan dama zuwa gidan Turaki yanzu Dole ne.

Bayan tafiyarsu motar daukar Momy zuwa airport tazo bakowane acikiba sai driver da Kawu a gaba.
Shigowa Kawun yayi Suka zauna Palo daga momyn sai shi sai Anne wadda kai tsaye tafara magana da cewa"

ZAINAB kamar dai yanda Kika sani Allah Yana jarabtan bawansa ne Dan gwada qarfin imaninsa Dan Haka ki dauka komai na rayuwa na samu da rashi dakuma wasu sauyin duk cikin jarabawa da qudirar ubangiji ne,
Kamar yanda kikafi kowa Sani da shaidawa idan rabo ya rantsa tunda ga Laylah Nan Kin gani ishara
Hakane yakuma faruwa auren da aka daura jiya da Laylah aka daurashi sbd itace da haqqin hakan kin sani
Dan Haka idan da ansaka son Rai an daura da Sa'adah to wlh matuqar akwai rabo tsakanin Turaki da Laylah wannan Rabon saiya kashe Sa'adah ta rasu Dan kawai ayi auren a haifosa yazo duniya Dan Haka mudai munyi adalci kamar yanda Sa'adah da kanta tazo tafada Kuma ta roqemu akan hakan sbd hakan dai shine daidai,

Zainab ki godewa Allah daya Baki 'ya kamar Sa'adah wadda wlh samun 'ya kamarta ayanzu Abu ne Mai wuya,
Tayi hankali sosai nakuma yaba Mata iya yabawa shiyasama Zan tafi da ita a hannuna na dauka riqonta da yardar Allah harsai Mahmoud yasamu lafiya Inshallah.

Wani irin kuka Mai sauti da shiga Rai Momy tasaki tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta dake wata irin rawa.

Shiru sukai dukkaninsu sbd Bata damar kokawa Dan sunsan hakan akwai tsananin ciwo
Tana ganin ta aurar da 'ya yanzu Ana fada mata ba wani aure.

Kuka takeyi sosai wanda yasakawa Anne tausayinta tafara Mata nasiha da rarrashi har zuciyar momyn ta Dan Yi sanyi Amma Kam wani nauyi da 'daci sun Riga sun dasa Mata shi Dan Haka share hawayenta kawai tayi batareda ta dago ta kalli Annen ba murya a cikin yanayi na sanyi da 'dacin zuciya tace"

Nagode nakuma bar Sa'adah a hannunku.

Jinjina Kai Anne Tayi tana sake Jin tausayin momyn sbd bayan qunci da baqin ciki Babu abinda yake zagaye da rayuwar momyn tsayin shekaru
Dan Haka tana Mata fatar samun budaddiyar zuciya Nan gaba.

Kasa ganin Sa'adah Momy tayi Dan bazata iya hada idanuwa da Sa'adahn ba Dan Haka Kai tsaye fice ta shige mota suka wuce airport
Suna Isa jirginsu ya daga.

Bayan tafiyar Momy da awa biyu Suma masu jirgin ya daga Wanda yasaka daga Sa'adah har Laylah cikin wani mugun yanayi Dan kuwa Babu Wanda yataba ko barin gari acikinsu bare Hawa jirgi har gwara Sa'adah tana Dan yawan tafiya wasu lokutan tareda umma Jamila kokuma Haj Karima Amma ba Wai tafiyar nesaba.

Tafiyar awanni sukai sai gasu a garin Abuja inda manyan Mercedes beymach ke jiran saukarsu Aka daukesu zuwa *_AB TURAKI RES_*.
##MAMUH#



*_SAKINA VENDABLES_* 🔥🔥
*_Ina ma'abota son qamshi da gyara? Ina masoya qamshi dasuka San darajar qamshi da gyara

22, August 2025
Haura'u

Interested

22, August 2025
Haura'u

Interested

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login