Showing 105001 words to 106967 words out of 106967 words

Chapter 36 - NOOR ALBI COMPLETE BY MAMUGEE

Unknown   

28 Jun 2024

25462

yakeyi Sbd ba qaramin kafa Mata hakoran tayiba suka shiga qafar sosai.

Agogon Kan gefen gadonta ta fizgo da qarfi tareda bugawa Na'iman a Kai take azaba tasakata sakin kafar tana somewa agurin.

A haukace ta fito daga gidan ko gani batayi sbd jinin da kafarta ke fitarwa Sosai ga tashin hankalin da siddika ta sakata a haukace ta fada motarta tana tayarwa motar Jamian tsaro tsayawa gaban motarta Dake kofar gidan.

Wata motarce ta Parker siddika da A Abdoul Suka fito sai alokacin gaban Zinat din yayi mummunan faduwa dan da farko Bata tsororaba tunda tasan Babu wani dalilin zuwan hukuma gurinta Amma ganin siddika tareda A Abdoul ya tabbatar Mata da komai.

Reverse tafara Yi da motarta cikin tsananin gudu sbd batada damar yin gaba tunda agabanta suke tanayin Bata Suka bita da motacinsu a guje

TURAKI daya iso gidan Tuni siddika harta janyo Na'iman Dake sume tamkar Babu Rai tareda ita ya qaraso ya dauketa gabaki daya yakai mota tareda rufewa yashiga yaja motar yabar gurin.

Sosai Zinat ke gudu da motarta cikin reverse sbd tasamu ta tserewa jamian ta hau titi,

Kwana zatasha da mugun speed
Tayoyin Suka qwace Mata motar tayi cikin wata sabuwar transformer Dake street din take kuwa transformern tafara yayyafin wuta suna zuba Kan motar
Hankali tashe tafara kokarin bude motar dukkanin jikinta na rawa tana ihun a taimaketa Azo abude Mata ta fita Amma kowa yakasa qarasawa sbd wuta tafara cin gaban motar tata,

Tana gani tafara sakin ihu tana bubbuga glass din motar,

Dole Jamian tsaron aka fara kokarin cetonta Amma Sam wutar Taki Bari kowa ya matsa sbd transformer na barin wuta motarma naci Dan Haka kowa ma guduwa yafarayi da motarsa Daga gurin ga ihunta da bubbuga glass dinta anaji Ana gani tana konewa da ranta cikin tsananin azaba
Tun Anajin ihunta har aka dainaji Haka Wutar ta cinyeta qurmus kafin akashe a fiddota.


Asibiti aka Kai Ms Na'ima itama sbd yin nasu binciken asalin akan qwaqwalwarta.

Anne da idonta ta ringa tsiyayarwa da Na'ima hawaye sbd tana cikin mawuyacin hali.

Laylah ma kusan sai dataiwa mum din tata kuka sbd tausayi,

Ga Abbanta daya taba hankalinsa uku akansu,
Rabi na Kan baby, rabi nakan mum rabi Kuma Yana kanta sbd itama har lokacin takasa dawowa daidai duk da ta sakawa kanta tawakkali yanzu fatarta abba da Momy su samu lafiya,
Har gwara Momy ta farfado sbd wutarta batai yawan ta abbanba.


A Abdoul ne ya tsaya aka rufe case din Zinat da Na'iman akan rasuwarsu Sa'adah tunnda Zinat din tabisu inda ta aikasu din.

Bincike Mai kyau tsafta ya tabbatarda Ms Na'ima qwaqwalwarta tagama juyewa Amma Basu cire ran dawowarta daidaiba Dan Haka tana Jin sauki aka sallamota gida.

A sasshen Anne take itama wannan karon dakin Sa'adah yakoma nata siddika itace Mai kula da komai nata sbd yanzu komai nata datakeyi kallo daya zakai Mata kasan tana matsalar qwaqwalwa.

Tsananin tausayinta yasa kaunarta Mai girma wanzuwa a zukatansu,

Anne har cikin ranta take Jin Na'iman sbd ba qaramar qaddarar jarabawa bace mace Mai girma kyakkwa ace kanta a juye yakeba,

Siddika Takoma tamkar uwar data haifeta takejin Na'iman sbd duk da tasamu matsalar dukkaninsu suna cikin gata da kwanciyar hankali da kauna daga kowa.

Yanayin matsalar ta me Na'iman sai tazo Mata da qaunar Laylah Babu Wanda takeson zama dashi kokuma yabata maganinta Tasha ba gardama kaman Laylan.
Shi Turaki qarfi da yaji Abbah take cemasa kaman yanda taji Laylan na fada.

An sallamo Baby Sa'adah kaman yanda ta roka Abban ya sakawa babyn Dan haka sai alokacin farin ciki da walwalar gidan tadawo
Abbah ya fidda asalin tsananin kaunar dayakewa 'yarsa danma baya kwana guri daya dasu.

Dazai koma Babu yanda baiyi da laylanba su kebe taqi sbd Anne da kamar ta saka Mata ido sbd gyaran da ake Mata Wanda Bata samuba na aure
Dan Haka Haka ya lallaba ya koma yaso tafiya da Na'ima sbd asibiti da za'a kaita Amma taqi yarda ta matsa koina idan bada Laylah da baby Sa'adah za'ai tafiyarba
Dole ya kyaleta kafin Laylan ta tashi dawowa saisu dawo tare.

Momy tana samun sauki sosai sbd kullum Laylan na tareda ita a asibitin danma Anne ta Hanata kwana asibitin sbd Kar a daukowa baby Sa'adah sanyi shiyasa iyakacinta wuni kullum tadawo.

Momy tunda tasan Sa'adah ta tafi tabarta Babu Wanda yayi tunanin zatai dangana da karfin zuciya irin Wanda tayi saima kurawa baby Sa'adah Ido datakeyi Koda yaushe tana kallonta amatsayin Sa'adahnta datana jinjira.

Baby Sa'adah nada wata uku Suka Gama zamansu a Nigeria suka tattara suka koma Amma Saida Suka fara zuwa kaduna itama taje tayiwa iyayen Ruky gaisawa bayan su Turaki sunje gurinsu tun farkon al'amarin sun musu baya da duka sauran abun daya kama.

Itama alkhairi tayiwa iyayen Ruky din sosai kafin tabaro.

Sbd samun sassauncin komai na dawainiyar data hau kanta Momy da abbanta da haryanxu baya komai bayan Dan numfashin da shima sai can daqyar yake fita anan wata babbar asibiti Atlanta akai kwantar dasu.

Ms Na'ima ma kwanansu hudu da zuwa yatafi da ita nata asibitin itama sukai admitting dinta akan za'a dorata Kan treatment data fara dawowa daidai za'a sallameta sai aqarasa treatment din a gida.

Cindy tunda Suka dawo itada sofia aka Rasa waye yafi tsananin kaunar baby Sa'adah wadda yanzu kamanninta da Abbanta yake fita sosai sbd farace tas ta dauko farar fatarsa da idanuwansa harma da hancinsa.

Tunda suka dawo sai yanzu tasamu cikakkiyar nutsuwar kanta data gidan sbd yanzu itace Matar gidan.

Masu aikin gidan sunanan kaman yanda suke ada Cindy da Siddika dan Haka yanzu gidan komai anatse cikin kwanciyar hankali musamman batada wata damuwa akansu Momy sbd asibitin akusa take koyaushe ta tashi zuwa takeyi gurin momyn wadda zuwa yanza tana magana saidai komar koyaushe Bata iya kallon Laylan Sosai Amma wannan karon sbd kunyar ne da fargabar fuskar Sa'adahnta datake gani akan fuskar Laylah badan komaiba sai Dan koyaushe burin Sa'adah inganta rayuwar Laylah ne gashinan ta tafi tabarsu daga ita har Laylan basuda kowa yanzu sai juna.

Ita baby Sa'adah kuwa lokaci daya Allah ya dauki tsananin kaunarta Mai qarfi ya jefa a zuciyar momyn saidai Bata iya nunawa sosai sbd gudun zaqewa tunda tasan irin yanda suka taso da Laylan,
Ga Yan uwanta ko a waya Babu Wanda yataba Kira yaji yanayinta shikenan dai ta tabbata batada kowa sai Laylahn sai kuwa Mahmoud idan Allah ya tada kafadunsa.



********Wanka ta fito daureda qaramin towel da Bai Gama rufetaba
Duk santala santalan cinyoyinta a fili sai daukan ido sbd tsananin haske da hutun da fatarta ke samu na kwanciyar hankali.

Zama take kokarin Yi Kan kujera taji an rungumota ta baya
Tayi saurin waiwayowa tana kallonsa tace"

Abbah yaushe kadawo?

Qamshin shower gel din datayi wanka dashi yafara shaqa Yana bin wuyanta da wani qananun kiss murya can qasa yace"

Nayi kewan Noor,tana Ina?

Janyewa tayi daga jikinsa tana cewa"

Noor kayi kewa kawai??

Sake janyota jikin NASA yayi Yana rungumewa ya kalli Dan bakinta dayafi komai yimasa dadin Sha Yana Kai bakinsa Kai yace"

Nayi kewan babyn Abbahh ma fiyeda komai,
Daban dawo yauba bazan iya gane komaiba Kuma acan.

Bakinta ya hade da nasa Yana kissing cikin tsananin kewarta data kusa wargaza nutsuwarsa a Sweden...

Wuyansa ta sargafo tana sake basa damar kissing dinta da Kyau...

Hannu yasa ya fincike towel dinta ya jefar tareda cirata sama ya Dora Kan madubin Dake gabansu kayan dake kusan duka Suka wargazo qasa yasa hannuwa Yana shafa wuyanta zuwa kirjinta wasu jijiyan control dinsa suna katsewa ya fara lasarta tana kissing koina,

Rigar jikinsa ta balle wa botira atareda fincikewa Suka Yar tafara binsa da wasu shegun kiss a kirji
Take ya dauketa suka koma gado Yana bin ko'ina jikinta da kiss Yana gigita qwanyar kanta.

Daqyar ya saurara Mata a ranar ta iya saukowa sukai Abincin breakfast sbd idan yana gari da ita ake aikin abinci.

Kasancewar idan yana gari Babu ruwansu soyayya suke zubawa kaman su hadiye juna yasa matuqar yananan su Cindy iyakacinsu kitchen sai dakinsu kokuma sakin baby Sa'adah gurin rainonta.

Momy data gama warkewa sumul aka sallamota sai aka Kama Mata apartment Mai kyau ita kadai aka zuba Mata komai na Jin Dadi harda Mai aikinta Dan Haka kullum su siddika suka samu gurin zuwa
Suna Gama ayyukansu zasu dauka baby Sa'adah akaita gurin Momy,

Hankalin momyn ya kwanta sosai saidai haryanxu wnnan rashin maganar tata sosai yananan Amma Kuma ko a kallo Laylah tasan momyn yanzu itace momyn da Anty Sa'adah take Mata fatar samu sbd soyayyarta data 'yarta baya boyuwa agurin momyn,
Ga Turaki shima Yana Shiga time to time Yana dubata,

Shi Dana A Abdoul tuni takoma tamkar Mahaifiyarsa dan yanzu gidan yakecin abinci shima kusan koyaushe cikin kyautata Mata yake.


Baby Sa'adah nada shekara daya da wata goma Sha daya takuma haihuwar wannan karonma mace ta Haifa Kai tsaye Abban ya saka Mata Na'ima sukuma suna Kiranta da princess sbd shine sunan da Ms Na'ima take kiranta dashi tunda aka Kai Mata ita har asibitin taganta.

Anne tunda tazo haihuwar princess Bata komaba sbd itama zata huta sosai din kafin takoma Dan Haka a gidan Momy take zaune itama siddika tunda Anne tazo tadawo gidan sbd dama Baby Sa'adah tunda aka yayeta dama tana gurin Momy sai tayi kukan dadynta wani lokacin sai akaita
Shima matuqar yaje yadawo office indai tana gidan Momy babu ruwansa saiya biya.



Saida abbanta yayi kusan shekara uku Yana jinyar wutarsa kafin Allah yasa ya warke saidai wutar tabar Masa tabon Wanda asibiti bazasu iya fitar Masa dasuba duka Dan Haka siddika Dole ta tattaro ta dawo gida baby Sa'adah kawai aka baro can wadda Abba yakejinta shima tsakiyar ransa sbd ta hada komai da kowa..

Itace jikarsa ta farko daya samu,
Itace 'yar laylansa dayaketa buri da fatar ganin jinin laylansa,
Itace 'yar Amininsa Kuma Dayazama dan uwansa tamkar na jini,
Itace Sa'adahnsa daya rasa Kuma Dan Haka tako Ina kaunarta yake shima.

Anne dama takoma Nigeria duk da ba jimawa zatayi ta dawoba.


****Zaune take tana cin pizza da akayo Mata order hankalinta kwance sbd yanda yanzu kullum sai tacita takejin Dadi taji anyi sallama da wata kamilalliyar murya a natse.

Tabbatarda Mai muryar yasata dagowa da sauri ta kalli kofar taga mum dintace tsaye cikin maroon abaya Mai tsananin tsadar gaske fuskarta fresh tana sakar Mata murmushi

Wani dadine ya mamayeta ta aje pizzar hannunta tareda tasowa da gudu... Turaki Dake riqe da hannun Ms Na'ima yayi saurin saki ya riqe Laylan tareda dakatar da ita da Ido ya kalli cikin kusan wata biyar dake gabanta a natse yace"

Ki kula.

Zare hannunta tayi tareda qarasawa ta rungume Ms Na'ima tana cewa"

Mum Allah yasa kin dawo kenan
I'm so happy mum.

Princess dake fitowa daki riqewa abun wasarta na Sofia the first tana ganin Ms Na'ima ta jefar tana qarasawa gurinta da gudu tana cewa"

Mum,mum,mum." Dayake duk hakan suke Kiranta Suma yanda sukaji mammy dinsu na cewa.

Ms Na'ima ganin yanda Laylah tagama cika gidan Turaki da yara yasa jikinta yin sanyi saidai Kuma har abada batada bakin godewa Turaki da kaunar daya nuna gareta na tsayawa tsayin daka lafiyarta ta dawo gareta gashi yanzu tasamu cikakkiyar rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwa da aminci cikin daular datake fatan dawwama acikin,
Ga Arziki yaqari sosai Dan Haka Bata wani tsaya cutatar da kanta da noke nokeba ta dara tata sabuwar rayuwar tafara komawa Yar gayunya sbd ganin Laylah gabaki daya tagama lalata Turaki tako Ina da iya shagar lalacewa da birkita qwaqwalwarsa,

Tasan tabbas wani abun Bata iyaba Kuma Bata saniba akansa tunda Laylan tafita saninsa ayanzu Dan Haka ba cutar da Kai ta ringa nutsuwa tana Dan fahimatar wasu abubuwan kafin takoma nata gidan sbd ba guri daya zasu zaunaba sbd gujewa Sharrin shedan Dana kishi Dan yasan Laylah nada zafin kishi yanzu ne zata hade fuska Bai sake ganin dariyarta duk yabi ya rude ya rasa gane kansa saita sauko.
#MAMUH#☑️
ZAFAFABIYAR.

ALHAMDLLH YA ALLAH🙏

ALLAH YA YAFE MANA KURAKUREN CIKI AMIN,

IDAN NAYI MANTUWA KO KUSKUREN WANI ABUN ACIKI AMUN AFUWA AJIZANCI NE IRIN NA DAN ADAM,
ALLAH YA YAFEMANA GABAKI DAYA.

INA BAKU HAKURI SBD WASU ZASU FADA KAMAN YANDA SUKA SABA CEWA YAQARE DA WURI
DAN HAKA KUYI HKR LABARIN NE YAKE AHAKA.

ALLAH YA SADAMU A LITTAFI NA GABA.
AMIN.

22, August 2025
Haura'u

Interested

22, August 2025
Haura'u

Interested

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login