Showing 99001 words to 102000 words out of 106967 words

Chapter 34 - NOOR ALBI COMPLETE BY MAMUGEE

Unknown   

28 Jun 2024

25461

ta zauna bakin gado tana kunna wayarta da Abbahh ya koya Mata kashewa duk zata kwanta daga bayan Nan sbd Kar aringa damunta alokacinda take bacci ga yanayinta Kuma.

Tana kunnawa Kiran Anne yafara shigowa ta gyara zama suna wayar harda tambayar jikin mum Na'ima tayi Anne tace taji sauki sosai ba laifi.

Suna gamawa Abbahh na Kira ta kalli wayar zuciyarta na samun nutsuwar ganin kiransa ta daga wayar tareda komawa ta kwanta jikin gadon tana amsa sunanta na asali daya kirata dashi.

Bacci Takoma bayan Gama wayarta da Abban Bata farkaba sai guraren 11 lokacin Ruky tagama Mata komai na abubuwan datasan tana breakfast dasu
Anty Sa'adah kuwa sai kulawa takeyi da komai data shafi Laylahn sbd har cikin ranta Jin so da kaunar cikin take itama harma takejin inama Allah zai nuna Mata ranarda zata raini nata cikin harma ta Haifa idan tanada rabo.

Momy kuwa da wuri ta shirya ta fice daga gidan sbd ganin kamar yarta takoma itace naiwar Laylah yanzu tunda suna zaune gidan mijinta,
Hakan ke son saka 'daci cikin ranta Dan Haka ta shirya ta fita Bata dawo gidanba sai magriba sbd qarin Bata kaunar Yan uwanta ko daya yazo gidan a yanzu,
Duk sukazo sukaga Laylah da ciki zasu tada hayaniya da Rigima ne kawai shiyasa duk qarin fitarta sbd idan batanan karsu zo.

Washe gari ma Haka ta wuni gurin harkokinta a cikin gari sai dare tadawo.

Itadai Laylah koyaushe tana tareda abbanta da anty Sa'adah dasuke debe Mata kewa da Bata tsananin kulawa da kauna,

Wata tsananin shaquwa da sabuwar kauna suke nuna Laylan da cikinta Wanda wasu lokutan sai taji jikinta na yin sanyi har hawaye takeyi idan taga yanda anty Sa'adah ke Mata ta.

Ta bangaren abbanta koyaushe sake tunatar da ita yakeyi karta taba riqe abinda Momy ke Mata a ranta sbd koma menene itace ta zauna dasu alokacinda suke basuda kowa Kuma tunda Bata taba cutatar da itaba shi ko ahakan Yana godiya.

Da wannan take sake girmama momyn duk da duk wani girma da kaunar momyn datake sbd itace ta Haifa Anty Sa'adah,wadda takewa kallon uwa awani bangaren.


******Ms Na'ima taji sauki sosai tadawo hayyacinta hakan yasa Zinat ta sakata taqi Kara ko kwana asibitin sbd Kar a zurfafa bincike akanta agano batada hankali cikakke
Dan Haka Kai tsaye Ms Na'iman ta tattara ta tafiyarta gidan Haj zinat batareda ta sanarda Turakin ba Saida Dr faruk yakirasa ya sanar dashi cewan ta tafiyanta.

Cikin nutsuwa Turakin yace"

Ba damuwa tunda tasamu lafiya,
Kawai dai ayi gaggawar bincika syringe din da aka samu gurin bincika sanadin gobarar sbd ba daya bane Wanda aka samu kusan gudan biyar ne,
Inason sani menene takeyi da alluran koma wane irine.

Inshallah Allah sir Turaki Muna Kan bincikawa cikin qanqanin lokaci zamu Gama dubawa,

Sai maganar results din Ms Sa'adah shima ya fito tana tareda _Leukemia_ Sir and tayi nisa.....

Shiru Turaki yayi cikin wani yanayi Mai girma daya taba zuciyarsa..

Mahmoud da momyn Sa'adah din yafara Jin sun tsaya Masa arai kafin A Abdoul dinsa daya Riga yasan maganar Dake tsakaninsu Bayan yasan A Abdoul dinsa Bai taba soyayya da kowace mace ba sai akan Sa'adahn...

Gangaro da tunaninsa yayi akan tasa Matar da batada kowane makusanci bayan Sa'adahn take yaji zuciyarsa ta karye da labarin.

Cikin nutsuwa ya bude Baki yace"

Menene nisanta??

Ajiyar zuciya Dr faruk ya sauke cikin sanyin jiki shima yace"

Tayi nisa sosai sbd inaga ta Jima tana samun symptoms dinta Amma Bata saniba inaga kokuma tasani Bata tana zuwa ganin likita ba.

Dr faruk ka shirya Mata ganin likitan cancer dayakeda qwarewa da sani sosai akowace qasar yake cikin gaggawa zai duba ta.

Inshallah Allah Turaki zanfara aikin hakan ayau dinnan.

Yana Gama waya da Dr faruk kasa sanar da kowa yayi sbd Babu Wanda abun bazai tababa acikin mutanen Nan Dan Haka yasa A Abdoul yayi masu booking tickets na tafiya.


Na'ima yafara Kira dan jinta itama Amma taqi daga wayar yana kashewa massage dinta yashigo wayarsa cewar zata zauna gurin Zinat kafin agyara Mata sashenta Dan Haka yabarta tasamu nutsuwa anan din kafin kwana biyu.

Yana gama karanta massage din ya kashe wayarsa ya aje gefe Yana sake shiga nazarin rayuwar Sa'adah da Allah yabawa kyakkawar zuciya Ashe tanada tata qaddarar agabanta itama.


Haj Zinat data turawa Turaki massage din ta ajiye wayar Na'iman a gafe tareda kallon siddika Data dauko Mata wayar daga daki Na'ima na wanka tace"

Tafiya zamuyi gobe tunda safen Kuma goben zamu dawo karki kuskura Koda Wasa wani yasan munyi tafiya munbar garin Abuja a goben.

Kallonta siddika tayi cikin tsoron fadar abinda ke bakinta tace"

Akwai yiyuwar Anne zata iya zuwa Nan din dubata idan tazo mezance Mata?

Wani mugun kallo Haj Zinat tayi kafin tace"

Kice munje asibiti kokuma kice munje siyan kayan sawar Na'iman tunda kusan komai ya kone.

Gyada Kai siddika tayi tareda juyawa tabar gurin Takoma daki.

Waya Haj Zinat ta dauka ta lalubo wata number tasaka Kira
Ana dauka tace"

Komai ya zama ready kufara wucewa yau zamu sameku goben acan.

Kashe wayar tayi tareda miqewa daukeda wayarta data Na'ima ta nufi dakinda Na'iman take tana shiga ta aje Mata tata wayar ta fito.

Bata fadawa Na'iman komaiba Saida tasa aka siya musu tickets din tafiya da daddare sun fara cin abincin Na'iman na zaune tarasa meyake Mata Dadi acikin Rai,
Bata cikin nutsuwa zuciya data ruhi
Qunci da damuwa takeji sosai wanda ta rasa inda zata saka ranta taji sanyi,

Zinat ta kalleta cikin son sake cakuda Mata qwaqwalwa ta gyara zama ta kalleta dakyau cikin yanayi na bayyanarda damuwa tace"

Na'ima ki nutsu kiji sauran gaskiyar da aka rufemu baibai akanta sbd yaudara da son zuciya irin na Anne Dan wlh itace taci mafi girman Amana a lamarin..

Ba cikin shege neba a jikin Laylah,
Ciki dai Dan halak ne,
Dan cin Amana, Dan zamba cikin aminci,
Laylah itace asalin matar Ba Sa'adah ba.......

Abincin Dake bakin Ms Na'ima ne ya dawo Mata da qarfi tana sakin wani tari Mai qarfin gaske ta dauki cup da sauri zata Sha ruwa Haj Zinat ta jefa Mata wata qaramar qwaya aciki batareda ta Ankara ba takai ruwan bakinta Tasha tanajin zuciyarta na balbalowa da wuta....

Wurgi tayi da cup na glass yafashe ta kalli zinat da idanuwanta dake neman sauyawa tace"

Wlh bazai yiyuba,

Laylan ce Matar Turakin?

Kishiya ta ake nufin na Raina?

Ba gaskia bane sbd yamata ciki ne zasu boye mutuncinsa suce ita matarsace Amma qaryane,
Bazai yiyuba tana matarsa shekaru masu tsayi bansaniba......

Riqota Zinat tayi Dan qarasa yamutsa kanta da qwayar data Bata tace"

Gskiyar kenan Na'ima,
Laylah matar Turaki ce Kuma uwar yayansa tunda gatanan da cikinsa a jikinta,

Abin haushi da baqin ciki ke yanzu ba lallai ki haihuba tunda qwayoyin ciwonki sunada qarfi zasu iya lalata qwayoyin haihuwarki Dan Haka bazaki taba yardaba da wannan Cin Amanar da yaudarar da akai Mana....

Jikin Na'iman har wani irin rawa yakeyi idonta yayi jajir tafara bubbuga kanta tana maimaita kalmar"

Bazan yardaba,
Cin Amanata sukayi,
Yaudarata sukayi,
Saina kashe Laylah da cikinta sunbar duniya...
Sai sun bar duniya..

Miqewa tayi tana tareda ture duka kayan abincin Dake Kan dining din tana bin hanya ko gani Sosai batayi sbd masifar Dake ci acikin jikinta.

Wani murmushin cika aiki Zinat tasaki tana kamota ta riqe da qarfi tana cewa"

Ki nutsu Zinat zamu ladabtar da Laylah Amma ba yanzuba sbd Bata gari tana gidansu Turakin ya aikata Dan Haka gobe tunda safe zamu tafi da hannuwanmu zamu dasa Mata tarihi kaman yanda ta dasa Mana.

Qwacewa Na'iman tayi tana cewa"

Bazan iya Bari sai gobe ba wlh ayau saina tafadamin da bakinta yanda ta auri mijina taje tazauna a gidana harta damu wannan cikin.....

Ubantama yau saiya amsamin tambayoyina kafin na qarasa gurgunta rayuwarsa...

Yanda taringa fizgewa tana hauka tuburan sbd qarfin qwayar data Bata yasa Dole tayi Mata allurar wadda zata saukar da ita kafin gobe da safe ta saketa tayi Mata abinda takeso din.

Anan palon tabarta yashe takira siddika tace ta shigar da ita daki.

Cikin kayan Na'iman da aka kawo ta qarasa ta bude ta kwashe duk wasu dukiyar manyan sarkokin gold dinta dasu diamond ta zuba Jakarta ta fice dasu daga Gidan.

Daqyar siddika ta iya Jan Ms Na'ima tana hawayen azaba da baqin cikin halinda suke ciki sbd tabbas tasan tana gamawa da Ms Na'ima Dole zata kawar da ita tunda tasan sirrin komai,

Ita bazata iya gudu ba tunda Haj Zinat din taje har garinsu ta daukota Dan tayiwa Na'ima aiki takuma ringa daukan Mata rahoton komai dakomai na rayuwar Ms Na'iman musamman akan yanda take Bata qwayoyin dasuka juyar Mata da qwaqwalwa tsawon shekarun tana juyata sai abinda tace tayi,

Dan Haka tasan Kota gudu Bata tsiraba saima sake bawa Haj Zinat din damar kawar da ita Dan Haka bazata gudu ba zata ceto kanta da Ms Na'ima ko zasu samu rayuwar kwanciyar hankali da 'yanci agaba.

Tana Kai Ms Na'ima daki ta fito ta nufi dakin Haj Zinat dayake tasan inda take aje takardun shaidar haukar Na'ima dakuma takardun maganin datake Bata harma Dana allurar da wani likita yake batasu
Tun farko shinema yake yiwa Zinat aikin komai na juyar da qwaqwalwan Ms Na'ima.

Dauke takardun tayi duka ta fita da sauri..

Harta Kai kofar dakinta ta tuna da Babu ranarda Zinat Bata duba takardun Kuma ta tabbarda dasu zata tafi duk inda zasu goben
Dan Haka da sauri taje ta debo wasu takardun makarantar 'dan Haj Zinat din data gani a Palo taje ta Sanya Mata ta fito da sauri.

Daukan takardun tayi ta daure cikin leda kafin takaisu can baya cikin sharar kitchen ta Sanya tadawo ciki jikinta na zuciyarta suna rawa tana fatan kada wannan abun datai ya kashesu gabaki daya itada Ms Na'iman agurin zinat,
Dan Haka har dare yayi Haj Zinat tadawo hankalinta ba'a kwance yakeba zuciyarta bugawa takeyi da qarfi matse take da goben tayi su tafi itama ta tafi gidan AB TURAKI RES takaiwa Anne takardun sbd tasan bazata iya samun ganin Turakin Kai tsayeba ta isar Masa takardun.

Har akai sallar asuba siddika na zaune tana yawon bandaki sbd tsoro da jiran wani tashin hankali daga Zinat Amma shiru
Dan haka tana Gama sallah ko wanka batayiba ta fito tana aikin kaida kawo na aiki a kitchen ko zataji wani zancen Amma shiru duk da hakan hankalinta har lokacin a matuqar tashe yake.

Qarfe goma Suka fito Haj Zinat shiye tsaf cikin wani arnen tsadadden lace brown sai handbag dinta da takarman Dior sai qamshi take zubawa.

Ms Na'ima kuwa doguwar Rigar Dubai ce ajikinta ta wani tsaddaden material blue fuskarta ta fada sosai a dare daya sbd qwar da aka Bata Mai tsananin karfice wadda har lokacin ajikinta Bai saketaba saima tsananin juyar Mata da qwaqwalwa datake qara Yi Amma allurar da akai Mata yasa Bata iya komai sai jikinta a sake sake take ba qwari sai sun Isa zata banka Mata wata qwayar abun ya tashi.

Dan Haka ko breakfast Basu tsaya sunyiba Suka fice zuwa airport.

Suna fita da awa daya siddika ta Isa dakin Haj Zinat ta hau bincike jikinta na wata irin rawar tsoro da tashin hankali ta ringa watsi da Kaya tana bincike dakin.

Daqyar tagano jakar data fita da ita jiyan da gwalagwalan Ms Na'ima tadawo da ita Kila ba'a siya yanda takeso ba Dan Haka Bata tsaya Bata lokaciba ta dauke jakar ta fito ta nufi kitchen ta zazzage kwandon sharar ta dauki ledar takardun ta fito sanyeda doguwar Riga da qaramar hijabi ko ganin gabanta batayi Sosai
Har saidata ga anason Gane Bata hayyacinta tukuna tayi kokarin saita kanta ta dauka drp din mota zuwa Gidan TURAKI.




*******Cikin kwanakin datayi a gidan tasamu kwanciyar hankali da nutsuwa
Hakama anty Sa'adah zuwan laylan yasa tasamu kanta cikin wata sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwa sbd zuwanta yasa shaquwa da sabuwar kauna ta qaru tsakaninta da Abbansu sbd dama ba wani shaquwa tsakaninsu Sosai.

Momy gabaki daya tun zuwan Laylah ta Rasa walwalarta ta zaman gidan
Koyaushe Bata zama gida,
Abba baida magana saita Laylah da cikinta,
Ga yarta da abban sun koma tamkar wasu bayin Laylan hidimarta kawai suka sani,

Ta bangare daya ma Sa'adahn batada lfya tana fama da yawan habon jini koyaushe Amma taqi tsayawa suje asibiti sbd idan adacan zafi ne yanzu suna rayuwar AC koina tayaya za'ace zafi ne tafi kyautata zaton Dan kanoma ne sbd idan yayiwa mutum tsanani yakan saka hakan wani lokaci...

Ita babbar damuwarta kada ya taba lafiyar Mara Kota mahaifar Sa'adah
Ganin yanda takewa Laylah ta tabbatarda tanajin tsananin kewar inama zatai auren ta Haifa nata 'yayan.

Yau tunda safe ta shirya itada Sa'adah Suka nufi asibiti sbd Abba da kansa yace Sa'adahn taje asibiti.

Daga Laylah sai Ruky da hadiza Dake aiki ne a gidan ko Abban bayanan ya fita tareda Abdullahi zuwa tsohon gidansa da ake gini.

Zaune take Palo sanyeda doguwar Riga Mai qaramin hannu sai farar hula akanta
Fuskarta tayi fresh sbd hutu.

Furar dataji Madara d fresh nono takesha cikin cup tana duba wayarta dataketa Kiran Abbahh Bata shiga,

Yau tun safe take kiransa takasa samu..

Hankalinta baya Kan tv Dake aiki Yana Kan wayar hannunta Dan Haka ko dataji sallama bata dagoba sai data aje wayarta Dake hannunta gefe tareda kallon kofar tunaninta su Anty Sa'adah ne suka dawo.

Cup din hannunta ne ya subuce Mata lokaci daya tana sauke kafarta data miqe daga Kan table dake gabanta gabanta yayi mummunan faduwa ta miqe tsaye tana kallon umma Jamila dake gaba Haj Karima na biyo bayanta sai Anty fatima.

Cak umma Jamila ta tsaya tana kallon fuskarta da kyau sbd kwanakin tana fama da Ido ta waiwayo ta kalli Haj Karima Dake qarasowa ciki idonta akan cikin Laylan itakuma tace"

Haj karima wannan Kuma dai gata Kamar 'yar Mahmoud da kishiyar zainab kokuwa idon ne?

Anty Fatima datake qanwarsu tace"

LAYLAH?????

Qarasowa suka fara Yi umma Jamila na sake qure kallonta akan Laylan da mugun mamaki tace"

Harda tsarabar cikinta tadawowa Mahmoud gashinan ajikinta.

Wata muguwar dariya Haj Karima tasaki tana nufar kujera ta zauna tace"

Allah sarki,
Shikuwa Mahmoud ahaka zai qare daga haihuwar 'yar da ba'a tabbatarda aurensa da uwartaba sai samun jikan wata hanyar.

Hannu umma Jamila takai ta janyeta da qarfi ta watsar gefe tareda zaunawa tana cewa"

Can ya matse musu idan shege dari zata Haifa su Suka sani,
Fata dai wlh baza'a haifawa zainab shege acikin gidaba,
tunda bin baza ta zaba taj ta bisu can kowama ya huta.

Tashi tayi daga jefar da ita da umma Jamilan tayi tareda Dan sauke Kai cikin girmamawa ta gaidasu Amma Babu Wanda ya kalleta bare ya tanka
Ta juya tabar gurin jiki Amace ta shige daki.

Tana shiga su Momy na shigowa
Tun a haraba da Momy taga motar umma Jamila tasan suna gidan hankalinta yaso tashi Amma Kuma ta Dake tunda ba ruwanta da shaanin Laylahn ita yanzu ta yarta da aka dinga diban jinin Dan gwaje gwaje take.
##MAMUH#



*_Mamuhgee 55_*
Momy na shigowa palon ta kallo daya tayiwa fuskokinsu ta dauke Kai tana qarasowa ta zauna tareda bude Baki a sanyaye ta gaidasu sbd ganin yanda umma Jamila ke Mata kallon datasan maganar da za'a fada Mata bamai Dadi bace.

Ita kanta Sa'adah jikinta mutuwa ya sakeyi akan na zazzabin data dawo dashi na dibar jininta da aka ringa Yi dakuma kaida kawo,
Daqyar ta iya driving dinsu Suka dawo gidan.

Cikin sanyin murya ta gaidasu ta juya ta nufi dakinta ta shige.
Gabaki daya jikinta a mace yayi yayi Sanyi sosai hakanan yau zuciyarta take sakayau Bata Jin nauyin komai Kamar wadda ba zuciyar a kirjinta.

Laylah na zaune tashigo Bata iya cewa komaiba ta wuce toilet tayo wanka da alwala tafito daureda qaton towel ta shirya cikin Riga da skirt na atamap ta Sanya qatuwar hijab ta tada sallah.

Tana idarwa hadiza ta shigo ta kawo Mata abinci Amma Sam batajin cin abincin
Ruwa kawai Tasha ta Haye gado ta kwanta tareda rufe ido koina na gabobin jikinta suna Mata ciwo.

Cikin kulawa Laylah tayi Mata sannu tareda gyara Mata rufarta Jikinta na sanyi tace"

Anty Sa'adah ko dai zaki koma Abuja ne saikiga likata acan?

Girgiza Kai tayi tana cewa"

Bafa komai bane Momy ce itama duk tabi ta daga hankalinta.

Wani sanyayyan murmushi Laylan tasake ahankali Jin abinda anty Sa'adahn tafada,
Ahankali tace"

Momy Dole zata damu tunda bakida lafiya Kuma jikinki ya nuna hakan.

Yanda Laylah tayi mganar cikeda sanyin jiki Dana murya yasa anty Sa'adahn bude idonta ta zubawa Laylahn sbd tajiyo 'dacin rashin mahaifiya acikin sautin maganarta.

Ahankali ta bude Baki tace"

Laylah kinsan cewa kinfimu gata dagani har Momy?

Rashin mahaifiya bashine rashin uwa ba,
Kina tareda soyayyar mahaifinki tun lokacinda kike qaramarki cikin Hali na maraicin uwa,

Kin taso cikin Rashi na makusanta Amma Kuma nida Momy mun rayuwa cikin Yan uwan da makusantan Amma Kuma a qasqance sbd ganin Ana tallafe damu,

Ki godewa Allah da wani kadaicin da wani rashin makusantan alkhairi ne tunda gashi yanzu daga mu din har makusantan mu muna qarqashin inuwarki,

Wani gatan da Jin dadin da Turaki ya sakar Mana bana kusancinsa da Abba bane kawai na girman dakike dashi ne a zuciyarsa..
Dan Haka Laylah ki daina Jin daci arayuwarki Dan bakida maraici yanzu.

Murmushi Mai ciwo Laylah tasaki tareda maida hawayen dasuka ciko idanuwanta ta bude Baki akaro na farko datai maganar maraicinta na rashin uwa tace"

Anty Sa'adah duk gatan dazan samu a duniya zanso inada mahaifiyar da zata kalleni tasan ciwona da damuwata saidai Allah Bai kaddareni da samun wannan gatanba saiya bani wani gatan na daban...

Tashi zaune anty Sa'adah tayi tana kallon fuskarta tace"

Laylah maraicin mahaifiyar data haifeki kawai Zakiyi sbd Babu Wanda zai taba maye gurbinta Amma na tabbata Anne da abbah turaki bazasu taba Bari kiyi wani maraicinba har lokacinda Momy zata bude Miki zuciyarta ki Shiga ta karbeki amatsayi na 'ya..

Wani sanyayyan murmushi takuma saki hawayen datake riqewa Suka ga gangaro Mata sbd tasan qaddararta da Momy Allah Bai rubuto musu zama makusantaba.

Murmushi Sa'adah tayi tana cewa"

Kina mamaki ne?
Inshallah wata Rana zaki samu gurbi Mai girma a azuciyarta.

Shiru kawai Laylah tayi Bata sake cewa komaiba har bacci ya dauke Anty Sa'adahn
Ta zuba Mata idanuwanta dasukai ja sbd hawayen datayi.,

Anty Sa'adah zuciyarta Mai tsafta ce shiyasa take ganin Momy zata kaunace kamar 'ya wataran,

Ita basai momyn ta karbetaba ahakama tana kaunarta sbd itace mahaifiyar Anty Sa'adah.

Wayarta Dake gefenta takuma dauka ta saka Kiran Abbahh Amma still Bata shiga,

Hakanan takejin kadaici da maraici na shigarta Dan Haka ta koma Kan kujera ta zauna rakube tana kallon fuskar Anty Sa'adah Dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Hayaniya ce ta kaure a Palo ba zata ba tsammani sai ganin umma Jamila tayi akanta tana dago fuskarta kuwa ta kifa Mata wasu fararen Marika a jere tareda finciko ta tayo Palo da ita jikin

22, August 2025
Haura'u

Interested

22, August 2025
Haura'u

Interested

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login