Showing 75001 words to 78000 words out of 106967 words

Chapter 26 - NOOR ALBI COMPLETE BY MAMUGEE

Unknown   

28 Jun 2024

25434

ta tabbata akwance na huta Dan jikina naban itace aka gani tareda Turaki L.A,
Zuciyata zafi take zancen Nan ya dagargaza hakurina wlh...

Na'ima ki nutsu ki saurara abinda yafi Wanda kikaji abakin khairat Chiroma,

Wannan yarinya dai ta tabbata itace atareda Turaki a L.A,
Gatanan a cikin Jakarta wlh nasamu sakamakon tana daukeda ciki harna wata hudu....

Dan shiru Ms Na'ima tayi na seconds kafin ta Dan gyara murya tace"

Ban fahimtaba,
Meye Kuma sakamon ciki ajikinta harda wasu wata hudu akai..
Kutumar ubanta zakicimun agurin na tafiyar datai da mijina tin kafin wannan maganar da kike ta tabbata Dan kuwa kasheta zanyi duk ta dauka cikin mijina.....

Na'ima maganar zahirin da gaske nake Miki akan abinda idona Suka ganemin Wanda tabbas takardar Babu qarya acikinta,
Wannan yarinyar cikine a jikinta
Na watanni hudu koma fiye...

Yawun da Ms Na'ima zata hadiye tayi numfashi ta nema ta Rasa abakinta
Gigice tafara taba wuyanta zuwa maqoshinta tana neman yawu Amma ya dauke qaf ta Rasa na hadiyewa....

Laylah data shigo dakinta idonta Suka sauka Kan yanayin momyn da sauri ta qaraso cikin firgici tana Kiran sunanta da Dan qarfi
Amma Ms Na'ima kokarin shaqurewa take sbd rashin yawun dazaibi maqoshinta yabi ta kirjinta kafin ya Isa cikinta ko zatai rage zafin wutar data taso cikin kirjinta...

Hankali tashe Laylah ta kamota duk da tafi karfinta sbd yanayin jikinta datake ba Mai qiba sosaiba Amma tanada nata jikin ba laifi musamman tunda tabaro Nigeria tana gaining weight ba laifi sbd ta daina dieting datake tuni.

Palo tayo da ita tana kwalawa siddika Kira tana cewa"

Yi sauri kawo ruwan sanyi ba sosaiba abawa mum, inaga tasamu attack ne
Yi sauri.....

Ruwan siddika taje da gudu takawo
Cindy ma da sauri tabiyota da wasu ruwan a qaramin bowl da towel qarami
Cikin sauri Laylah ke Bata ruwa abaki suna wucewa a wahale
Cindy ma cikin sauri take gogewa mum din qafafu da towel Mai sanyi hankalinsu duk a tashe.

Ruwan na bin kirjinta suka shiga cikinta ta dago idanuwanta cikin masifa ta tayi wurgi da robar ruwan gabanta tana miqewa Laylah tayi saurin riqota tana Kiran sunanta cikin tsoro tace"

Mum, mum lafiya kuwa?
Wani abun yafaru ne?
Please mum kina bamu tsoro.....

Wayarta take ware ido nema Dan Haka Bata iya cewa komaiba sai ture Laylan datai da qarfi tayi baya da qarfi tana sakin salati Mai qarfi Dan kuwa kife ta tafi zata Fadi
Da sauri Cindy ta tarota cikin tsananin firgici da tashin hankali...

Kallon juna sukai itada Cindyn lokacinda ta tsayu daidai suka kalli cikin tare jikinsu duka Yana Yar rawa
Take tsoron halin data tashi fadawa data fadin yasata shiga yanayi na tsoron ta dago idanuwanta da tuni Suka ciko da hawaye tabi bayan mum da kallo harta shige dakinta ta rufo...

Kasa tafiya tayi da kanta sbd ta firgita sosai itama Dan Haka hannun Cindy ta Kama suka Isa har cikin dakinta ta zauna bakin gado tareda cewa Cindy takawo Mata ruwa Mara sanyi.

Ruwa Cindy takawo Mata Tasha kadan ta Haye gadonta ta kwanta sai Alokacin tasake Ajiyar zuciya tana Dora hannunta Kan cikinta daya Dan taso.

Ms Na'ima na shiga daki ta dauki wayarta Dake yashe tsakiyar dakin ko gani Sosai batayi ta Danna Kiran Zinat.

Zinat data kasa barin asibitin sbd yanzu Kam aiki yadawo musu sabo,
Dan kuwa aikine gagarumi ya taso musu bayyanar wannan cikin.

Tana dauka tace"

Na'ima Shiga wannan halin na some some ba naki bane yanzu,
Menene abin Yi Dan Kiran da waccar tsohuwar najadun keyi yasa Dole ansanar da ita yarinyar na asibiti Dan Haka inaga.......

Zinat Ina hanyar zuwa,
Acikin Daren Nan zanyi booking ticket nadawo nayi maganin matsalar Nan kowa ya huta Dan idan bada hannuna nayi sanadin cikin yarinyar Nan ba bazan iya nutsuwaba,
Zinat kafin ki wuce Anne tazo inason kisa ai Mata allurar wata masifar koma wace iri ce Dan wlh zuciyata wuta takeci,

Turakin da akansa nake duk wani Abu danakeyi,
Yaushe Turakin ya samu lafiyar duka duka da har wata zata rigani daukan cikinsa¿
Shin yaushema har Suka sabane har Haka tafaru Banda labari?Tabbas nayi sake Amma wlh sai tayi Dana sanin kallonsama amatsyin Miji bare hada shimfida dashi.

Kashe wayarta tayi tareda .

neman numbern A Abdoul tace tana buqatan ticket na zuwa Nigeria cikin gaggawa.

Bai tsaya tambayar komaiba tunda ba huruminsa bane Dan Haka yace to tareda bincikawa ta waya ba Bata lokaci yayi Mata komai kwana biyu kafin tafiyar.

Kamar zata Ara hauka taji daya kirata ya sanar da ita sai Bayan kwana biyu Dan Haka duk saita qara Shiga bacin Rai Dan kuwa Bata taba Jin Dana sanin baro Nigeria ba sai lokacin.

Acan Nigeria a asibitin kafin Haj Zinat ta san abin Yi akan Sa'adah din Anne ta iso asibitin Dan Haka Dole ta fuske Akan itace takawo Sa'adahn asibitin harma ta biya komai tana jiran isowarsu ne dama.

Anne Bata nuna komaiba saima jinjina Mata tayi da kokarin datai na kulawa da Sa'adah kafin su zo duk da aranta tabbas tasan da wuya idan tsautsayin ne sbd tasan halayensu ita da Aminiyar tata na boye Dana bayyane.

Duk yanda taso samun ganin likita ko nurses din dake kulawa da Sa'adahn Bata samu dama ba Anne ta toshe koina ta hanyar dauke Sa'adah daga asibiti ta aka maida wata Dan Haka damarsu ta lalace saidai ta jira isowar Na'ima su San abin Yi tun kafin cikin yawuce lokacin illatawar.


*******
Laylah kwana biyu gidansu baya cikin kwanciyar hankali sbd gabaki daya sun Rasa gane Kan mum
Ta birkice gabaki daya laifi kadan fadan gaske take rufe mutum dashi har ita Laylan Yar gaban gashinta Bata ragawaba saima tsanarta datake ji ta wani bangaren tunda sun hada jini da Sa'adah duk ba komai yasa batama kawo alaqarsu araiba sanin irin muguwar qiayyar Dake tsakanin Momy da Laylah da uwar Laylah tasan ba lallai akwai qauna a tsakaninsu ba tunda Laylan bamai surutu bace Dan hakanema batasan irin kusanci da qauna Mai qarfi Dake tsakaninsu ba,ita koyaushe kallon ba wata alaqar a tsakaninsu sbd qiyayyar Momy akan Laylan.

Kama kanta tayi daga kusantar inda mum din take sbd fushinta a kusa yake yanzu,

Ba ita kadaiba har su siddika da Cindy a kame kowa yake da gudun bacin ranta.

Makaranta ma idan Laylah ta tafi dai kusan magrib take dawowa gidan Sam gidan ba Dadi koina kayi motsi masifar mum ce ke ci ga Abban Bai dawoba bare ya iya sanin matsalarta ko zata sauko dan Haka kowa ya kame kansa Ana kaucewa fushinta.

Sai datai kwana biyar kafin tasamu wuce Nigeria data matsu Bata isaba Dan har wani tsalle zuciyarta take na zaquwa sai dataga jirgi ya saukar da ita airport din Lagos tafara jinta daidai,
Bata kwana agarinba ta hau wani flight din ta isa Abuja kafin ta sauke ajiyar zuciya tareda Jin nutsuwa da kwanciyar hankali sun shigeta.


Asibiti anso sallamar Sa'adah bayan tayi kwana biyu taji sauki sosai saidai test din da akai Mata wasu suna nuni da wata matsalar Dan Haka ba Bata lokaci Suka sake diban jininta Dan yimata wasu test din kafin aka sallamesu kafin result na test din su fito.

Bayan dawowarsu gida tayi waya da Laylah wadda ba'a fadawa abunda yafaruba sbd karta damu,
Itakuma Sa'adah abin dayasa ta nace akan Kar afadawa Laylan sbd yanayinta da lafiyarta..

Ms Na'ima ko data iso Nigeria anriga an sallami Sa'adah daga asibiti Dan Haka tana isowa Bata shigo gurin Anne ba sai data kwana ta wuni tagama danne kanta da zuciyarta sbd karta Bari Annen tagane tasan da komai sbd tunda Sa'adah ta dawo gida bazata iya komai akantaba Kai tsaye Saida wata dabarar.


****Tafiyar mum da kwana uku Abban yadawo daga tasa tafiyar murna gurin Laylan Bata boyu ba musamman dayake mum Na'ima da siddika tadawo Nigeria tunda itace Mai aikinta Koda yaushe Dan Haka Yana dawowa da kanta ta fito da gudu tayi kansa
Ba Bata lokaci ya dauketa Kan jikinsa Yana kallon haske da cikar data qara Bai sauketa koinaba sai palonsa na sama Yana kallon fuskarta datasha simple makeup sai qamshi takeyi,
Ga wata qaramar chiffon free half gown a jikinta data qara Mata kyau kaman yarinya Yar Sha uku.
##MAMUH#


*_Mamuhgee 42_*
Yasan Ms Na'ima Bata Nan ta tafi Nigeria sbd ta sanar Masa da suna waya akan zata tafin, Bai Saba hanata fita ko tafiyaba shiyasa baice komaiba Bayan Allah yakai lafiya Dan fitarta Bata fada Masa dama tafiyarce dai wasu lokutan take sanar Masa bayan tagama tsara abarta.

Hutawa yayi sosai bayan dawowarsa wannan tafiyar sbd sakewar dasuka samu dagasu saisu sai Cindy wadda take tamkar secretary din Laylah Dan yanzu maganinta ma Sofia ta damqa Mata ita ke Bata anan gida tana Sha Amma a dakinta yake boye sbd gudun tsautsayi.

Samun wannan sabuwar damar dasukai yasa suqa qarasa lalacewa juna Dan kuwa yanzu tamkar wasu chewing gum suke musamman da cikinta yaqe qara Masa Jin nutsuwa da ita duk da baisan tana daukeda cikinba,
Itama cikin yasa taqarasa lalace masa,
Babu inda basa shaaninsu musamman dayake ba sauran wata kunya a tsakaninsu bayan kamewarsa Dake motsawa wani lokacin musamman idan Yana tuno Amininsa sai yanajin wani iri duk ranarda shaidar abinda ke faruwa tsakaninsu ta fita wato ciki idan tasamu.


*****Babbar ranar farin cikinta tasameta ne lokacinda Abban ya sanar Mata an sallami abbanta sbd saukin daya samu Yana iya magana yanzu harma da motsa jikinsa yayi komai
Tafiya ce kawai bayayi yanzu Yana Kan kujera sai antura Amman tafiyarma zaiyi ahankali wata Inshallah.

Rumgumesa tayi tana kukan farin cikin samun lafiyar abbanta,
Jin takeyi inama zata zauna guri daya da abbanta,

L.A Suka tafi inda mum tuni ta wuce samun labarin tsautsayin Sa'adah Dan Haka ba kowa agurinsa Saida suka Isa,

Harhada komai sukai Suka Gama duk wasu formalities na sallamar Suka tarkata suka kaisa wani lafiyayyan hotel da Turaki yasa A Abdoul yayi Masa booking.

Acan suka barta ta wuni da abbanta suna magana akan yanda zamanta yake da Ms Na'ima cewan batasan ita Matar Turakin bace.

Abba Bai wani ja zancen da tsayiba sbd yanda zancen ke sanyata kasa hada ido dashi,
Hakama shima zancen baya Jin sakewa acikinsa tunda 'yarsa ake magana da Amininsa dayasan haryanxu baigama karban aurenba,
Ya riqeta ne saboda inganta rayuwarta harma data 'yar uwarta,har abada bazai daina gode Masa akan hakanba,
A taqaicema ya karba auren ne sbd halinda shi yake ciki yanzu kuma tabbas bazai takura Aminin nasaba zai basa tabbacin zai iya sauwakewa Laylan aurensa tunda ba Kamar taimakone yayiwa Wanda yake halin ciwo da rashin gata,
Yanzu Kuma alhamdllh yasamu lafiya, Kuma Laylan tasamu ilimi Mai zurfi ko ahaka zasu iya tallafar rayuwarsu.

Da wannan tunanin Abban ya yankewa kansa shawaran idan ya natsa bayan komawarsa guda zai bawa Turaki damar ya sallami Laylan tunda dama Babu Wanda yasan da aurenta dashi Kuma yasan bazai taba karbanta amatsayin matarsaba sbd shi da Zainab Dan 'yarsu tamkar 'yarsa daya haifane.

Sai dare A Abdoul yazo ya dauketa suka koma gida sbd Turakin Bai dawo gurin abbanba barinta yayi ta sake da mahaifinta suyi magana yanda yakamata sbd a kusancinsa da ita yagama fahimtar irin girman kauna dake tsakaninta da Abbanta Wanda duk ya kalli hakan ranarda ya biyawa Mahmoud sadakin zainab take Fado Masa Rai irin yanda suke tsananin son junansu baitaba saka ran ya biya sadakin da za'a hadu a Haifa Masa Mata bane...

Bayan sun kwanta tana cikin jikinsa kwance da wata qaramar fingilalliyar rigar bacci data Gama barkewa ta Samanta sbd irin yamutsar dasuka Gama Amma dayake tanason bacci da rigar sbd rashin nauyinta yasa ta maidata ahakan sbd saman ne ya Gama fincike hannuwan rigar dasuke sirara.

Cikin sigar roko da Yar yarinta ta bude Baki ahankali tace"

Abba, zanbi Abbana Nima Dan Allah naje Nigeria..

Ahankali ya lumshe fararen idanuwansa masu Dan girma ya budesu akan bakinta da yayi maganar kafin ya bude Baki ahankali cikin nutsuwa yace"

No.

Marairaice murya tayi tareda sake shigewa jikinsa tana zagaya hannuwanta zuwa bayansa tasake Dan rugumarsa Suka manne fiyeda yanda suke tace"

Please Abbahhh.
Nayi kewan gida,dasu Anne,
Inason bin Abbana gida Dan Allah.

Zakije Amma ba yanzu ba saikin Gama exams dinki tukuna na wannan session din,
Karki manta kina last year dinki.

Sanyi jikinta yayi tace"

To waye zai kaisa gidan tunda momy ta tafi?

Tare zamu tafi Inshallah gobe Zaki koma Atlanta daga Nan zamu wuce ki zauna gida kiyi karatun exams.

Sanyi jikinta yakuma yi ta kallesa tana Jin kewarsu duk su dukan shida abbanta tun Basu wuce ba ahankali da sanyin murya tace"

I will miss everyday Abbah....
Please kadawo da wuri tunda mum tace ba yanzu zata dawoba zanyi kadaici da yawa bakanan mum batanan ga abbana ma ya tafi.

Kissing lips dinta yayi ahankali tareda gyada Mata Kai batareda ya bude Baki yayi maganaba Dan kewarta zaiyi Kamar sabuwar haihuwa yasani shima saidai ba Daman nunawa shiyasa yake wahala yanzu duk yayi tafiya sbd rashinta Yana azabtar da zuciya,Ruhi da gangar jikinsa.
Da Dan zazzabi ta kwana sbd kadaici data fara tun lokacin da Yar damuwar zuwa gidan dataso Yi,

Har asuba jikinta akwai zafin zazzabi irin Wanda yake Dan damunka Ahankali ahankali,

Da safe guraren 10 Da kansa ya shiryata cikin kayan sanyi da qatuwar jacket Suka Fito yakaita tayi bankwana da abbanta Amma Bai shigaba a mota ya tsaya sbd idan yashiga bazai iya fitowa kaita airport da kansa ba saidai A Abdoul yakaita Dan Haka Bai shigaba Ita kadai tashiga tareda A Abdoul Suka Gama suka fito.

Tunda suka Kama hanyar airport take kwance jikinsa Yana kissing hannunta akai akai har Suka Isa airport din A Abdoul yafita motar yabarsu.

Fuskarta ya Kama yayi kissing bakinta ahankali tareda shafa fuskarta ahankali da muryarsa Mai dadi da aji ciki yace"

Ki kula sosai okay??

Gyada Kai tayi tareda Dan shigewa jikinsa ta rumgumesa yanajin zafin jikinta ahankali.

Dagota yayi ya Kama hannunta Suka fito motar Yana riqe da hannunta A Abdoul na bin bayansu da qaramar suitcase dinta.

Yanayin yanda taketa neman rikice Masa ta sanyashi sauya ra'ayi akan rashin barinta zuwa yasa Basu jira lokacin tashin jirginsu ba suka tafi Suka barta.


Yamma sosai ta iso gida bayan sofia taje har airport ta daukota da motar gidansu sbd zazzabinta qarfi yayi kafin su iso Dan Haka suna isowa gida daqyar da Taimakon sofia tayi sallah Cindy ta kawo tea Mai dumi da cupcakescake taci guda biyu Tasha magani ta kwanta a wahalce.



***Anne ce zaune tareda baqi suna magana saiga isowar baqi halima tazo ta isar Mata dama tagama da baqin zasu tafi ne Dan Haka Kai tsaye aka shigo dasu Momy...

Momy CE tareda Haj Karima Dake zaune a Abujan suka zo gidan,
Tunda momy tadawo tana gidan Haj Karima anan Abuja sbd Sa'adah tana zuwa dubata akai akai,
Bata taba zuwa tareda Haj Karima ba sbd gudun sugano gaskiyar ayi tashin hankali batareda sa'adahnta tagama karatunta tafara aiki Mai kyau ba su Bata Mata gobenta Dan kuwa saninta ne bazasu taba barwa Allah ba Koda Sa'adah bazata aura Turaki ba sunfi son ayi biyu Babu Dan kuwa dukkaninsu qiyayyar mahaifiyar Laylah da Laylah a jininsu take mai qarfin gaske.

Qarasowa sukai Anne na musu barka da zuwa cikin mutuntawa da sakewar fuska.

Mintuna qalilan aka zagayesu da kayan tarban baqi,
Drinks ne masu sanyi da sabon madarar nono Mai sanyi sai dambun Naman kazar sai snacks.

Haj Karima duk gaisawa da firar da Anne ke Dan Jansu hankalinta nakan tsabar dukiya Dake magana koina a gidan,
Ta duba tasake dubawa Babu wani Abu a gidan da bana manya bane Dan Haka ita saima taji hankalinta yakuma tashi akan ayita Mai yiyuwa bazai yiyuba Sa'adah na aure gidan arziki irin wanna ace Basu more Mataba bayan dawainiyar dasukai da uwarta da ubanta ya lalace akwance da sunan ciwo,

Tunda gida zasu dunguma su tafi ba har Sa'adah da momyn tunda Mahmoud din zai dawo ai zasuje can ayi magana
Wlh bazata Sabu ba ko kadan,
Zainab bazai yiyu su saka Mata ido tabar yarinya tayi watsi da dangin uwarta ba,

Waccar samun wahala wato Laylan sun samu ta fita rayuwarsu tunda Ms Na'ima ance ta tafi da ita sunsan aikin wahala kawai ya Isa ya juyar da sauran qanqanuwar lafiyar qwaqwalwarta.

Sa'adah Bata gida ta fita karban wani sako a school Dan hakan ma suke zaune palon Anne da tuni ankaisu palon Sa'adah din
Dayake kusan bankwana Suka taho yi tareda Jin idan tareda Sa'adahn zasu tafi tunda abbansu dai dawowa zaiyi Dan Haka suka dasa sabon zaman jira,

Anne sakawa Tai halima takaisu palon Sa'adah Dan su sake yanda yakamata kafin dawowan Sa'adah din.

Tun Rana suke jiran dawowarta har kusan yamma batadawoba
Momy tayita Kiran wayarta Bata dagawa
Anne ma tayita Kira itama Bata dagawa.

Momy ce tafara Shiga damuwa sai Anne sbd magrib da aka fara Kira sbd tun dawowar Sa'adah hannunta Bata tana fita takai dareba a waje da sunan makaranta saidai idan biki ta fita kokuma tare suka fita sukai daren
Dan Haka take tasan ba lafiya ba.

Hankalinsu tashi yayi sosai Anne tafara kiran wayoyi tana tambaya ko Sa'adahn na can,

Momy tsabar tsoro da damuwa bin Anne kawai take da Ido tana jiran Jin labari Mai ma'ana Amma Babu inda ba'a buga wayaba da ake tunanin samunta acan saidai Bata can din.

Tashin hankalin dasuke ciki zuwa yanzu yagama girmama sbd har qarfe Taran dare ba labari Mai.

Kokarin Kiran M Kabir tsohon Secretary din Turaki tayi ta sanar Masa abinda yake faruwa yace Mata gashinan zuwa yanzu.

Kafin ya iso gidan yafara shigarda missing complaint sai gashi tun kafin ya isa gida aka sanar Masa ansamu accident tunda Rana na wata motar data buge motar wata budurwa.

Bai Isa gida ba Saida yaje ya tabbatarda Sa'adah ce,

Ita din ce saidai Kam tanajin jiki sbd ta bugu sosai qafafunta da hannunta dama kanta duk bandage ne
Qarin baqin cikin abin Wai Wanda sukai hakan sun tafiyarsu ba'a kamasu.... Saidai baya tunanin guduwa sukai yafi tunanin koma su waye sunada kudi sun biyane Ana barsu sun tafiyarsu ake cewa sun gudu.

Su Anne yakira ya sanar musu halinda ake ciki
Take jikin Momy ya mutu sbd yanda takeji azuciyarta gameda lamarin tasan akwai masifar da zata sameta...

Suna Isa asibitin kallo daya Momy tayiwa Sa'adah takasa riqe kanta wasu hawaye masu tsananin zafi suka balle Mata ta share tana kokarin Kame kanta sbd Anne data bayyanarda damuwarta Mai tsanani a fili Kan al'amarin,

Haj Karima kuwa cewa tayi sai an Nemo wainda sukai wannan hadarin Dan bazai yiyuba ace sun gudu ba dalili bane.

Cikin gaggawa aka sauya Mata daki raga emergency din dasuka sameta.

Suna cikin wannan tashin hankalin su Turaki Suka sauka Nigeria tsakar Daren.

Gida aka kaisa direct bayan ankai Abba lafiyayyar masaukinsa.

Dole Momy

22, August 2025
Haura'u

Interested

22, August 2025
Haura'u

Interested

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login