Showing 78001 words to 81000 words out of 106967 words
ce aka Bari ta kwana a asibitin su Anne Suka koma gida
Haj Karima ma ta wuce gida.
Washe gari tunda Turaki da kansa yakai Abban asibiti
Yakuma qi sanarda Laylah abin daya samu Sa'adah.
Sauyawa Sa'adah asibiti akai washe garin aka maidata asibitin dasuke zuwa..
Bayan sun fito yashiga mota ya zauna ya Dan dago tareda kallon A Abdoul dake gaban motar zaune cikin kamewa da murya Mai daukeda girman kamewarsa yace"
Abincika komai akan wannan abun daya faru sbd ance ko kwanaki mota tayi kanta,
A bincika komai inason sani.
Gyada Kai A Abdoul yayi Yana cewa"
Inshallah.
Barin asibitin sukai Suka nufi gurin wasu baqinsa dazai gani Dana abbansu Laylan yabar Masa Mota daya da drivern dazai maidasa masauki idan yagama.
Dr faruk daya dubata last time shine yanzu ma take hannunsa Dan Haka ya kalli Anne da zata wuce gida yace"
Anne akwai wasu result dinta na farko da basa cikin folder dinta inaga last time dasu kukaje gida Muna buqatansu Dan result dinta na yanzu munason duba wani abun.
Ok ba damuwa inaga suna cikin handbag dinta da akazo asibitin da ita last time din zansa aduba sai akawo Inshallah.
Ok, sai abada da wuri Muna jira Dan treatment dinta zai tsaya saimunga wancan result din.
Anne na Isa gida dakin Sa'adah tafara wucewa direct tafara duba handbags dinta daya bayan daya.
Kasa ganin komai tayi Dan Haka ta nufi drawers tafara dubawa Suma.
Nanma bataga komaiba dan haka ta nufi wardrobe dinta ta bude tafara dubawa.
Handbag dinta daya tagani kicin kayanta a boye Dan Haka ta janyo tareda budewa ba Bata lokaci taga takardun asibitin aciki..
Ta kwaso ta fito dasu gabaki daya tasaka a handbag dinta kafin ta nufi bedroom dinta.
Sai dare suka tafi Kai abincin dare asibitin itada halima.
A dakin Suka tadda Abba da momy sai Haj Karima da zuwanta kenan itama tareda umma Da tuni ta iso garin yau Dan Shiga al'amarin tunda Turaki na qasar yagansu ya Sansu amatsayin dangin uwar matarsa.
Cikin girmamawa sukewa Anne barka da zuwa tana amsawa cikin yabawa karamcinsu,
Takardun Datazo dasu ta kalli halima tace"
Halima bawa Dr faruk takardun gasunan.
Dr faruk karba yayi ya fice daga dakin Dan dama yagama abinda zaiyiwa Sa'adahn data farka Amma Bata iya magana ko kadan sbd azabar ciwon da kanta keyi.
Minti hudu da fitar Dr faruk ya dawo dakin daukeda folder din Sa'adah ya Ciro wata takarda yana kallon Anne dake kallonsa ganin ya dawo
Kowama kallonsa yakeyi suna jiran Jin Mai zaice ya miqawa Anne takardar Yana cewa"
Wannan inaga ba nata bane Dan a cikin namu gwaje gwajen bamu samu ciki a jikinta ba.....
Tsit sukai gabaki daya dakin suna kallonsa,
Anne da Momy da Abba dasukasan batada aure da mamaki da suke kallonsa,
Umma Jamila kuwa cikin kasa boye halin data shiga tayi saurin cewa"
Takardar ciki ta nuna ita ko me?
Miqawa Anne takardar yakuma Yi ganin tana Masa kallon buqatan qarin ya kalli sauran Yan dakin yaga duka iyayen Sa'adahn ne ya maida kallonsa kan Anne cikin nutsuwa yace"
Takardar pregnancy test ne tareda scanning Amma banajin nata ne sbd ba'a qasar Nan akaisa ba,
A America ne,Los Angeles....
Anne najin hakan ta karba takardar da sauri ta karance tsaf taga abinda yake ciki da sauri ta dago ta kalli Sa'adah Dake zaune tanajinsu Bata iya cewa komai sai rufe Ido datai cikin yanayi na rashin abin Yi.
Qamshin Bois elite ne yafara shigowa dakin Abba da Anne dasukan asalin waye Mai wannan qamshin Suka kalla kofa kafin shigowarsa
Tukuna ya shigo A Abdoul na bayansa
Dukkaninsu suka waiwayo suka kallesa yaqaraso cikin tsananin kwarjininsa daya Hana su umma Jamila tada hayaniyar murnar batun ciki da ake lokacin....
Haj Karima ce tayi qarfin halin gaidasa tana maida kallonta Kan Anne Baki washe tace"
Barka da arziki,
Ashe ciwon dai harda juna biyu ajikinta,
Allah ya raba lafiya yasa anbude hanyar tara zuria kenan...
Kujerar da A Abdoul ya gyara Masa ya zauna Yana kallon Abba dake neman rudewa da zancen da ake...
Anne ganin Kar rashin fahimtar tayi yawa ta bude Baki tana dauke kallonta daga kan Turaki daya Gama cika musu Ido dakin da kwarjini tace"
Ba sunan Sa'adah ne ajiki ba, takardar ba tata bace sbd ba komai ajikin Sa'adah.
Miqawa Turaki takardar tayi tana cewa"
Duba kagani ko zaka gane sakamakon waye.
Karba yayi tareda Dan kallon takardar akan sunan Mrs AB TURAKI idonsa yafara sauka kafin ya kalla date din jike jikin takardar.
Da sauri ya gangara da idonsa Kan signing dinta Dake qasan takardar.
Wani irin yanayi Mai wuyar fassarawa ya Shiga saidai mutanen Dake gurin ya sanyashi dannewa ya kame,
Miqawa A Abdoul takardar yayi bayan ya nade Yana miqewa yace"
Allah yabata lfy.
Kofa ya nufa ya fice A Abdoul na bayansa
Yan dakin duka kowa tsit yakuma Yi Dan su Kam Basu gane komaiba Kuma yanzu.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 43_*
Yana ficewa Momy taqi waiwayowa ta kalli Yan uwanta da duk anbi anhansu gane komai,
Sunanson nuna mrnarsu da farin cikin wannan samu daya samesu Amma Kuma ganin daga uban gayyar Turakin ya fice baice komaiba hakama Anne takasa cewa komai Dan itama kanta duk da tana zargin cikin idan bana Laylan bane Amma Kuma da wuya hakan ta faru, ita Tama Rasa tunanin kamawa,
Abbansu Sa'adahn ma kasa Kama kowanne tunanin yayi Dan Sam Bai kawo ma Laylah a zancenba tunda yasan karatu takeyi tukuna,
Kuma Turakin ma baida ranar amsarta amatsayin Mata shiyasa ma zai nema sallamarta daga Turakin Dan gudun shiga haqqin takurawa Amininsa.
Momy ce kawai tunanin farko daya shigeta shine tabbacin cikin Laylah ce take dauke dashi ba kowaba, sbd sanin barewa bazatai gudu 'danta yayi rarrafeba,
Ms Na'ima tayi babban kuskuren daukan riqon Laylah sbd batasan cin Amana a jininsu yakeba.. yanzu gashi itada Yan uwanta za'a kunno Mata masifa Dan kuwa su umma Jamila Allah kawai yanda zasu dauka wannan al'amari da aka rufesu baibai tsabar son Rai da cin Amana irin na Kawu saidu daya daura auren.
Anne Bata Gane sauran zancen da ake a dakin sbd hankalinta gabaki daya baya Kai tunani take shiga daban daban na wannan takardar...
A saninta babu wata Mrs AB TURAKI Bayan Na'ima da Laylah,
Babu Kuma wata tsautsayi ko kaddaran dazai kawo sakamakon awon cikin Na'ima hannun Sa'adah,
Laylah ce kawai duniya sukeda kusancinda al'amari irin wannan Bata zaizo hannun Sa'adah...
Idan Natane to shi wannan ciki Kuma..... Lumshe ido tayi Ahankali tana cire zancen cikin kanta gabaki daya Dan kuwa bazata taba Gane komaiba ayanzu zata saka ido taga Inda ciki zai bullo daga Mr Turakin koma wacece acikinsu.
Gida ta miqe ta wuce tabarsu suna buqatan kebancewa da Momy Suma Amma ta Hana kanta sakat da aikin hidimarta Sa'adah da zata bawa tea Mara zafi Dole Suka tafi Suka barta ba Dan sunbar zancenba Wanda Dole ayisa ai.
Saida suka wuce kafin Abba ma ya fito ya wuce da drivernsa da motarsa da aka Ware Masa.
********
Tunda suka baro asibitin Yana zaune a motar Bai ce komaiba Yana zaune hankalinsa kwance Kamar Babu komai cikin ransa
Saidai wasu feelings da tsantsar nutsuwa yakeji na wanzuwa cikin ransa.
Harsuka Isa gida Babu wata magana daya furta
Dan Haka A Abdoul na ganin yafito motar ya Ciro takardar da tuni ya sanyata cikin envelope ya miqa Masa a ladabce Yana cewa"
Mu kwana lafiya.
Karban envelope din yayi tareda wacewa ya nufi hanyar shiga makeken palonsa Dake sashensa dayafi na kowa girma a gidan ya shige.
Yana shigewa A Abdoul ma motarsa Dake gidan yanufa ya bude ya shige tareda tayarwa yabar gidan ya nufi gidansu Dan Mahaifiyarsa anan Abuja take zama duk da mahaifinsa ya Jima da rasuwa.
Bai tsaya palonsa ba Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya shige tareda nufar jikin drawer gefen gadonsa ya janyo ya sake tareda rufewa Yana aje wayar hannunsa ta nufi toilet yashige.
Wanka yayo yafito sanye da farar bathrobe ya nufi gaban mirror ya tsaya Yana goge jikinsa da qaramar towel fara.
Abubuwan daya Saba na kafin kwanciyarsa yayi kafin ya Sanya fararen pyjamas da slippers masu taushin gaske
qamshinsa na Bois elite na sake mamaye dakin ya nufi Kan sofa Dake dakin ya zauna anatse tareda daukan wayarsa Dake silent sbd rashin son damuwa
Kai tsaye numbernta dake sama yasaka kira.
"Hello Abbah" tafada cikin muryarta Mai taushi dake son bayyanarda kewarsa datai.
Boyayyan numfashi ya sake sbd koyaushe muryarta ta sauka kunnensa tana motsa duk wani jini dake yawo jikinsa.
Ahankali ya bude Baki Kai tsaye ya sakar Mata tambayar"
Are you pregnant?
Wata nawa ne?
Yana Nan ko kuwa?
Tsit tayi Jin tambayar data zuwar Mata a bazata
Kuma cikin yanayi na kamewarsa yayi Mata tambayar Dan Haka sai jikinta yayi Sanyi tana neman daburcewa,
Cikin kame kame tace"
Abbah kayi.....
Akaro na farko a rayuwarsu daya sakar Mata tsawa Yana cewa"
Amsa nake fara so, are you pregnant, yes or no¿
Ahankali tayi qasa da murya cikin sanyin jiki tace"
Yes Abbah.
Rufe ido yayi ahankali cikin yanayinda yakasa fassarawa tsawon mintuna kafin ya bude idon ya sake bude Baki ahankali yace"
Meyasa bansaniba?
Tsawon wane lokaci¿
Abba Ina tsoron mum ne tasani,
Nima bansan dashiba farko
Daga baya ne nasani
I'm sorry abbah, kayi hkr Dan Allah"" hawaye ne Suka balle Mata Jin yanayinsa kaman ransa ya baci akan rashin fadar Masa din.
Lumshe ido yayi yanajin yanda numfashin kukanta ke sauka cikin kunnensa Yana taba zuciyarsa
Sai daya sauke ajiyan zuciya ahankali kafin cikin nutsuwa ya bude Baki yace"
Ya Isa Haka,
Daina kukan,
tell me, is everything okay? I mean the baby, kinajin komai lafiya?
Ki taba ganin likita?
Share hawayenta tayi tanajin kewarsa na sake kamata sbd cikinta yafara motsawa yanzu,
Gabaki daya cikin tsoro da tashin hankalin dawowar mum take ta bude Baki ahankali cikin yarinta tace"
Abba yayi girma Ana ganinsa,idan mum tadawo zata gansa,
Bansan me zataceba..
Babu abinda zai faru okay¿
Zan dawo da wuri zan kaiki kiga likita da kaina,
Ki ringa kula sosai yanzu, and ki daina saka su skinny jeans dasu kayanki masu matsewan nan Zaki takura kanki da babyn.
Zansaka akawo Miki nurse dazata ringa kuka Dake kafin nadawo.
Kwantawa tayi Kan kujeran datake zaune tana Jin son Abbanta na sake shigewa koina nata musamman cikin jikinta yanzu duk lokacinda ta Dora hannu akansa Abban takeji har cikin jininta sonsa na sake kamata.
Ahankali ta furta"
"Abbah, are you happy with th...."
kasa qarasawa tayi sbd nauyinda kalmar Tayi Mata saidai Kamar daga sama taji saukan muryarsa Mai dadi da Kamala cikin kunnenta yace"
I love the baby,and I love his mother....
I love you both.
Cikin tsananin farin ciki da nutsuwa
jikinta na mutuwa da kalamansa tace"
We love you too Abbah.
Ms Na'ima Dake tsaye bakin kofar bedroom din nasa kasa tsayuwa tayi sbd wani jiri jiri datake gani,
Me take ji Abu kamar a mafarkinta.
I love you taji abakin Turaki,
Maganar baby da uwar baby yake bayan saninta Sa'adah na asibiti Kuma tabbas sun biya kudin gaske likitan asibitin da aka fara kaita ya tabbatar musu da Babu ciki ajikinta suna murnar ya zube me take Shirin ji yanzu??????
Innalillahiiiii"" tafada a fili idonta na rage ganin haske ta juya da sauri Takoma inda ta fito tana bude idanuwanta da hannuwanta Dan bakin Rai Bata gani Sosai.
Tana Shiga palonta a haukace ta zubawa siddika Kira tana cewa"
Kaini dakina bana gani Sosai.
Da sauri siddika takaita daki ta fito sbd ganin masifar Dake cikeda idon dayasa Bata gani Sosai...
Hannu ta Dora akai tanason kurma ihu Amma maqoshinta yaqi budewa ta zube bakin kujera tana cewa"
Wace kaddararrarce Turaki yake cewa I love you harda baby?
Neman Mata Turaki ya fara kokuwa wani auren yayi Basu saniba?
Nashiga goma na lalace,
Mata nawa Turaki yakeson nabi Ina hallakawa¿
Walh bazan yarda da wannan masifarba,
Ko ba aure yayiwa koma wacece wannan cikin bazata Bari a haifesaba,
Ta yarda tayi koma menene Amma wlh bazata yarda wata ta haifawa Turaki 'yayaba.....
A haukace ta dauki wayarta tafara neman numbern Zinat....
Tana dauka cikin yanayin tashin hankali Mai tsanani da rudewa tace"
Zinat abun yamun yawa Turaki zai cinnamun hauka,
Zinat Turaki wata yayiwa ciki wlh,
Zinat Turaki I love you yake furtawa wata.... Zuciyata bugawa zatai..
Cikin gajiya da wannan masifa itama Zinat din tace"
Ki nutsu Na'ima tunda kema kingano Cinna Miki hauka al'amarin Turaki zaiyi,
Tashin hankali bazai Bari musan abinda mukeson saniba...
Turaki yagama bamu mamakin duniya tunda yayi aure bare yanzu Dan yayiwa wata Mai rubutacciyar qaddara a hannunmu ciki,
Fatan dai kin gano wani Abu akanta ba haukar banza kikayoba Kika dawo?
Kasa magana Ms Na'ima tayi sbd batama San Mai zataceba,
Da alama gwara shaanin Sa'adah shi data san komai akan wannan da batamasan ta Ina zata faraba saidai Abban abin data sani shine koma yayane itace ta Los Angeles da khairat ta fada Mata Dan Haka sake tattarawa zatai Takoma Dan sai tana Atlanta zatafi Gano wani abun Dan idan zata mutu tadawo duniya Turaki bazaice Mata komaiba akan lamarin Koda ta tambaya kuwa sai lokacinda yaga Dama yaso fada.
Cikin takaici Haj Zinat tace"
Koma meyene Anne tasani Amma dayake batada adalci shine tayi shiru tabarsa ya rufeki a baibai saidai kawai akawo miji jaririn 'da ace Miki gashi na Turaki ne tsabar a nuna bakida wani amfani bayan tun farko shi tukarin ai shine Mara amfanin,
Tunda ya warke yanzu Dole zai ringa tsalle tsallen zuwa gurin Mata bazai iya tsayawa akan wadda ta zauna shekaru dashiba.... Mtsss Ni ke kanki Na'ima wani lokacin kayan takaicine Dake,
Ki tattare dukiyar ki rabu dashi yaje ya nema matan duniya idan zai iya Amma kin tsaya ke acikin bacin Rai Nima aciki...
Zinat wallahi bazan iya rabuwa da Turaki ba tun wuri daina maganar rabuwar Nan,
Zaunawa zanyi naringa cin uban duk wadda tayi gangancin shigowa rayuwarmu nidashi tunda kwadayin abun duniyar kowa a zuba Masa a zuciya.
Haj Zinat tafi Jin zafin Anne Akan Turaki sbd Babu kalar asirin da basuyiwa matarnan ba Amma yaqi ci,
Idan suka mallaketa tamkar sun mallaki Turaki ne sbd a duniya ba maganarta dayake tsallakewa saidai tsohuwar tamkar wadda take kwana rungume da Qur'an Dan kudin dasuke narkawa bokaye da malamai bama gaskia bane Amma a banza Dole Suka watsar sbd basa Wasa da lissafi, bazasu iya cigaba da hasararda Babu riba acikiba.
Cikin son Kai qarshen matsalarsu kowa ya huta Haj Zinat tace"
Zan Kira khairat mugun bincike za'ai Mana asan koma wacece daga Nan sai asan matakin dauka...
Cikin zafin Zuciya Na'ima tace"
Bazan iyaba kasheta zanyi har ita har cikin..
Idan kin kasheta acan saikiyi bankwana da Turakin da kikai kisar dominsa Dan kina gidan yari ko lahira zai aura wata Matar.
Zinat meyasa bakya fadar alkhairi yanzu koyaushe muguwar data kikemun,Wai ko mun fara samun matsala ne?"" Tafada ranta na baci Sosai akan baqin datake ciki.
Cikin takaici itama Zinat din tace"
Aiki da hankalinkine bakyayi koyaushe irin Haka ta taso kedai maganarki kisa,
Kinsan hukuncin kisane?
Kin aikata Abu Dan wani Amma kinaji kina gani za'a rabaki da duniyar Kuma Babu abunda zaiyi miki,
Ni bana komai ba lissafi kin sani,
Inada 'yaya idan Ina rufe Ido Ina biye Miki gurin yin komai da tuni mun Jima da zama Yan gari a lahira,
Dan Haka bazan biye Miki mu hau jirginda ba saukaba sai filin Danasani da lahiraba Dan hake kema ki nutsu cikin ruwan sanyi zamu zuba rashin arzikinmu batareda mun barwa kanmu abun fada ba.
Naji zancen ya Isa Haka sbd Zinat yanzu kin daina gane ciwona,
Kedai idan magana Bata fitowar kudi bace batada babban mahimmanci agurinki,
Yanzu kisa Fahad yamun komai cikin gaggawa inason komawa,
Tunda Turaki ya fara fadar I love you kinsan Yana gap da gane mace ciki da wajenta da halayensu da kyau Wanda kema kinsan hakan nada barazana agun mu daga lokacinda yafara karantar son dukiyarsa a jinina yake.
Zamuji da wannan idan mungama da wannan babbar matsalar dake gabanmu Dan Nima ko a mafarki bana Mana fatan wata macen da haifawa Turaki 'yaya idan bakeba to kowama bazai masaba a zauna ahakan yafi tunda kunada 'yar riqo.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 44_*
Anne shiru tayi Bata sake tada maganar al'amarin takardar cikin ba sbd batasan wa zata Kama zancen dashiba,
Sa'adah dai batace komaiba sai cewa ba nata bane Haka kawai tace musu tabarsu a duhu,
Momy Bata damuba sbd tasan Babu abun daya hada sa'adahnta da wani zancen ciki Dan Haka itama tayi watsi da zancen tunda cikin Laylan Bai shafeta ba.
Abbansu ma share zancen yayi sbd Ganin Anne batace komaiba Kuma yasan tarbiyar yaransa daidai gwargwado duk da yajima baya taredasu
Amma tunda yanxu tarbiyarsu a hannun Anne take bashida ta cewa Akan maganar yabar zancen tunda yasan sunsan abinda suke.
Umma Jamila ce ta daga hankalinta Kan ayi maganar qarshe Sa'adah da kanta tace"
Ba'a son tada zancen ne sbd matar Turakin Ms Na'ima da ake gudun fitinarta.
Wata dariyar bin iska Umma Jamila tayi tana cewa"
Akwai Wanda ya Isa aji shakkarsa akan samu da qaruwa daya samemu na farin ciki,
Ita Ms Na'iman inace da Turakin take takama? To shine ake wani boye boyen karta sani.
Haj Karima dake Shan tea ahankali cikin nutsuwa da takama tace"
Sune sukasan wata Ms Na'ima
Mu abunda yake gabanmu mukeyi,
Ciki dai tunda Allah ne ya badashi ai Babu wata Na'imar dazata sakamu kame kamen rashin fadarsa.
Cikin sanyi Sa'adah Dake sin plantains ahankali tace"
Wlh tanada ban tsoro mama,
Komai zata iya,
Dan Allah abar maganar shine yafi zama alkhairi..
Tsoronta kike kenan? "" Cewar haj Karima tana kallon Sa'adahn a zube.
Ba boye boye tace"
Eh wlh Ina tsoronta mama,
Nasan komai zata iyane.
Umma Jamila ce ta kalli Momy dake saka kayanta cikin akwatinta sbd tafiyar da zasuyi Dan ansallamo Sa'adahn suna gidan Haj Karima daga Nan zasu wuce gabaki dayansu duk da sai Sa'adah Takoma gida ta dauko kayan da zatai tafiya dasu,
Cikin mamaki da takaici tacewa Momy"
Yanzu Zainab Haka Kina kallo Kika koyarda Sa'adah tsoron kishiya?
Sbd ke Taki zuciyar ta mutu gurin jinyar mijin daya zaba Taki kishiyar akanki da yarki shine Zaki kashewa yarinya zuciya da tsoron kishiya kina kallo harda bakinta take fadar tsoronta takeyi.
Rashin Jin dadin maganar da ake fadawan Momy yasa Sa'adah kallon Momy da batace komaiba ita sai shiru datai tana cigaba da shirya kayanta cikin akwati,
Ta maida kallonta Kan umma Jamila dake fada cikin takaici zatai magana Haj Karima ta katseta da cewa"
Yi mana shiru mutuniyar banza,
Shiyasa kika kasa gaba Kika kasa baya acikin gidan,
Kinkoma tamkar Yar riqo a gidan ma Matar gidan ba,
Tsabar rashin yanci a bangaren Mahaifiyarsa aka Baki Palo da daki
Bayan ita tanada makeken bangaren guda a gidan da zata aje irinki guda nawa,
Drivers ke janta da motacin Alfarma tana yawo a agarin Abuja da wajenta Amma ke kece kike tuqa kanki Dan kina ganin ansiya Miki tsadaddiyar mota bayan motocin Turakin da ake fita da ita cikinsu daya zata siya biyar din Taki harda canji Mai yawa...
Umma Jamila da Shirun Momy ke Bata ranta ko yaushe tace"
Ahaka me tasamu bare mu iyayenta
22, August 2025
Haura'u
Interested
22, August 2025
Haura'u
Interested