Showing 93001 words to 96000 words out of 106967 words

Chapter 32 - NOOR ALBI COMPLETE BY MAMUGEE

Unknown   

28 Jun 2024

25464

komai...

Fizge fizge Ms Na'ima keyi tana ihun daya qarasa Bata ransa qarshe cikin mummunan bacin Rai ya fizgota ya nufo kofar fita da ita Batareda ya bude Baki yace Mata qala ba Dan iya zafi ransa ya dauka zafi
Bayason aikata abin daba halinsaba na taba lafiyan mace Dan Haka janye Na'iman daga gabansa shine zai basa damar riqe kansa Dan ba qaramin dukan wulaqanci tayiwa Laylahnba...

Fizge fizge take tana qwacewa tana ihun Kiran sunan Laylah
Ta raruma wani qaton flower vase da hannunta daya ta jefawa Laylan tana cewa"

Wlh kin tabo wadda ba'a cin Amanarta tabarwa Allah sai nayi ajalinki harma da gurgun ubanki da uwarki da kowama,
Har Wanda ya daure Miki kikamun hakan bazan ragawa wlh...

Jehota Palo yayi da qarfin gaske ya juya yakoma dakin tareda rufe kofar dakin da key...

Yanaji tanata buga kofa da fashe fashen kayan palon komai tasamu dauka takeyi ta buga a kofar shigowa dakin...

Laylan ya nufa ya daukota gabaki dayanta Yana kallon fuskarta ransa na tsananta baci,
Wani zafi zuciyarsa keyi na fuskarta dayaga gefen bakinta na jini,
Cikin tsananin kulawa yake goge Mata da tafin hannunsa yace"

Are you ok?
Yaya babyn?
Tashi muje asibiti adubaki
Dole zamuga likita yanzun Nan...

Jajir idanuwanta sukai takasa Koda dago Kai ta kallesa bare ta bude Baki tayi mgn sbd radadin da zuciyarta keyi na abubuwan da shikenan sun fito fili Allah ne kawai yasan abunda zai faru Kuma yanzu.

Riga da wandon pyjamas da Abayar datazo da ita tayi sallah da asuba ya saka Mata kafin ya shirya cikin black Rugby's ya kamo hannunta
Fuskarsa babu alamar rahama ko kadan ya kamo Laylan ya shigar da ita jikinsa har lokacin takasa qwaqwaran motsi bare magana ya bude kofar dakin...

Kallo daya yayiwa yanda tayiwa palon mummunan tashin hankali ya dauke idonsa
Tana ganinsu tayo kansu gadan gadan da qatuwar qwalban glass a hannu ta tunkari ckin Laylah......

Ba zato taji saukar lafiyayyan gigitaccen Mari akan kumatunta daya sata faduwa kwance qasa ya sakar mata...

Sakin hannun Laylan yayi Tareda kallonta fuskarsa a matuqar hade yace"

Wuce kintafi Ina zuwa.

Kamar mai naquda tafara daga qafarta ta wuce gaba...

Ms Na'ima ta Kuma zaburowa tana sake damqar kwalban ta jefawa Laylan ya tare da hannunsa take qwalban ta yankesa sosai jini yafara fita a hannun Amma Bai tsaya duba hakan ba ya kalli Laylah data tsaya cikin tashin hankali tana kallon jinin dake zuba a hannunsa yace"

Kije I will handle this.....

Rike Na'ima data taso tana ihun Kiran sunan Laylan yayi yafara Jan hannunta ya sauko da ita qasa ya fito da ita daga bangarensa ya nufi nata bangaren da ita tanata faman daga murya da fizge fizge Bai tsaya da ita koinaba sai cikin palonta ya saki hannunta tareda kallonta da idanuwansa dasukai jajir da wani razanannan sauti da bai taba fada acikinsa ba yace"

Idan Kika fito daga bangaren nan Zakiga hukuncin dazan iya dauka....

Cikin rufewar ido da masifar dake cin koina acikin jininta ta nufi kofar ko gani batayi tana cewa"

Zandawo kanka idan nagama da qaramar karuwar Dana kawo maka cikin gidana.......

Cikin bacin ransa Dake sake bayyana da kalman datake fada da fushi cikin muryarsa Mai amsa amo yace"

I dare you.....ki fita kofar Nan idan kin Isa...

Kafar ta nufa batareda ta tsaya saurarensa ba Dan kuwa Bata Gane komai bayan ganin Laylah a hannunta...

Haj Zinat data iso gidan a gigice da wani irin sauri tayi saurin riqeta ta dawo da ita tsakiyar palon cikin tsananin firgici da ganin irin tashin hankalin Dake gudana....

Jini a jikin Turakin na hannunsa dayake fita duk ya Bata jikinsa Dana Na'iman
Hankali tashe take kokarin riqe Na'iman tana cewa"

Na'ima Dan Allah ki nutsu ayi Abi komai a hankali.....

Gabaki daya ciwon Na'iman yagama tashi Babu yanda zata iya tarota Saida Allura Dan gashi ita kanta Na'iman tajiwa kanta ciwuka da glasses Dan Haka ta riqeta da qarfi tana Kiran sunanta.

Juyawa yayi ya fice batareda yabar bangaren gabaki daya.

Kai tsaye bangarensa yakoma ya sauya Kaya yafito yana Kiran Laylah a waya ta fito zuje asibiti.

Sai alokacin ta iya fasa kuka Mara sauti sosai tana Jin rashin dadin zuciya,.

Kashe wayarsa yayi tareda nufo Sashen Annen Yana kiran dr Meenah a waya yace tazo gidan yanzu.

Kuka take sosai ko daya shigo dakin
Tana hada Ido dashi tasake Jin radadinta na qaruwa sbd ganin yanayinsa tasan baya cikin dadin zuciya da kwanciyar hankali shima
Ga rauni a hannunsa.

Zaunawa yayi gefenta tareda Kama hannunta ya riqe kawai batareda ya iya cewa komaiba sbd Sam ba Dadi cikin ransa,
Baisan Na'ima d iya duka wannan tashin hankalin ba,
Baiyi tunanin zafin zuciyarta yakai hakan ba,
A qataice baiyi tunanin iliminta da wayewanta zasu Bari ta iya wannan abin ba.

Isowar Dr Meenah yasashi fita yabasu guri.

Kallonta Dr Meenah tayi tana son tambayarta lafiya Amma sbd Turakin Dake jiran aduba aga lafiyanta Dana cikin yasa tayi abunda yakawota Kai tsaye ba Bata lokaci.

Fitowa tayi Tai Masa bayanin Babu wata matsalar kawai raunin bakintane daya fashe sai fuskarta data dan kumbura tayi ja sbd kyawawan Marin da Ms Na'ima tayi Mata
Haka Yan ciwukan kawai tayi Mata treating ta tafi.

Bazai iya barin sashen Annen ba sbd Bata Nan Na'ima zata iya zuwa Dan Haka Yana fitowa ya tabbatarwa dasu halima karsu Bari kowa ya shigo Sashen idan ba Anne ce tadawoba ya juya ya fice.

Koina na palonsa a hargitse yake sbd Babu abinda Na'iman ta ragawa duk tabi ta fasa komai Dan Haka a palon qasa ya tsaya Dr faruk yazo gida yaduba nasa raunin akai dressing tareda abubuwan dasuka kamata ya tafi.


*****Allura Haj Zinat ta fidda Jakarta da sauri tayiwa Na'iman da sauri sbd yanda jikin Na'iman ke rawa sosai da tashin hankalin datake ciki..

Tana yimata allurar dukkanin jikinta yayi Sanyi ya saki
Ta jata zuwa bedroom dinta ta kwantar Kan gado
Sai alokacin Ms Na'ima tasake wani irin kuka Mai tattareda ciwon da zuciyarta ke Mata.,

Ba'a taba cin Amanarta ba arayuwarta sai yau,
Cin Amana mafi muni Laylah tayi Mata Bayan tagama sanin duk duniya Babu abinda tafi tsana irin cin Amana da zafin kishinta akan Turaki..

Kuka take Yi sosai hawaye na gangara gefen idanuwanta suna Isa har kunnunta
Radadi da zafin datake ji tamkar zasu qarasa Zauta Yar sauran hankalin data rage Mata cikin qwaqwalwa..

Ita kanta Haj Zinat damuwa da baqin ciki Mai girma tashiga ganin yau Na'ima ce ke kuka Haka,
Tabbas al'amarin ya baci Dan Na'ima Bata kuka sbd Allah ya Ara Mata dama dakuma lokaci tana yanda takeso sai yanzu da babban alamari mafi girman mamaki daya samesu..
Allah yasa ba darasin duniya zasu fara ganiba Dan basa fata.

Jin tayi ita kanta wata irin tsana mafi girma da nauyi ta Laylah na sake mamayeta,
Badan sanin girman power da Turaki yakeda itaba da ayau ko ita da kanta saita dauka mataki mummunan gaske akan Laylan...
Ko ahakan tabbas saisun dauka fansar wannan Cin Amanar da wannan toazarcin....

Sam Na'ima batajin zafi ciwukan Dake jikinta da fuskarta datai jajir sbd Girman Marin datasha,

Zafi zuciyarta ke Mata sosai,
Bata taba dauka abin zaizo ahakan ba sbd Koda Zinat ke fada Bata taba yarda da hakan zai tabbataba LAYLAH DA CIKIN TURAKINTA ajikinta,
Abokin mahaifinta, mijin Yar uwarta hakama mijinta ita uwar datai Mata riqon da Matar ubanta batai Mataba...

Yanda Na'iman ke kuka sosai ya Kuma tada hankalin Zinat jikinta duk yabi ya mutu sbd a fili yake bayyane alamarin daki Na'iman sosai sbd Bata taba kawo hakan zai faruba.


Daqyar allurar ta sanyata baccin qarfi da yaji tanayi tana fizga kadan kadan Kuma badan idonta ya daina tsiyayar hawaye ba.

Fitowa Palo Haj Zinat tayi ta zauna tareda Shiga tunanin mafita dakuma yanda zasuyi ta tafi da Na'ima gidanta su samu zuwa ganin likitanta Dan wannan karon abun yayi nisa saisun hada da ganinsa
Daf Na'ima take da bayyanarda haukarta afili asani...

Daga lokacinda Turaki yasani ta tabbata ko ganin Na'iman bazai Bari kowa yasake yiba sai ya nemar Mata lafiya,
Itakuma idan tabari ta warke sarai yanzu suna cikin gagarumar matsala sbd ba kudi a hannunsu sosai,
Komai nasu yayi qasa sbd wainnan fitintinun dasuketa faruwa
Komai tsaya Mata zaiyi.
##MAMUH#


*_Mamuhgee 52_*
A gidan zinat ta wuni tana saqa da warwara,
Ga Na'iman cikin baccin sai Dan fizgawa takeyi lokaci lokaci,
Kanta ya dauka zafi sosai ita kanta yanzu komai ya tsaya cikin kanta,

Na'iman takeson fara dawowa da ita saiti kafin tafara tunanin abin Yi akan Laylah tun kafin afara Ankara da halinda suke ciki.

Sai dare tabar gidan bayan tabawa siddika kyakkwan gargadi akan kula da Na'iman karta Bari ta fita idan ta farka.


*****Laylah ma a daki tayi wunin ranar idanuwanta sun kumbura iya qarshe sbd kukan datasha,
Gabaki daya kewa da kadaicin rayuwa takeji gashi ta kashe wayarta sbd Kiran da Abban keyi Mata cikin damuwar halinda take ciki sbd yakasa yarda da lafiyarta kalau...

Abinci ma kasa ci tayi Haka ta wuni cikin damuwa,
Gab da magriba Anne tadawo ta tadda wannan tashin hankalin sbd zazzabin gaske daya sauka ya rufe Laylah Dake dunqule a daki jikinta na rawa.

Fada sosai Anne taringa Yi Akan su halima Basu kirataba sun sanar da ita abun dayake faruwa ta dawo..

Ba Bata lokaci ko zama bataiba ta Kira dr Meenah tace ta taimaka tadawo tasake duba musu laylan.

Koda Dr Meenah ta iso da daddare jikin Laylan yayi tsanani sosai da zazzabin,

Magani aka Bata tareda tea Mara zafi Sosai
Dr Meenah na tafiya ta ringa zuba Amai a gabaice.

Damuwa sosai Anne tashiga ta Kira Turakin a waya ta sanar dashi yace a a shirya Laylan ta fito zasuje suga wani likitan.

Da Taimakon Ruky ta shirya suka fito ta kaita har jikin motar dayake zaune Yana jiranta da kansa zai ja motar Wanda rabonsa da driving bama zai iya tunawaba.

Dr Dawood sukaje ya dubata daqyau harda scanning yayi Mata ya tabbatar musu da lafiyan babyn kalau
Bp dintane kawai ya hau sai zazzabin sosai dayake damunta da rashin qarfin jiki na galabaitan datai.

Maganin bp na masu ciki yabata Suka fito Yana riqeda hannunta Suka dawo gida.

Yanayin da ake cikine kawai yasa yabarta Takoma bangaren Amma yanajin yanayinta a zuciyansa.


A Daren kusan dukkaninsu kowa kwanan damuwa yayi sbd Babu Mai cikakken dadin zuciya..

Washe gari tasamu saukin jikinta sosai saidai gabaki daya tashiga damuwa da sanyin jiki
Babu abunda takeso bayan zuwa gida ko zata samu kwanciyar hankali kafin tadawo idan mum ta sauko sbd tasan mum bazata taba Bari ahaka ba sai tayita kokarin Daukan mataki akanta shiyasa gabaki daya take cikin sanyin jiki da damuwa..


Qarfe goma na safe Anne ta nufa Sashen Na'ima sbd dubota dakuma magana da ita sbd tasan wannan Shirun nata bayan abinda yafaru bana lafiya bane.

Siddika ce ta tarba Annen cikin tsananin girmamawa tareda sanar da ita Ms Na'iman tana bacci magani Tasha sbd ciwon Kan data kwana dashi.

Kallonta Anne tayi cikin jinjina Kai tace"

Idan ta farka kizo ki Sanar Dani Zan dawo na dubata nakuma Yi magana da ita,
Allah ya sawwaqa yabata lafiya.

Amin" Siddika tace tana kokarin bawa Annen Hanya sosai ta wucewa.


Shigowar Haj Zinat yasa Annen dan dakatawa tana kallonta.

Cikin tsananin girmamawa Haj Zinat ta qaraso tana gaida Annen cikeda biyayya tana qarawa da cewa"

Na'iman ta tashi ne?

Aa Bata tashiba ance Bata jima da komawa bacci ba Tasha magani ne,

Cikin nutsuwa da bayyanarda Mahimmancin maganar da zatai da Na'ima idan ta farka Anne tace"

Zinat ki kula da Aminiyar taki sbd nasan halinta da zafi da fitina,
Tabbas akwai rashin kyautawa aciki Amma Kuma yanayin ne duk yazo ahakan sbd Babu Wanda yayi niyar cutatar da ita ko boye Mata komai,
Tun farko itace ta kawowa kanta rashin tsayawa fahimta,..

Turaki Bai boye Mata qarin aurensa ba, nikaina ban boye Mata ba saidai Kuma itace da kanta ta zabarwa kanta waye kishiyar tata
sbd azauna lafiya yasa ba'a sanar Mata ba Dan Babu Wanda ya dauka auren Mai dorewa ne tun farko
Saidai Kuma kaddara da rabo na ubangiji ba'a tsere musu,

Laifi dai anyi Mata na rashin fadar Dan Haka nakeson rarrashinta nabata hakuri duk wannan tashin hankalin zata sakawa kanta damuwane tunda bawa baya wuce qaddararsa....

Laylah Allah yayi dai Matar Turaki ce Kuma uwar yayansa........ Dan Allah kifara tausarta kafin nadawo
Ki Bata hakuri sosai sbd mum Mata laifi mun yarda Amma Inshallah za'a gyara komai....

Mutuwar tsaye Zinat tayi zuciyarta na neman Faso kirjinta tafado tsabar shiga tashin hankali da rudu
Amma dayake gwanace gurin riqe kanta sai Bata bayyanarba ta jinjina kai kawai sbd bazata iya magana ba bakinta rawa yake.

Anne na fita tayi wurgi da Jakarta da keys din motarta tareda dankwalin kanta tanajin kaman zata Ara hauka akaron farko.....

Wane mugun labari ne wannan takeji abakin Anne?

Kallon siddika tayi cikin tsananin tashin hankali tace"

Daidai naji Anne tace Laylah ce Matar Turaki???

Da sauri siddika ta gyada Kai cikin nata zallan mamakin da firgici Dan sai yanzu take sake tabbarda akwai masifa a kwance kenan idan Ms Na'ima ta tashi ta samu wannan sabon zancen.

Zama Zinat tayi tana fifita fuskarta da hannunta Dan wani zafi taji tanaji
Cikin shiga rudin tunani tace"

Tabbas Basu fada Mana cewan Sa'adah Matar Turaki shiyasa shegu tsinannu suka bar Na'iman ta tafi da Laylah wato takai Masa matarsa har gidansa......

Tun farko wane Dan burauban shegen ne Yafada Mana Sa'adahn ce Matar Turaki????" Tafada tana dago da jajayen Idanuwanta ta Dora Kan Siddika da jikinta yafara rawa tana neman zancen fidda Kai tana kokarin magana Zinat ta sauke Mata wasu kyawawan Marika guda biyu tana fizgota tace"

Dama bakida sani akai Kika kawo Mana wannan zancen kokuwa da gayya kikace Mana Sa'adahn ce?

Cikin azabar Marin datasha tafara rarraba Ido tana hawayen tsoro sbd komai zasu iya Mata tunda tafi kowa saninsu ba Imani ne dasuba musamman Haj Zinat din tunda har Ms Na'iman itake fada Mata yanda za'ayi komai.

Dukan fita hayyaci Zinat ta ringa yiwa siddikan tana cewa"

Kece Kika lalatamun komai da shirina na shekaru Dana Jima Ina fafutaka akansa,
Matsiyaci wlh zanyi lokacinki idan nagama da Laylan da Na'iman tukuna..

Tattarawa tayi tabar gidan sbd zata iya kashe siddikan idan Bata bar inda take ganintaba,

Sabon tashin hankali tashiga na musamman sbd na farkon duk Mai saukine a daukansu cikin shege ne jikin Laylan ba Turaki Dan Haka komai zaizo da sauki,
Amma Jin Laylah Matar Turaki ce yasata Shiga matsananciyar tashin hankali sbd Dan halak ne wato zata Haifa masa,

Magajinsa fa kenan??

Magajin dukiyar dasuka Dade suna shirka akanta Dan su mallaketa koba dukaba su mallaka Rabin,

Magajin dukiyar da akanta taketa durawa qawarta dasuka taso tare tun yarinta maganin data juyar Mata da qwaqwalwa ita ke controlling dinta....

Amma ace Rana tsaka wata qanqanuwar yarinya ta samesu daga sama Bayan tagama lalata mata komai na wargaza gashi sanadin hakan Turaki zai iya gano halinda Na'iman take ciki Wanda Yana ganowa tasan labarinta yaqare daga Nan Kuma...

Wlh bazata yardaba,
Komai zata iyayi dan ta tsira,

Yanzu babban burinta ta fito da Na'ima daga gidan,
Sbd sai Na'iman Bata gidan zata samu damar kawar da Laylah da cikinta daga duniya Kai tsaye sai laifin ya rataya Kan Na'iman wadda ita Kuma takardun shedar haukanta zaisa hukunci bazai hau kantaba
Dan Haka duk tsanani saita fidda Na'ima daga gidan
Kuma zata fiddatane daga gidan ta hanyar da Laylah zata daga hankalinta itama ta fito daga gidan.


Washe gari da gangan tana sane taqi zuwa gidan sai dare tazo
Lokacin Na'ima ta farka Amma Bata iya komai sai Ido datake Binsu dashi Haka ta sake sakarwa Na'iman wata allurar data sake maidata halinda ta fito idanuwanta suka rufe Takoma baccin wahala.

Fitowa dakin tayi siddika na biye da ita Saida suka zo palon ta kalli siddikan cikin bayyanarda Mahimmancin aikin da zata sakata ta kalleta tace"

Aiki Mai mahimmanci Zan sakaki
Idan Kika Bata mun aiki wannan karon Wlh yanda na maida Na'ima fin hakan Zan maida rayuwarki,kina Jina????

Gyada Kai tayi tana cewa"

Zan kiyaye Wannan karon.

Ciro qaramar kwalba daga jakar hannunta tayi tareda qaramar lighter ta miqa mata..

Karba siddikan tayi tana bude idonta akan kwalban da warin fetir ke tashi acikinta
Ta hadiye wani mugun yawu tana kallon kwalban da lighter din cikin rawar murya tace"

Wannan fetur.....

Katseta tayi da cewa"

Nafiki sani tunda nice nabaki,

Anjima da daddare ki zuba a akan gadon Na'ima Kuma ki zuba Mata kadan a jiki saiki janyota ki fito da ita daga bakin kofar dakin ki kunnawa dakin wuta,

Karki Kira jama'a sai wutar taci sosai Kuma ki tabbatarda ta shaqa hayaqin wutar saiki fita ki Nemo jama'a,

Kafin akirani idan antambayeki garin Yaya kice itace ta kunnawa dakin wuta da kanta tana cewa kunnawa gidan wuta zatai kowa ya mutu har Laylah.

Tsananin tsoro da mamakin girman rashin Imanin Zinat din da zata cutatarda Ms Na'ima sbd son abun duniya..

Cikin sake bayyanarda zata iya Mata abinda tace zatai Mata idan ta Bata Mata aiki tace"

Idan Kika aikata kuskure daya komai ya lalace wlh ke Zan cinnawa wuta kifara Isa lahiran kafin muzo.

Wucewa tayi tabar siddikan tsaye tana binta da kallon mummunan tsoro da tashin hankali...

Kasa zuwa kitchen tayi da fetir din ta nufi dakin Ms Na'iman dashi ta boye bayan Kan gadonta tana kallon fuskarta...

Akaro na farko da Tausayin Ms Na'iman ya ratsata sbd batada Mai qaunarta bare yabata shawara,

Tayi watsi da qanwar mahaifiyarta data riqeta sbd samun duniya a hannu gashi yanzu tazo tana neman Rasa komai...

Duk da Ms Na'ima Bata kyautata Mata saima izza da bossing dinta datake koyaushe Amma Bai kamata a cutatar da ita hakaba abun yayi yawa bayan arzikin dasuke ci suna Tarawa daga Haj Zinat din har ita duk qarsqashin Ms Na'iman suke samunsa...

Itadai gaskia bazata yarda tayi biyu babuba wlh ta koma rayuwar wahalar data fito,
Dan gwara Mata wulaqanci da masifa harma da bala'in Ms Na'ima akan barin gidan AB TURAKI Dan Haka Dole zatasan yanda zatai bada saninsuba ta bayyanarwa da Anne ko Turakin lalurar da Ms Na'ima take dauke da ita ko za'a rabata da Zinat a cetota tasamu taci gaba da cin arzikinta lfy kafin Zinat din ta wargaza musu Suma komai.


Ba yanda ta iya da daddare Haka ta cinnawa dakin wuta
Aikuwa wuta Mai qarfi ta tashi wadda batama tsammata ba
Tsoro ya kamata ta fito da gudu tunda wuri ta nema jama'a sbd wutar kamar jiratake a kunna koina yafara dauka.



Hankali tashe securities da kowa gidan ya fito,
Anne na dakin Laylah a Daren sbd wani zazzabin datake fama dashi na damuwar Dole data sakawa kanta,
Gashi taqi yadda ko ganin juna suyi da Abban nata sai zaman boyo take a daki duk ta Hana kanta sukunin zuciya shima ta hanasa sbd rashin ganinta yafi komai daga hankalinsa ita kanta rashin ganin nasa ne yaketa nukurkusanta.

Jin

22, August 2025
Haura'u

Interested

22, August 2025
Haura'u

Interested

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login