Showing 102001 words to 105000 words out of 106967 words

Chapter 35 - NOOR ALBI COMPLETE BY MAMUGEE

Unknown   

28 Jun 2024

25437

har wani irin rawa yake tana cewa"

Nafada nakuma fada wannan itace muguwar qaddarar rayuwarki Zainab Dake da 'yarki Kika qi Jina ga irin kyakkwan sakamakon data nuna na cewan ita jinin Mahmoud da uwarta ne,

Mahmoud ne da matsiyacin Kawun can suka daure gindi akai wannan gagarumar cin amanar ta sauyawa Sa'adah Miji a daurawa wannan maciyar Amanar butulu wadda Bata gade alkhairi,

Tsawon shekaru Muna dakon aure Sa'adah keyi shine sai yanzu kike sanar damu riqonta akeyi a gidan turaki¿
Kutumar uban riko duk inda yake
Wlh yau Mahmoud saina wanke Masa allon rashin mutinci.

Haj Karima dataga mutuwa tsaye da baqin cikin zamtowar Momy Yar uwarta murya cikeda baqin ciki tace"

Allah ya Isana tsakanina Dake zainab,
Wlh ban dauka lalacewar da mutuwar zuciyarki yakai wannan zarafinba Dan kuwa ke ko ajikin danginmu kinfi kowa zama asararrar,

Miji ya cuceki ya aura watacan daban bada saninkiba harda haihuwar asara Amma Kika kasa rabuwa dashi saima zaman jinyar nakasasshe,
Keda yarki kuka Gama zama 'yan maula shine yanzu anyi wannan Cin Amanar an rufemu kema Kika biye aka ringa binmu da kallon shashashu gamu Yan iskan iska wato,

To wlh kuwa Zainab daga yau babuni Babu ke,
Dan kin Haifa mace mun nuna munasonta muna fatar tayi aure gidan hutu taj dadi shine muka zama makiyanki kika biye musu aka rufe mu wato mu makwadaita..

Tsabar baqin ciki daya Gama rufe idon umma Jamila sake fizgar Laylahn tayi batareda la'akari da cikin dake jikinta tayo palon waje da ita inda ta tabbatarda Mahmoud na Nan

Ido rufe ta saki Laylahn agabansa tareda kallonsa cikin tsananin baqin ciki da bacin rai tace"

Mahmoud kaji kunyar duniya saura ta lahira wlh,

Duk cin Amana da quncin daka saka zainab akan uwar yarinyar Nan Bai issaba ta kashe rayuwarta gurin jinyar Maci Amana irinka duk da hakan Bai isaba shine yanzu aka tozartata ta hanyar aurar da 'yarka ga Wanda kakeso bayan Sa'adahn ce babba qarshen wulaqantawa kowa na Mata kallon Matar aure sai yanzu ace wannan ce Matar ita riqonta akeyi...
Shin Mahmoud kana ganin Sa'adahn ta cancanta hakan daga gareka?
Kokuwa ita 'yarka bace musani wannan ce kawai yarka???

Abba shiru kawai yayi Mata baice komaiba sbd jikinsa da yayi Sanyi da abinda tayi din gaban Wanda yakeda matuqar mutunci da girma a idonsa Kuma uban 'dan cikin datake kokarin aibantawa.

TURAKI kuwa Dake zaune tareda Abban shigowarsa kenan
LAYLAH daya riqe jikinsa Lokacinda ta sakota zata Fadi yake kalla idanuwansa sun sauya take saidai yanayin Shirun da Abba yayi dakuma Laylan da idanuwanta suke rufe tana tsiyayar hawaye batareda ta iya dagowab ya sanyashi dakewa kamar baya gurin ya miqe tsaye da kyau sai alokacin ta waiwayo ta kalli Wanda ke zaune Tareda Abban batace komaiba ta juya ta fice tana Jin zuciyarta Kamar zata tafashe tsabar baqin cikin dasuke ciki yau.

Mahmoud ya haifar musu masifa
Ya haifar musu bala'i.

Acan cikin Koda ta iso Momy kuka takeyi sosai na irin cin zarafi da maganganu masu dacin gaske da Haj Karima ke fada Mata,
Umma Jamila Jin tayi ta tsani momyn da Sa'adahn gabaki daya Dan Haka komai bazata iya cewaba ta fizgi Jakarta tayi gaba tana cewa"

Har ababa bazaki sake ganinaba a gidanki zainab,
Kin zabi namiji kinbar Yan uwanki Zaki Kuma ganin sakamon da Zaki samu daga garesa.

Fita sukayi Haj Karima kuwa duk wata alaqarta ta yanke da momyn daga ranar taje sunbarwa Mahmoud ita.

Bayan fitarsu sakinta Turaki yayi Ahankali tareda kallon fuskarta a shaqe ya iya cewa"

Je ki shirya kifito zamuje ganin likita.

Batada karfi ko tunanin tsayawa musu Dan Haka ta juya Takoma ciki mararta har murdawa takeyi sbd tsabar dacin zuciya da damuwa Mai qarfin gaske data shigeta.

Kusan koina batada farin jini qinta suke kamar tabar duniyar su daina ganinta.

A Palo Momy kuka takeyi sosai Mara sauti Wanda yasa jikin Laylah qarasa yin sanyi hawayen dake idonta Suka fara saukowa suna gangara,

Tasan radadi da 'dacin kalaman dasuke fadawa Momy tun ba yanzuba basa fadar kalma Mai Dadi akanta sbd batada abun duniya,
Sun kasa barinta taji ta runguma kaddarar rayuwar aurenta koyaushe cikin sakata qunci suke fa kalamansu.

Batada iko ko damar bin gaban momyn sbd kada ta qara Mata quncin zuciya ta sanadin ganinta tunda ko yanzu itace silar da hakan tafaru.

Daki tashige cikinta na juyawa tareda Mararta sake ciwo kadan kadan.

Zama tayi bakin gadon da anty Sa'adah ke kwance har lokacin tana bacci cikin nutsuwa
duk hayaniyar da akai Bata tayar da itaba bayan Kuma batada wani nauyin bacci.

Bata iya sauya kaya ba sbd juyawar dataji cikinta yakuma Yi Dan
Abaya kawai ta dauro akan doguwar rigar Dake jikinta Mai qaramar hannu.

Tareda Ruky ta fito suna Isa jikin motar Abba yace Ruky tayi zamanta sbd Turakin nema da kansa ya karba tukin A Abdoul zamansa zaiyi gida su sake gaisawa da Abbansu Sa'adahn.

Kallonta abbanta yayi cikin kulawa da qauna Mai tsanani yace"

Zainab¿

Dakatawa tayi tareda waiwayowa ta kallesa da Idanuwanta dasukai jajir saidai takasa amsawa,
Zuciyarta nauyi take Mata sai kawai hawaye Suka gangaro Mata ta kallesa cikin kauna ta mahaifi.

Laylah ki kula kinji,
Allah yasa muji alkhairi,
Karki damu da maganganunsu komai lokakacine dashi idan Kika tafi Babu Mai sake ganinki acikinsu.
Karki damu kinji?

Ahankali jiki amace ta gyada masa Kai tareda shigewa motar suka fice daga gidan yana kallonsu.

Hannunsa daya yakai ya riqe hannunta Dake aje Kan cinyarta zuciyarta wani irin nauyi da harbawa take mata dayasa takejin rashin nutsuwa Sosai.

Kasa dagowa ta kallesa tayi saima mutuwa da jikinta yayi har suka Isa lafiyayyar 5star hotel din daya sauka suka Isa qaton dakinsa dake floor din sama karshe.

Zaunar da ita yayi kafin ya zauna gefenta sai alokacin ta dago ta kallesa ya Dan rintse manyan idanuwansa dasuka sauya haryanxu Basu koma yanda sukeba sbd har lokacin zuciyarsa radadi da zafin abinda akai Mata sukeyi.
Kasancewarsu Mata Kuma harkan family yasa Bai tunanin daukan matakiba ko kadan saidai Kuma tabbas bazata sake zuwa duk inda dangin momyn sukeba,
A qataice za'a Samar Mata da nata gidan daban ta yanda idan tazo zata ringa zama acan kafin tagama kwanakinta ta tafi duk da ko zuwanma bayajin akwai ranarsa kusa matuqar ta koma.,

Shi gabaki daya wannan yawon ya ishesa tattara matansa zaiyi yakoma US hankalin kowa ya kwanta.

Dr Amatullah ce tazo har hotel din taduba Laylah Babu wani matsalar komai sai damuwa data sakawa kanta Wanda ya hawar da bp dinta shine yasakar Mata cin Dan ciwon Mara gashi Daman cikin yashiga wata bakwai yanzu.

Bayan tafiyar Dr Amatullah magani kawai ta iya Sha taso zuwa gida Amma ya hanata saita cire Mata kayanta da yayi sukai sallar magriba,
Daqyar ta iya Shan tea kawai sbd hakanan komai batajin dadinsa zuciyarta takasa samun nutsuwa
Suna Gama sallar isha baccin Dole ya dauketa sbd cikin maganin da aka Bata hardana bacci sbd yanayin datake ciki duk tabi takasa samun nutsuwa.




********Qarfe biyu da mintuna ashirin cif na dare baqar motar Honda ta Parker bayan gidansu Abban daga nesa.

Haj Zinat ce zaune aciki tareda Na'ima data Gama bankawa wasu irin mahaukatan qwayoyi masu qarfin gaske dasuka qarasa buga qwaqwalwar Ms Na'ima gabaki daya sai abinda Allah ya rage..

Tana cikin motar zaune yaran datazo dasu Suka fita Suka tunkari gidan.

Babbar katangace kewaye da gidan gakuma security electric wire Dake zagaye da katangar Amma Haka Suka zagayafa suka fara disconnecting CCTV cameras Dake zagaye da bayan gidan kafin suka kame katangar Suka fada gidan sbd qwararrine a harkar na karshe.

Mintuna kusan goma Sha shiga da fadawarsu gidan wuta ta tashi take koina tafara ci Kuma tako Ina.

Masu gadin gidan guda biyu Koda suka Ankara Suka firfito tuni wutar takama sosai Tako ba halin tunkarar ciki Dan Haka Suka fito waje suna neman daukin jama'a a fito.

Yanda wutar ke ci sosaine yasa jamaar dasuka fara firfitowa ihun neman agaji da taimako.

Momy da Allah yasa tanada rabon fitowa Daren a gurin Abba ta kwana sbd tashiga quncin da Bata taba Jin zuciyarta tashigaba a ranar,
Maganganun Yan uwanta sun Kama sakata cikin tsananin dacin zuciya da kunci Wanda yasa Abba da kansa ya kirata dakinsa ya zaunar da ita tareda qasqantar da kansa yabata hakuri sbd koma menene shine suke ganin ya cutatar da momyn.

Yanda ya qasqantar da kansa yakuma Bata zabin idan shine matsalarta da baqin cikinta idan tanaso zai sauwake Mata taje ta shirya da Yan uwanta idan tanaso.

Kalmarsa tasata sake Shiga mawuyacin halinda yakaisu ga shiryawa a Daren harma ya sauke Mata haqqinta na aure da sukafi shekaru masu yawa Basu samuba.

Wutar zafi da tsananin hayaqi ya sanya Abban fara farkawa yaga wutace takeci harta fara shigowa dakin dasuke sosai.

Tayarda Momy yayi yace tayi maza idata keda lafiyayyan kafafu ta fita takira su Sa'adah su fito.

Gigice Momy ta tashi tana tarin hayaqin daya fara fin karfinsu tana kokarin kamasa su fita ko Babu kujerarsa tunda Amma yayi Mata nauyi Dan haka yace ta sakesa taje ta dubo su Sa'adah idan wutar batakai can ba.

Kasa tafiya tayi tabarshi Dan Haka tafara jansa cikin wutar cikin tsananin azaba wutar Dake cinsa din suna kaiwa kofa ya turata waje da sauran qarfinsa daya rage.

Kokarin dawowa takeyi Amma wutar taci karfi ita kanta take kanta yafara juyawa sbd haqayqi da zafi Bata gani batansan inda kanta yakeba Haka taita jefa qafa har wutar taci karfinta ta Fadi a inda take.


Wuta Kam sosai takecin gida tako Ina ba damar Shiga ceto sbd tagama mamaye koina na gidan...

Kallon Ms Na'ima Zinat tayi bayan tasake wani mamalacin murmushin kawarda matsalar Laylah a rayuwarsu tace"

Na'ima kinga ga wutar gidansu Laylah can tanaci suna konewa jeki ki tabbatarwa idonki.

Bude mota tayi tareda janyo Na'iman ta fito Kai Tsaye kuwa ta nufi gidan ta wuce jama'a tana cewa"

LAYLAH Kinga sakamakon cin Amanar da kukaimin Nan....
Turaki nawa ne Ni daya bazai taba zama nakiba kije lahiranki ke daya.....

Kallonta jama'a Suka fara cikeda son tabbatarda abinda take fada sbd kuwa idan itace jefata zasuyi a wutar kafin fireservice sugama kashe wutar....

Juyawa tayi tabar gurin da sauri kamar yanda Zinat ta sanar da ita karta Bari a kamata aikuwa tana zuwa da gudu ta fada motar suka ja sukabar gurin,

Murmushi Haj Zinat tayi sbd dama burinta da amfanin tura Na'iman sbd aganta asamu shaidar itace ta kunnawa gidan wuta,
Itace tayi kisan kenan Kuma takardunta na hauka bazata taba bayyanardasuba sbd kafin agano Na'iman batada lafiya ta Jima a gidan yari ko lahira shikenan ta rufe babin Turaki da matansa duka,
Dukiyar Na'iman dama tajima da zama tata, batada sauran wata matsala a rayuwar Kuma.
##MAMUH#



*_Mamuhgee 56_*
Cikin bacci Kiran A Abdoul yashigo wayarsa,
Baya kwana da waya a kunne Amma ranar mantuwa ta sanyashi kwana da wayar a kunne.

Dayake baccinsa baiyi karfiba sbd Laylan daketa firgita cikin bacci gabaki daya ta kasa kwantar da hankalinta Kan abunda yafaru..

Daukan wayar yayi da mamakin ganin Kiran karfe hudu saura na dare.

Cikin tashin hankali da firgici duk da Yana kokarin controlling kansa Amma yakasa akaro na farko daya fasa kuka arayuwarsa gaban Turakin yace"

Turaki wutan gobara ya tashi a gidansu Sa'adah,
Abbansu da Sa'adah da sauran masu aikin duk sun.... Kasa qarasawa yayi sbd kuka Mai qarfin gaske dayake Yi.....

Da sauri Turakin ya miqe Yana zare Laylah daga jikinsa ya sauka daga Kan gadon Yana cewa"

Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Innalillahi,
Ganinan zuwa yanzu,
Masu kashe wutan sunzo?
Dan Allah ayi gaggawar fidda kowa daga gidan ganinan zuwa yanzu.

Jallabiya fara qal ya janyo ya saka Yana kokarin daukan keys ya fice Laylah Dake kwance tana jinsa ta tashi zaune gabaki daya jikinta yagama mutuwa ta kallesa daqyar ta iya hada kalmar"

Gidansu Abbane yakamata da wutan?

Dakatawa yayi batareda ya waiwayo ba yace"

Ki jira zanje na dubo.

Ficewa yayi yabarta zaune takasa ko qwaqwaran motsi sbd jikinta yagama Bata gidansune gobarar,
Wanna quncin dataketa faman ji tun safiyar ranar na wani abun ne kila zai samesu.

Yaye rufarta tayi tareda zuro qafafunta ta sauko dasu qasa ta miqe tsaye ahankali sbd bayanta dayake riqewa.

Kujera ta nema ta zauna tareda qurawa kofa Ido tana sake Shiga tsoro da fargaba.



Ko daya Isa hankali tashe wutar saura kadan agama kashewa gashi har anafar Kiran sallar fari a wasu masallatan,
Cikin tsananin tashin hankali da firgici daya Shiga shima yake tambayar Ina mutanen Dake gidan...

Momy da Abba da aka samu damar fitarwa da sauran Rai kawai aka nuna Masa sauran kuwa Babu Wanda Allah yayi zai fita wutar.

Wani mummanan jiri ne ya debesa aka taso za'a riqesa ya dafa motar Dake bayansa Yana cewa"

Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Innalillahi wainna ilaihirrajiun

Ana Gama kashe wutar ba'a samu damar fidda gawar jamaar gidanba saida gari yayi haske sosai aka jeresu su uku.

Momy da Abba sun kone sosai ta yanda gabaki dayansu sun sabule musamman Abba har gwara momyn,

Daukarsu su tun kafin sallar asubar aka nufi asibiti dasu cikin gaggawa.

Sauran gawarsu Sa'adah ma asibitin aka nufa dasu.

Halinda A Abdoul yake ciki yasa hankalin Turaki sake tashi sbd Laylah komai itama zai iya faruwa da ita tana samun wannan mummunan labarin.

Haka yadawo jikinsa Babu inda baya rawa da tashin hankalin al'amarin...

Yana shigowa tana zaune inda take sallah kawai ta iyayi daqyar tadawo ta zauna tana jiran tsammanin dawowarsa.

Kallo daya tayi Masa ta sauke Kai sbd wata Ajiyar zuciya data tsinke mata batareda tasan Kota mececeba.

Qarasowa yayi ya wuceta yashige toilet yayo wanka sbd kayan jikinsa dasuka naci.

Bayan yafito Babu Wanda yayi magana acikinsu Saida ya shirya ciki suturarsa kafin ya zauna ya kalleta cikeda tsananin tausayinta da sonta,

Baya kaunar dagula zuciyarta da wannan mummunan labarin Amma Kuma Dole za'a a sanar Mata Dan Haka tea tafara Bata ta karba n
Ba musu ta Sha rabi ta aje cup din.

Magani ya sauka ya Bata shima ba musu ta karba ta shanye.

Kallonta yayi cikin kulawa da nutsuwa Yana Kuma kamo hannunta ya riqe Gam cikin nasa yace"

Qaddarar gobarace ta fadawa gidan acikin daren Amma....

Dan shiru yayi Yana jinjina girman munin labarin yace"

Kiyi hakaru ZAINAB bawa baya wuce kwanakin da ubangiji ya dibar Masa.....

Bata motsaba har lokacin idanuwanta na Kan bakinsa sbd tariga da tagama qulle zuciyarta cikin wani Hali na tsananin qunci ahankali ta bude Bakinta daya bushe Nan take tace"

Abbana ne ya rasu?????

Girgiza Mata Kai yayi yana kokarin janyota ya rungume cikin bayyanarda tsananin alhinin wannan tashin datayi gana 'yayan mutane dasuka kone daga zuwa aiki murya a karye yace"

Abbanki na asibiti tareda Zainab....

Wani mummanan faduwar gabe ya risketa ta janye jikinta cikin mummunan yanayi da rawar da jikinta yafara dauka tace"

Anty Sa'adah ma na asibitin????

Girgiza Mata Kai yayi Kai tsaye yana cewa"

Kiyi hakuri Zainab
Sa'adah Allah ya karba ranta....

Kafin halinda take Shirin Shiga tashiga wani mummanan ciwon marane yataso Mata gadan gadan cikin tsananin azaba da tashin hankali..

Cikin sauri ya riqota Yana Kiran sunta Amma Ina ciwon nakuda ya taso Mata Kai tsaye ba shiri Kuma lokaci baiyiba.

Cikin gaggawa da wani sabon tashin hankalin akayo asibitin da ita itama
Suna dubawa kuwa Suka tabbatarda nakuda ce bakwaini zata Haifa.

Hankalin Turaki Bai taba tashi irin na ranarba sbd ganin bayan duk wannan abubuwan da rashin rayukan da akai ga Kuma nakudarta alokacinda ake cewa cikin Bai Isa haihuwa.

Koda su Anne Suka iso garin hankali tashe tuni Laylan ta haifi jaririyar 'yarta Yar qarama da ita ansaka cikin kwalban aje yara irinta.

Laylah tasha matuqar wahala sosai gurin haihuwa duk da hakan tana haihuwa abin data fara shine sakin wani tsimammen kuka Mai taba zuciya na rashin Yar uwarta Rabin jikinta datayi,

Kuka takeyi sosai wanda tasaka harsu Annen kuka dasuma dama da kukan rashin Sa'adah sukazo,
Halima tayi kuka har idonta Baya budewa sosai.

A gidan umma Jamila data ringa Suma tana farfadowa Kan rashin Sa'adah da halinda Momy ke ciki akayi jana'izarsu aka kaisu makwancinsu take Kuma aka watse sbd Babu zaman gaisuwar dasu Anne zasuyi.

Iyayen hadiza dasuka zo suma anjaajanta musu wannan babban rashin kafin akayi musu duk wani Abu da akasan ya kamata ayin.

LAYLAH takasa kwantar da hankalinta sbd tasakawa ranta damuwa da qunci sosai.
Halima ma kukan rashin Sa'adah itama bazata iya barinsa yanzuba sbd sunyi wani irin shaquwa da sabo.

A Abdoul ko mahaifiyarsa datazo gaisuwa ta tausaya Masa sosai sbd Allah yasani tasa irin kaunar daukewa juna Kuma ita kanta ta yaba da nutsuwar Sa'adahn.

Anne taso kebewa ta sanarda Turaki maganar Laylah da aka gama tabbatarda itace ta bankadawa gidan wuta Amma ganin yanda komai yake neman cakudewa na halinda Laylah take ciki yasa ta dakata tareda fara Shirin komawarsu duka abuja hardasu Abban da Momy da za'a fitar waje Amma saisun fara Dan samun sauki tukuna.

Suna sauka Abuja daga airport motar asibiti aka dauki su Abba da momy aka wuce dasu
Sukuma da motar gidan Suka tafi Suma asibitin Suka nufa direct aka Kai baby aka Kuma admitting dinta.

Suna Isa gida Babu sauran Bata lokaci Anne ta gabatarwa da Turakin bayanin komai da komai sbd ganin yanda yariga yahau sosai akan tabbacin dasuka samu na Na'ima ce ta tada gobarar sbd wanna karon tabbas zai dawo da ita hankalinta idanma hauka takeyi..

Bayanan Anne da takardun daya gani da bayanin komai yasanyashi Kiran Dr faruk take agurin.

Cikin nutsuwa Dr faruk ya tabbatarwa da Turaki sakamakonsu na alluran da aka samu Sashen Na'iman dama sakamakon qwayoyin maganin allurar dasuka samu ajininta sosai tare Kuma da babbar illarsu ga qwaqwalwarta Dan kuwa zuwa yanzu idan Ana yimata ya tabbatarda qwaqwalwanta yagama juyewa gabaki daya.


Bai taba Jin takaici da baqin cikin kansa ba da rayuwarsa kamar yau daya samu wanna mummunan labarin,

Sakacinsa akanta yasa mummanar kaddarar aminya cutatar da rayuwarta ta hanya mafi Muni,

Meyasa Bai taba tsayawa yayi lamarinta kyakkyawar fahimtaba da zai iya gano lafiyarta da rashinta..

Rintse idanuwansa dasukai jajir yayi kafin ya miqe ya fita yauma da kansa ya ja mota a irin tuqin da Babu Wanda yataba ganinsa yayi ya Isa gidan Zinat Dake haukace tagama hargitsa gidanta koina bataga gwalagwalan Na'ima ba data ajiye ga siddika batanan ta gudu ga takardun asibitin Na'iman ma sun nata
Siddika ta tattara ta gudu.

Haukace take tanajin kamar zata Kama da wuta sbd sune dukiyar Na'iman datake taqamar zasu zama natan tayi arzki dasu Amma Rana tsaka ace ta rasa wlha bazata yardaba neman siddika zata tafi saita nuna Mata ba'a irin wannan gangancin da ita.

Tsallaka Ms Na'ima Dake kwance a qasa tana bubbuga kanta tayi cikin tsananin Azabar abinda takeji suna Mata yawo cikin Kai
Jin kafar mutum ta tsallakata yasata cafke kafar da sauri tana cewa"

Kece Laylah,
Kece Laylah,
Meyasa kikaci Amanata bayan Ina kaunarki da gaskia...
Meyasa?

Haqori tasa ta cafke qafar da wani irin cizo Mai azabar gske.

Ihu Zinat keyi tana dukan Na'iman da qafarta daya Amma Taki saki qafar ga jini sai fesowa

22, August 2025
Haura'u

Interested

22, August 2025
Haura'u

Interested

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login