Showing 81001 words to 84000 words out of 106967 words
muce 'yarmu na auren Amb AB TURAKI,
Alhaji Qarami Babu shige da ficen da bayayi Dan yasamu ganin Turaki shida honourable kwangila sukeso kamar me ko manyan kudi zasu saukar musu Amma koyaushe yarinyar Nan cewa takeyi baya qasar
Ashe tsoron zuwa gurinsa take sbd kishiya,
Wlh Allah yayi wadaran naka ya lalace.
Yanzu dai tagama wannan shashancin mutafi ai muma lokacinmu yazo Dan idan muka tafi zamu bude namu asusun lissafin agurinsa tunda ga ciki
Kafin ki dawo saikin haihu tunda ba qasar yake zamaba Kuma kingama karatun ai dama Dan Haka muma Bismillahi.
Daga Sa'adahn har momy Babu Wanda yasake cewa komai,
Suna sauraron su umma Jamila nata musu fada kokuma fade da gorin dawainiyarsu dasuke Dan taimakawa tun lokacinda Sa'adahn na qarama da Abban baya wani zama har lokacinda yake jinyarsa sune suke Dan taimaka musu.
Har dare daga ita har momyn Basu huta da fadan umma Jamila ba Saida Haj Karima ta tsayar da zancen da cewan ai yanzu tunda Sa'adahn na hannunsu zasu qaru da Turakin.
Da wannan umma Jamila ta sarara musu har drivern Anne yazo ya dauki Sa'adah a gidan Suka tafi gida.
Tana Isa gida komai na dakinta halima ta gyara ko'ina sai qamshi da sanyin AC ke tashi Bata wani zauna ba ta shige ta kwanta sbd kunyar Anne takeji batasan Mai zatace Mata gameda cikin Nan da Allah yayi bayyanarsa gaban kowaba,
Takardar acikin hanbag dinta dasukaje asibitin tun wancan lokacin take Kuma tunda tadawo take boye hanbag dinma gabaki daya sai ranarda zata fita ta janyota ta fita da ita Kuma ranar ne tsautsayi yahau kanta har tayi murnar Babu Wanda yagani a jakar shiyasa takuma boye jakar sai yanzu Allah yanufa zancen zai fita,
Kunyar Anne datake ji shine na boye Mata itama Basu fada Mata ba bayan ta cancanta tasani sbd yanda ta daukesu tamkar jininta
Kuma tasan idan Annen tasani Babu yanda zatai tabari a cutatar da Laylan gashi rashin wayonsu yasa tasamu zancen daga sama gashi taqi cemata komai akan zancen
tamaqi tayarda zancen tayi kaman ba'ayiba.
Kwantawa tayi tareda neman numbern Laylah wadda yanzu laulayinta yafara yawa ba komai take iya ciba sai fruits datake Sha kaman me,
Ringing wayar taitayi baa dagaba Dole ta hakura ta qyaleta.
Washe gari jirgin safe zasubi Dan Haka tunda safe ta tashi ta shirya Kaya cikin qaramar suitcases guda biyu ta shirya tafito sbd driver na jiranta zai kaita gidansu Haj Karima dagacan zasu dauka su umma Jamila su wuce airport Abba daban zaiyi tafiyarsa ba taredasuba saiya gana sosai da Amininsa duk da kusan kullum tunda suka zo Abujan suna tare.
Anne cikin kulawa Tace Mata ki kula Sa'adah kinji,
Allah yadawo Dake lafiya duk da nasan Zaki kwana biyu sosai acan kafin kidawo.
Rumgume Annen tayi jikinta na sanyi tace"
Zanyi kewarki Anne,
Kuma Inshallah bazan Dade sosaiba Zan dawo.
Murmushi Anne tayi tana cewa"
Ba komai ki zauna da momynki tayi kewan zama Dake idan tagama ganinki da kyau Kya dawo,
Allah ya tsare.
Amin" tace tareda juyawa ta wuce halima na bayanta.
Harta Kai kofa tadawo ahankali ta tsaya gaban Annen cikin sanyi da nutsuwa tace"
Anne,
Anne Laylah ce take daukeda cikin,
Yanzu wata cikin na biyar......
Da wani irin mamaki Annen take kallon Sa'adah,
Wani murmushin manyanci ne ya subuce Mata sai kawai tace"
Ita Laylan?
Har wata biyar Kuma shine take zaune gida daya da Na'ima?
Shiru Sa'adah tayi tana Rasa abin cewa sbd yanzu Kam kowa yasan idan Na'ima Takoma yanzu ba shakka zataga ciki jikin Laylah, saidai rashin sanin mahaifin ciki shine saukin masifar.
Wuce driver na jira karkiyi latti.
Wucewa Sa'adah tayi tabar Anne zaune tareda Shiga mamakin duniya dama jinjina zurfin ciki irin na Laylah,
Tabbas tasan Na'ima zata buga rikici na gaske idan tasamu maganar cikin mijinsu a jikin 'yar datakewa kallon Yar riqonta...
Tuno lokutan datake waya da Turaki tanajin mace tayi kusan lokuta da dama,
Kenan Laylah ce....
Kasa tunanin komai tayi kawai sbd daga Turakin har Laylan sun tsundumata mamaki harma batasan Mai zatace ba,
Me zata fadawa mutanen data gama tanadin gyaran Amarya agurinsu da sauran shaaninsu...
Abu daya ta yanke a ranta shine dauko Laylah kafin Na'ima Takoma.
*****Zaune suke a lafiyayyan palon Turaki Dake cikin gidan
Yana zaune 2seater sanyeda skyblue yadi Mai tsananin taushi daya sake bayyanarda kwarjininsa
Gabaki daya turaren Bois elite ne ke sanyaya palon da qamshin ga sanyin AC daya Gama Kama koina hankalinsu akwance,
hankalinsa na Kan wayarsa yana kallon sakon LAYLAH yashigo na wasu kisses data turo Masa.
Ya Dan dauke Kai Yana Kama kansa cikin basarwa sbd Abban Laylan dasuke tare Yana zaune shima suna magana.
Dan gyara murya kadan yayi sbd neman sarkewar Dake da emojis din datake sake turowa
Yadauki wayar ya kashe gabaki daya sbd zata iya rikitasa ya Rasa meyake fada gaban Mahmoud dayake basarwa sbd karya gano waye.
Cikin nutsuwa Abba ya kalli Turakin bayan yagama kashe wayarsa ya aje gefe da sautin bayyanarda zallar gadiyarsa a natse yace"
Turaki Babu abinda Zan saka maka dashi sai godiya kawai,
Kayiwa Allah,
Kayiwa abota,
Kayiwa zumuncinka da Zainab,
Kakuma yiwa marayin Allah Dan Haka Banda bakin godiya daga Kai har Anne Ina muku fatar samun sakamakon gidan Aljanna.
Cikin basar da zancen ya Dan kalli Abban yana cewa"
Inaga ai mun rufe wannan maganar right¿
Numfashi Abban ya sauke ahankali da Jin nauyin abinda zai fada
Yadai Daure tunda ba boyo tsakaninsu da Aminin nasa ya dago ya kallesa yace"
Sai maganar Laylah.....
Sai alokacin Turakin ya dago a hankali ya kalli Abban Jin sunanta.
Gyara zama Abban yayi Yana cigaba da cewa"
Nasan Bai kamata ba nashiga zancen tunda ikonta a hannunka yake yanzu Amma tunda kamar alfarmace tun farko kayimin ka amince da Aurenta
Yanzuma Ina riqon Alfarmar karka duba tarayyata dakai idan har bakada raayin auren zaka iya sawwake Mata tadawo gida ko ahakan kayi matuqar kokari da taimakawa sosai wlh........
Tunda yafara hada shimfida da LAYLAH Bai sake kallon cikin idon Mahmoud ba sai yanzu daya dago ya zuba Masa manyan fararen idanuwansa akansa batareda ya bude Baki yace Masa kala ba,
Abban yasan Turaki farin sani,
Babu halinsa da Bai saniba sai Wanda yaqara daga bayan Nan saidai duk da hakan idon da Turakin ya zuba Masa bazai iya cewa na menene ba
Dan Haka ya Dan muskuta Yana gyara zama jiran mgna ta fito daga bakin Turakin Dan Yama kasa qarasa sauran zancensa...
Ahankali Turakin ya dauke ido daga kan Abban Yana saukewa Kan Tv Dake aiki batareda ya iya cewa komaiba,.
Shi kansa Abban shiru yayi sbd yasan maganar na buqatan nazari Dan Haka ya kalli Turakin murya a mace yace"
Inaga gobe Zan wuce Nima A Abdoul yagama min booking ticket da komai...
Tafiyar safe zanyi saidai idan naji daga gareka.
Har lokacin Turaki Bai iya cewa komaiba sai gyada Kai da yayi Ahankali cikin nutsuwa.
A Abdoul ne yatafi maida Abbansu Laylan daga can ya wuce gida shima sbd dare yayi Daman.
Tunda Mahmoud yatafi Yana zaune inda ya barsa qafarsa daya Kan daya idanuwansa sun sauya sosai ya rufesu ahankali ya bude saiga Ms Na'ima tashigo sanyeda doguwar Riga idonta a hargitse sbd kwanakin gabaki daya Bata cikin nutsuwar zuciya.
Zama tayi gefensa cikin kokarin danne baqin cikin dake cin ranta tace"
Turaki gobe Zan wuce Lagos acan jirgin da zanbi zai tashi komawa zanyi,
Ga Laylah anbarota ba kowa nasan tana cikin kadaici....
Batareda ya waiwayo ya kalletaba Kai tsaye a karon farko tsawon shekarun aurensu dazai fara hanata tafita yace"
Ba yanzu Zaki komaba ki zauna anan tukuna.
Da mamaki ta kallesa tana juyowa gabaki daya suka fuskanci juna
Tace"
Nariga nayi komai na tafiya zakace bazanjeba?
Babu ruwanka da dukkanin tafiye tafiyena sai yanzu Kuma,
Kayi hkr sbd nariga na shirya tafiyata Banga zamanda nakeyiba anan nabaro yarinya ita kadai acan Dan Haka Ni tafiya zanyi....
Jajayen idanuwansa dasuka sauya tun kafin shigowarta ya dago ya Mata kallo daya dayasa gabanta faduwa Amma batajin zata yarda ta zauna sbd abinda yake gabanta,
Nafada Babu inda Zaki ki
Idan Kuma Zaki tafin ki tafin Amma Kar qafarki ta Isa kofar gidana....
Miqewa yayi tareda daukan wayarsa yabar gurin.
Cikin masifaffen tashin hankali da tsoro harma da firgici Ms Na'ima tabi bayansa da kallo tana shedar da tsananin bacin Rai data hango cikin idonsa,
Karta Isa kofar gidan fa yace????
Batasan lokacinda ta miqe tana neman zunduma ihuba ta fito tana cewa"
Wlh anshiga tsananina da Turaki andau hanyar rabamu....
Ina Zinat ga bala'i Mai zaman kansa na neman sauka rayuwata
Turaki na fadar karna Isa kofar gidan.
##MAMUH#
_Mamuhgee 45_*
Tana Isa bangarenta ta zube Palo tareda fasa ihun dataketa riqewa tun daga can,
Wayyo Allah na shiga uku Ina neman lalacewa Ni Na'ima,
Duk Wanda ya Shiga tsakanina da Turaki Allah ya bayyanarmun dashi na shiga tsakaninsa da nasa farin cikin da kwanciyar hankali....
Kururuwar ihun datake saki tana tsinewa duk macen data taba ko kallon Turaki harda uwarsa data haifesa tsine Mata takeyi tana rusa ihu zuciyarta da kirjinta Kamar zasu babbake da wutar dakeci aciki...
Siddika lafewa tayi a kicin taqi fitowa Dan ko ruwan zafi zata iya konata dasu idan tana wannan masifar tata komai fasawa take tana haukarta Dan Haka tunda tasan halinta ta daina tsayawa idan al'amarin yazo
Dan Haka ko yanzu tana jinta tana dure duren masifarta cikin tashin hankali Amma ta lafe taqi fitowa.
Duk da tana Mai aikin Ms Na'iman Kuma take yarinya akan Ms Na'ima tanada tabbacin wataran Ms Na'iman idan Bata kashe wani ba akan masifar kishi, zata kashe kanta to,
Idan Kuma duk hakan Bai faruba to zata haukace.
Ganin abin na Ms Na'ima ba qarewa zaiyiba ta fidda wayarta takira Haj Zinat ta fada Mata abin dayake faruwa ta kashe wayarta tana ajewa gefe ta nufi fridge tana cewa"
Yau ranar Jin dadina tunda batada kwanciyar hankalin yimun fada Bara na girka abinda nakeso naci abuna hankali kwance.
***Haj Zinat cikin quluwa da lamarin Na'ima da haukarta ta dauki wayarta tafara Kiran Na'iman Amma Bata dagawa,
Tsoki ta saki tareda jefar da wayar Kan gadonta tana cewa"
Na'ima haukarki tafara yawa wlh muna buqatan komawa ganin likitan qwaqwalwanki tun kafin Turaki yagama gano kinada matsalar hankali,
Yanzu da Daren Nan bazan iya zuwa gidanki ba sbd dare yayi Kuma Turakin na gari ba'a Shiga gidan idan karfe bakwai ta wuce matuqar ba Yan gidaba,
Indama baya garine sun Saba take dokar sbd securities na ragewa idan bayanan,
Amma yanzu Yana gari ubanwa zai Bari tashiga gidan da wannan lokacin¿
Allah yasa dai haukarki ta tsaya iya bangarenki kafin nasamu safiya tayi nazo karta budemun aiki Turaki ya gano batada cikakkiyar lafiyar qwaqwalwa mun shiga uku Dan kuwa take zai gano duk wani abun da Na'iman keyi kusan itace take dorata akai.
Ms Na'ima kuwa tun tanada karfin iya tashin hankalin ita kadai har qarfinta yaqare ta zube kwance qasan dakinta tana Jin kamar ta cinnawa gidan wuta kowa ya mutu har ita...
***Washe gari tun qarfe 6 na safe ta kwadawa zinat Kira batareda ta damu da lokacinba,
Dayake itama da ita ta kwana cikin ranta ba wani baccin arziki tayiba Dan Haka Kai tsaye ta daga Kiran tana cewa"
Thank God nasamu kin dawo hayyacinki,
Na'ima Ina fatan bakiyi abunda zai Bata Mana komaiba da janyo Mana matsala?
Bata amsa tambayar Zinat din ba tafara koro Mata bayanin abinda ya faru jiyan ta qara da cewa"
Zinat wlh saina tafi tunda ya nuna bayason zuwan nawa na tabbatarda yasan idan naje zansan sirrin dayake boyewa shida Waccar tsohuwar.,
Wlh Zinat idan ban illata ko waceceba qwaqwalwata bazata dawo daidaiba....
Can you imagine Ni Turaki yake cewa idan naje karna Isa ko kofar gidansa......
Wait wait"" Haj Zinat tafada tana tashi zaune daga kwancen datake cikin wani tunanin daya shigeta tana kasa yarda da hakan tace"
Idan yace ko gidansa karki Isa kenan ba tafiyar takice matsalarba zuwa gidan nasane¿
Idan hakan ne kuwa to wlh kila bayan barowarki akwai wata a gidan kokuma Laylah Dake gidan tasan wani abun bayason ki koma ta sanar Miki...
Shiru Na'ima tayi sbd yanzu Bata Gane komai Bayan taganta a jirgin komawa, idan ta Isa koma menene ayi sauran tunanin acan...
Kira Laylah ki tambayeta komai gameda gidan kiji idan wani Abu yafaru Bayan barowarki sbd itama bazata yadda acucekiba.
Cikin yanayi na kosawa tace"
Zinat me Laylan zata iya fadamin ko bincikamun wadda sanyin jikinta kawai ya Isa yasa na isa qasar Bata Gama sanin me gidanma yake cikiba bare wajensa,
Zinat Naga Kamar kin daina Gabe baqin cikina dakike maganar tsayawa ayi magana da Laylah....
Cikin gundura Haj Zinat ta katseta da cewa"
Na'ima meyasa kanki yafi na kowa tashewa ne Ana ce Miki ga abinda Zakiyi kina cewa aa,
Idan Kika tafi kin manta abinda yace ne?
Gidansa yace karkije,
Idan Kika tafi a yanda yakeda wata a zuciyarsa yanzu wlh Kika take dokarsa igiyarki daya data rage sakinta zaiyi kila Kinga shikenan kowama saiya huta,
Mama Baraka da bakya kaunar komawa gurinta saiki Koma can Dole Dan ayanda kasuwanci yake rawar Nan yanzu anata samun asara tako Ina wlh bazaki wafta kudi acikiba ki siya gida ko kamawaba,.
Dan Haka idan Zaki nutsu ki nutsu mubi komai a daki daki
A hannu zamu Kama komai kafin mu lalata koman kuma.,
Yanzu kiyi hkr ki aje maganar tafiyar a gefe kizo Nan muyi magana a tsanake idan yasan wata baisan wata ba ai.
Ba Haka Na'ima tasoba Amma Kuma tasan yanda Zinat ke cewa ayin koyaushe itace Hanya Mai bullewarsu Dan Haka Dole tabar maganar tafiyar saidai Bata fasa fitaba tunda uwar safiyar ta fice daga gidan cikin motarta _Mercedes Benz C-class_ da Bata cika hawaba ta fice gidan cikin wani Irin speed dayasa har securities din gidan Gane madam din na cikin bacin Rai.
Turaki dake zaune cikin sofa a dakinsa tun bayan Gama sallar asubarsa Yasan dama ba zataji maganarsa ba sbd idonta yagama rufewa da taje din...
Wayarsa Dake gefensa yakai hannu ya dauka a hankali tareda saka Kiran Numbern A Abdoul Dake qasan ta Laylah daya Gama waya da ita ya Danna kiransa cikin nutsuwa.
Cikin bacci A Abdoul yaji wayarsa na ringing ya Dan mirgina tareda Kai hannu inda wayar take ya daga yana duba Mai kiransa wannan lokacin..
Ganin sunan TURAKI akai yasashi sake Ajiyar zuciya Dan dama yasan bayan Turaki Babu Wanda zai Masa wannan Kiran yanzu
Dan Haka ya tashi zaune Yana wartsakewa daga bacci cikin girmamawa ya daga wayar Yana cewa"
Good morning TURAKI.
A gajarce ya amsa cikin nutsuwa ba hayaniya tareda cewa Kai tsaye"
Ayiwa Zainab komai na Shirin tafiya duk ko yayane inason ta baro Atlanta ta sauka Lagos zuwa jibi.
Yes Turaki Inshallah angama.
Kashe wayar yayi tareda maidata gefe ya ajiye Yana maida kansa ya jinginar jikin kujeran dayake zaune tareda rufe fararen idanuwansa dasuka kasa samun komai face ganin Laylah ta iso garesa cikin koshin lafiya Dan baisan iya abinda zai iya faruwa idan Na'ima ta Isa qasar ta taba lafiyarta Dana cikin jikinta.
Ms Na'ima ma data Isa gidan Haj Zinat kasa Shan Koda ruwa tayi sai data Kira Laylah Dake fama da kanta ta ringa jeho Mata tambayoyin dasuka sakata shiga fargaba da shakka saidai duka amsoshin data bawa momyn basu gamsar da itaba Dan Haka ta kashe wayarta tana cewa"
Dama nasan ba wani amfani ne da Laylan ba kikace sai ankirata gashinan na batawa kaina lokaci da Rai abanza.
Da qyar da dabara Haj Zinat tasaka Ms Na'ima Shan tea kafin ta banka Mata maganin qwaqwalwan datake akai aikuwa tana shansa ba jimawa baccin Dole ya dauketa ta zube a gadon Haj Zinat Dake cikin lafiyayyar bedroom dinta tana baccinda ba shiri.
Bata farka ba sai yamma wanda daman Haka maganin yake wani irin mugun bacci yake sanyata harsai qwaqwalwanta ya dawo Yana Dan aiki daidai,
Hakama da mutuwar jiki zatai kusan wuni biyu sbd bazata samu qarfin wani tashin hankalin ba shiyasa batason maganin idan tanajin masifarta Amma so da yawa Zinat ke yaudararta tabata gashi yanzu Bata iya wani dogon tashin hankali sai bayan kwana biyu kuma Dan Haka ta tattara Fahad babban Dan Haj Zinat din ya dawo da ita gida.
Tana Shiga bangarenta tun a Palo siddika dake Mata sannu da zuwa tana karban handbag dinta ta fahimci maganintane ke aikinsa Dan Haka wani dadi ya mamayeta tana Jin kwanakin duka na Sa'artane Dan kuwa yanzu rayuwar Jin Dadi da kwanciyar hankali takeyi a gidan tunda masifar gaban Ms Na'iman ta isheta da Bata lokacinta
Dan Haka daki takaita ta kwanta ta fito tareda janyo Mata dakin ta wuce kitchen tana cewa"
Faduwar wani tashin wani.
Kwananta biyu Bata tako ko kofar fita Dana bangarentaba tana fama da kanta sai data cika kwanan biyu cif tadawo daidai ta nufa Sashen Anne ta gaidata Kamar Dole ta fito Takoma bangarenta tana wayoyinta da Zinat data dagawa hankali akan ita ta tafi Ta binciko musu sbd zaman Nan a baibai bazai kaisu koinaba sai gurin baqin ciki da bacin Rai sbd suna Bata lokaci cikin Yana da uwar cikin suna sake samun qarfi tunda ciki zaina cigaba da girma.
*****
Qarfe 5 na asuba jirginsu ya sauka a Murtala Muhammed International airport dake Lagos,
Sanye take da _Moja majka_ Abaya maroon Mai shaking material
Kanta nade cikin Marron veil qarami na Abayar sai black Gucci suede loafers a qafarta da qaramar _Bottega veneta_ small shoulder bag Dake rataye a kafadarta,fuskarta tayi haske sosai ta yanda ko kafin idonka ya sauka a cikinta zakasan tana daukeda juna biyu dayayi Mata kyau matuqa,
Bata qara wata qiba ba hakama Bata rameba shiyasa cikin ya fito sosai iya watanninsa...
Wani numfashi ta sauke lokacinda ta shaqi iskar Nigeria ta lumshe ido cikin gajiya da Yar yunwar Dake damunta ta fito Ana biyeda ita da luggages dinta.
Tana fitowa Wanda idonta yafara sauka akansa ne tsaye Yana waya cikin black Rugby's Riga da wando da jacket Mai girma datakai Masa har gwiwa...
Duk da Yana sanyeda face mask black da hular sanyi,
kallo daya tayi Masa tagane shine duk koina nasa kusan a rufe yake Kuma Bata taba tunanin zai iya zuwa airport da kansa tarbonta ba
Da haka wani sanyi ne ya mamaye zuciyarta har batasan idonta Yana cikowa da hawayen kewarsa dataiba da farin cikin ganinsa...
Ahankali take takowa idonta cikin nasa daya zuba matasu cikin kallo Mai wuyar fassarawa,
Akan cikinta daya turo Ana ganinsa da kyau ya sauke idanuwansa kafin ya ware Mata hannuwansa ahankali Yana cewa"
Finally.
Ahankali tashige jikinsa tareda rungunmesa da sauri hawayenta suka sauko tana cewa"
Abbahhhh.
Hannunta ya Kama A Abdoul ya wuce gaba tareda kayanta aka shigar mota kafin ya bude motar Turakin da kansa ya bude Mata motar yana riqeda hannunta ta shiga kafin shima ya Shiga A Abdoul yaja motar suka bar airport din.
Hannunta na cikin nasa a sarke yake kallon cikinta Yana kallon fuskarta Dake glowing tana daukan idonsa da hankalinsa..
Wani malalacin murmushi ya saki Mara sauti
22, August 2025
Haura'u
Interested
22, August 2025
Haura'u
Interested