Showing 27001 words to 30000 words out of 55353 words
Yayi,
Ta kunna taga akwai layi tana gama rebooting Kira ya shigo, tasan shine shiyasa ta yi picking
"Hmm kawai ya fada batareda ya ce komai ba kudin shi natafiya na wani lokaci Kafin yace "kin koresu duka baby kinki mayemin gurbinsu duka, Ina rayuwa mara dadi mai kuma wahala,
"Meye kika mun? ( I have change am not my self) gaba daya banda natsuwa yaushe zaki dawo barrack? Ki dawo baby idan kina Kusa natsuwa ta zata dawo am (leaving a lonely live) Ina rayuwa nikadai banajin dadi baby,
Magana yakeyi kamar baida laka cikin kwantar da murya, "baby bana iya magana da mace da yawa magana ta da mace daya ce ta gamsar dani,
"You are different ke ta daban ce baby kidawo Kusa dani am missing your soup please come and cook for me Abincin ki nakeson ci) nayi kewar miyarki inason kidafa min Abincin ki inci
Sirrin zuciya ta kadan ne NA iya fada miki akwai da yawa gashi zanyi tafiya next week kizo kafin intafi don Allah,
Tunda ya fara magana ta yimai uzuri tasan ba laifinshi bane laifin Allurar nan da ake cewa ana yimusu ce taja lallai tashi ma Allurar ta mahaukata ce, Toh ita hauka take zata kai kanta wurin shi Allah ya tsareta da fadawa halaka
Haka yagama sambatu ya Ajiye batareda ya gaji ba ya runtse idanun shi gam don Abinda yakeji yafi karfin feelings kawai abunda da yakeji is morethern feelings yafi karfin sha awa kirjinshi har wani zafi yake mai kamar mai asma
Gashi zaiyi tafiya zuwa gambiya sati mai zuwa kuma zai yi wata shida kafin ya dawo.
Ya dade yana Addu ar wannan tafiyar tazo sai gashi tazo a wrong time..........?
*hmm my fans me kuke tunanin zai faru da rayuwar YASMIN da MA da kuma ismail to mudaije zuwa masoyan YASMIN*
*Matar soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: π»π»π»π»π»π»π»
*BARIKI*
_Auren Soja_
π»π»π»π»π»π»π»
_written by FENERH_
Maman Ammar
*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby
19&20
Kusan kullum sai ya kirata sau ba adadi gashi baida lokacin kanshi da ya samu d'an sarari ita zai kebe ya Kira,
Hajiya ma tasan ya canja don yanzu sau da yawa zaije gidan ya Kasa ce mata komai sai dai kwanciya maganar Aure kuwa tama daina wahalarda miyanta da sauran shekarunta,
Gefen maganar Auren ta kuwa tana nan baba yace a Bari kawai takarasa tunda saura Y'an watanni ya rage,
Sai shirye shirye ismail keyi yana cikin zumudin wannan Auren yauma zuwa yayi tana zaune rike da wayar ta tana chart ya shigo dakin cikin sallama tayi saurin tashi zaune,
Wayar hannun ta ya zubawa ido tare da waro su waje" gimbiya ta kin karo wulakanci baba ya siya miki irin wannan wayar?
Saurin girgiza kai tayi tareda saurin kashe zancen "Aunty ce tabani, "OK dama nazo inji size ne nagama siyayya saura iners so number nawa ne gidan ruwan namu?
Yafada tareda daga gira hannu tasa tareda rufe fuskarta cike da kunya ta kudundune a katifar, kai maza basuda kunya Wallahi ko kadan harda shi da take ganin kamar ko yatsar mace bazai iya tabawa ba,
"Ki fadamin kinsan dai sunkusa zama nawa ko don haka kicire kunya kawai don watarana har a tsakiyar hannu na zasu kwana,
"Na bani yau ta fada, mikewa yayi yana dariya a hankali "ki fara sabawa don rayuwar wayewa zamuyi a gidan mu baby na,
"Kituromin a text Ina jira ya fita tareda barmata kamshin shi ta yi Ajiyar zuciya tareda kallon kirjin nata tana tuna lokacin da MA ya shafasu tayi shiru tana tunanin maganganun shi
Na jiya,
"Baby zanje wuri mai nisa yanzu bazaki iya zuwa koda sau daya bane inganki? Baby inashan wahala tsawon rayuwata bantaba jin irin Abinda nakeji akanki ba Kowa tanbayata yakeyi lfy ta kalau kuwa?
"Ni nasan banda lfy a jikina ki taimakeni ki bani kulawa koda kalma daya ce mai dad'i guda daya kifada min inji sanyi please
Wayarta ce da tayi Kara tasa ta dawo hankalinta ganin numbar shi ce yasa tayi picking tareda sanya hands free ta Ajiye tana mai kankare kunbarta da nail cuter
Shiru yayi Kamar kullum nadan lokaci kafin ya fara magana, "yaushe ne Zaki fara daga waya ki kirani? Yaushe Zaki fara bude baki kibani Amsar tanbayata,?
"Yaushe ne Zaki sama min natsuwar da zuciya ta ke bukata? Jibi zantafi baby please do something kafin mahaifiya ta tarasa ni,
Tsayawa tayi kawai tana nazari kafin ta daga wayar ta cireta a hand free ta fara magana cikin natsuwa, " me kake so da rayuwata? Meye tsakani na dakai? Kai ba saurayina ba ba d'an uwana ba you are nobody to me please free me ka barni in fuskanci masoyina mai burin Aurena mai nufin raya sunna dani bawai mai shirin zaman BARIKI dani ba,
Kai ba sona kakeyi ba kawai rayuwar banza kake burin yi dani kuma bazai faruba da ikon Allah aniyarka ta bika,
Toh ni ko a tarihi bantaba jin irin rayuwarka ba ba kalmar so ko daya sai mugun nufi a kullum "kai Wallahi nakara tsanar rayuwar ka da duk wani Mai halin BARIKI irin naka,
"Hmmm Meye so? Ya ake agane mutum nason wani? Meye jin dadi A soyayyar bayan Ajiyar da juna dad'i ? Kit ta katse kiran idanun ta na zubar da ruwa tana mai jin wani sabon bakin ciki MA ya gama da rayuwar ta Wallahi sai Allah yasa ka mata gashi ta Kasa fadawa Kowa halinda take ciki,
Ya takura mata duk da tun ranarda ya bata waya bata kuma ganin shiba, number yayarta ta Kira,
"Aunty na tafada cikin murna bayan ta daga "Wai YASMIN kin manta dani ko bayan kin gudu kinbarni gashi baban Auwal ya wuce gambiya jibi ogan Shima zai wuce sai sunyi wata shida zasu dawo,
Ajiyar zuciya ta sauke haka kawai taji Dadin tafiyar zataso ma kafin ya dawo Adaura mata Aure da ismail sai taga yanda zaiyi,
"YASMIN ki dawo don Allah kinga nakusa haihuwa kuma kinga baba bazai taba Bari indawo gidaba ki taimaka kidawo kodan yaronki yana kewarki,
Wani irin tausayin y'ar uwar tata taji nan take ta canja shawarar zuciyar ta na kin komawa BARIKI bayan ga rabin jinin ta a ciki,
*****************
Karar wayar ta tayar da ita daga dogon baccin datakeyi mai cikeda mafarkai masu dadi ta Sa hannu ta janyo wayar batareda ta duba ba tayi picking tareda kangawa a kunne ta cikin muryar bacci tace,
"Hello, wani irin Ajiyar zuciya ya sauke a hankali cikin natsuwa "hy baby' ya fada cikeda kasala, ba arziki ta bude idonta don jin muryar shi da tayi,
"Baby please say something sweet Gobe fa zantafi ki fadamin kallama mai dad'i da zanrika tunawa da ita,
Shiru tayi mai don tasaba da jin wa innan kalamai daga gareshi basa wani damunta, "um ki fadamin me kikeso inkawo miki kafin intafi,
"Banason komai naka nagode, "hmm dole kiso Abinda yake nawa baby kuma kidaina hawa machine natsani mace na hawa machine,
"Yanzu nafara hawa kuwa tunda dole inje school kuma Ina ruwanka ba,? "Niko keda ruwa harma da tsaki aciki yazaki rika kwanciya a bayan kowane irin kazami da jikinki mai matukar muhimmanci,
"Zankawo miki mota ki koyi driving, "banaso haka kawai kajamin bala'i wayar nan ma nasha question akanta bare ka kawo wata mota ince wa ya bani?
"Kice Muhammed Abdullah ne yabaki wani Mai nacin ki, "bakaji da kyau ba, a wane dalili zai bani mota Meye relation din mu dashi,?
"Blood relation inajinki har cikin jini na baby give me chance zanzo infadawa baba sai inkawo miki motar,
"Karufamin Asiri don Allah kabarni ingama lfy da iyayena ni yanzu banason duk wani Abinda zai dagamin hankalin su ta sanadiyata,
"Ni ai hankalina ba akwance yakeba tafiyar nan da zanyi ji nake kamar bazan dawo inganki ba wata shida kamar shekara shida nake hangosu please take care of your self
Zan nemi napep personal ya rika kaiki school please don't say no to this one, sannan ki kiyaye Wallahi ba a sake zantafi inbarki ba zansa tsaro donni ba sakarai bane idan wani namiji ya kusanta ki zaisha wuya I promise don haka ki kiyaye,
Wani irin tsoro taji ya shigeta ita kam ta hadu da rayuwa itada ke murna zai tafi shine zai hada ta da wani tsaro, wayarshi ma tana dauka ne saboda kawai a rabu lfy batason yana zuwa Unguwar su da tawagar shi,
"Baby' yakirata cikin kasala tareda yin mika mai karfi har bones dinshi na amsawa
"Zanzo inganki kafin in wuce please karki mun musu zanzo gidan ku,
"Aa karka zo don Allah katafi tunda muna waya, "I can't inason ganinki please allow me,
"Zanzo idan baki fitoba zan shigo gidan, saurin tashi tayi zaune tareda fara rokonshi da ya rufawa rayuwarta asiri, Gobe zanje school mu hadu a can ka ganni don Allah karkazo nan gidan baba na nan,
"Is OK to kifito da wuri saboda karfe tara jirgin mu zai tashi, shiru kawai tayi don tasan ita Allah ya jarrabeta da ala k'ak'ai a rayuwa,
"Kazo kai kadai karka kwaso yaranka kaga yanda kuke janyo idanun mutane a kanku banaso, "as you wish ya fada tareda katse kiran,
Kwance yake yana maijin bugun zuciyar shi na karuwa ga wani uban feelings dake taso mai kamar Yayi hauka sai mulmula yake a gado,
Bacci ya gagareshi ya mike tareda nufar durowar gadon shi ya ciro magani ya jefa a baki tareda daukar ruwa ya kora ya koma ya kife,
Yana cikin wannan halin Yaji ana shafashi tareda kissing wuyan shi da yatashi duk wata tsiga ta jikinshi ya wani irin juyowa tareda runtse idon shi gam yana mai ayyana Ina ma YASMIN ce tazo,
Jin an Dora baki akan lips dinshi yasa shi saurin bude idanun shi ya zuba mata ido batareda ya motsa ba ya dauke kanshi don kiss idan ba YASMIN ba baya bukata
Zuby ce ta marairaice fuska "haba MA yanzu da Emanuel bai fadamin zaka tafiba da saidai inji lbr ko, "Muhammad Kasan Ina matukar kaunar ka meyasa kake wahalar da zuciya ta,
Kallon hawayen ta kawai yakeyi kafin ya tashi kamar ba akan jikinshi takeba ya juya tareda zuba mata ido,
"Me ya kawoki,? "Nazo muyi sallama ne nakasa daurewa yau ko zaka kasheni bazan tafiba Allah sai kabani natsuwa Kasan munriga munsaba da juna yanzu kakeson ka juyamin baya bazan iya rayuwa dakowane namiji ba sai kai please marry me '
Tafada tana riko hannun shi ya bata wani irin mugun kallo"you are insane nine zan Aureki? Nataba fada miki Ina son Aure? Muntaba Alkawarin Aure dake?
"To me kakeso dani? Bana bukatar komai a wurin ko wace mace please leave me alone, kuka tasa sosai tareda fadawa jikinshi tana lalubarshi,
Gim ya tsaya kamar dutse ta Karachi fitinarta ta mike ta koma gefe tana kuka don jikinshi ko motsawa baiyi ba, "bakada lfy MA kaje kaga doctor
Mikewa kawai Yayi tareda komawa can karshen gadon Yayi kwanciyar shi bai kuma komawa ta kanta ba,
******************
Cikin Sauri YASMIN ta gama shirin ta ta fito tana rike da Jakarta ta Yayi irin wadda Y'an mata ke son ratayawa yanzu mai doguwar igiya bakomai aciki sai wayarta da ID dinta na school da kuma Y'an canjin ta,
Tsayuwar napep agaban ta ya bata tsoro tayi baya kadan ya leko da kanshi "Hajiya shiga muje umarnin Oga ne, batada zabi ta shiga ya tukata,
Wayarta ta fito da ita tafara dannawa tana mai bude sakonni a watsp bata kuma dago kanta ba saida yace munzo Hajiya,
Ta dago kanta taganta bakin tafkeken gate din dake dauke da manyan rubutu a jikin shi, GAMJI tagani,
"Yazaka kawoni nan? Maganarta ta kafe lokacin da tayi ido biyu da kyakkyawar fuskarshi yana sanye cikin shigar shi ta kaki yau Como flag ne a jikinshi Yayi matukar yin kyau gayen akwai fitinannen kyau a tare dashi kuma shine sojan da ta taba gani fari sosai kamar baya aikin wahala Abin tsoro atareda shi bai wuce muscles dinshi ba kamar wani roman reigns,
Matso da fuskar shi Yayi gab da ita tareda hure mata idanu tayi saurin dawowa hayyacinta,
"Wannan kallon fa karkiga munina baby ya fada yana dariya da gefe daya irinta muiskilayen maza,
Hannun ta ya riko tareda cewa ''let go kamar wata magnet haka ta biyo shi ya bude gaban katuwar motar da yazo da ita ya zaunar da ita kafin yazagaya ya shiga,
Facing dinta Yayi sosai ya zuba mata ido kamar zai hadiyeta kare mata kallo yake ta ko Ina ya sauke idanun shi ya gaban hijabinta ya sauke ajiyar zuciya
"Baby kintara komai da nakeso I love your body and your beautiful face bansan y'anda zanfada miki ba, katuwar wayar shi ya janyo tareda saita ta ya fara daukarta Hoto kafin yasa hannu ya janye hijabinta kamar wani mai tsafi batareda ta ankareba, har saida ya cire ya ajiye a kafar shi,
Wani irin zabura tayi tareda zubamai ido ita tarasa dalilin da yanzu Sam take Kasa fada mai mugayen magan ganun ta gashi yau ya mata wani irin mugun kwarjini duk ya cika mata motar
Sarkewa idanun su sukayi ta yi saurin sauke nata batareda ta ce mai komai ba don kamar ya daure mata baki yau,
"Ni dai kamar bakin nan bashi bane mai tsiwa? Kodai kinbada kaine infasa tafiyar nan baby mu gwangwaje?
Dauke kanta tayi gefe ya zubawa sajen dake fuskar ta ido tareda cewa wow domin ta kwantarda shi da gel Yayi wani irin kwanciya mai ban sha awa ga sumar ta tufke ta da katon ribbon ja ta nannade shi kamar kwallo jelar baisan lokacin da hannun shi yakai kantaba ya fara shafa shi tuni lafiyar shi ta motsa,
Tayi saurin dafe hannun shi domin kokarin cireshi akanta ya ware idanun shi akanta wa inda suka sauya launi harda wani ruwa ruwa suka tara a ciki,
Ya Kara riko hannun ta gam yanajin wani dadi yau ne karon farko da mace ta rike hannun shi haka Yaji wani iri har tsakiyar kanshi hannun ta kamar magic,
Baisan sanda ya fisgota kan cinyar shiba, wata y'ar Kara tasa tareda kokarin sauka tana dukan kirjinshi mai kamar dutse take duka,
"Meye haka Wai kaga shi yasa natsani halayenka banason iskanci,
Wani irin ajiyar zuciya kawai yake sauke wa duk da ta cure jikinta wuri daya amma he is feeling the hug he gave her deep down,
Saida Yaji yana shirin sumewa ya saketa ta koma gefe ta dunkule tareda sakin kukan da tarasa dalilin shi, "meyasa kakemun haka kaje wurin Y'an matan ka da suke nema mana saini kakeson kazo ka batamin tarbiya Allah sai ya sakamin,
Kanshi ya Dora akan sitiyarin motar na dogon lokaci kafin ya dawo dai dai wayar shi tayi Kara ya yi picking "OK kawai yace ya kalleta,
"Am sorry for making you cry ni zan tafi, saka hannu ya ciro wallet dinshi ya ciro ATM guda uku ya zube mata su akan laps dinta "gashi if needed kiyi duk abinda zakiyi dasu zantura miki pin din duka a text
Wani irin kallo tabishi dashi tareda ajiyemai kayan shi "bana bukata inada maiyi min, Kasa cewa komai yayi kawai ya mika mata hijabinta tareda kallon kirjinta for the last time yai ajiyar zuciya tareda fesar da huci mai zafi yaja motar saida ya kaita kofar school din kafin ya bude dash bord ya ciro rafar Y'an dubu dubu ya Ajiye mata guda biyu ganin bazata karba ba ya fisgo Jakarta ya bude tareda sakawa ya ajiye mata,
Bude motar yayi ya fita saida ya zagaya ya bude mata ba bata lokaci ta fito ko sauraran shi batayi ba tayi wucewar ta yabi bayanta da kallo har ta bace ya fada mota ya tafi,
**************
Yau kimanin kwana biyu kenan da tafiyar MA tunda ya tafi bai kirata ba kusan duk bayan minti goma saita duba wayar tarasa me yasa ta damu da rashin kiran nashi
Gashi yanzu data zauna sai tunanin shi ya fado mata wani iri takeji d'an gane dashi tarasa meke damunta,
Mama ce ya shigo dakin ta kalleta "YASMIN Wai meke damunki ne kwana biyu duk bakida walwala gashi sai aukin kwanciya kamar mara lfy,
"Ki kitafi y'ar uwarki nata kirana kije kitaimaka kitsaya da ita kinga mahaifinku ya Riga yayi ratsuwa tunfarko bazata dawo mai gidaba ta haihu,
Tashi tayi saida ta gyara ko Ina a gidan kafin ta fada wanka ta shirya cikin atanfa mai saukin kudi Riga da sket tayi kyau sosai ta sanya hijabi tareda daukar akwatin da ya shirya Kayanta,
Ismail ne ya shigo gidan cikin shigar alfarma ya karbi jakar ya fita da ita mama ta fito da Wasu kayan data shirya mata ta karba ta ce "ki kaimata zankirata inyi mata bayanin yanda zatayi dasu,
Tunda suka Kama Han ya batace mai komai ba sai shine keta zuba yana bata labarin yanda ya tsara musu gini da kuma tanbayar ra ayinta,
"YASMIN meyake damunki kwanan nan ba yadda kike ba nake ganin ki you are too silent this days
"Bakomai ta fada, bata kuma cewa komai har saida ya kaita har kofar gidan ya fitar mata da kayan kafin ya mata sallama batareda ya shiga ba ya wuce don Sauri yakeyi,
Tunda ta fito idanun ta ke kallon kofar gate din gidan nashi yana nan fes kamar koda yaushe sojoji na wurin kamar yana nan aciki,
Ji