Showing 42001 words to 45000 words out of 55353 words

Chapter 15 - BARIKI (AUREN SOJA)

07 Jul 2024

8301

Don Allah kafita kajirani ina zuwa please kaje waje karsu mama su fito suganka muh'd ka rufa min Asiri don darajar iyayenka,



Aikin banza domin shi yayi nisa tunda ya Dora idanun shi akan boosty boob dinta ya rikice idanun shi suka juya Kala yayi wani irin kalar tausayi tareda kokarin rikota taja baya da sauri tareda kare kirjinta da rigar, cikin tsoron Abinda tasan zai iya yi,


Baya baya yakoma ya fada kan katuwar katifar tata mai cike da kamshin ta mai dadin gaske ya runtse idanun shi tareda kokarin natsa kanshi,



Gaskiya yau yayi namijin kokari DA bai yi striping dinta a cikin gidansu ba don ta mugun kunnashi sosai d'auriya iya d'auriya yau yayi,


Ganin y'anda ya runtse idanun shi yasa ta yi saurin saka rigar tareda janyo d'an karamin mayafin ta ta yafa ta matsa kadan kusa dashi' katashi mutafi don Allah karsu mama sufita inshiga uku,




Bude idanun shi yayi tareda zuba mata su cikeda shaukin zazzafar soyayyar ta "love you baby more and more, ya fada cikin kwantar da murya kafin yabi dakin nata da kallo,


Bayan katifar sai walldrp mai kofa biyu da mirror dinta dake dauke da turaruka da kayan shafa gefe data akwatunan tane guda shida pink masu kyau domin su ba talakawa bane don duk Wanda keda maganin lalurar yau da gobe ya wuce talaka, don Albashin baba ya ishesu suji dad'i har ma suyiwa Y'an Uwa Alheri,



Kan bangon dakin ya sauke idanun shi dake dauke da hotunan su Kala Kala ita da maryam tundaga na kuruciya har zuwa yanzu,



Murmushi yayi mai kyau ganin wani hoto nata tana sanye da kayan ta na nurse tayi masifar kyau, yatashi tsaye tareda kakkafe shaddar shi data fara squzing ya nufi wurin tareda ciro hoton ya rungume yasaka hannu ya ciro wani datake sanye da wata doguwar Riga pink kamar babie kanta da crown daga gani na wani occasion ne,



Kallon shi kawai takeyi, ga kamshin shi yacika dakin nata tab ya matso gab da ita" tank's for this beautiful pictures muje inbaki tsarabarki tana waje,



Bai jira komai ba ya fita tabi bayanshi cikin sauri domin ganin ko ba Wanda ya fito, tayi Ajiyar zuciya har suka kai kofar gidan bakowa,


Yana rungume da hotunan kamar kwai saida ya bude gaban motar ya ajiyesu kafin ya dawo wurinta,

Baki Yasmin ta saki wurin kallon motar da tagani y'ar karama tayi mugun yi mata kyau tana sheki duk da dare ne akwai d'an hasken wutar nefa a Unguwar kota ina,


Matsowa yayi tareda sanya hannun shi cikin pocket din Aljihun shi ya d'an rankwafo ta fuskar ta kadan "hope you like it? Idan kuma batayi ba a canjo miki'


Wani irin kallon shi tayi cikin tsoro, " me kake nufi? "Motarki ce akwai tsarabarki ma a ciki ya bude motar tareda bude bayan boot din ya Wasu irin akwatuna ne guda uku Kala daban daban manya duka girma daya blue red da kuma purple ya fito dasu kamar bakomai a ciki ya dauki biyu ya shiga dasu cikin tsakar gidan kafin yadawo ya dauki dayar ya shiga da ita,


Takasa cewa komai saida ya dawo yace "zomuyi magana kai tsaye ya riko hannun ta suka shiga gaban motar,


Juyowa yayi dakyau ya dafe kumatun shi ya zuba mata ido "baby nasan kinfi karfin wannan y'ar kyautar Amma kiyi hakuri zamuje kasuwa insiya miki komai ya d'anka mata key din motar a tafin hannun ta,



Gaba daya tarasa nayi ita yanzu ta ina zata fara tasan kotace mai bazata karba ba Aikin banza zatayi don ta lura dashi mutum ne mai ra ayin rikyau idan yayi niyyar Abu ba Wanda ya isa ya hana shi, don haka kallo kawai take binshi dashi,


Saida ya bata key din ne tayi saurin girgiza kai" aa nidai ka bar ni banason mota ta ina zanshiga da wannan key din incewa su baba me? Bayan kayan da kashiga dasu nidai don Allah kabari ingama dasu Lafiya,


"Hhhh yayi dariya sannan yace "tom idan bakyaso sai ki yi sadaka nidai nakawo kuma bazan koma dasu ba don kiji,


Matsowa yayi tareda riko hannun ta ya kashe mata ido, "baby kinfa dauki alhakina yau, kiri kiri Kinyi min kwalelen Abin kallo na inaji ina ganin su kin hana ni morewa,


"Tun fa shekaran jiya rabon da in rage ruwan Marana kinga yau Kim in wani Abu Inba hakaba yau bazan iya bacci ba,


Kallon nariga nasaba da halinka kawai takemai kafin tayi magana, "wannan ne soyayyar taka da kake fadar kanamun?


"Sosai baby da banasonki da na danne ki wallahi na rabaki da wannan y'anar dakike yanga da ita tuntuni, "dama kasaba yiwa yaran mutane '


"Point of correction, yaran dake ra ayi dai ko yanzu zuby najirana a gidana zanje ta ragemin wannan ruwan dole yau sai sun zuba zan iya bacci ya fada tareda shafo marar shi,


Cikin takaici ta bude motar ta fita, yana kiranta ta shige abinta Allah yagani tana tareda aiki don KO Auren MA tayi to sai tasamu hawan jini domin shi mutum ne mai yin Abinda yaga dama ba Wanda ya isa ya hanashi,


Fitowa yayi tareda rufe mata motar ya shigo gidan bai koma takanta ba ya ajiye key din akan akwatunan ganin karfe goma harda rabi yasa ya wuce gidan shi,


**********************

Tundosowar shi kofar gate din ya ga motar zuby a wurin ya matse fuska kafin ya shiga cikin gidan, tundaga falon yaci karo da Emanuel,


Yafara yimai ruwan bala'i akan yadawo zai fara barin mai gida kamar gidan karuwai ko, ya fara bashi hakuri jiki na rawa "Oga sory sir I no go do one again, ys fada yana sarawa kamar koda yaushe,



Dakin dake kasan falon ya nufa tareda kullewa gam da key ya fada kan katon gadon ya kife tareda runtse idanun yana tuno Abincin zuciyar shi Yasmin,


Kasa daurewa yayi ya kirata, lokacin tana kwance cike da kishin Kila yana can wurin karuwan nashi har Wasu hawaye takeyi na bakin ciki taga Kiran shi,



Ba jan Aji ta dauka domin tanason tasan halin da yake ciki, "babyyyyyy ya furta yana nishi "ad'aura min Aure zuwa jibi kar inkara lalacewa, I can't sleep Marana babyyy, ya fada cike da bukatuwa tareda sauke mata huci mai zafi a kunne,


Ajiyar zuciya kawai ta sauke tareda fara magana, "kana ina ne yanzu? "Ina gida na a BARIKI, "kaida waye agidan? "Nida zuby ne tana sama ni kuma ina kasa nazo nasame ta agidan,



Wani kululu ne ya tokareta yanzu don iskancin MA yake fada mata shida wata ne a gidan? Tsaki taja mai karfi, ya dago da kanshi daga kwancen "baby ina fatan tsakin ba nawa bane?


Banza tayi mai "Hmm you must pay that, ya katse Kiran, minti biyu ya kuma kiranta again "karki kuma yi koda badani kike ba banaso zan shigo gidan da safe injira baban mu da zai mana Aure,



Ajiyar zuciya tayi tareda rike wayar gam a kunne. "No matter how he is she love him to the extend da bata taba iya fushi dashi tana jin son MA kamar fitar numfashin ta,



"Baby barci kikeji? "Aa tace cikin sauri tareda Kara rungume wayar kamar shi ta rungume "kaifa bacci kakeji? "Aini idan ina tareda ke banajin bacci baby banki mukai safe ba ahaka,



Tuni ta baje idanun ta bude ido tarai domin zataso su kwana tana jin shi kar yaje wurin zuby don jitake ina ma tana barikin yau sai takoreta a gidan, ko yanzu jitake kamar tace ya koreta Amma ita a wa?



Haka suka kusan kwana yana zuba mata sambatu har karfe hudun Asuba kafin ya katse "baby bari inje inyi wanka inyi salla kafin akira asuba kinsani zubarda ruwa jin numfashin ki kawai "baby kema kinajin me nakeji kema kin yi yo yo? Kit ta katse Kiran tana dariyar halin muh'd , shidai baruwan shi saidai inbaiyi niyayyar magana ba duk abinda yafito abakin shi sai ya fada,



Saida tayi Alwala tafara nafila tareda yin Adduar neman zabin Alkhairi a rayuwar ta kafin akira salla tayi ta d'an karanta qur ani kadan tarufe ta haye katifa domin biyan bashi don yau gaskiya saidai mama tayi mata hakuri, Aikin gidan nan saita tashi,



Saidai karfe shida baba ya doki kofar ta ta zabura ta mike idanun ta cike da bacci ta fito waje tana hada Han ya, idanun ta a waje ganin baba ya zubawa akwatuna ido, mama na gefe rike da carbi,




"Fatima wa innan kayan fa ga mota nagani awaje tun jiya ga kuma makulli a anan? Bakin ta na rawa tafara in ina" baba shi ya kawo min Wai tsaraba,



"Harda mota? Inji baba cikin karaji, Amma y'ar nan me kikeso kimayar dani ne karamin mutum? Aurenki saura kwana uku ki karbi kayan wani kato haka akeyi me kika bashi zai miki irin wannan kyauta haka harda motar da har in mutu kudin Albashina bazasu taba siyan rabin taba,



Kuka tafarayi najin maganar baba, mama tace "malam kabi a hankali idan mamuda yazo sai asan nayi KO ka bashi hakuri kawai yadai na zuwa,


Kallon ta yayi da kyau "lallai Saude to bari mamuda yazo muji shi zaisan nayi tunda shine uban yarinya, "aa ai kai zakayi wani Abu akai kafin shi yazo saika jamai layi,


"Anki aja layin kifita idona saudatu inkinaso mu shirya kema ai uwarta ce kija mai layin kuma ki binciki y'ar ki sarai nidai nafada miki kuma itama maryam ina nan yau ina jiranta,



Ya wuce ciki fuuu, mama ta kalleta "saiki kwashe kayan kishigo dasu ciki ai kin kyauta, jikinta na rawa ta Sa hannu ta ja daya dakyar take janta ta shiga da ita tana mamakin yanda taga ya dagasu kamar empty Ashe uban nauyi garesu,


Baccin da bata koma ba kenan ta fara Aikin gida saida ta shirya break takai dakin tajera a falon su mama tasame su suna dramar da ta kun no gidan yanzu na zancen MA, baba yasa ta bude akwatunan duka kayane English wears da takalma masu tsada sai zannuwa masu tsada da jakun kuna da sarkoki harda gwal da passion masu aji ga inter wears dai dai size dinta kusan kowane dozen yakai biyar,


Idanun ta awaje lallai MA d'an iskan ciki da waje ne na bugawa a calendar, baba yakasa magana ya kalleta kwashe kikai dakin ki ai nakine tarkacen,


Haka ta kuma kwashe su baba ya karbi makullin motar yace bari mamuda yazo zanbashi ya mayar mai da ita, "hmm kawai mama tace,



Karfe goma ismail ya iso da jerin saitin akwatunan shi har saiti biyu na yayi ya shigo dasu tsakar gidan da taimakon Abokin shi suka baje su a wurin kafin ya leka falon mama yace tazo tagani in akwai Abinda baiyi ba ya karo natane Dana zainab,



Mama kallon kayan kawai tayi tana tunanin gwaramar dazata biyo baya tasa Albarka tareda cewa "Allah dai ya muku zabin Alkhairi ismail in Yasmin rabonka ce Allah yasa ayi damu in kuma ba rabonka bace Allah yabaka dangana,.......... 🖊️

Kujira sabon post zuwa dare mutane na insha Allah,

*lamarin nan yafi karfi na my fan's kuyi Addu ar sauki don akwai gwarama nake gani gaba akwai kura*



*Matar Soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻



_written by FENERH_
Maman Ammar


*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby


31&32

Yasmin na daki tana maida bacci batasan ma me yakeyi ba a tsakar gidan, karfe sha daya baban zango ya iso Shima, ya tarar da kayan a nan,


Bayan sun gama gaisawa da mama ya zauna takawo mai Abin kari yanaci yana kallon kayan saida yayi kat ya fara tanbayar yayan shi,


"Saude ina Yaya? "Malam ya fita yanzu zai dawo baiyi nisa ba, "wa innan kayan zainabu ne ko? "Eh da na Yasmin, "waya kawosu? Yafada cike da rainin hankali, "na ismail ne, "Wato duk maganar da mukayi dashi baiji ba KO?



"Mahmud Kayi mai Addu ar zabin Allah kawai kubi komai Ahankali, "to nidai Yaya yakirani akan maganar soja kuma nidai Saude inkinga ba ayiba to bana numfashi,



Ko kuma shi yace bayaso ai ni tunda ismail yakawo maganar Auren Zainabu naji hadin yafita araina banason Auren shi da mama na nafison tayi Auren hutawa ba gidan kishiya ba,



Dariya mama tayi "Au shiyasa Kuka kasa Aure kaida malam? "Ai kune Kuka hanamu keda hinde "aa karkuyi mana sharri baruwan mu mukan,


Rahar su suka taba kafin dawowar baba suka zauna domin neman mafita "ai ni Yaya inada mafita don gobe su liman zasuzo mu Amshi kayan Aure shi yaje can yakai ma zainabu wa innan duk mun yafe,



"Mamuda kana Abu kamar mace wallahi nidai ismail zanbawa Aure "to mu zuba muga uban ya' Sallamar MA ce ta tsayar dasu ya shigo cikin haiba sanye da kakin nashi green kanshi ba hula yayi matukar fitowa kayan na mugun Amsar shi,


Suka gaisa mama ta kawo wata kujera ya zauna, baban zango yace "Saude karo mana kosan idan akwai da kokon, ta ce to ta shiga kitchen tareda hado wa kan tray cikin jug mai kyau ta dakko kular kosan hade da cup da kuma robar sugar ta Ajiye musu tareda komawa daki,
Domin basu wuri su tattauna,


Baban Zango ya ce "suriki na bismillah ga Abin karya wa ko bazaka iya cin Abincin mu ba,?
"Noo baba ai inason gargajiya sosai ya dauki karamin kofi ya tsiyaya kokon tareda Sa sugar kadan domin ciwon shi,


Yasaki jiki dasu sosai yanasha yana zuba musu hira har baba dake d'ari d'ari yasaki jiki baban zango daman shi akwai son shafta, saida yaci sosai don kosan Yamai dad'i yayi hamdala daman dokin ganin Yasmin bai Sa ya tsaya karya waba daga office kawai ya gudo, gashi baiji ko motsinta ba Anya ma tana gidan,?



"Toh muhammadu kake ko? Inji baban Zango yace "Alhmdulillah naji dadin da kakeson jinin mu kuma Kayi mutunci daka zo kai tsaye ka same mu kuma indai nine mad'aurin Auren mama na to nabaka gobe muna jiran zuwan manya,


Saidai kuma wani hanzari ba gudu ba kasan da zancen Aurenta da Dan uwanta to yanzu dai yasamu wata kaga iyaye mata muke jira yanzu sukai akwati in Allah yakai mu jibi a daura Aure,


Toh yanzu dai naku maganar Auren sai manyanka sunzo sai muga kamar wata nawa zamu sa, yayi saurin kallon baban dake magana


"A gaskiya inaso a daura da namu jibin ni basai kun tsaya wani shi shiri ba tunda dama a shirye kuke da Auren don haka don Allah Karku daga a barshi a hakan,


Baba kallon shi kawai yakeyi y'anda ya ke rokon a daura mai Aure jibi sai kace y'ar tsana ko kuma mara Gata,


Baban zango yace "ka bar magana sai su manyanka sunzo wannan tsakanin mune zamu tsara komai,

Shiru kawai baba yayi yana ganin zamani agabansu yaro yazo yana zaben ranar Auren shi,
MA shiru kawai yayi bai gamsu da wani zancen daga Aure ba, don bazai haifarda da Mai idoba don gaskiya hakurin shi yakai bango,




Kamar a mafarki Yasmin take jiyo maganar shi atsakar gidan tareda kamshin shi mai rikitarwa duk da haryanzu katifar ta na kamshin jikinshi Amma Wanda takeji tasan fresh ne, ta zabura tareda lekawa ta window shine da gaske tana mam akin y'anda ya zage sai hira sukeyi kamar sundade da sanin juna gashi harda kofin koko a gaban shi lallai MA baida ta I do,


Kamar yasan tana kallon shi yakalli dai dai window sukayi ido biyu ya kashe mata ido tareda bata wani shegen murmushi, tayi saurin sakin labulen ta koma tana dafe kirji kawai tagama sallama wa MA,



Wayar shi ya danna ya tura mata sako _"kifito ko intashi inshigo kinsan zan iya_
Ai ba wasting time ta sako guntun hijabi akan kayan doguwar rigar dake jikinta kana kallon ta kasan bacci ta tashi,


Tafito kamar mara gaskiya ta gaida su baba batareda ta kalleshi ba baban Zango yace "Aa mama na dama kina ciki a she? "Eh baba bacci nakeyi, "to y'ar Albarka kwashe kayan nan ki shiga dasu mungama,



Tunda ta fito ya zarga mata na mujiya tareda yin Ajiyar zuciya yana jin wani irin nishadi Allah yasa su baba su yarda su mallaka mai wannan halitta ko zai samu natsuwa shidai gaskiya ya mutu kan kaunar Yasmin,



Kasa fitowa tayi daga kitchen din tarasa Abinyi idanun shi sunyi mata kaifi sosai, jin yana musu sallama yasa tayi Ajiyar zuciya tareda hamdala,


Saidai yana fita ya dsnna mata Kira ta daga ba bata lokaci yace "ki fito inganki ina waje,


Zuru tayi Rashin mafita yasa ta fito sum sum ta fice, a jikin motar shi ya dogare tareda zubawa kofar gidan ido,


Tsayawa tayi daga nesa ta kasa cewa komai, "good morning madam Muhammad Abdullah, murmushi tayi mai kayatar wa kafin ta Gaishe shi yace ki motso ko inzo indauke ki,


Karasowa tayi cikin takunta mai ban sha awa "wow masha Allah yafada yana kallon ta kamar ya rungumota yakeji,


"Baby Hajiya tayi farin ciki sosai da maganar Auren nan Hajiya ta na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login