Showing 15001 words to 18000 words out of 42953 words
suna hira hirar da rabinta kan yanayin aikin sune har suka karasa aiport ya sauka a mashin ɗin sukai sallama ya nufi ciki, awa guda cikin jirgi ta kawo su garin kano bayan ya fito daga cikin airport ya shiga da zai kaisa unguwarsu wayarsa tayi kara ganin sunan Rubina yasa yai murmushi ya ɗaga kiran da ƴar dariyarsa
"Ƴammatan Candy nayi diley ko afuwan sister laifin Captein ne"
"Assalamu alaikum" ras gaban Uwaimeer ya faɗi jin muryar namiji jikinsa yai sanyi sosai bugun zuciyarsa ya karu yana fita fat fat jin abinda ake faɗa masa ta wayan
"Yanzu kuna wanne hospital to?"
"Nan Annury hospital"
"Gani nan" Uwaimeer yai magana da mai nape ɗin ya gaya masa inda zai kaisa yanzun kana ya kira BAFFA yasanar masa hankali tashe Baffa dake zaune a kasuwa yasa Amjad suka nufo hospital ɗin
Uweir hankali tashe ya shiga hospital ɗin ya kira lamban Rubina Nureed deen ya ɗaga ya fito ya masa jagora ɗakin da Rubina ke kwance mintina kaɗan Baffah da Amjad suka iso, ganin a halin da Rubina take ba karamin tashi hankali Uwair yayi ba, ganinta kwance vata ko motsi, Uwaimer ya sake dubata sosai kasancewarsa na likita ya tabbatar tana nan lafiya barci kawai take
"Amjad ka kai Uwaimeer gida ya samu ya cire wannan kakin ya huta gajiyar hanya ka tawo da Fatima Ummi"
"Baffah dan Allah basai na tafi ba ka barni anan da dare bayan ta farka saina koma gidan"
"Kariga ka sani bana magana biyu," Baffah ya maida hankalinsa ga Nura da Lameen dake rakuɓe waje ɗaya kallo ɗaya zaka masu kasan suna cikin tashin hankali, ya yafito Nura da hannu alamar yazo, Nura yakaraso gaban Baffa ya tsugunna har kasa
"Kaima ka tafi gida ka huta kaji ɗan samari mun rigada mun san kaddara koda mutuwa Rubina tayi lokacinta ne yayi to alhamdylillah tana ma raye, Amjad a sallami police ɗin nan shima yatafi bakin aikinsa"
"Tam Baffah" Amjad ya amsa yana kokarin zaro kuɗi daga aljuhun sa na wando, Lameen ya kama Nuraddeen suka futa bayan sunyi sallama dasu Uwair da ɗan sandan dake lasar leɓe ganin Amjad ya fito da sababbin kuɗi yana ƙirgawa
Ummi tsaye a compound na gidan BAFFA sai faɗi in faɗa suke da Hajiya Zainab mahaifiyar Sulaiman da take karewa Sulaiman faɗan da Ummi ke masa
"Zainab na rantse da Allah ki fita cikin magan nan inba haka ba zan matukar saɓa maki wallahi zan nuna maki ni ɗin jinin kanuri ce zan nuna maki bansan tsoro ba banda rashin mutumchi motar danshi kaɗai aka siya ko danshi kawai aka ajje driver yarinka kai sa makaranta kunbi kun tsamgwami yarinya itada gidan ubanta"
"Ahayye nanaye cass gidan ubanwa nace gidan ubanwa nan ne gidan Uban Rubinan can dai adaije can anema mata wani uban amma ba dai Baffah Yarima ba wallahi, kuma sulaiman abinda kayi kamin dai dai Allah ma yataimaka da yau kun gama school ɗin dana gaya maka daga yau karka kuma sakewa ka zauna mota ɗaya da wannan shegiyar ƴar wama ya sani kilama ungulu ce ta koma gidanta na tsamiya, kuma idan baki nuna min ke jinin kanuri bace ba yau baki haifu cikin Yagana ba" Ummi ta fusata sosai jinta take iya wuya zaryar ta biyu a motarta zuwa makarantar su Rubina amma ba ita ba dalilinta a fusace ta shammaci Hajiya Zainab takai mata wani duka a fuska sai ga jini ya fara zuba daga hancin Hajiya Zainab ɗin, da sauri Ummu da shigowarta gidan kenan ta dawo daga unguwa ta ruko Ummi ganin tana kokarin sake kaiwa Hajiya Zainab wani dukan
"Subhanallah Ummin Rubina mai zan gani haka yau mai yasa zaki biyewa Maman Rahama kuzo kuna wannan abin kunyar kamar wasu kana nan yara"
"Barni Ummu barni yau na nunawa matan nan ba tsoronsu nake ji ba, ba Baffah bane sabida shi daman nake ragawa kowa a gidan nan to daga yau na daina ɗagawa kowa kafa wanda duk ya taka ni nima zan taka sa akarshe maine dai sakine ko to ya sakeni na ɗauke Rubina na bar maku gidan da ita natafi inda zamuji daɗin rayuwarmu"
"Ki tafin mana wane bai sani ba kowa ai daman ya sani wajan biye biyan mazanki kika samo cikinta ai" Hajiya Umma ta faɗa wacce bata daɗe da zuwa wajan ba
"Na samo ɗin ki bari mata masu aji suyi magana ba irin kiba mara mutunchi da asali" da kyar Ummu ta iya jan Ummi zuwa part ɗinta tana vata vaki tareda nuna mata illar biye ma Hajiya Zainab da tayi, acan Hajiya Umma itama ta taimakawa Hajiya Zainab jinin dake zuba daga hancinta ya tsaya taci gaba da mita tareda cin alwashin saita kawo karshan zaman Ummi da Rubina a gidan kota halin kaka, Amjad da Uwaimeer sanda suka shigo gidan sukaga ma'aikatan gidan mata da scurity sunyi cirko cirko suna magana kasa kasa sam basu kawo komai ba azatonsu sun sami labarin haɗarin Rubina ne kai tsaye Uwaimeer ya wuce part ɗin hajiyarsu shima Amjad nasu part ɗin ya nufa ya tarar Ummu na rikeda Ummi da har sannan take mita da sauri ya karasa gaban Ummu yana tambayarta lafiya nan ta zayyane masa komai Amjad ya shaida masu abinda ya sami Rubinan Ummi ta gyara kanta suka koma hospital
Hajiya Zainab ta koma part ɗinta tana mita ta kira lambar Baffah tana kuka ta fara magana "Baffah ka dawo gidan nan kafin matarka ta kashe ni, harni wannan yarinya Fatuma zata saka hannu ta daka"
"Zainab wai mai yasa bakwason zaman lafiya ne in an girma asan an girma mana kuna abu kamar kana nan yara"
"Zakace haka mana Baffah tunda ba nice na taɓa ta ba to wallahi ko ka taka mata birki ko kuma na aika a rama min"
"To yi hakuri bari nazo gidan muyi maganan yi hakuri" kwafa Hajiya Zainab tayi ta katse kiran tana zagaye a falon nata
Baffah yabi Ummi da kallo ganin yanda ta shigo ɗakin tana cika da batsewa ko kallon inda yake batai ba, Baffa yai murmushi kana ya ce "Kinga tsautsayin da Rubina ta gamu da shi yau ko?"
"Ka kira haka da tsautsayi mana bayan ɗanka Sulaiman shiya biyo driver suka tawo suka barta a can wannan ba tsautsayi bane gangancin Sulaiman ne"
"Kiyi hakuri ai tafaru ta kare nan da ƴan watanni Rubina na gidan mijinta kilama bata kanon ma gaba ɗaya" wani kallo Ummi taiwa Baffah kafinta ta magantu
"Aure kuma Baffah dan Allah ba yanzu ba duka nawa Rubina take sixteeen fa dan Allah ka bari ta cika burinta a karo na farko na roki wannan alfarmar dan Allah" Ummi ta karashe magana tana haɗe hannunta biyu waje ɗaya alamar roko
"Idan nai haka zai tabbata kenan banyi adalchi a tsakaninta da sauran ƴan uwanta ba, inda zan iya barin mace tai karatu bayan ta sami mijin aure to Sanah ce sabida kokarinta da burinta ako da yaushe amma na take haka na mata aure to akan Assama'u ma bazan karya wannan dokar tawa ba"
"Baffah Rubina batada wani wanda kesonta a hanzu ko yazo da maganar aure"
"Gani ko yanzu a shirye nake dana karɓarwa kaina auranta" da sauri Ummi da Baffah suka kalli bakin kofa inda Aliyu ke tsaye bakin kofar ya harɗe hannayansa a kirji yana murmushi, Ummi ta wurga masa harara batare da ta ce komai ba ta karasa gaban gadon da Rubina ke kwance, Baffah yai murmushi irin nasu na manya kana ya ce
"Na baka dama kaje ka nemi soyayyar Rubina idan har ta amince maka na baka ita...."Ni kuma bada yawuna ba ban amince Aliyu ya tunakari Rubina da wannan maganar ba mai kuke zato wanne hali kuke ganin Rubina zata shiga ni a gaba ɗaya gidanka ma bazan taɓa laminta wani ya ce yana sonta ba" Aliyu ya buɗi baki zai magana Ummi ta katse sa da "Billahil aIzim Aliyu kai sake wani sirri ya fita har Rubina tasan ko ita wacece ban yafe maka nona daka sha ba"
"Subhanallah Fatima maine haka mai kike kokarin yine kin san kuwa mai kika faɗa"
"Na sani Baffa ina sane sabida ina cikin hankalina" Aliyu ya koma ya jingina da bangon ɗakin dayake ji yana zagayawa da shi ya jima a haka yana bin su Baffa da idanu da suke ta musayar yawu kafin zuwan su Uwaimer da Daddy Mahmud yakatse masu maganan
🔯🔯🔯🔯🔯
Alhaji Sammani ya fito daga cikin motarsa yana sanye cikin shiga ta mutumchi kai tsaye ya shiga cikin division ɗin ya nemi da yana son magana da D P O daga farko ƴan sandan dake gaban kanta sun so masa gardama amma daya fito da I D card ɗinsa nan da nan sukai masa iso wajan D P O bai jima a ciki ba aka kawo masa Sani aka cike takardu ya tawo da shi bayan ya sallami D p o ɗin dayai masa rakiya har wajan motarsa, a mota suna tafe yana yiwa Sani faɗa akan laifin da ake tuhumarsa da shi saida yakaisa bakin titin layinsu sannan ya sauke sa ya ce ya karasa gida bayan ya basa 5k yace yaje ya canza askin kansa yayi mai kyau sannan yai gaba, Mama tana zaune a tsakar gida tana gyara shinkafa saiga sallamar Sani tsam ta mike tana yiwa Allah godiya kafin kuma jikinta yai sanyi tuna yanda sukai da Alhaji Sammani, ta karɓi wayar Salima ta shiga ɗaki tasa lamabar Sammanin ta kira sa amma tai ta ring bai ɗaga ba, shi kuwa Alhaji Sammani ɗokacin yana tare da Matarsa dan bayan ya sauke Sani gidansa ya wuce
Mama ganin Alhaji Sammani bai ɗaga kiran ba yasa ta bawa Salima wayarta taci gaba da sabgoginta na gida tana jin Salima da Marwa nawa Sani faɗa batace masu komai ba, acan gidan Alhaji Sammani kuwa jin ring na waya yayi yawa yasa matarsa tai magana da
"Alhaji wayarka fa ake kira kana ji"
"To wayarki ko tawa Halima? ko haka kurum daga ganin bakuwar lamba saina ɗaga kira bansan wane ba" wani kallo na tuhuma matar tasa tai masa kamar zatai magana kuma dai saita fasa taci gaba da kokarin haɗa masa abincin da take
"Amma Abban widad ka dawo da wuri, nifa na zaci ma ko shigar dare zakayi?"
Alhaji Sammani ya gyara zama kana ya ce "Ai ina gaya maki ba ina kadunan ba kawai yau da sassafe saiga kira daga katsina wai akwai wata ganawa ta musamman da zamuyi da gwamman katsina a daran yau shine fa ba shiri na baro kaduna na shigo kano da wuri danna samu na ɗan huta da yamma nabi jirgi zuwa katsina" ta ɗan ɓata rai kaɗan tana kallon mijin nata kana ta ce
"Yanzu Abban Widad yau ma bazaka kwana a gida ba gaba ɗaya satin nan fa baka kano baka Abuja kaduna yau kuma katsina gaskiyya nidai wannan karon dani za'ayi tafiyar nan" ɗan zaro idanu Alhaji Sammani yayi kafin ya basar ya saki murmushi
"In tafi dake kuma haba sai kace nine na mamajo sarkin mata, tona ajjeki a ina duka awa nawa zanyi na dawo nai maki alkawarin gobe karfe goma na safe nadawo gidan nan nima kwana biyu ina matukar kewarki"
"A'ah nidai Allah ban yarda ba gaskiyya dani zaka"
"Mubar maganar nan Halima ni kaɗai zanyi tafiyata nai maki alkawarin da safe zan biyo jirgi zakiga kamar a gida na kwana" bata sake cewa komai ba tamaida hankali ga danna wayarta ya mike bayan ya kammala cin abincin ya shiga ɗakinsa yana faɗin
"Halima bari na ɗan warware gajiya a ɗaki ina futowa" ya nufi ɗakinsa Halima ta bisa da kallo harya shige ɗaki ta sauke ajjiyar zuciya kafin ta mike ta shiga ɗakinta itama, Alhaji Sammani na shiga ɗakinsa ya saka key ya zauna gefan gado ya dannawa lambar da aka kirasa yanzu kira wacce yake zaton Abu ce ke kiransa sai dai muryar da yaji ta amsa masa sallamar dayai ta doki dodon kunnan sa lokaci ɗaya muryar ta doki zuciyarsa yaji ya kwaɗaitu da son ganin fuskar mai wannan muryar.....
07039793439
🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹
Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Association* ☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA
Episode seven7️⃣
*Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne*
"Hello hello banaji" Salima ta faɗa jin shuru tai saurin katse kiran tana kallon Mama
"Mama wannan kamar lambar da kika kira jiya fa" Mama ta karɓi wayar dai dai kira ya sake shigowa ta danna wajan amsa kira ta kara wayar a kunnanta tai sallama, Alhaji Sammani ya sauke ajjiyar zuciya kana ya amsa sallamar tata
"Alhaji barka da rana ya aiki na gode sosai da kokarinka ɗazun nan naga sani yadawo mungode sosai"
"A ba komai ai yiwa kaine, amma wannan wayar wace?"
"Ta Salimah ce"
"Ok to to hakane fa na tina jiya kin gaya min kin saida taki to bari na siyo maki wata babbar taki in mun haɗu anjima saina baki"
"To" ta faɗa jiki a sanyaye sukai sallama tabawa Salima wayar, Salima ta karɓa tana aikawa Mama kallon tuhuma, harta mike zata shiga ɗaki ta ce
"Mama wannan ɗin wai waye kika kira"
"Kanin hajiya Sakina ne shiyaje yatawo da Sani daga wajan ƴan sanda" Salima ta gamsu da maganar mahaifiyarta ta juya ta shiga ɗakinsu ta kwanta lamo tana tunanin mafita ga rayuwarsu, mama har akai mangariba jikinta sanyaye yake ta rasa ta yanda zata sanar da yaran nata zata fita harma taje wani wajan ta kwana sai sake sake take a ranta, wayar salima ta karɓa tai bloking lambar Alhaji Sammani sannan ta goge lamban bayan sallar mangariba ta mike tai wanka tai sallah ta kalli Salima dake zaune tana danna waya ta ce
"Salima zan fita gidan hajiya Sakina zani anjima zan dawo"
"Mama mariri a daran nan har yaushe kikaje yaushe kika dawo"
"Zuwan ya zama dole Salima inta kama ma zan kwanan yau Babanku banan gidan yake ba in kunjini shuru ku rufe gida"
"To" Salima ta faɗa jiki sanyaye ta saka hijab ɗinta taiwa Maman tasu rakiya zuwa titi har tahau abin hawa sannan ta dawo gida, kai tsaye Mama hotal ɗin da suka saba haɗuwa da Alhaji Sammani ta nufa ta shiga kanta tsaye kasancewar ba wannan ne zuwanta na farko ba harta ɗakin dayake zama ta sani hakan yasa kai tsaye ta nufi can, lokacin data shiga ɗakin yana zaune kan kujerar dake cikin ɗakin yana kallon wasan kwallon kafa a t b daga shi sai gajeran wando ko arzikin singlate babu a jikinsa yana ganinta ya wani washe baki yana mata dariya kallo ɗaya Mama tai masa ta ji gabanta ya faɗi ta raɓa gefan gado ta zauna har sannan gabanta na faɗuwa
"Harna zaci bazaki zo ba nayita kiran layin nan na ɗazu da mukai waya baya shiga kinga wayarki" yafaɗa yana ɗago mata kwalin sabuwar waya tsadadda, mama ko kaɗan bataji wayar ta burgeta ba
"Na siyo maki babbar waya wacce zamu ringa vidio call sannan daga yau bana son mu kuma haɗuwa dake anan a kwai keɓantaccan gidana dake wajan gari mu koma can da hulɗa"
Mama dai na zaune gefe ta kasa cewa uffan, harya gama kallon kwallo yadawo kusa da ita yafara sarrafata tana jinsa hawaye kawai ke zuba daga cikin idanunta wai yau ita ke zina da auranta abinda bata aikata lokacin kuruciya ba sai gashi yanzu da shekarunta tana aikatawa tsawon lokaci tana jinsa yana sarrafa jikinta tun bata biye masa har shaiɗan ya kawata mata abin ta fara mayar masa da martani kasancewar ta jima bata ji irin haka daga mijinta ba tsawon shekaru, sun jima sosai a wata duniya kafin suka dawo duniyarmu, gaba ɗaya Alhaji Sammani ya gigice sabida yanda sheɗan ya kawata masa Mama yaji daɗinta fiye da na duk matan dayake hulɗa da su, washe gari da kyar ya barta ta tafi sai nan nan yake da ita ya bata wayarta da kuɗi dubu ashirin bayan sunyi alkawarin sake haɗuwa nan bada jimawa ba ta nufi gida cikeda ɗokin ganin iyalanta
🔯🔯🔯🔯🔯
Nuraddeen jiki sanyaye yake tuka motar tasa tsakanin shida Lameen ba wanda yai magana har suka karasa gidansu bai shiga da motar ciki ba yai parking ɗinta a wajan gida suka shiga gidan a tare, Innah na zaune cikin babbar barander tana shan iska taga shigowar Lameen da Nura a kallo ɗaya datai masu ta lura ba lafiya ba, tabisu da kallo har suka karaso inda take Nura ya zauna gefan tabarmar da take kai Lameen ya tsaya daga tsaye ya jingina da bango ta bisu da kallo kafin ta maida hankalinta duka ga Nura ta ce
"Lafiya kuwa Nuraddeen maiya sameka bayan fitar taka ina motar ka? kai Lameenu yaushe ka fita daga gidan nan naga motarka na zaci kana ɗaki kana barcin naka daka saba"
"Innarmu Nura ne ya gamu da tsautsayi ya buge wata yarinya"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku ni Fatsima la'ilaha illallahu yanzu ina yarinyar maiya same ta Nura garin yaya haka ta faru"
"Innah tsautsayi ne karki tashi hankalinki dan Allah ba wani ciwo bane babba tana ma asibitin da kike ganin likita" Inna ta mike tana laluban mayafinta ta shiga ciki ta fito sanye da hijab
"Kai Lameen kaini asibitin yanzu yanzu" Lameen da Nura suka kalli juna Nura ya mike ya kama Inna suka shiga ciki ya zaunar da ita kan kujera ya zauna gefanta ya saka hannunsa cikin nata ya ce
"Inna na gaya maki karki damu, Baban yarinyar yace nadawo gida na huta anjima saina koma ki kira mai tayaki aiki a girka abinci sai a tafar masu da shi anjima bayan nai wanka saimu koma tare"
"E fa kuma hakane Nura nida harna fara ruɗewa to bari na kirata a waya saita zo kai Lameenu zo mu fara aikin tare da kai kai kuma Nura jekai wanka ka canza kayanka zuwa sannan mun gama Allah yasa munada komai a gidan nan kamar ka san haka zata faru jiya kayo uban siyayyar nan Allah dai yamaka albarka Nura"
"Innarmu Nura kaɗai banda ni"
"To yi hakuri bansan kashigo ba ai kaima Allah maka albarka" Innah da Lameen keta aiki cikin kicin ta kira wayar yarinyar tace mata bata nan sun fita unguwa da Mamanta, har Nura yai