Showing 18001 words to 21000 words out of 42953 words
wanka basu gama ba shima ya shigo suka taru suka dafa haɗaɗɗiyar shinkafa da miya da taji tsokar nama dai dai misali girkin sai kamshi yake suka kammala komai Lameen ya zuba komai cikin babban basket suka fito a bakin titi suka tsaya suka sai ruwan roba katan biyu da lemun gora shima katan biyu, lemo ayaba kankana duka suka saya sannan suka ɗau hanyar hospital
"Ummina wayyo Ummi kaina hannuna wayyo Yay Meer zan mutu" da sauri Uwaimir da gaba ɗaya hankalinsa ke kan Rubina ya karasa gaban gadon ya ruko hannun Rubina mai lafiyar a ruɗe yafara magana da
"Rubie Rubina buɗe idanunki kin ganni anan kusa dake ga Ummi ma"
"Yay Meer idanuna sun min nauyi kamar bazan iya buɗe su ba"
"Zaki iya zaki iya Rubie ambaci sunan Allah kice bisimillah sai ki buɗe su a hankali, maza maza buɗesu dan Allah nagansu" ahankali ta fara motsa idanun nata kafin ta buɗe su tarwai akan fuskar Uwaimir takai hannu ta shafo fuskar tasa sannan ta maida ganinta ga Ummi dake tsaye a gefe, ta zare hannunta daga na Uwaimir ta mikawa Ummi hannu, Ummi ta karaso gaban gadon tana gyarawa Rubina gashinta
"Sannu mamana Allah yabaki lafiya kinji kin gamu da tsautsayi" hawaye suka zubo daga idanun Rubina Uwaimir yasa hannu ya goge mata zuwan baffa gaban gadon yasa Uwaimir yai baya ya bawa Baffa waje
"Sannu sannu Asma'u kinji Allah yabaki lafiya"
"Baffana" na faɗa a hankali ina kai hannuna mai lafiyar na ruko hannunsa "Baffah bana son hospital mu koma gida Baffah"
"Sannu to zamu koma amma sai kin warke kinji yarinyata Allah yabaki lafiya"
"Assalamu alaikum" Innah tai sallama ta shigo ɗakin bayanta Lameen ne da niki nikin kaya a hannunsa shima yayi sallama kamar yanda tayi
"Alaikus salam sannunku da zuwa" Ummi ta faɗa da fara'arta kamar ta sansu ta nunawa Innah wajan zama tareda faɗin
"Sannu mama ga wajan zama" Innah tai murmushi tana faɗin
"Na zauna kuwa bari na fara duba mara lafiya" Nura ya shigo shima da sallama hannunsa rike da lemu da ruwan da suka siyo ya gaida Baffa cikin girmamawa kafin ya gaida Ummi yana tambayarta yamai jiki, yabawa Uwaimir hannu sukai musabaha kafin ya koma kusa da Lameen ya tsaya yana kallon Innah
"Nuraddeen zoka ga mara lafiyan taka ta farfaɗo" inna ta faɗa batare data juyo ta kalli Nuran ba ahankali ya tako yazo har gaban gadon ya kalli Rubina kallo ɗaya kana ya ce
"Ya jikin Allah yakara lafiya" daga haka baice komai ba ya juya ya koma kusa da kaninsa ya tsaya, Innah ta kalli Baffah cikin girmamawa tana mai basa hakuri kan tsautsayin daya faru
"Ba komai Hajiya ai kaddara tana kan kowa" Baffah yamaida hankalinsa ga Ummi ya ce
"Fatima zan koma gida sai dare zan dawo inaga ma zanyi magana da Dr ɗin nan a canza mata hospital ko zuwa gobe ne" Ummi tabi bayan Baffah tai masa rakiya har wajan da Amjad ke zaune cikin mota yana jiran fitowar Baffan, Ummi tai masa fatan sauka lafiya ta maida murfin motar ta rufe masa ta koma ɗakin daya rage daga Uwaimir sai Su Innah
"Hajiya ga Abinci nan munzo maku da shi ba yawa"
"Mungode Allah yasaka da alkhairi, Uwaimer zuba mata abincin taci" Uwair ya mike ya ɗauki plat ya ɗauraye kana ya zuba mata abincin ya karasa gabanta, Rubina ta kauda kai gefe ta ɓata fuska
"Yay Meer ni na koshi fa"
"Mai kikaci? kila rabonki da abinci tun safe fa, dan Allah tashi ki wanke bakinki ki ci"
"Nidai A'a" ya ajje plat ɗin abincin kan pridge ɗin dake gaban gadon ya harɗe hannunsa a kirji yana kallo Rubinan, Ummi ta karaso wajan ta taimakawa Rubina ta zauna ta kawo mata ruwa ta kuskure bakinta sannan ta ɗakko abinci tai bisimillah takai mata cokalin abincin bakinta ta karɓa ba musu ta fara ci, Uwaimeer ya fita bayan ƴan mintina sai gashi yadawo ɗakin hannunsa rikeda leda mai tambarin shoprite ya zauna kusa da Rubina ya buɗe ledar lemun da taga ya fito da shi yasa ta washe hakora takai hannu da sauri ta karɓi kwankwanin lemun da har Uwair ya buɗe mata ta kafa kai ta shanye sa tas bata damu da sanyin sa ba,
"Thank you Broth" murmushi kawai yayi bayan ya fito mata da choculate ya mika mata, kafin wani lokaci ɗakin ya cika da yayun Rubina mata ƴan ɗakin Ummi, Ummi da mamaki take kallon Warisha ta ce
"Waya gaya maku Rubina na hospital"
"Uwaimeer yai posting a family group" Ummi ta kauda kai gefe tana kallon ƴaƴan nata mata, tai murmushi kawai, washe gari Baffa ya canzawa Rubina hospital bayan yabawa Nura hakuri aka cigaba da kulawa da lafiyar Rubina Uwaimeer ya koma wajan aikinsa sai dai ko yaushe suna wayada Rubina wani binma vidio call suke ta wayan Amjad ko Ummi, kafin wani lokaci Rubina ta warware hannunta ya warke aka sallaesu suka koma gida akaci gaba da kula da ita, Nura da farko bayan sun koma gida yakanje kullum ya dubata ganin ta ji sauki sosai yasa ya daina zuwa sai jifa jifa
Rubina yau ina zaune gaba ɗaya rashin waya a hannuna yadaman data Ummi nake amfani hakan yasa yau da muna wayada Yay Uwair na masa korafin rashin wayata
"Rubie nasai maki waya tun randa tsautsayin nan yasameki simcard ɗinki na cikin wayarma suna nan a wajena da tsohuwar wayarki"
"To yaushe zaka zo?"
"Cikin satin nan zan samu nazo ko kwana ɗaya nayi kinsan yanayin aikinmu Rubie"
"To Allah ya kawo ka lafiya"
NURADDEEN
Yau kwanansa biyar kenan baije yaga mara lafiyarsa ba gaba ɗaya sai yaji yadamu sosai, Allah Allah yake yau ayi sallar juma'a yaje baisan maike fisgarsa ba yake son yakai mata ziyara, bayan sallar juma'a da kyar yabari akai la'asar ya nufi gidan Alhaji Baffah Yarima a kofar gidan ya faka motarsa ya nufi kofar shiga get na farko na gidan, ɗaya daga cikin scurity masu tsaron kofar ya mike yana yiwa Nura barka da zuwa tuni sun saba da shi kasancewar Nura mutum ne mai barkwanci gashi da hannun kyauta sam abin hannunsa bai damesa ba kusan duk randa yazo suma suna samun rabonsu
"Barka da zuwa Brister"
"Barka dai" Nuraddeen ya faɗa yana mika masu hannu sukai musabaha kana ya shiga can cikin gidan kai tsaye ya nufi part ɗin Ummi ya tsaya bakin gate ɗin sashin yana knocking, Khalipha ya zo ya buɗe masa kofa ya basa hannu suka cafke kamar wasu abokai
"Khalipha cewa Ummi gani nazo" Khalipha ya koma ciki ya sanar da Ummi, Ummi ta gyara zaman mayafin abaya dake kanta kana ta ce
"Kace masa ya shigo" Khalipha ya juya ya fita suka shigo tare, Nuradden ya tsugunna yana gaida Ummi
"Barka da yamma Ummi fatan an wuni lafiya"
"Lafiya kalau Nura ya gida ya Innah kwana biyu"
"Inna tana nan lafiya tana gaidaku"
"Muna amsawa ga waje nan zauna mana" Ummi ta faɗa tana nuna masa kujera, ya zauna ta kalli Khalipha ta ce
"Ka cewa Habiba ta kawo ma bako ruwa da lemu da snack" Khalipha yace "to" ya mike ya nufi ɗakin da mai aikin take ya sanar mata abinda Ummi ta ce sannan ya fita, Ummi ganin Habiba ta kawo ta mike ta basa waje tana faɗin
"Nuraddeen kasha ruwa bari na turo maka mara lafiyar taka, yau zaman ɗaka take" ta nufi ɗakin Rubina, Nura ya cire hularsa ya ajje kusa da shi ya saki murmushi yana kafe kofar ɗakin da Ummi ta shiga da idanu haka nan yarasa mai yasa zuciyarsa ta kagu da taga fuskar Rubina, minti biyu tsakani saiga futowar Rubina da Ummi a tare Ummi ta nufi kichin yayin da Rubina ta fuskanto inda yake zaune tana masa murmushi, wani abu yaji ya caki zuciyarsa lokacin datai masa murmushi
"Lah Yaya Nuri kaine yau nayi fushi kwana biyu baka zo duba ni ba" Nura ya gyara zama yana jin wani sanyin daɗin sunan data kirashi da shi "Nurii" ya maimaita sunan a cikin zuciyarsa
"To ayi hakuri na shiga sabgogi ne shi yasa amma amin afuwa yau gani nazo ya kike ya hannun" Na washe baki ina mikar da hannun na nuna masa
"Kaga hannun ai ya warke nifa na zata ma bazai koma dai dai ba" na karashe faɗi ina dariya
"Gashi nan kuwa ya koma kam masha Allah ya Baffah"
"Baffah alhamdulillah jiya nan shida Yaya Amjad suka tafi saudiyya umara"
"Masha Allah, ubangiji yadawo dasu lafiya"
"Amin, yanaga baka ko sha ruwa ba" na faɗi haka ina mikewa daga inda nake zaune na buɗe gorar lemun na tsiyaya masa a cup na mika masa yasa hannu ya karɓa idanunsa cikin nawa ya ce
"Thank you" na zuba masa snack a plat na tura masa a gabansa naja masa teble ɗin yaje gab da shi
"Bisimillah"
"Wai wannan duk ni kaɗai kawai ma samosa ɗin nan guda ɗaya ma ta isheni"
"Ah haba ai kuwa sai ka cinye su duka" na faɗa ina ƴar dariya, ya zaro idanu kamar wata mace ya lumshe su ya ce
"Ni awa na cinye wannan kuma ina zan kai abincin Innah"
"Sai ka gaya mata a koshe kake kazo nan kaci snack" yai murmushin gefan baki yanabin Usham da kallo daya fito daga wani ɗaki hannunsa rike da waya yana ɗan gudu ya ce
"Anty Rubina ga Yaya meer ɗinki ya kira Ummi ta ce na kawo maki" na gyara zama tareda karɓar wayar na washe baki nakai wayar kunne na na shagwaɓe murya
"Allah nayi fushi Yayana ba yau kace zaka dawo ba kuma baka zoba bani da waya fa zamana ba waya ya daman har ramewa fa nayi"
"Allah! da gaske ƴar lukutar Ummi ta rame mu gani bari na katse ina laptop ɗin Khalipha muyi vidio call" na daɗa haɗe rai kamar yana kallo na ce
"Aina daina taɓawa Khalipha komai nasa jiya har gori yamin akan kawai na ɗau wayarsa nai game ai insha Allah bazan kuma taɓa komai nasa ba, nama gayawa Yaya Amjad yatawo min da laptop nima"
Uwaimeer ya ɓata rai kamar yana gabanta aɗan fusace ya ce "Waya ce ki tambayi wani abu sau nawa zan gaya maki komai kike so ki gaya min nasai maki"
"To kayi hakuri ni da naga kana ta ginin nan ga biki ya matso shi yasa ma fa na tambayesa anjima idan mukai magana da shi zan gaya masa yabarshi yayana zai tawo min da ita"
"E ki gaya masa, gobe zan zo, zan taho maki da wayarki sannan in nazo sai muje asiyo laptop ɗin"
"To nagode Allah yakara arziki yakawo karin girma a wajan aiki"
"Amin, wane a kusa dake?" ta kalli inda Nura ke zaune yana cin snack ta ce
"Nuri ne yazo dubani"
"Ba kin warke ba name kuma zai rinka zuwar ma mutane gida, bama wannan ba wane bakon masoyi a wayarki?" na ɗora hannu aka tareda mikewa tsaye na kasa cewa komai ni gaba ɗaya ma na manta da wannan halittar,
"Bazaki magana ba waton bakiji maganan dana gaya maki ba ko Rubina yaushe muka fara haka dake, kodai aure kike so"
"Ni bance maka ina son aure ba ni bana ma sonsa fa shine kawai yake shirmansa"
"To ki jini da kyau zanyi bloking ɗinsa zan kura gaya masa karya sake maki tex messages kina jina idan ya sake zansa a kawo min shi nan inda nake zan basa gwale gwale irin na sojoji, Rubina bata kowa bace akwai mai ita yana nan ina ta masa tanadinki"
"Ni yaya duk ba wannan ba yanda zanyi Baffa yabarni maganar makaranta ni ita tafi damuna ba wata soyayya ba"
"Gobe innazo zamuyi maganar jirgin safe zan biyo anan zanyi breakfast fancake kunun gyaɗa doya da kwai na keso"
"Bakada damuwa Yayana kafin ka sauka na gama komai nida Khalipha zamu zo tararka a filin jirgi in Ummi ta bamu aron matar ta"
"Ki cewa Khalipha ya karɓi makullin motata a wajan Ameer ko ma dai zanma Amir ɗin magana yabawa Khalipha key ɗin"
"Tam sai gobe mu kwana lafiya"
"Kin gaji da jin muryata"
"E mana na gaji wannan muryar taka wazai yi marmarinta inba Anty Raiha ba" Uwaimir yai dariya tareda katse kiran wayar, karaf idanuna cikin na Nuraddeen dayai kuri yana kallona da alama ya jima yana kallon nawa batare dana sani ba, ya sauke ajjiyar zuciya har sannan idanunsa cikin nawa ya ce
"Uwaimir ɗan Ummi ne?"
"A'a ɗan Hajiya Umma ne"
"Ok" yafaɗa tareda mikewa ya ce zai tafi, harya fara tafiya ya nufi hanyar fita daga ɗakin ya juyo ya kalleni ganin ina zaune anan inda nake zaune ya jiyo yadawo kusa da ni ya miko wayarsa ya ce
"Samin lambar Ummi anan" na karɓa ba musu na saka masa lambobin Ummin na mika masa wayarsa
"To kizo ki min rakiya mana" na mike ina dariya muka jera nida shi muka fita har wajan gidanmu na raka sa inda ya ajje motarsa ya shiga ya tafi sannan nadawo cikin gida ban wuce part ɗinmu ba na shiga na Ummu jin hayaniyar su yaya Usman da alama kwallo suke bugawa ina gafda shiga cikin part ɗin naji an jawo min rigata ta baya na tafi luu zan faɗi naji an haɗa ni da bango nan take gani na gaba ɗaya ya ɗauke na kwalla wata kara ina ihun kiran sunan Ummina
*sakamakon wasu dalilai yasa na daina fitar da link na group ɗina idan har kinsan novel ɗib nan yamaki kina son cigaba da karantawa to kai tsaye yiwa Anty Mami magana ta wannan lambar zatai adding naki a cikin group ɗinmu da muke posting*
07039793439
🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹
Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Association* ☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA
Episode Eight8️⃣
*Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne*
"Wayyo Allah na Ummi wayyo idona na daina gani, Yaya Khalipha yaya Usman kuzo ku taimake ni" ji nai an rufe ni da duka a duka jikina kafin na soma jin maganar Hajiya Umma tana faɗin
"Yawwa Amir dakar min ita daketa iya karfinka naso ma ace dana haɗa kanta da ginin nan na haɗa mata jini da kwakwalwa ta haukace ma kawai mu huta banda iskanci da rainin hankali mai zakiyi da makullin motar ɗana da har zai zagi kaninsa dan kawai ya ce bazai baki makullin motar ba, ubanki ne yasai masa motar shegiya mayya mitsiyaciya mara galihu, yau saina nakasa ki yau saina maki illar da wannan kyan naki bazai amfane ki ba idan ma kyan ke ruɗar Uwaimeer yau zan kawo karshan sa zan nakasa ki"
"Ummmiiiiii" nafaɗa da wani sautin da ban sake sanin inda kaina yake ba, Ummi na zaune gefan gadonta tana danna waya chat suke da yayarta dake maiduguri tana sanar da ita dawowar da aka masu da aiki kano Ummi na murnar ta sami ƴar uwa a kano, Khalipha ya shigo hankali tashe sai haki yake ya tsugunna yana nuna wa Ummi hanya yana haki
"Ummi...ummi ki fita ga Hajiyarsu Yaya can zata kashe maki Rubina Ummi kilama sun kasheta itada Yaya Ameer" Ummi wurgi tayi da wayarta kan gado ta futo a guje ko arzikin mayafi babu a kanta sai hular kanta ta fito da gudu kamar wata karamar yarinya wata irin fincika tayiwa Hajiya Umma saiga Hajiyan yarab a kasa takai hannu ta bugawa Amir a kirji ya saki Rubina ta faɗo a hannunta ta fara girgiza Rubinan tana kiran sunanta
"Driver!! Driver kawo mana mota da sauri dan Allah" Ummi ta koma part ɗinta ta ɗakkowa Ummi hijab a cikin nata a mota ta bata ta saka ta shiga motar suka nufi Asibitin malam Aminu kano da Rubina
"Kai Ummu na rasa wacce kalar zuciya Hajiya keda ita mai Rubina ta tsare mata ne data tsane ta haka nikam wannan shine karo na karshe da zan kuma ɗaukar rainin Hajiya Umma a wannan karon da kaina zan shigar da report wajan ƴan sanda su mana tsakani da Hajiya Umma da Rubina na godewa Allah dayasa Baffah baya gari bare har ya taka min burki naga kamar shima tsoronta yake ji"
"Ummi muyi fatan Rubina ta samu lafiya komai za'ayi saiya biyo baya ni ganima nake kamar bata numfashi" Ummi zaune a recepsion ta kama kanta kusan ta kasa aikata komai duk abinda ake bukata Ummu keyi ita dai tana zaune kamar wata stetus bin mutane kawai take da kallo har sanda Aliyu ya shigo hospital ɗin shida Abbakar babban ɗan Ummu,
"Sannu Ummi ya Rubinan?" Aliyu ya tambayya sanda ya zauna kusa da mahaifiyar tasa, Abbakar na tsaye kamar gunki wayarsa tai kara alamar kira ya shigo ya ɗaga kiran ganin Baffa ne
"E! gamu munzo hospital ɗin, e to ban sani ba Baffah bana gidan ina gidana Usman ya kira ya gaya min abinda ya faru da nazo gidan saina tarar sun taho hospital gamu dai yanzu munzo" yai shuru alamar yana sauraron ɗaya ɓangaran kana ya ce
"A'a Baffah Ummi kaɗai muka gani gata nan bari na bata wayar" ya mikawa Ummi wayar
"Abbakar ɗauke min wayarka a gabana kafin ya ragargaza maka ita anan bazan maganar ba bazan magana da shi ba bare ya hanani abin da nai niyya, ku kaini police stetion dan Allah na shigar korafi na"
"Abubakar sa wayar a speaker ina jinta" yai kamar yanda mahaifin nasa ya ce Ummi taji muryar Baffah na magana
"Fatima dan Allah kiyi hakuri kina jina kibar komai a hannuna zan tawo gida zan ɗau mummunan mataki akan Bintu" Ummi bata ce komai ba sai mikewa da tayi tabar wajan tabi Dr office ɗinsa
"Kiyi hakuri Hajiya Rubina idanunta sun samu matsala jijiyoyin idanun sun tsaya a aiki yanzu dai muna kan bincike mu gano shin zasu tashi suci gaba da aiki ko kuma sun mutu kenan" Ummi ta jingina da bango tareda zamewa ta faɗi kasan tayals ɗin ɗakin ta fashe da kuka
"Wayyo Allah na wayyo ni Fatima yau naga bakar rana yau naga masifa ido buɗe mai nake shirin ji, Rubina ta rasa idanunta Dr dan Allah a cire nawa a saka maka, dan Allah Dr kutaimaka min ku taimaka" ta karashe faɗe tana fashewa da kuka
"Kiyi hakuri bamu ce ta makance ba har abada muna saka ran idan jijiyoyin idanunta basu matu ba