Showing 6001 words to 9000 words out of 42953 words

Chapter 3 - RASHIN MAHAIFANA COMPLATE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

133

Class Writer Assosciasion* ☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA

Episode Three3️⃣

*Kirkirarran labari ne in wani Ɗangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne*


Afusace Aliyu ya shiga motarsa ya mata key yabar gidan ko inda Fauzan yake bai sake bi ba, Hannah da kallo ta bisa lokacin daya shigo gida a fusace bata ce masa komai ba saima taɓe baki da tayi taci haba da sabgoginta na gida a kokarinta na ganin ta gama da wuri uku takson fita zataje Zooread wajan kitso, a fusace yakai hannu ya ɗauki wayarsa yana dannawa Daddy babban yayansu kira sau uku yana kira kiran baya tafiya sai hakura yayi ya kwanta jiki duk ba kwari,

Yau ba kamar yanda muka saba zuwa masallaci ba ada nida Yayana in muka tawo daga masallaci bayan an sakko muna ziyartar yan uwa, sosai muke zaga gidajan yayunmu amma yau ko gida ɗaya bamuje ba kai tsaye gida mukayo, tunda muka rabu a wajan adana motoci na gidan ban sake saka yayana a idona ba sai da ya aiko Khalipha da babbar leda da bansan maine a ciki ba yace na kaiwa Anty Raihana, Raihana budurwar Yaya Uwaimir ce sosai suke zuba soyayya kamar baza'a matu ba, ba yau na fara zuwa gidansu Raihana ba kusan ko yaushe in yayi zuwa irin haka ko kuma zai'a kai mata wani abu ni yake aika nake kai mata Raihana ƴar kawar Hajiya Ummah ce kawa kuma aminiya sai dai sam Hajiya da Maman Raihana ba halinsu ɗaya ba Raihana da Mamanta nada mutumci sosai da sosai hannu bibbiyu suke karɓata aduk sanda naje gidan yauma haka suka karɓe ni cikin fara a
"A'a lale da zuwanki kanwarmu Rubie" Raihana ta faɗa sanda nai sallama a gidan, Mama dake zaune kasan bishiya tana shan iska itama murmishin tayi tana amsa gaisuwar danake mata na zaune gefan Maman dake zaune kan karamin carfet ɗin data shimfiɗa

"Wai anan zaki zauna kizo mu shiga ciki"

"A'a Anty Raiha ki barni na zauna nan kusada Mama" Anty Raiha ta zauna itama kusa dani na mika mata ledar da Yayana yace na kawo mata " ta karɓa tana min godiya ta mikawa mamanta mun jima a gidan muna hira nida Anty Raihana dan tanada kirki sosai, dana tashi tafiya 1k Maman Raihana ta bani ta ce nahau nape danaki karɓa Raihana ta karɓo min ta min rakiya har bakin titin ubguwarsu nahau abin hawa ta bawa mai nape ɗin 1k ɗin tace yaban canjin mai nape yaja tana ɗagamin hannu

🔯🔯🔯🔯🔯

Salima tai juyi a gado juyo kukan Amira da tayi a bakin kofa yasa ta duro daga kan ɗan karamin gadon nasu ta zo bakin kofar tana kallon Amira dake kuka, damuwa karara ta bayyana akan Fuskar Salima ta ɗauki yarinyar mai shekaru huɗu ta shiga da ita ɗaki ta zaunar da ita kan katifa tana kallon ta ta ce
"Maine kike kuka da safan nan"
"Mama mama har yanzu bata dawo ba kuma yunwa nakeji" Salima damuwa ta kuma mamaye fuskarta ta figi hijabinta dake ajje jikin kofar ɗakinsu ta fita, gida gida nan makotansu take shiga tana tambayar dan Allah su san mata abinci zata bawa Amira ko wanne gida ta shiga amsa ɗaya wallahi bamu da sauran abinci ranta a ɓace ta dawo gidan ta zauna tana aikawa Mamansu kira a wayarta amma bata shiga ta kuma ɗaukar hijab ta fita ta zaga baya inda matasan unguwarsu ke zama kan dakalin wani gida taji daɗi data hango Ameer zaune cikinsu ana musu daga nesa da mazan kaɗan ta yafito Ameer da hannu alamar yazo tsam ya mike ya karaso inda take tsaye tana wasa da gefan hijab ɗinta tai kasa da kanta
"Salima gani muɗan matsa daga nan gayun can nasan yanzu duk idanunsu na kanmu" batace masa komai ta juya ta soma tafiya yabi bayanta suka zagaya kofar gidansu
"Ameer dan Allah ɗari biyar zaka ranta min mamanmu bata nan har yanzu bata dawo ba inata kiran wayanta a kashe ga Ameerah nata mana kuka" baice komai ba yasa hannu a aljihu ya zaro kuɗi masu yawa daga aljihun nasa ya zaro dubu ɗaya ya mika mata ta karɓa
"Ameer ɗari biyar fa nace"
"Ki karɓi dubu ɗayan kawai kuci ko indomie ce zaku rage kafin Maman ta dawo, kyauta na baki ba rance ba a tsakanina dake ba rance" yana gama faɗar haka ya juya bai koma wajan samarin ba yai hanyar gidansu, itama juyawa tayi tai kamar zata shiga gida amma saita fasa ta nufi kanti tsayawa tai a kofar kantin tana tinanin ta inda zata sai indomie duka kuɗin indomie biyu zai sai mata bazata ishe su ba itada kannanta guda biyu ta juyo tabar kantin ta karasa gidan mai abinci tasiyowa Amira na ɗari biyar ta siyo dankali soyayye na ɗari biyu awara ma ta ɗari biyu ta dawo gida, sanda ta dawo ta tarar kanwarta mai binta Marwa ta tashi ledan abinci ta mikawa Ameerah itada Marwa sukaci dankalin da awaran sukai shuru na tsawon lokaci kafin Marwa ta katse shirun da faɗin
"Yaya Salimah wai ina Mama ta shiga ta manta da mu numberta tun jiya bata shiga yau kwana biyu fa bata nan ta barmu bata damu da halin da muke ciki ba haba dan Allah ko kaji MAMA Ta bari aita binciki lafiyarsu"
"Hakane Marwa muyiwa Mama uzuri da fatan Allah yasa tana lafiya shurunta jiya zuwa yau ya daman duk wannan faɗi tashin da Mama keyi sabida mune kina kallo babanmu ba abinda ya damesa da mu, baisan cinmu da shan mu ba baima damu da yaya muke rayuwa ba mama ce dai itace kullum ke faɗi tashin yanda zamuci muyi rayuwa walahi Marwa nima na fara gajiya da wannan rayuwar tunda muka taso haka baba yake yaki ya canza haka kamar ba ubanmu ba" Marwa shuru tayi tana bin yayartata da kallo tsawon lokaci ba wanda yace komai har sanda sukaji sallamar kaninsu Sani da ya shigo yanzu
"Yane ya mai zan samu ne nifa yunwa nake ji, e yane kun gane ko" Salima ta watsa mashi wani banzan kallo batace komai ba ta mike ta fita yabita da harara ya kai hannunsa mai rike da hankaci baki yaɗan zuka kana ya maida ganinsa ga Marwa
"Ya Anty Marwa mai zan samu ta wajanki ita daman Yaya Salima ba wani mutumchi ta cika ba"

"Sani mai kuwa zaka samu mai zan maka ba rayuwar daka zaɓa kenan ba kullum kana wajan abokai kwana a gidama ka daina ka lalata rayuwarka da shaye shaye haba Sani dan Allah kaiwa kanka faɗa mana kana ɗan karamin yaronka dakai duka duka shekarunka nawa"

"To faɗan me zanwa kaina Yaya Marwa nifa bana shan komai kawai dai ina ɗan zukar wiwi ne ya kin gane ko itama sai naji kaina ya ɗau caji to saina ɗan zuka nayi fresh kin gane kuma ai su jakob ke bani idan nace su ban nacin abinci sai su ce saina ɗan zuka, kin gane ina zuƙa naji fresh to abinci sai wanda nace inaso zasu sai min"

"Hmm Allah ya shiryeka Sani ya ganar dakai gaskiyya ni ba abinda zaka samu yanzu a wajena banda ma ko sisi yau haka na tashi yanzuma sai Yaya Salima ce tasai mana dankali da awara muka ɗan ci muka rage, in zaka je ka nemi sana'a kaje tun wuri ka nema ka daina zuwa makaranta gaba ɗaya kana son ka cuci kanka"

"Kai wai Anty faɗa ma kike min, kai wallahi dan de kece amma da ace wani ne kemin faɗan nan da tuni nakai masa naushi" Sani yafaɗi haka yana wani rangaji irin na bugaggu yasa kai yafita daga gidan Marwa ta goge hawayan dake zubowa daga cikin idanunta.

🔯🔯🔯
Sanda na koma gida daga gidansu Anty Raiha na tambayi Ummi ko yaya Uweer ya shigo tace min bai shigo ba nai shuru ina tunani can dai nacewa Ummi bari na shiga wajan Ummu ta ce "To" na mike na fita kai tsaye part ɗin samarin gidanmu na nufa dake can karshe gidan wajan tsib ba alamar motsi sai bishiyu dake kaɗawa kasancewar yamma tayi sanyin la'asar yafara kaɗawa, na tura kofar babban falon a hankali nabi kofofin ɗakunan nasu da kallo idanuna suka tsaya kan kofar Yaya Uwaimeer na karasa a hankali nai kamar nai knocking na kofar sai kuma dai kurum nasa kai na murɗa handling na kofar na shiga da sallama, saurin ɗagowa yayi yana kallona ya maida kansa ya ɗora kan diary ɗinsa na karasa bakin gadon nasa na zauna ban damu da a yanayin da yake ba, na sake binsa da kallo yana kwance daga shi sai gajeran wando na kakin soji ko singlate babu a jikinsa ganin bai kalli inda nake ba yasa na ce

"Yaya Meer wai dai ko bakada lafiya ne najika shuru baka fito ba"

"Ke fita falo ki jirani na fito" yafaɗa rai ɓace yana aika min da kallon gargaɗi, tsam na mike na fito falon nasu na zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon minti biyu tsakani ya fito yana sanye da bakar jallabiya fuskarsa ba walwala ya zauna a kujerar danake kai yakai hannu ya kama kunnena ya ce

"Daga yau karki sake shigo min ɗaki kai tsaye Rubie ki rinka tsayawa iya falon nan ko kuma ki fara neman izinin shiga" na ɗaga kaina ina binsa da kallo jin a karo na farko na rayuwata da yayi min magana da tsawa

"Yayana gaba ɗaya yau ka canza min kamar ba kai ba ai ba yau nafara shiga ɗakin naka ba baka taɓa min magana na daina ba ɗazu kamin tsawa yanzu kamin magana da ihu shikenan Yayana na lura ka daina kaunata zan canza yaya" na mike zan fita ya ruko hannuna ya dawo dani kusa da shi ya zaunar yana leka fuskata ya ce

"Ko kaɗan ban daina kaunarki ba Rubie ina nan a yayanki mai sonki har gobe"

"To mai yasa ka canza Yaya Meer yaufa ba gidan wacce mukaje daga masjid ka dawo damu gida kuma kazo ka rufe kanka a ɗaki ko abinci baka ci ba"

"Naci abinci wajan Hajiyarmu ɗazu dana dawo daga sallar la'asar, da dare ki dafamin abinci zanci bayan sallan insha"

"To mai zakaci?" na tambayesa ina turo baki

"Yaya Meer baida wani zaɓi duk abinda hannun Rubina ya dafa zaici koda kuwa maɗaci ne to zaiji daɗin sa kamar sweet"

Nai murmushi ina kallonsa na mike zan tafi na sunkuyar da kaina dai dai kumatunsa na sumbata nace "Yayana Ilove you da yawa da yawa gaba ɗaya cikin yayuna ba kamar kai da yaya Amjad"

"Amjad amjad kuma nidai bana so a kuma haɗani da kowa a cikin yayun nan na zama nine na gaba gaba kuma ɗan gaban goshi" nai dariya na mike na fita ina masa bye, Uwair ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana sakin ajjiyar zuciya ya mike ya koma ɗakinsa ya ɗauki diary ɗinsa ya maida cikin jaka ya fito da choculate da yawa daga cikin jakarsa ya ajje a gefan gado ya maida jakarsa ma ajjiyarta kana ya zuba choculate ɗin a wata leda ya fito daga part ɗin nasu, kai tsaye ya wuce part ɗin Ummi ya tarar Rubina bata nan ya bawa Ummi ledan choculate ɗin ya ce ta ajjewa Rubina, Ummi tai godiya ya fita a gidan cikin motarsa

Rubina saida nai sallar insha sannan na shiga kichin nama rasa mai zan dafawa Yayana Uwaimeer ina cikin kicin ɗin Yaya Aliyu ya shigo kamar mai neman wani abun naga yana ƴan dube dube a kichin ɗin ni kuma ina tsaye ina tunani har ya karaso inda nake

"Rubina mai za'a dafa mana da daran nan"

"Yah Aliyu nima kaina ya kulle na rasa mai zan dafawa Yay Uwaimeer" annurin fuskar Yah Aliyu ya ɓace lokacin dana ambaci Uwaimeer, yaja tsaki tareda duba agogo ya fice daga kichin ɗin, banji komai a zuciyata ba na ɗakko indomie guda biyu na ɓare ta na zuba mai a prying pan mai yawa na soya indomie min na tsane ta a colander sannan nai gretting attaruhu da albasa a gretter na zuba su a gefe kana na fasa kwai na zuba specias kaɗan a ciki na ɗebi albasa da attaruhu danai gretting na zuba a ciki na soya kwai guda bakwai, na dafa carrot da pies sannan na soya attaruhun danai gretting na tsaida ruwa bayan ya tafasa na kawo green beans da pies da cartot na zuba a ciki na ɗan lokaci sannan na zuba indomie da specias ɗin cikin indomie ɗin na dafata na ƴan mintina sannan na juyeta a plat na kawo wainan kwain na ɗora akai na fito da shi daga kichin ɗin na kawo danning na ajje na ɗau wayata na kira lamban Uwaimeer
"Sorry gani nan a hanyar part ɗin ku" yana gama faɗin haka ya katse kiran minti biyu tsakani ya shigo da sallama, bayan sun gaisa da Ummi dake zaune a falo tana kallo ya hawo step inda danning yake yaja kujera ya zauna yana kallona, na tura masa plat ɗin indomie ɗin gabansa ya buɗe idanu ya ce "Wow dilicious gaba ɗaya kin tada min yunwa" nai murmushi tareda dafe fuskata da hannu biyu ina kallonsa yanda yafara kai indomie ɗin bakinsa yana gyaɗa kai

"Rubie yanzu inna tashi fita na tafi ɗakina ta ina zanbi?" fashewa nayi da dariyar data saka Ummi kwala min kira, na mike na tafi har sannan ina dariyar tambayar da Yaya Meer yamin, wani kallo Ummi tamin kallo na ki shiga tai tayinki ina dariya nace

"Afuwa Ummina bazan sake wannan dariyan ba Yay Meer nefa ya fara santin abinci" tai murmushi tana gyaɗa kai tareda maida hankalinta ga kallon da take tamin alamar na koma, na ɗakkowa Yay Meer lemun gora da ruwan Gora na ajje masa a gabansa dana tarar har yaci rabin indomien

"Watonko maganar gaskiyya Rubie girkin nan yai bala'in daɗi gaskiyya mijinki yai dace da wacce ta iya sarrafa tukunya"

"Kai dai yay Meer kaci indomie kawai maiye wani kawo maganar aure ana zaune kalau kama daina maganar nan kar Baffah yaji bana son yamin maganar aure harga Allah karatu nakeso ina fata da burin na zama babbar likitar mata"

"To Allah ya ida nufi amma dai ban gani anayi ba a gidan nan karatun ƴa mace"

"Za'a fara daga kaina ni zan kafa wannan tarihin insha Allah zan zama likitar mata a cikin gidan nan gaban Ummina da Baffana gefe ga Yayana Uwaimeer" shidai baice komai ba harya gama cin indomie ɗin ya sha ruwa da lemu muka ɗan taɓa hira kafin muka mike muka nufi part ɗin Baffa, atare muka shiga wajan Baffah yana zaune kan carfet ya kishingiɗa a jikin tum tum yana lazami gefansa ga Hajiya Zainab data gama jera masa kalolin kulolin abinci ga bwols da plat plat a ajje kusa da shi, Baffa yana fara'a sosai ya amsa mana sallamar mu yana aika mana da murmushi

"Maraba lale da zara da wata" Yaya Uwaimeer ya zube a gaban Baffa ya ruko hannunsa kafin yai masa wata runguma sai hawaye

"Lala mai zan gani Uwaimeer hawaye kuma duk na daɗin gani na ne"

"Baffah baffana nai misssing naka da yawa sati kusan takwas ban saka ka a idanuna ba"

"Kai Uwaimeer bana son sharri ko shekaran jiya ai munyi vidio call dakai kaifa ka zaɓi tafiya ka barmu kai ka zaɓi wannan aikin mai tsanani"

"Baffa Aikin nan taimako ne wa kasa fa"

"To masha Allah ubangiji ya taimaka Uwaimeir yakare ka"

"Amin" muka faɗa lokaci ɗaya nida Yay Meer kamar waɗanda suka haɗa baki, Baffah yabimu da kallo kana yai murmushi ya ce

"Ɗazu mun tafi masallaci Mahmud ke gayan wani labari mai daɗi masha Allah nida na zaci tanan zanji wannan labarin mai daɗi kuma sai na jisa ta wani waje daban to nayi farin ciki da hakan Allah yasa ayi damu" Uwaimeer yai kasa da kansa yana murmushi a zuciyarsa kuma yana nanata maganar Abba yana son gano mai yake nufi, duk da bansan maine ake addu'a akai ba amma ni na amsa Amin ɗin Baffah kafin yaci gaba da faɗin

"Jibi lahdi nida Mahmud da abokina Alhaji Sada zamuje in mukaje mai gaba ɗaya zamuyi da kuɗi da sadaki zamu saka wata biyu zan maka lefe sai akai daga baya sannan ka karasa ginin ko?" kai kurun Uweir ya gyaɗa alamar e batare dayace komai ba na kalli Yay Meer daketa doka murmushi yanzu na fuskanci inda maganar tasu ta dosa waton dai auran Uweimeer da Raihana za'a tsayar take naji wani kunci da bansan na maine ba ya mamaye zuciyata na fara kokarin mikewa zan bar wajan Uweimeer ya dafe min hannuna ya hanani ta shi

"Baffah ka manta da yaran nan kaci abincinka" Hajiya Zainab ta faɗa tana wani haɗe rai tareda aika min harara a fakaice

"Rubinan Baffah kinci abinci? in bakici ba zonan muci tare wanko hannunki" na ɗago zanyi magana karaf idanuna cikin na Hajiya Zainab aiko ta aika min sakon harara da kallon gargaɗi nai kasa da kaina ina murmushi nace

"Baffah munci abinci da Ummina ɗazu"

"Masha Allah, to zuba min" nakai hannuna saman kula zan buɗe Hajiya Zainab ta warce sarving spoon ɗin dake hannuna zatai magana Baffa yai saurin katse ta da

"Shikenan Hajiya Zainab ya isa basai kince mata komai ba, Rubina kuje Allah yamaku albarka" muka mike nida Uwaimeer muka fito har sannan hannunsa na cikin nawa mun baro part ɗin Baffah kenan muka hango Hajiya Umma na tahowa da sauri Uwaimeer ya saki hannuna yai saurin wucewa gaba kamar ba tare muke ba wani kallo tabimu da shi tun daga nesa ina hango kallon datake aiko min ta cikin hasken daya hasga gidan

"Uwaimeer baka jin magana maina gaya maka ɗazu? Hajiya Umma ta tambayesa bayan ta tsare sa da idanunta yai kasa da kansa, na tsaya kusa da shi nima nayi kamar yanda yai

"Muna fuka ɓace min daga nan kuma wannan yazama karo na karshe da zan sake ganinki da ɗana, mayya kawai" gaba nai sau biyu ina juyowa ina kallon Uwaimeer dake yiwa Umma magana harna shige part ɗinmu suna nan tsaye suna magana, a karshe a fusace tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login