Showing 30001 words to 33000 words out of 42953 words
yau ka nemi soyayyar Rubina fatana ta amince da kai tabbas idan ta sameka ta yi dace da masoyin kware" Innah sukaiwa Baffa sallama bayan Nuraddeen ya karɓi lambar Uwair ta can zai kirasa ya haɗa sa da Rubinan,
London
Ummi ta gama shirinta na kwanciya barci ta kalli Rubina dake zaune a kusa da ita, Uwair ya buɗe kofar ɗakin ta shigo da sallama hannunsa rike da System da sabuwar wayar daya saiwa Rubina tun a randa tai Candy, yaiwa Ummi barka da dare bayan ya zauna kan sofa idanunsa nakan Rubina dake danna wayar Ummi
"Rubie ga wayarki da system ɗin danai maki aljawari" da sauri ta ajje wayar Ummi nan kan gadon ta tawo da gudu ta faɗa kan Uwair dake zaune, da sauri yasa hannu ya cirota daga jikinsa ya kankance ido yafara aika mata ruwan masifa
"Waike yauahe zaki girma sau nawa ina gaya maki ki daina faɗo min jiki irin haka bakiga kin girma bane yanzu da da aiba ɗaya bane" Ummi kallo ɗaya taiwa Uwaimir ta kauda kai tana murmushi, Rubina ta koma gefan gado ta zauna tana kallon Uwair dake ta faɗa har sannan idanunsa rufe, taja tagumi hawaye suka wanke mata idanu yana buɗe ido yai tozali da hawayanta gaba ɗaya ya ruɗe yadawo kusa da ita yasa hannu ya janye mata tagumin
"Kinga toyi hakuri nai maki masifa nima bansan nayi ba kin gane kawai ki daina faɗo min jikina idan nai maki wani abu da kikai farin ciki kimin addu'ar samun cikar burina kina ji ko Rubie dan Allah daina hawayan karya haifar maki matsala kuma a idanunki" ya ɗora mata wayar da System ɗin a kan cinyarta ya mike ya fita daga ɗakin, Ummi ta kalli Rubina da har sannan bata taɓa wayar da system ɗin ba
"Kinji haushin abinda yai maki gaskiyya ya faɗa maki Rubina ki daina irin haka" kai kurum na ɗaga mata na ajje Wayan da system ɗin kan madubi na fita daga ɗakin na shiga ɗakin da yake, yana zaune kan tayels ya ɗora kansa a gefan gado duka hannuwansa ya ɗora akan nasa na jima ina kallonsa kafin nai magana
"Yay meer" da sauri ya juyo yana kallona batare daya ce komai ba, na karasa inda yake zaune na tsugunna na kama hannunsa na rike ina kallon cikin idanunsa da har sun canza launi na ce
"Kayi hakuri bazan sake ba kaji na tuba" ya kakalo mirmishi ya ce
"Ni banyi fushi dake ba Rubie Yay Meer ɗinki baya taɓa fushi da Rubinan sa, jibi zanbi jirgin safe zan koma wajan aikina ga Ummi nan tazo kuci gaba da zuwa hospital kuna ganin likita"
"Yanzu Yay tafiya zakai ka barni nidai mu tafi tare ai naji sauki idan nasa glass a idanuna ina gani sosai"
"Kidai zauna ɗin yau saura sati Uku bikina da Raiha inaso na tafi a larasa ginin kasan nan saman a yanda yake zan barsa wata nakewa tanadin sa" na zaro idanu ina kallon sa da mamakin maganar tasa
"Yay Mee wai da gaske wata ka gano cab amma baka kautawa Anty Raiha ba"
"Ita waccan daman tun tuni take a zuciyata ban sami dama bane amma yanzu na fara ganin haske da ace zan sami yanda naso da ita zan aura daga ita bazan kara wata mata ba sabida tsananin son da nake mata na rayu da kaunarta yau sgekaru da dama kenan, Rubina kimin addu'a Allah ya mallakamin Husnah" na washe baki na ce
"Lah sunan mu ɗaya a ina take najw na ganta dan Allah nai mamaki ashe duk son nan da kakewa Raiha akwai wacce zata iya takushe soyayyarta a zuciyarka"
"Tabbas inason Raihana saidai ko wacce mazauninta daban a zuciyata kawai kidai sani Husnah ta dabance a zuciyata tafi ki kwanta barci" na mike na fita daga ɗakin na koma na tarar Ummi batai barci ba har sannan naɗau wayana ina dannawa cikeda jin daɗi, ya saitan komai facebook whatsapp instergram duka
Raihana sun fito daga lacture itada kawarta Rahima suna tafe suna hira can Rahima ta canza akalar hirar tasu dai
"Raiha biki nata matsowa yau saura sati biyu kenan banga kin fara shirye shirye ba"
"Hmm" Raihana ta sauke numfashi ta ce " Sonake wai saura sati biyu saina fara gyaran jiki maganin sanyi dai na fara sha Momy ba na bani wasu maganin mata kuwa nidai inaga bazan sha komai ba" Rahima ta tsaya daga tafiyar da take tana aikawa da Raihana wani kallo kamar zata kai mata duka ta ce
"Bazaki sha komai ba kamar yaya yau nakejin wani shirme a wannan zamanin da mazan kar sukw kallonmu kice bazaki sha komai ba iya maganin sanyi zakiyi ai wallahi karma ki soma wannan gangancin magani zaki sha sosai ina gaya maki zan yiwa yayata magana tana zamfara ta iya haɗin amare na bala'i zan bada kuɗi a kawo maki amma fa ba'a fara sha sai ana saura sati guda auran karki kai kanki bamu shirya ba" Raihana tai dariya suna cigaba da tafiya har suka fito daga cikin makarantar hirar bikin suke da tsara event ɗin da zasuyi,
"Amma dai Raihana zakiyi allurar planing karkije daga shiga ki kwaso tsaraba kalli dai yanda kawarmu Safiyya ke fama da laulayi duka ko wata uku ba'ayi da bikin ba"
"Wallahi Rahima kamar kin shiga zuciyata nima tunanin dayake raina kenan ina ta cewa anya ba Allura zanyi ba nifa so nake na mori amarci na ba daga zuwa sai ciki ba kaita fama da laulayi"
"Ai bama cin amarcin ba ni karatun nan nafi jiye maki ma munyi rabi saura rabi mai zai hana satin bikin muje hospital amaki allurar wata uku daga nan sai ki cigaba da yi bayan wata uku ukun"
"To haka za'ayi ma Allah yakaimu lokacin"
"Amin" Rahima ra faɗa ita ta fara samun abin hawa ta tafi kafin daga baya Raihana ma ta sami nape tahau zuwa unguwarsu
🔯🔯🔯🔯🔯
Amir tsaye gaban falon Hajiya Umma dake saman benenta yana rikeda littafin karami yana nazarinsa kamar ance ɗago ya ɗago yana kallon waje, Salma tafe tana gyara zaman mayafinta sabida iskar dake kaɗawa a yammacin karaf idanunsa suka sauka kan kirjinta gabansa yai wata irin faɗuwa yai saurin kasa da idanunsa kafin yabar inda yake jingine da bango ya shigo falon ya biyo step ya sakko kasa yai sa'a hajiya bata a falon yai saurin shigewa ɗakinsa dayake shi ɗan gaban goshi hajiya ne kuma autanta yana nan ciki wajanta bai da ɗaki a boys Quaters na gidan yana shiga ɗakin sa yafaɗa kan gado yana faɗin wash Allah yai wani juyi can kuma ya mike ya fita daga gidansu ya zaga layinsu Amira ya zauna a dandamalin kofar gidan yana danna wayarsa kamar wanda ke jiran wani abun, Salima kamar wacce aka ce leko ta leko taga Amir zaune a kofar gidan nasu cikin mamaki ta kira sunansa
"Amir" juyowa yayi da sauri yai sa'a Salima bako mayafi a jikinta sai ɗan kwali data ɗaura gaba ɗaya halittun kirjinta sun leko ta cikin rigar dake jikinta kasancewar ta zauna sosai a jikinta idanunsa akan kirjin nata ya sauke gwaron numfashi kafin ya basar ya ce
"Kwana biyu banga gilmawarki ba shine fa nace bari na leko layin naku" Salima ta koma ciki ta sako ɗan karamin mayafinta shantali mini ta fito ta zauna kusa da shi tana dariya
"Kasan nima rannan na gama cigiyarka wajan Ghali yace min baka nan kaje wudil makaranta"
"Jiya nadawo nai weekend a gida shi yasa nace bari na nemi ki mu gaisa tunda ke bakya neman mutane"
"Nifa da inada lambarka amma yanzu banda ita bansan ina ta shiga ba" ya kallo wayar hannunta ya taɓe baki kana ya ce
"Kina babbar yarinya dake kina rike keypad gaskiyya yakamata ki canza waya kema ki faso gari, bari na mike na tafi zanje tal'udu na karɓowa Hajiyarmu atamfaofin ankon wana da za'ayi" Salima ta mike
"Wai har tafiya zakai"
"Ko zaki min rakiya na fito da mota mu tafi" Salima ta zaro manyan idanunta tana murmushi
"Wace ni na shiga motarka irin taku ce sai ƴaƴan manya irinka"
"Kema kin kai jirani kawai na shiga na fito da motar jirani a bakin layi sabida munafukai" Salima tai jim tana kallon kofar gidansu kamar ta shiga ta faɗawa Mama saima ta tuna Maman tun safe sun fita aikin abincin biki tasa kai ta nufi bakin layin.....
🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹
Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Association* ☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA
Episode Twelve1️⃣2️⃣
*Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne*
Tana karasawa karshan layin ta hangi mota parke a gefe ta nufi wajan murfin motar da taga an buɗe mata yasa ta karasa da hanzari ta shiga kusa da mai tuki ta zauna
"Karigani zuwa" yai murmushi yana mata wani kallo kasa kasa ya ce
"Ko'a kafa nake ai na rigaki zuwa nan bare a mota nake wannan tafiyar taki ta musamman ai ba duk mata ba, wai ni kuwa Salima kina kallon kanki a madubi kuwa gaskiyya ke kyakkyawa ce so cut masha Allah" Salima ta rufe fuskarta da hannuwanta tana murmushi kafin ta ce
"Nagode" yatashi motar suka fara tafiya slowly suna hira, cikin wayo da dabara ya nuna yana sonta da gaske auranta zai yi har suka karasa tal'udu ya shiga gidan ya fito hannunsa rike da manyan ledoji ya saka a bayan motar yadawo mazaunin driver ya zauna yana aika mata da wani kallo, ahanya ya tsaya yai mata siyayya sosai kama da kayan kwalam da gashashshiyar kaza sai wajan mangariba suka koma gida wannan karon a kofar gidansu ya ajje ta kaina yai gaba ya wuce gidan su dake ɗan gaban nasu Salima sosai, da sallama Salima ta shiga gidan tai tozali da Mama daake alwalar sallar mangariba ta washe baki
"Sannu da zuwa Mama bayan na fita kika dawo"
"E! dana dawo Marwa ke gayan kin fita ɗazu ina kikaje" Salima ta ajje mata ledojin hannunta a kusa da ita ta ce
"Amir ɗan gidan Alhaji Baffah muka fita tare da shi shine yamin wannan siyayyar" Mama ta dafe kirji idanunta akan Salima ta ce
"Salima fita kuma kuka je ina ya ce dake mai"
"Mama bafa wani abu bane kawai rakiya na masa ya karmowa hajiyarsu kayan ankon bikin yayansa da za'ayi da mukaje ma ko gidan ban shiga ba wallahi mama da muka tawo a hanya yake gaya min sona yake aure na zaiyi"
"Salima ashe daman bakida hankali kin taɓa ganin jirgi yabi hanyar mota ina haɗi keda Ɗan Alhaji Baffah Yarima duk faɗin unguwar nan wane kamarsa ke Salima fita a idanuna ki tsaya iya matsayinki karki ɗorawa kanki abinda zai zo yadame mu" Salima ta zunɓuri baki tai fuu ta wuce ciki tana magana kasa kasa Mama ta harareta bata kalli inda Salima ta ajje ledojin ba tai shigewarta ɗaki ta tada sallah,
Marwa ta kalli Salima dake ƴan kananun maganganu tai murmushi ta ce
"Yaya nifa banga laifin Mama ba maganar gaskiyya ta gaya maki kirma ki biye masa wallahi ba auranki zai ba Amir bama kalarki bane, ni Yaya magana ma nakeso muyi zaman nan ya isheni haka tunda nai candy ina zaune a gida ba cas ba as shine da nace kodai aikin company zan fara na rinka samun ɗan na kashewa ina biyawa kaina ƴar bukata ta da bata fi karfina ba saika yini baka da ko sisi" Salima taiwa Marwa wani kallo na kaskanci kafin ta ce
"Aikin Company kuma kina mace haba dan Allah"
"Yaya ba haramun bane ai da zaman nan danake na banza ai gara na yi aikin" Mama data idar da sallah ta juyo ta kalli Marwa ta ce
"Marwa ki je ki nemi aikin inkin samu kiyi abinki Allah ya taimaka zaman haka ba daɗi" Marwa taji daɗi sosai bayan ta idar da sallah ta tafi gidansu kawarta Hannatu da itace tai mata tayin fara aikin companyn tunda itama acan take aiki ta gaya mata gobe in zata tafi ta biyo mata su tafi tare Allah yasa a ɗauketa, ai kuwa washe gari kafin bakwai na safe ta gama shirinta bakwai saura kwata Hannatu tazo suka tafi bayan ta amince da dokokin companyn ta amsa tambayoyi take anan ta fara aiki kullum ɗari biyar in kanaso za'a baka kullum ko bayan kwana goma ko na wata guda itadai wata ta cw zata rinka karɓa tana ganin kamar saiya fi mata auki lokacin data fara aikin goma ga wata ne hakan yasa kuɗin da zata ɗauka dubu goma kenan.
🔯🔯🔯🔯🔯
Nuraddeen yai shuru yana kallon number Uwaimir daya ke shirin kira, gabansa yai wata irin bugawa da karfi tuna wayar daya taɓa ji uwair ɗin nayi da Rubina, ya sauke ajjiyar zuciya jikinsa sanyaye yama fasa kiran lambar Uwair ɗin yabari akan inta dawo kawai sayi magana tunda dai har ya samu Baffah yabasa dama to yana ganin yayi maganin rabin matsalar ya shiga ɗakinsa yai shirin barci zuciyarsa fal da tunanin Rubina
*LONDON*
Randa Uwair yabaro kasar ranar Baffah ya sauka nai tsalle nai murna da zuwan Baffah duk kewa da ɗacin ran danake na tafiyar Uwair gaba ɗaya ta tafi sabida murnar ganin Baffah na, ya saka ni jikinsa yakai hannu ya zagaye ni da shi ya ɗago kaina yana kallo hawaye suka zubo daga cikin idanunsa nakai hannu na share masa hawayan dake zuba daga cikin idanunsa
"Allah maki albarka Rubina kici gaba da hakuri haka rayuwa take tana zuwarwa da mutane kaddara ta ko'ina ubangiji ya jarabaka danya ga imaninka kici gaba da hakuri Asma'u wataran sai labari kinji Allah yabaki lafiya yadawo maki da ganin ki"
"Amin Baffah ko iya haka gani na ya tsaya ina gidewa Allah bazan manta da karamcin yaya Uwaimir a gareni ba hakika shi ɗin ɗan uwana ne na musamman mai maganin duk wasu matsolina"
"Allah maku albarka gaba ɗaya ya haɗe min kanku"
"Amin Baffana" Ummi dake tsaye kan step tana kallon Baffah da Rubina murmushi shimfiɗe a fuskarta ta ce
"Rubie sake sa mana ya zauna ya huta ko ruwa ba'a kawo masa ba kin wani eukunkume sa kamar zai gudu ya barki" Nai dariya tareda barin jikin Baffah na koma gwfe na zauna ina dariya
"Ranka yadaɗe barka da zuwa, zuwa ba sanarwa"
"To hankali yayo nan ba Rubina ba Umminta gida duk ba daɗi" Ummi ta taɓe baki tana aikawa da Baffah ƴar harara, Rubina ta haye sama tana dariya kai tsaye ɗakin da Uwair ya zauna ta shiga har sannan kamshin sa na nan daram a cikin ɗakin, ta faɗa gado tareda rungume lallausan bargon da har sannan ke fitar da sassanyan kamshin turaran Uwair daya gama bin jikinsa
"Hummm Ina missing naka Yayna ko ka sauka yanzu Allah ya tsare min kai aboki" na faɗa ina sake kai bargo kan hancina na lumshe idanu a zuciyata ina ayyano suffofin Yayana Uwair a fili na firta
"Anty Raiha kinyi da dacw da samun mijin kware mai sanyi hali sassanyar zuciya kyau da ilimi Allah ka dube ni nima ka bani miji mai kalar halin yayna Uwair ina sonki fiyeda duka sauran yayuna ɗan uwa"
Baffah tsaye gaban madubi futowarsa daga wanka kenan yana tsane kansa da karamin tuwel ɗin dake hannunsa Ummi na gefansa tana ƴar dariya kasa kasa da alama tare sukai wankan
"Allah fa da gaske nake Fatima shekaran jiyan nan yazo ya samw ni na eiga na gaya masa wace Rubina a wajanmu kuma ya yarda ya amince zai aureta a haka ki gayawa yarki zai kira lambarki anjima ɗazu da mukai waya da shi na basa lambar wai ta Uwair dana fara basa bata shiga"
"Cab ai wallahi gara da baima samu uwair ba da kai tsaye zai katse sa randa na sauka kasar nan ya kalli idanuna ya bayyana min alamun na yana son Rubina" Baffah ya juyo da sauri yana kallonta
"Da gaske kike uwair ɗin, to mai yasa ni yakasa faɗi min"
"Ni abinda nake tunani kamar yana jin tsoron mahaifiyarsa ne kuma nima bana goyon bayan auransa da Rubina hajiya bazata taɓa batinsu suji daɗin rayuwa ba shi yasa ma ban wani ɗau maganar da mihimmanci ba koma dai maine ni nayi farin ciki da zuwan Nuran nan daman ina tsoron Aliyu" Ummi ta karasa faɗa damuwa bayyane a fuskarta
"Mai yasa bakya son Aliyu ya auri Rubina?" Ummi taiwa Baffah wani kallo kafin ta ce
"Dalili ɗaya ne banda shi da zanyi farin ciki da auranta da Aliyu sosai, na farko Hannah matarsa ƴar kanwata ce uba ɗaya idan na ɗau Rubina na basa mai nayi kenan sannan ni bana so Rubina tasan ita wace"
"Koba daɗe ba ba jima dole wataran Rubina zatasan ko ita wace ni ina fata na sanar mata da bakina da nata, akwai company na na sharaɗa nai aniyar barmata shi gaba ɗaya Rubina ko yau na mutu batada gado na nayi magana da Amjad zasu zauna da lauyoyi na zan saka hannu bansan ranar mutuwata ba Fatima bana son na mutu na bar Rubina a tagayare nayi iya bakin kokari na in nemo iyayanta na kasa na gaza mata ta wannan ɓangaran shi yasa nakeson bar mata wani ɓangare na dukiyata da zata tsira da shi ko bana raye"
"Amma dai kasan hakan da zakai zai iya jawo cece kuce Hajiya tayita korafi gefe ga Dada ni ban son kananun maganganu"
"Dukiya dai tawa ce ko? ba uban dayake tayani nema sanda nasha faɗi tashi na harna tara ta waya sani"
"A'a fa arinka dai tunawa Hajiya dai da ita akaita faɗi tashin nan" Baffah yai murmushi yana faɗin
"Nawa ta zuba a cikin dukiyar, mubar ma maganar nan nifa wallahi a yunwa ce nake" Ummi tai dariya irinta basawa tana zura bakar abaya ta ce
"Mu sauka kasa to a sama maka abinci" Baffah yakaraso kusa da ita ya tsaya yana kallonta yasa hannu ya ɗago fuskarta
"Kinsan yunwar ai kema Fatima, na rasa gane wannan sirrin naki kullum bakya tsufa kina nan a yanda kike bayan tarin jikokin da kika ajje" Ummi ta rungomo Baffah tana dariya taja sa