Showing 33001 words to 36000 words out of 42953 words

Chapter 12 - RASHIN MAHAIFANA COMPLATE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

137

suka faɗa saman gado

Uwair bakwai na dare ya sauka garin abuja wani jirgin yahau zuwa calabar sanda ya isa cikin gidansa yai hamdala yana godiya ga Allah yai sallar insha kana yai shirin kwanciya barci dan gobe ya sani fitar sassafe ce, shi gaba ɗaya ma wallahi sai yanzu aikin nan daya zaɓarwa kansa yadamesa gaba ɗaya ba sakewa idan da ba soja ne shi ba ba abinda zai baro sa da Rubina take kewar Rubina ta mamayesa yaji kwalla na zubowa daga cikin idanunsa ya rasa wanne irin so zuciyarsa kewa Rubina da kullum burin zuciyarsa shine su kasance tare a ko yaushe har barci yafara ɗaukarsa yaji wayarsa na ring ganin lamabar kasar waje yasa yai saurin ɗaga kiran

"Yay meer" yaji sassanyar muryar Rubina ta daki dodon kun nan sa

"Uhmm Rubie yane"

"Yay Meer yaka sauka gida fatan kana lafiya gaba ɗaya ma sai naji nan ɗin ba daɗi nima Allah dawowa zanyi"

"Kizo kiyi mai anan ki zamanki kawai Baffah ya ce bazaku wuce sati ba zaku tawo tare sabida bikin.."sai yai shuru ya kasa karasawa Rubina tai dariya

"To karasa mana bikinka nima daman ai shi nake tunani amma tunda haka ne nayi farin ciki Allah yasani akai bikin abokina yayana bana kasa ba'a kyauta min ba nima fa biki zanyi sosai kama ware min kuɗin party ɗina daban saina gayyato duka kawaye na da muka gama schools tare, nima nayi shiga irinta amare" ba karamar dariya Rubina ta basa ba wai tayi shigar amare

"To waye angon ko dai na tawo maki da wanda nakeson ki aura"

"Nifa ka gama kashe min zuciyar nan Yayna va lissafin aure a cikinta karatu ne kawai"

"Yawwa nai farin cikin jin haka yanzu dai barci nakeji kinga nan mu dare ne yanzu zan cigaba da barcina da safe zan kiraki muyi magana" Rubina bata sake cewa komai ba ta katse kiran harya mai da kai zai koma barci kawai ya tashi ya faɗa bayi ya ɗauro alwala ya tada sallar nafila

Hajiya Umma tsaye sakeke tana kallon Amir ɗanta cikeda mamakin maganar da yake

"Na rantse da Allah Umma da gaske nake maki da kunne na na jiyo Yaya Amjad da Barister Shitu suna maganar ni bakin cikina ma shine yanda na rinka lallaɓa Baffa a kaini companyn nan yaki wai dole sai dai na zauna a kasuwa amma yanzu zai ɗauki wannan companyn babba yaba wata can mara asali nidai Hajiya kiyi wani abu akai gaskiyya kafin munaji muna gani wanan matar Fatima ta mallake komai mu amu tashi a tukar babu" Hajiya Umma tsabar takaici tayi ahuru tama kasa cewa komai sai numfashi da take furzarwa, ta mike tana zagaye a ɗakin nata

"Amir ban taɓa shiga malamai ba ama yazama dole a wannan gaɓar na shiga malamai nabi bokaye amin ɗayan biyu kodai a farraka tsakanin Rubina da Ummi rikon Rubina da iko da ita duka yadawo hannuna ko kuma a farraka min tsakaninta da Baffah ya koreta a gidan nan ko kuma a kashe min ita gaba ɗaya"

"A'a Hajiya duk ba haka za'ayi ba inada tawa shawarar mai kyau" Hajiya Umma ta juya tana kallon kofa ta saki lallausan murmushi ganin mai maganat datake tsaye a bakin kofa ta fara takowa zuwa cikin falon na hajiya

🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹


Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Association* ☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA

Episode 1️⃣3️⃣

*Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne*

Amina ce ƴa ta biyu ga Hajiya Umma wacce ke bin Mahmud, ta zauna a falon tana aikawa Amir da harara, Amina masifaffiya ce ajin farko ko cikin kannan nata suna matukar shakkarta Amir ya sami waje ya zauna ya nutsu sosai yana aika mata da gaisuwa dan shi harga Allah ko iyayan sa da suka kawo sa duniya baya tsoro kamar yanda yake jin tsoron masifar Anty Amina

"To wai kana wajan nan zamuyi magana kana jinmu" Amir ya kalli Hajiya ya marairaice fuska, Hajiya ta dubi Amina

"Kinga bari muyi magana yana zaune Amir na waje na ne banda abokin magana sama da shi wani bin shike sharan hawayan damuwata, Amina ta gyara zama ta ce

"Hajiya ba kowa zaki kama ba illa ki kama Baffah ram a hannunki idan kika mallake Baffah yazama mulki da ikon gidan nan gaba ɗaya yana hannunki idan kuma company ya zama na Rubina toya zama dole a aurawa Amir Rubina mu samu company ya zama na Amir kinga mun karu" da sauri Hajiya ta mike tana zare idanu ta ce

"Allah ya tsari gatari da saran shuga wanne Amir ɗin wannan amir ɗin Allah ya kiyaye Amir ɗin danakewa tanadin auran Nabiha ƴar dubuty Govenour ki wani haɗasa da bara gurbin yarinya Rubina ƴar da akai zina aka haifa zan haɗa da ɗan danafi so fiye da kowa" Amina tai dariya itama ta mike tsayan

"To Umma wai kina zaton barta zamuyi ta zauna tare da shi daga zarar ya aure ta zamu aika da ita lahira a dabarance bayan nan kinga batada kowa komai zai zama na Amir"

"Ke nidai mubar maganar nan da ina murna kinzo da sabuwar dabara amma kinzo kin kauce hanya bari nayi magana da hajiya laurah maji mai zataje" Amir ya gyara zama zuciyarsa na ayyono masa da kyakkyawar surar Rubina ya ce

"Ai hajiya kawai ayi yanda Anty tace inaga kawai hakan zaifi mana sauki wajan ganin an kawo kashen munafuka Rubinan nan nima na tsaneta wallahi gaba ɗaya Baffa yafi sonta fiye da kowa a gidan nan nida kafin ki gaya min wace ita bakiga kishinta da nake ba amma sanda nasan ita ɗin ba jininmu bace sai naji salama"

"Kai Amir kiyaye ni har abada bazan taɓa bari jini na ya haɗu da Rubina ba ku tashi kuban waje" Amina ta taɓe baki tareda gyara zamanta a falon taɗau wayarta tana dannawa Amir ya shige ɗakinsa Hajiya tai samanta a fusace ta dannawa Hajiya Laurah kira


RUBINA
Kwanan Baffah shida a Londan muka juyo nageria bayan likitoci sun bani magani zamu koma karshan wata bayan bikin uwair, lafiya kalau muka sauka kano da sanyin asuba Yaya Amjad yaje ya ɗakko mu muna shiga gida na wuce ɗakina nayi sallar asuba sannan na kwanta barcin gajiya ban tashi ba sai goman safe, nai wanka sannan na ciro wayata daga handbag ɗita system ɗina na wajan Khalipha ina kunna wayar sakon Bakon masoyi yafara shigowa wayata

_"Wellcome back masoyiya, nayi farin cikin dawowarki da murnar samun lafiyar idanunki a shirye nake yanzu da ki bani dama na fallasa maki sirrin zuciyata ki bani dama na bayyana gareki masoyiya"_ dariya nayi bayan na gama karanta sakon kiran Yayna ya shigo na ɗaga bamu jima muna waya ba yagayan zai shiga office inya dawo zamuyi waya wai na kwanta nayi barci sosai na huta sanan kar nayi wasa da abinci na rinka ci har rabonsa, nai dariya kurum bayan na katse kiran, da yammacin ranar sai ga bakon lamari Ummi ta shaida min ina da bako a waje na tsaya ina kallonta da mamaki ta haɗe rai tana faɗin

"Ko bazakije ba" bance komai ba na saka mayafin abayar dake jikina saman kaina na gyara zaman glass ɗin idanu na nakai kofa zan fita daga falo ummi ta kira sunana a sanyaye

"Rubina Ki tsaya kiyi tunani kan abinda bakon ya gaya maki karki yanke hukunci da garaje" tana gama faɗar haka ta mike ta shiga ɗakinta, jiki sanyaye zuciya fal zulumi haka na karaso farfajiyar gidan namu can karkashin wajan hutawarmu dake kusa da garden na hango mutum zaune kan farar kujera yai kasa da kansa yana danna waya, na karasa wajan idanuna a kansa na ja ɗaya daga cikin kujerun dake ajje a wajan na zauna, sai sannan ya ɗago mukai ido biyu, na wangale ɗan bakina ina dariya

"Kai amma dai har naji faɗuwar gaba walahi da Ummi tace min wai nayi bako ashe kaine" yai murmushi idanunsa a kaina ya ce

"Kin zaci saurayinki ne"

"Saurayi kuma kai Allah na tuba ina ni ina wani saurayi ƴar karamar nan dani karatu fa zanyi"

"Aure bai hana karatu Husnah, kamar yanda kika sani Sunana Nuraddeen Kamal mahaifina haifaffan garin gaya ne mun taso acan munyi karatun pramary da sakandiri duka acan kafin muka dawo cikin garin kano da zama inda naci gaba da karatu na karanta low a bayaro university mahaifina ba wani mai kuɗi bane yanada rufin asiri yana da gidan kansa inda muke rayuwa da mahaifiyarmu Innah mu uku ta haifa nine babba sannan kanina Lameen da kanwarmu Sakina dake aure yanzu a katsina mahaifinmu ya rasu shekaru goma da suka wuce lokacin na gama jami'a na tafi low school yanzu haka muna zaune da Innarmu a gidanmu dake gandu ni lauya ne mai zaman kansa kanina Lameen yaci gaba da kula da shagon mahaifinmu dake ƴan kaba ni kuma nakan ɗan taɓa kasuwancin zamani" nabi Nuraddeen da kallon tausayi hakanan nake jin tausayin wanda duk ya rasa ɗaya daga cikin iyayansa nakan hango kaina randa zan wayi gari na rasa Ummi ko Baffah na aduk ranar danai wannan tunanin wuni nake bana iya cin abinci tausayin Nura ya mamaye ilahirin zuciyata

"Allah yajikan Baba, yakarawa Innah lafiya"

"Amin na gode Husnah, bazan ɓoye maki ba Rubina na kamu da sonki watanni da suka shuɗe bazance ga rana ba amma dai nasan kawai ina sonki Husnah nai magana da Baffah ya ce nazo na nemi soyayyarki inkin amince ya bani ke na fito ayi mana aure" dam gaban Rubina ya faɗi a fakaice take ɗan karewa Nuraddeen kallo ba laifi kyakkyawa ne to amma inta amince da shi kuma ya zatayi da karatunta kuma mai zatacewa Yay Uwair daya ce karta kula kowa zaiyi magana da Baffah taci gaba da karatu to ga kuma Baffah ya turo mata da saurayi, data tuna dokar Baffah sai jikinta ya kuma yin sanyi,

"Kinyi shuru Husnah inban maki ba ki faɗa min saina nemi wata"

"A'ah ni bance maka ba ama dai ka bani lokaci nayi tunani"

"Zan iya kuwa Husnah na faɗo sosai fa to amma dai na baki nan da dare dan Allah" kaina na ɗaga alamar to ya mika min wayarsa ya ce samin lambarki na karɓa nasa masa na mika masa ya kafe ni da idanunsa ya ce

"Yimin save" ban musa masa ba sabida sabo nane na riga na saba da Yayana Uwair bama musu komai yace to nake cewa nai masa na mika masa ya ɗago ya kalleni bayan yaga sunan da nasa

"Haba Rubina kuma bari kiga" bayan ƴan dane danne dayai a wayar ya ɗago min ita ya nuno min

"Love" na faɗa ina zaro idanu ya karɓi wayata yasa min lambarsa yai save ya nuno min screen na wayar na zaro idanu tareda dafa hannu a kirji nace "Na shiga uku My one ya zaka sakan wannan sunan Yayna zaiyi faɗa fa" annurin fuskar Nuraddeen lokaci ɗaya ya ɗauke ya mike yamin sallama nima na mike harya fara tafiya sai naji ba daɗi na ce

"Kayi hakuri" ya juyo yadawo kusa da ni ya tsaya yana kallona nai kasa da kaina

"Mai akayi na bani hakuri kin rigada kin gaya min ne kina da wani"

"Wani kuma wallahi banda saurayi Yayna fa Uwair aika san sa" na faɗa ina zaro idanu

"To saime dan yaga wannan sunan basai ki gaya masa ba saurayi kikai karki sake ki canzan suna" kaina kurum na ɗaga alamar to yai gaba ina kallonsa ina nan tsaye wayata tai kara alamar shigowar sako

_Jiki da zuciya sun shaida min yau abar kaunata tayi bako sai dai ki sanar da shi ke tawa ce a duniya insha Allah baki da miji inba ni ba_ bakon masoyi na faɗa a fili ban masa reply ba nai gaba abina bayan naga fitar Nuraddeen daga gidan namu

Kamar da wasa saiga soyayyar Nura da nake kira da Nuri ta mamaye duka zuciyata ashe da gaske Yaya Aliyu yake dayace soyayya nasa nishaɗi lokaci ɗaya na rikiɗe na zama masoyiya kusan kullum muna kan network nida Nuri muna musayar kalaman soyayya Khalipha yayi ta min dariya wai Allah shima soyayyar nan zai fara yagan ni bini bini ina kasa kasa da murya kamar muna fuka, shirye shiryan bikin Uwair muke gadan gadan Baffah yasa aka kawo mana kayan fitar biki da zamuyi daga shagonsa na kwari lace biyu atamfofi bibbiyu takalmini jaka da mayafi duka iri ɗaya dubu ɗari biyu Yay meer yasa min a account waina kwalliya sannan na karo abinda nakeso in kuɗin bai ishe ni ba na kira sa, ni mamakinsa nake ga hidamar biki gata gini danma ya gama kasan gaba ɗaya saman ne ya kulle wai ba yanzu zai gyara ba Raiha ta zauna a kasan, nidai nasan tabbas da biyu yai haka yana nufin saman na budurwar sa ne Husnah kamar yanda yataɓa faɗan saura kwana goma bikin ya dira garin kano ba zama kusan tare muke yawon rabon aibi da shi duk kayan fitar bikinsa duka yana waje na yau saura mako guda bikin gida yaɗau saiti Baffah yai gyara a gidan an canza duka kujerun gidan an suba sababbi a ko wanne part, ƴan uwanmu na adamawa sun fara zuwa ina zaune kamar wacce aka tsikara na tafi wajan Uwair ganin har sha biyu saura bai shigo part ɗin mu ba harna tura kofar ɗakinsa zan shuga sai kuma nai saurin maida kofar na rufe na fara kwankwasa kofar

"Wane a shigo" Yaya Uwair yafaɗa lokaci guda na shiga da sallama yana tsaye yana saka kayansa cikin babbar jaka ɗakin duk a hargitse

"Yayana yanaga haka kamar mai shirin tashi?" na faɗa bayan na zauna akan gadon, ya kalleni murnushi shimfiɗe kan fuskarsa na rasa kalar wanan kallo na Uwair dayake yimin shi a ko yaushe,

"Tashin zanyi ma ai Rubina gidan nan yafara tara baki bana son hayaniya kin sani, ga gobe ƴan uwan Hajiyarmu zasu zo azo ayita surutun ƴanzu wane ga yar wance kaki aura ka zaɓo bare kindai sansu da surutun tsiya gidana zan koma kawai na rinka leko ku" take naji zuciyata tai rauni na kifa kaina jikin hannu na na fara kuka ina ce wa

"Yanzu shikenan inka tafi na daina ganinka, saidai kazo mana na yan mintina kilama sai kayi sati baka leko mu ba shikenan in kazo kano ba anan zaka rinka sauka ba gidanka zaka wuce" Uwair yai dariya yana cigaba da saka kayansa cikin jakar yana kallon yanda take kuka

"Yawwa cigaba da kukan inda ma nake godewa Allah kuka kyau yake kara maki ba muni ba" Ai inajin yafaɗi haka saina fara share hawayan fuskar tawa na kakalo murmushi nayi ina sauke ajjiyar zuciya

"Kiyi hakuri Rubina nima ba da son raina zan barki ba akwai lokaci, lokaci na nan zai zo da zamu rayu a waje ɗaya" na wangale bakina kamar kofar gari na mike nai tsallan murna ni a zato da fassarar da zuciyata taiwa maganar tashi yana nufin zan koma gidansa da zama ne, sai naji daɗi na zanzare muka cigaba da haɗa kayan ya gama haɗa jakar ya jawo bedsite drower ya fara haɗo takardunsa yana saka su a wata karamar jaka nakai hannuna kan diary ɗinsa cikin zafin nama yakai hanunsa kan nawa ya fisge da sauri garin saurin ya saka a jaka ya faɗi ya buɗe, ware idanuna nayi da sauri ganin zanen hoto na ya zagaye sa da zanan hart na dafe kirji, ya wani aika min da banzan kallo ganin yanda na dafe kirji ina ganin bugun zuciyarsa ya kara karfi har ina iya juyo bugun fat fat da sauri sauri irin dai ya kaɗu ɗin nan, na sauke ajjiyar zuciya bance komai ba saidai a zuciyata girma da kimar Uwair ta karu sosai

"Yayana wai ashe har haka kake ga kaunar ƴar kanwar nan taka?" baice min komai ba har ya gama ɗaukar abubuwan mihimmai ya tisa keyata muka fita ya ce naje nai sallah na rakasa yaci abinci yunwa yake ji bai karya ba, ya wuce masallaci ni kuma na koma part ɗin mu, bayan nai sallah nai wanka na fito rikeda wayata danake duba sakon da bakon masoyi ya turon sarkin naci

_INA KANO_ Iya abinda ya rubuta kenan alamun yazo kano kenan ban masa reply ba na fita waje inda Yay Meer ya sanar min yana bayan gidanmu yana jirana bayason Hajiya taga fitarmu tare shi yasa, na zauna cikin motar ya mata key yana kallona na mika masa wayata tareda masa bayanin sakon da ake turo min da wata lambar daban da ba tada dayai bloking ba, ya taɓe baki tareda maido min wayar kan cinyata yaci gaba da tukinsa

"Ki basa dama yazo mana koba ce maki yai zai zo ba bayan kin rigada kin karya alkawarinmu kallonki fa kawai nake da baki gayan kin fara soyayya da Nura ba na sani tun ina Calabar aka sanar min tunda shi kika zaɓa Allah ya sanya alkhairi"

"Nifa wallahi yaya ba....bame ba Rubina?" yakatse ni da saurinsa

"Cewa zaki bakya son sa to yaudarar sa kike kenan toya zakiyi da Baffah dake shirin kiranki a yau ya tambaye ki kina son Nura" na zaro idanu adai dai sanda wayarsa tayi kara

Amir dake zaune kofar gidansu Salima suna hira akan idanunsa Uwair suka wuce shida Rubina a mota ba shiri yaiwa Salima sallama ya koma gida ya shiga yana kwaɗawa Hajiyarsu kira ya isketa can bedroom ɗinta

"Kina nan Umma kina shirin aurawa Raihana Uwair ga can ya na yawo a gari da Rubina ya ɗauketa sun fita ko ina suka tafi bakiga wankan da sukai ba nifa na fara zargin Uwair laluɓe yarinyar nan yake ke kuma kin kasa fahimta"

"Kai Ubanka Amir Allah ya tsare can dai kan ƴaƴan wasu amma badai Uwair ba mutumin banza matsa ka ban waje ɗan iska kawai" Amir da zuciyarsa ke tafarfasa ya juya ya fita yana jin badaɗi shiga harga Allah zuciyarsa ta biya da Rubina ɗakinsa ya faɗa ya kunna sigari ya fara zuba ba kakkautawa

Har kiran da takewa Uwair ya katse bai ɗaga ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login