Showing 9001 words to 12000 words out of 42953 words

Chapter 4 - RASHIN MAHAIFANA COMPLATE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

140

baya ta fasa shiga part ɗin Baffa, ina shiga ɗakina wayata tai kara alamar shigowar sako saida nai shirin barci nasa kayan sanyi riga da wando naja bargo na lulluɓa sannan na ɗauki wayata na duba messages ɗin daga Yay Meir

_Kiyi hakuri Rubie ki yafewa Hajiya muna nan kalaman datake binki da su insha Allah wataran zata gane gaskiyya nidake jini ɗaya ne ba abinda zai rabamu ina tare dake zan zame maki bango majinginarki a ko yaushe_ nai murmushi ɗan wannan kalaman ya wanke min duka kuncin dake zuciya ta najima na yafewa Umma hajiya, nai addu'a na maida kaina na kwanta

Hajiya Zainab data fito daga part ɗin Baffa a maimakon ta nufi wajan ta saita nufi part ɗin Umma Hajiya ta sameta zaune nan falonta tana duba littafin muwadɗa malik kallo ɗaya Umma Hajiya tayiwa Hajiya Zainab ta maida hankalinta ga karatun da take

"Hajiya kina kallon abinda ke faruwa a cikin gidan nan kin zuba idanu ko to ki kuka da kanki randa wani abin kin ya fito daga wajan wannan shegiyar yarinyar Rubina da ɗanki Uwaimeer" Hajiya Umma ta mike a fusace ta karasa gaban Hajiya Zainab tana huci ta dafa kafaɗar hajiya Zainab ta ce..........

07039793439
[7/27, 4:58 PM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹


Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA

Episode four4️⃣

*Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne*

"Mugun nufinki yabiki Zainab mummunan zaton da kikewa Uwaimeer a gidan nan ki gansa a kan ƴaƴanki"

"Banzo nan danna gaya maki magana mara daɗi ba kawai nazo na nuna maki abinda tunaninki baikai nan ba amma tunda haka kika ce shikenan" ta juya ta fice faga ɗakin ta koma part ɗinta tana mita

"Umma ni kinzo sai mita kike min waya kaiki wajanta bayan kinrigada kinsan halin Hajiya bata ragawa kowa a gidan nan ba"

"Rahama daga zuwa gaya mata gaskiyya sai abin ya zama da gayar magana to na zuba idanu kamar yanda ta zuba nata in wani abin yafaru mu ƴan dariya ne"

"Allah ya kyauta" Rahma tace ta mike tabar falon ta koma ɗakinta

Kwana biyun da Yay Meer yamana a kano jinsa nayi kamar wanda mukai wata biyu sabida washe gari wajan goma na safe muka fita nida shi gidansa dayake ginawa dake unguwar bechi sabuwar unguwace hakan yasa gina ginen ma ɗai ɗaiku ne muka shiga gidan da har an rufasa anma yiwa wani wajan plastar dan kasan ma an gama plaster ko ina saura kaɗan ya kammala muka gama leka ɗakunan kasan muka fara hawa step ɗin da zamu hau saman benan

"Wato a rayuwa ina kaunar saman bene, Yay Meer nifa zan iya rayuwata a sama bazan sakko ba inba wani waje zani ba" yai murmushi ya jingina ta bango ya tsaya daga tafiyar da yake yana kallona da murmushi a fuskarsa ya ce

"Kawai kice inna tashi samar maki miji cikin abokai na na samo maki wanda gidansa bene ne" nai dariya ina cigaba da hawa step ɗin muka karasa saman

"Hmmm wayyo rayuwa Yay Meer nan ace ni za'a kawo ko to ina jin da kaina zanzo na tsara komai yanda falona da sauran rooms zasu kasance" yai murmushi batare daya ce komai ba muka gama kallon gidan muka fito yana lissafa min abinda yarage za'ayi a gidan, har muka karasa gidan Anty Sanah hirar gidan yake bamu jima sosai a gidan ba dan yau ziyara zamuyi saida mukaje duka gidan yayunmu mata waɗanda suke aure anan garin kano sai ƴamma muka koma gida bayan mun biya ta shoprite ya min uban siyayya haka muka koma gida da niki nikin siyayya a hannu na washe garin da zai koma calaber nayi kuka sosai har muka rakasa filin jirgin saman malam Aminu kano yatashi ina kuka sosai kamar wanda akace min yatafi kenan, Muna tafe a mota sanda muke hanyar komawa gida Yaya Amjad sai faɗa yake min "Kin wani cikan mota da ihun kuka kamar wanda aka ce maki yatafi kenan karyar banza nan da gobe ma kila kin manta da shi" shiru nayi ban tanka masa ba yinin ranar sam gidan bai min daɗi hakan yasa na tattara na tafi gidan Yaya Aliyu kamar yanda na saba nakanje wani bin nai sati guda na dawo Allah yahaɗa jini na da Anty Hannah matar Yaya Aliyu, Fauzan da Ni'ima mai sunan Ummi su nake wasa da su suka ɗebe min kewar Yay Meer har zuwa sanda Yaya Aliyu yadawo daga office shima yai murna sosai da zuwan nawa bayan yai wanka ya huta daga gajiyar aiki bayan sallar mangariba yace muzo mu fita shopping nida shi da Fauzan muka fita cikin nishaɗi sai bayan sallar insha muka dawo gida Anty Hannah na tsokanarmu ina nata siyayyan, nai dariya kawai batare dana ce mata komai ba na nufi ɗakin Fauzan, washe gari dazan tafi scool tare muka tafi da yaya Aliyu da Fauzan kasancewar Fauzan schools ɗinsu bata kai tamu nisa ba yasa shi aka fara ajjiyewa kafin ya ɗauki hanyar school ɗinmu a hanya yana tuki jefi jefi yana kallona da murmushi

"Wai nikan Rubina samarinki nawa?" saurin kallon Yaya Aliyu nayi ganin mun haɗa ido sainai saurin saka hanuna na na rufe fuskata ina dariya

"Au dariya ma na baki, tambayarki fa nayi ko bazasu lissafu ba?" kaina na girgiza ina murmushi kana na ce

"Banda saurayi ko ɗaya Yay Meer yace min karna kula saurayi inna bawa wani saurayi damar zuwa gidanmu to Baffa zai fara min maganar aure ni kuma Allah ya gani karatu nakeson yi bana ra'ayin aure" Yaya Aliyu ya taɓe baki kana ya maida hankalinsa ga tukin motarsa can kuma ya ɗago ya kalle ni ya ce

"Komai Yaya Uwaimeer komai Yay Meer to ya tsaya yana maki wayo shi yana can yana soyayya da budurwarsa ke kuma kin killace kanki kin hana kanki kula kowa ai soyayya bata hana karatu ko wanne zaman kansa yake, ki buɗe kunnaki da kyau ki jini haka ki buɗe idanunki daga rufe sun da Uwaimir yasa kikai kisani Rubina soyayya wata duniya ce mai zaman kanta soyayya nishaɗin rayuwa ce, musaman inkayi katari da wanda yake sonka kake sonshi, Rubinan Ummi ki buɗe zuciyarki kawai ki bawa masoyanki dama su fito su bayyana maki irin son da suke maki" bance masa komai ba nai shuru ina tunanin maganganunsa har muka karasa school ɗinmu sanda zan fita daga motan na juyo na kallesa na ce
"Yaya Aliyu kace na bawa masoyana dama su bayyana min son da suke min to ai ni ba wanda yataɓa zuwa ya ce yana sona"

"To dama wane xai zo yace yana sonki kin sa a ranki bazaki soyayya ba yanzu kiyi tunani mai kyau" na fita daga motar bayan munyi sallama ya bani 500 na break sabida ban tawo da abinci ba sai goran lemu dana ruwa kawai dana ɗakko,

Uwaimeer tun a cikin jirgi yaji gaba ɗaya kewar Rubina ta kamasa har wani sanyi sanyi yakeji a jikinsa sanda ya sauka a airport na garin yai waya a barreck ɗinsu akazo aka ɗauke sa tunda ya shiga gida ya kasa nutsuwa, kewa tunanin Rubina gaba ɗaya sun addabi zuciyarsa ya kunna data ya hau online mirmushi yayi sanda yaga stetus ɗin Rubina na one hourse daya wuce hotansa ne da emojis na kuka a kasa tai rubutu _Safe trip my Lovely broth_ lallausan murmushi yayi kana yai mata reply shima da emojis na kuka ya kashe datan ya fita wajan barreck ɗin,Washe gari Monday sassafe yai shiri ya nufi office ɗin mejor Usman Karaye,

Rubina sanda nadawo daga school gaba ɗaya maganganun da mukayi da yaya Aliyu ke min yawo aka da gaske ne abinda ya faɗa kodai shin tayaya zan tabbatar da gaske ne soyayya nasa nishaɗi yinin ranar nazarin maganan nake har sanda Yay Meer ya kirani muka gaisa kamar yanda muka saba mun gama hirar da muke duk dare akan karatuna yana shirin katse kiran na aka masa da tambayar abinda yake damun zuciyata tsawon yinin

"Yay Meer wai da gaske soyayya nasa nishaɗi wai soyayya wata duniya ce mai zaman kanta?" da sauri Uwaimeer ya mike zaune daga kwancan da yake harda wani dafe kirji ya ce

"Rubie waya faɗa maki wannan maganan?"

"Yaya Aliyu ne fa ya gayan da safan nan da muka tafi school ni kuma na wuni maganan naci min rai na rasa wazanma wannan tambayan da a gida nake to tabbas Ummina zan tambaya kuma sai gaka ka kirani" wani gwauran numfashi Uwaimeer yaja ya koma ya kwanta ya lumshe idonu yana murmushi "To yanzu mai kike so nace"

"Ka gaya min gaskiyya ne ko karya, in gaskiyya ne to tabbas nima ina son tsaida saurayi"

"To ba gani ba ki tsaida ni kawai"

"Subhanallah Yay Uweir Rubina ce fa"

"Au ai na zata da Assama'un Baffa nake magana" mukai dariya lokaci ɗaya kafin na katse kiran ganin Uweir na neman katse min tunani na danake son zurfafawa har nayi barci da tunanin araina washe gari bayan nayi sallah da asuba na kunna wayata sabida ka'idar Ummina ne kashe waya a duk dare nima abin saiya shiga jikina kullum karfe goma na dare nakan kashe wayata, ina kunna wayata sakone yafara shigowa na wata sabuwar lamba

_"Barka da safiya tauraruwar mata abincin ruhina, zuciyata na rayuwa kullum da begenki da kauna kullum ina mafarki da burin ganin ranar da zan fallasa maki abinda ke raina ki bani dama na buɗe maki zuciyata tauraruwa ta"_

Na karanta messages ɗin yafi sau goma karo na farko na amsa tex messages daga masoyi duk da bansan daga waye ba amma lokaci ɗaya naji zuciyata ta kamu da son ganinsa banyi reply wa sakon ba amma kam matuka naji daɗin sakon, dan koda nadawo daga school kafin na tafi Islamiyya saida na kuma karanta messages ɗin wani ikon Allah da dare ma da zan kwanta saiga wani zazzafan massages ɗin nayita karantawa ina murmushi ni kaɗai, abu kamar wasa saiga shi kullum messages saiya shigo min sau ba adadi a rana na zafafan kalamai masu daɗin gaske da sanya zuciya a shauki

Hajiya Umma zaune suke saman fararan kujerun dake ajje kasan bishiyar data yiwa gidan rumfa

"Hajiya Haule na rasa yanda zanyi da yarinyar nan nifa kullum na buɗi idanu na ga yarinyar nan na tuna alakar ta da Uwaimir zuciyata bata min daɗi ina zargin da wani abin makale a zuciyar Uwaimeer amma kullum inna titsiye yaron nan ce min yake ba komai nidai ina jin tsoron faruwar wani abin, ita kuma shegiyar ga bakin jini har yau fa babu wanda yataɓa zuwa yace yana sonta koda wasa nifa da cewa nayi kodai gidan bokanya zamuje amin aiki akan Rubina a sami wani yazo ya aure ta ko zuciyata ta sami salama"

Dariya Hajiya Laure tayi kana ta gyara zama ta ce "Ni daɗina dake wutar ciki ina ma haɗin Uwaimir da Rubina shegiyar da batada asali zaiyi gangancin aura idan yana son Rubina to ai bazai taɓa karɓar tayin auran Raihana ba duk da ina ganin gangancinki wallahi Hajiya Binta da har kikayiwa Uwaimir tayin auran Raihana har mai Rahina suke da shi aduk cikinmu kawaye kinsan itace koma baya a cikinmu itace mijinta baida karfi duk da mai kuɗi ne kinsan ai bai kai mazajanmu ba karma mijinki yaji labari mai makon ki shiga ki fita ki samo masa mata ƴar minista ko ƴar wani kusa a gwamnati kamar mu ko kuma cikin ƴaƴan manyan masu kuɗin kasar nan kika ɓige a gidan Rahina har mai suka mallaka da har zakiyi sha'awar haɗa zuri'a da su"

"Hajiya Haule sam ni bana burin ɗana ya auri ƴar mai kuɗi wanda ubanta yafi ubansa arziki to idan kai haka mai kenan kace mata mai bare ma kinsan Uwaimir duk cikin yarana shine mai karamin karfi to mai zaisa na ɗakko ƴar da zata zo ta raina min shi koba komai na yaba da tarbiyar Raihana tabbas Rihana tayi matukar kokari wajan bawa Raihana tarbiyar da ita ta jani"

"Hmmm to faɗa mana mu ƴaƴanmu basu da tarbiyya"

"Nifa bance ba ranki ya daɗe" Hajiya Bintu ta faɗa tana ƴar dariya

"Kece da abin haushi ana nuna maki gabas kina yamma ai auran ƴar manya babban jari ne kina gani saida na shiga na fita wajan ganin Faisal ya auri ƴar gwamna sannan zuciyata ta sami salama, Hajiya Umma tai dariya tareda ɗaukar hand bag ɗinta sukai sallama Hajiya Haule ta mata rakiya har wajan motarta ta shiga ta tashi motan ta ɗau hanya

🔯🔯🔯🔯🔯

Mama oyoyo oyoyo mama abinda Marwa da Amira ke faɗa kenan suna tsallan murnan dawowar Mamansu da yau kwana huɗu kenan rabonsu da ita, Salima dake kwance a ɗaki tana chat ta fito da sauri jin ihun Marwa da Amira

"Umma ina wayanki?" Salima ta aika mata da tambayya

"To uwata na saida ita" Umma ta faɗa tana kokarin zama kan kujera ƴar tsugunno dake tsakar gidan taja Amira jikinta tana shafa kanta ta ce

"Uwata nayi kewarki da yawa inata tunaninki"

"Mama mu kuma bakya tunaninmu?" Marwa ta faɗa tana turo baki gaba

"Marwa nayi mana ai gaba ɗaya nake tunaninku har wancan sakaran Sani baya ma gidan ko naji banji hayaniyarsa ba

"Mama yau kwana biyu kenan bamu saka sani a idanunmu ba tun shekaran jiya da yazo bai sake dawowa ba yau da safe naiwa Baba maganar sai cewa yayi maiya dame sa ko ina yaje ai zai dawo ba yaro bane shi ai

"Hmm lamarin Babanku saidai addu'a na rasa gane kan mutumin nan" Mama na rufe baki saiga Baban ya shigo yana masifa

"Ke Gambo ina kike Gambo ko baki dawo daga yawon ta zubar ɗin naki ba ne? to inma bata dawo ba ke Salima zo kiji wai an kama Sani yana police stetion saiki shirya kije nidai bazanje ba bare sisina tai kuka"

"Malam wai ko baka gani ne naga gani a gabanka amma kazo kana ta ɗaga murya"

"Au ashe kin dawo to maza kije division na sharaɗa ɗanki na can" yana gama faɗar haka ya shige ɗakinsa bai sake kallon inda Mama take ba, Mama ta share hawayan da suka zubo daga cikin idanunta ta ce

"Kai jama'a Sani so yake ya kashe ni da raina inba haka ba sau nawa ina gargaɗinsa yadaina abinda zai kaisa wajan ƴan sanda amma bayaji duka duka yau she aka karɓosa daga division na sheka Allah kana gani ka shirya min wannan yaron"

"Mama duk ba wannan ba ayi kokari aje kafin a mika sa kotu azo ana kici kicin biyan kuɗin tara"

"Salima toba magana bace ta kuɗi wallahi ko biyar ban sauka da ita ba a garin nan aikin girki mukaje kaduna fa gidan masu kuɗi sosai wallahi wayata na siyar nai kuɗin mota amma mutanan nan wai sai cewa sukai mu bada account number zasu turo mana kuɗaɗanmu nidai gani ma nake ba turo mana zasuyi ba,"

"Kema Mama nace maki ki daina yawon bin gidan bikin masu kuɗin nan kina masu girki kayi masu bauta amma su suna kyashin su bitaka hakkin ka kiga fa yanda kukai a gidan bikin Hajiya Maimuna haba Mama"

"Salima kenan inna zauna mai zamuci ko zuba maku idanu zanyi, kinadai ganin halin da ake ciki kin rigada kin san halin babanki"

Salima taja tsaki ta koma ɗaki tana mita, washe gari sassafe ta tafi stesion ɗin da akace Sani nacan yinin guda ta kwashe a wajan ƴan sandan sunki bata belinsa dole ta dawo gida cikin damuwa suke tattauna maganar da Marwa da Mamansu,

"Mama ni gaba ɗaya zaman nan haka yadaman kullum bakada kuɗi a hannunka kana kallo mutane kowa na kashe kuɗi musamman a break na makaranta yanzu fa takai matakin bana ma iya fitowa cikin makaranta sanda aka fito break sai kawaye na su rinka min dariya suna nuna ni wai na cika mammako da son kuɗi" Marwa ta faɗa tana share hawayan idanunta, Mama ta mike ta shiga ɗaki tana goge hawaye ta ari wayar Salima tasa wata lamba bugu ɗaya ana biyu aka ɗaga kiran

"Assalamu alaikum"

"Wai kece a daran nan ko dai zaki zone mu kwana yau zan baki ko nawa kike so"

"Ba wannan ba Sammani an kama ɗana Sani Salima yau taje wajansa amma a police stesion amma sunki bata balinsa haka ta dawo nace bari na kiraka ko zaka taimakan"
"Kinsan wannan ba wata matsala bace Abu kawai dai dole ayi abin nan da hausawa ke kira ban gishiri na baka manda gobe zanje inda yake zan kawo maki shi har gida da dare ke kuma kizo mu kwana tare kuma dole zaki bani dama naji zumarki ba kamar da ba" Mama tai shuru ta kasa cewa komai tana tunanin shin ta amince masa ko kuma? to inta ki yarda tayaya zata fito da Sani daga wajan ƴan sanda

"Ya kikai shuru ko na baki lokaci kiyi tunani nan da goben"

"A'a shikenan Sammani na amince inya fito ɗin zan zo inda muka saba haɗuwa" Alhaji Sammani ya gintse wayar ya kece da dariya harda kwanciyya a kan gadon dayake zaune ya kalli yarinyar dake ta barci kan gadon yana jin wani shauki na daban da burin ganin safiya tayi yaje ga ƴan sanda ko nawa zai bayar a saki yaron indai zai sami cikar burinsa akan Abu matar da suka haɗu watanni huɗu da suka wuce da farko sun haɗu a facebook ta fara da turo masa sassan jikinta a hoto yana biyanta har takai ga sun fara haɗuwa yana rage zafi da ita yana biyanta a cewarta inya biyata yaranta take saiwa abinci duk yanda yakai ga son ya shige ta taki basa dama sai dai kawai su haɗu a ragewa juna zafi ya biyata su rabu, sai gashi a ɓagas gobe zai sami cikar burinsa, a ɓangaran Mama ma shiru tayi tana tunani a zuciyarta ita kaɗai

"Na shiga uku ni Abu mai nake shirin aikatawa ne haka, ina zan kai gingimeman zunubin nan da aure na, kawai kima daina wani tunani ki amince kawai baga shiba ga kowa ma indai zaki sami abinda zaki rufawa ƴaƴanki asiri" taji ɗaya ɓangaran na zuciyarta ya bata amsar datafi aminta da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login