Showing 21001 words to 24000 words out of 42953 words

Chapter 8 - RASHIN MAHAIFANA COMPLATE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

141

zata dawo taci gaba da gani koda ba kamar na kowa ba" Ummi dai bata saurari mai yake cewa ba kuka kawai take Ummu ta kama ta suka shiga ɗakin da Rubina take

"Ummi ummi bana gani duhu nake gani Ummi kina ina bakya jina ina idanuna ina gani na ya shiga ba kowa ba kowa a kusa da ni na farka fa Ummi kimin magana dan Allah Ummi kodai bana duniya ne kodai Hajiya ta kashe ni ne Ummi nasan koba kowa a kusa dani nasan ke kina tare dani kimin magana Ummi wayyo inaga na mutu shikenan na bar duniya na daina ganin Ummina Baffana Yayana Uwaimeer Yay Meer kana ina ina kake to kazo kai kazo wajena da sauri" Ummi ta rungume Rubina tana kuka sosai jin kalaman ƴar tata ta ce

"Gani Mamata gani a kusa dake, ji kamshina kiji kamshin jikina Uwata ina tare dake har karshan numfashi na Assamu'u Husnah"

"Ummi maiya sami idona maiya sa na daina gani to"

"buguwa ce amma yanzu muna hospital verysoon zaki fara gani kinji Rubina ta, idan har kuɗi suna magani insha Allah zan nema maki magani ki dawo gani koda komai dana mallaka zai kare zan fara magana da Dr afara nema mana hospiral mai kyau a faɗin duniya ko ina ne zan kai ki insha Allah Rubina ko idanuna zan iya mallaka maki ni asamin nakin nasan zaki kula dani zaki min komai" Rubina ta kankame Ummi ta fashe da kuka jin sabuwar kaddarar data afko mata a wannan rana kuma

"Ummi mainayi wanne zunubi na aikata sati biyu da suka wuce na karye yanzu kuma idanuna wayyo Allah na tuba Allah ka yafe min" shigowar Dr yasa Ummi ta saki Rubina tana kallon Dr ɗin

"To Alhamdulillah sakamakon binciken mu ya fito jijiyoyin idanun Rubina basu gama mutuwa ba sanyi sukai zamu ɗorata a magani duk sati zakuna zuwa ganin Dr bayan sati huɗu zamu mata aiki insha Allah ganinta zai dawo"

"Masha Allah mungode Dr Allah yasaka"

"Amin hajiya zaku iya tafiya ga takardar magungunan da zaku siya a kula sosai da ita dan Allah"

"Ba damuwa" Ummi ta faɗa bayan ta mike tana kallon su Abbakar dasuke tsaye carko carko shida Aliyu da Ummu

"Abbakar ku tafi gidajanku muma zamu koma gida mun gode"

"To Ummi Allah ya kara afuwa, sannu Rubina Allah yabaki lafiya"

"Amin na faɗa ina makale jikin Ummina data kamo hannuna muka fara tafiya slowly tana kula da duk wani takuna har mukazo inda naji ta ce "Shiga mota a hankali kinji Mamana"

Na shiga na zauna bayan na matsa harna tarar da mutum nakai hannuna na taɓa, "Rubina nice Ummu na rigaki shigowa motar zauna dai dai kinji" Ummu ta faɗa da tausayawa naji mun fara tafiya a motar na kai hannuna jikin Ummi ina laluba ta ta kamo hannun nata cikin nawa ta ce "Mamana ya akai" na kwantar da kaina a jikinta na fashe da kuka

"Rubina nima kuka kikeso nayi, maine abin kukan to?"

"Ummi tsoro nakeji karna makance inna makance shikenan bazanyi aure ba ko" tambayar tata tasa Ummi ta murmusa kana ta ce

"Ko kin makance zaki aure Rubina saimu tafi tare gidan auran na rinka makikomai" nai dariya tareda ɗago kaina kamar ina gani

HAJIYA UMMA
Amir ne yataimaka mata ta tashi zaune ya kamata suka nufi part ɗinta yana mata sannu ganin yanda take ɗingisa kafarta

"Amir lalle wannan yarinyar Fatima ta siyowa kanta masifa da kuɗinta sai nayi maganinta a gidan nan saina nuna mata ita karamar yar iska ce zanyi maganinsu daga ita har shegiyar ƴar tata"

"Hajiya nifa tsoro nakeji bakiji yanda yarinyar ke kuka ba tana faɗin bata gani karfa muyi mata illa fa ina tsoron gamuwata da Baffah kinsan halinsa akan yarinyar nan"

"To sai me Amir karma kaji wani tsoro shikansa Baffan anan ɗina nake ganinsa wallahi" Hajiya ta faɗa tana nuna tafin hannunta

"To nidai hajiya kashe wayata zan bazan sake muyi magana da Baffah ba har sai yadawo kasar nan ma gamu kafin nan ya manta ko kuma na gudu adamawa gidan Nene itace zata hanasa duk wani abu dazaiyi ya hanu"

"Ni kama tuna min da ita bari na maza ma na kirata nayi riga malam masallaci" Amir dai yasa kai ya fita yana zuwa harabar gidan yaga babban yayansu Mahmud wanda suke kirada Daddy ya fito daga motarsa yana kallon Amir ɗin daya gansa ya basar yai kamar bai gansa ba, a fusace Daddy ya karasa wajan da Amir ke tsaye jikin motar Uwaimir ya fisgi hannunsa suka shiga part ɗin Hajiya

"Kai Mahmud lafiya zaka kamo min hannun ɗa haka kamar ka kama mai laifi"

"Hajiya kunsan abinda kukayi kuwa keda Amir, Rubina fa ta daina gani gaba ɗaya Ummi nacan tana ikirarin zata shigar da kara mai kike zato zai faru a gaban ƴan sanda"

"Komai zai faru yadaɗe bai faru ba Mahmud, akaini bangon duniya ma ba wajan ƴan sanda ba, duka kuma na daka ni na daketa ba shi ba bashida laifi komai duka nawa ne ehe, sai mai danna daki shegiyar ƴar da batada uba"

"Hajiya niki gaya masa ya sakar min hannuna nai tafiyata abokai na na jirana zamu fita" ɗau Mahmad ya ɗauke fuskar Amir da mari jin yanda yake masa magana gatsal

"Mahmud!!! ka kuma gangancin dukar min auta saina masifar saɓa maka ka sakar masa hannu yai tafiyarsa kafin nakai maka duka, idan kai baka kishina shi yana yi kai gaba ɗaya kana kan layin da Baffanku ya ɗora ku har maye kuda balle romansa mai akai akai wata can banza Rubina shegiyar waye baisan ita wace ba" Fuuuu Mahmud ya fice daga part ɗin Hajiyar ya nufi na Ummi daya hangi gilmawarsu yanzu

🔯🔯🔯🔯🔯
Nuraddeen shida Lameen zaune cikin gidansu karkashin bishiyun da suka zagaye wajan yai luf luf yana fitar da wani sanyin kamshi, ahankali Lameen ya ɗago idanunsa ya kafe yayan nasa da su wanda ya lura yai nisa a duniyar tunani yakai hannu ya taɓa sa, Nuraddeen yai girgigit ya ce

"Na'am Innah" dariya Lameen yayi harda buga hannuwa ya ce

"Ina kaga innar anan Innar da bata gidan nan ɗazu fa ta tafi gaya gaisuwa" Nuraddeen ya harari kanin nasa ya maida kansa ya kwantar jikin kujerar dayake kai ya ce

"Kawai ka katse min tunani na mai daɗi gani ga ita a zaune cikin lambu muna bawa juna fure" Lameen ya zaro idanu yana dariya ya ce

"Akaro na farko yau kayi zancan budurwa tun bayan rasuwar Hafizah" Nuraddeen ya buɗe idanunsa da suka fara canza launi ya kalli kanin nasa kana ya ce

"Na mato dayawa Lameen lokaci ɗaya na faɗa kuma saina shiga irin sosai ɗin nan" Lameen ya kuma tuntsurewa da dariya harda tafa hannu

"Wayyo Innarmu ga abin farin ciki gashi bakya gida ubangiji yadawo mana dake gida lafiya yau muyi farin ciki tuzuru ya kusa angwance wa"

"Kai banza nifa zancan nan danake maka banfa faɗa mata ba, tsoro nakeji kar ace tanada wanda takeso"

"Kanaji na yaya Noor kawai ka sami mahaifinta ai dattijon arziki ne ka fito sak ka gaya masa kana son ƴarsa yabaka dama ku dai daita, to in akwai maganar wani zai gaya maka in babu kowa kuma zai baka dama ku daidaita daga nan sai shirin biki bidiri wooni babban Aminin ango" Nura yakaiwa Lameen duka a kafaɗa ya ce

"Ji baika kai bakaji kunya ba ta ina ka zama aminin ango kadai tsaya a kanin ango bama haka ba ya akai kasan wacce nakeso har kasan mahaifinta dattijo ne" dariya Lameen yayi kana yafara magana

"To zamu gani Allah yanuna mana lokacin nidai nasan yaya Noor bashida Amini sama da ni, kuma tuni na gano ga wallahi yanda kake zarya gidansu Rubina ai kowa yasan ba iya duba lafiyarta kake zuwa ba harda gyara lafiyar taka zuciyar" Nuraddeen yai dariya kawai ya kalli agogon hannunsa ya mike ya nufi cikin gidan nasu yana sakin murmushi da cin alwashin Allah yadawo da Baffah lafiya ya gabatar masa da kansa

Uwaimir yana tsaye gaban ɗan ginin dake kusa da gidansa hannunsa rikeda cup a hankali yana shan copi, lokaci ɗaya yaji gabansa yai wata irin bugawa da karfin gaske kafin ya kware da Copi ɗin dayake sha yai saurin zubo dana bakinsa kasa ya ajje cup ɗin ya shiga cikin gidansa ya ɗau wayarsa yana ambaton "Rubina", wayar Ummi ya kira tanata ring ba'ayi picking call ɗin ba harta katse ya kuma kira a wannan karon bugun farko aka ɗaga a maimakon yaji maganar Ummi sai jin Khalipha yayi yana kuka kasa kasa

"Kha...Kha...li..pha" Uwair ya ambaci sunan nasa a rarraɓe gaba ɗaya ya ruɗe jin Khaliphan na kuka

"Na'am yaya Uwair"

"Ina Ummi tana ina bata wayar muyi magana mai ya faru maiya saka ka kuka yanzu?"

"Ummi ta tafi da Rubina asibiti Amir da Hajiyarku ne suka kamata a part ɗin Ummu sukai mata duka Yaya ina jinma Rubina ta mutu zuwa yanzu bafa ta numfashi aka fita da ita shikenan munyi rashi yaya Uwaimir Rubina ta mutu ta barmu" da sauri Uwair ya lalubi bango ya jingina kafin kuma ya sulale ya zauna kan tayels yana bin wayar da kallo kamar wani soko yakasa aikata komai ma zuciyarsa gaba ɗaya ta tsaya cak na ƴan lokaci kafin kuma ya mike a zafafe ya saki wani ihu ya ce "Ina karya ne karya kake Khalipha ba yanzu ba, ba yanzu mutuwa zata rabani dake ba Abar kaunata wayyo Allah Hjiya Amir mai kuka aikata haka" da sauri ya shiga ɗakin barcinsa ya saɓo jaka harya fito ya kalli kansa yaga kakin soji ne a jikinsa ya koma ciki ya cire ya canza kaya ya fito kai tsaye ya nufi tashar mota baya jin zai iya jiran jirgin safiya ya sani nan da safiyar ko basu kai kano ba kaɗan zai rage masu tunda kwanan hanya zasuyi, cikin mota yayi lamo ya kasa aikata komai kansa yakeji yana tsananin sara masa, layin Daddy ya kira saidai harta karaci ring ɗinta bai ɗaga ba, shikenan kila zancan Khalipha ya tabbata Rubina ta mutu, ya kunna data ya shiga whatsapp ɗinsa ya duba stetus na ƴan gidansu yaji ba wata magana ya duba group ɗinsu Baffah Family yaga nan ba ba wani labarin rasuwar Rubina ya koma group ɗinsu na iya ƴan ɗakinsu nan ma baiji komai ba, kawai ya kifa kansa a cikin kafafunsa yana sauke numfashi yana jin yanda motar daya hau ke shoshala gudu a hanya kasancewar homer yahau amma duk gudun nan shi gani yake kamar driver ɗin baisan aokinsa ba,

anan kano kuwa Daddy yana shiga falon Ummi ita kuma tana kokarin kiran waya tana magana da Khalipha

"Warisha nakeson na kira ita kaɗai zata ita tayani yakin nan tazo ta kaini wajan ƴan sanda na shigar da korafi na"

"Ummi dan Allah kiyi hakuri kibar maganar nan ayita a cikin gida family isshue ne fa"

"Kai kasan family ɗin Mahmud ni bansan shiba gari ne ko unguwa anan kanon, acuci ƴata kuma ana kokarin hanani na kwatar mata ƴancinta"

"Fatima idan baki kwatar mata ƴanci ba kinci kaza kazanci nace ƴan sanda ko maza maza kira min su suzo su tafi dani kiga inzan kwana a hannunsu, kai kuma mara zuciya soloɓiyo daman nan ka taho bada hakurin kar a kira min ƴan sanda dan Allah ba ƴan sanda za a kiramin ba barikin sojoji suzo su tafi dani ina shirye daga nan suje su jefani a teku koba komai burina ya cika yau na nakasta yarinyar nan Alhamdulillah, Ummi ta mike daga kan kujerar da take zaune ta fara naɗe hannun doguwar abayar dake jikinta tana nufar Hajiya Umma, da sauri Daddy ya shiga tsakanin su ya tare Ummi daya lura ta fusata

"Ummi wai maine kuke haka dan Allah dan girman Allah ku bari ku tsaya ayi magana ta fahimta"

"Mahmud fita daga cikin maganar nan ka matsa ka bani waje kafin na baje ka a falon nan, yau saina ramawa Rubina abinda matar nan ta mata billahil azim yau saina zubarwa da Bintu idanu a gidan nan dai dai nima a zubar min da nawa......"

07039793439




🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹


Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Association* ☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA

Episode Nine9️⃣

*Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne*

"Mahmud idan baka matsa ka bata waje tazo ta zubar min da idanu ba saina saɓa maka, dan Ubanka matsa ka bata waje in batada hankali ta karaso nan wallahi sai dai a ɗauki gawarta"

"Adai ɗauki gawarwaki dan wallahi kinyi kaɗan ki iya dukana na kyale ki ke a Mahmud ka bani hanya"

"Ummi Hajiya dan Allah dan Allah ku bari haba mana" Warisha ce ta shigo ɗakin hankali tashe ɗazu sukai waya da Aliyu yake faɗa mata abinda yafaru nan take ta baro wajan aikinta ta shigo ta tarar da wannan hayaniyar, ita taja hannun mahaifiyarta takaita bedroom ɗinta ta fito ta kama hannun Rubina suka shiga cika ko kallon inda Mahmud da hajiya suke batai ba

"Ummi gaskiyya yakamata kubarwa Hajiya gidan nan ko ki bani Rubina na tafi da ita har zuwa sanda Baffa zai dawo ni bana son wannan masifar ta Hajiya Umma gaba ɗaya taki bari gida ya zauna lafiya haba"

"Ba inda zata kamar yanda nima ba inda zani ni sonake ma yadawo ya sawwake min na koma maiduguri cikin ƴan uwana na zauna nida Rubina daman nice dolanta ai"

"Subhanallah Ummi daina faɗar haka dan Allah komai zai daidaita ni kawai sonai ace tuntuni Baffa ya fahimta sanda akaita ɗauki ba daɗin nan naso ya sake maki wani gidan da yayi hakan tun can lokacin da yanzu ba wannan maganar ake ba ai"

Dakyar Mahmud yasamu Hajiya ta fita daga part ɗin Ummi har bayan insha yana gidan saida ya tabbatar da Hajiyar tayi laushi sannan yabar gidan bayan yaje ya kara bawa Ummi baki da rokon tayi hakuri karta kula Hajiya komai zatayi sanda ya koma gida ya tarar matarsa Sadiya ta cika tai fam azatonta wani wajan yaje yaki shigowa gida kamar yanda ya saba, ya kalleta yana murmushi sanda ya zauna cikin falon nasa yakai ganinsa ga yaransa da suka zubawa Tv idanu, Samiha babbar ɗiyarsa ta karaso inda yake tana dariya

"Daddy barka da dawowa yaufa munyi fushi tuni har munyi dinner Momy tace kaje zance" Daddy yai dariya yana kallon matar tasa ya ce

"Ke mamana manta da rigimar momynku ina can gidan Hajiya yau gidan gaba ɗaya ya runcaɓe sai rigima suke kamar wasu kananun yara da kyar na samu na yayyafawa wutar ruwa na baro gidan nikam mai zanyi da mata da yawa fitinarsu ma aitasa wannan ƴar kibar tawa ta zaizaye" ran Sadiya yai fari tai dariyar dabata shirya yiba Samiha ta koma wajan kannanta suka cigaba da kallo

"To muje danning ga dinner ɗinka can a warmars"

"Gadai sauran abincinka can zaki ce" sukai dariya lokaci ɗaya kafin suka jera zuwa danning ɗin

Uwaimir karfe takwas na safe ya sauka tashar motar unguwa uku, gaba ɗaya yayi wani zuru zuru kamar mara lafiya adaidaita ya tsare zuwa unguwarsu lokacin da adaidaitar ta shigo layin ba karamin sanyi jikinsa yai ba shi gaba ɗaya yagama amanna Rubina ta mutu sanar masa ne kawai ba'ayi ba, ko kirga kuɗin daya bawa mai nape bai tsaya yayi ba kai tsaye ya faɗa gida zagayawa yayi ta can baya inda Hajiya bazata gansa ba ya faɗa part ɗin Ummi, Ummi na zaune a dannin room ta gama haɗawa Rubina abinci ta bata tana ci ta ajje mata ruwa da magunguna a kusa da ita tabar Khalipha yana kula da Rubinar, tsai yayi bakin kofar shigowa falon yana bin Rubina da kallon mamaki ganin tana lalube da hannunta kan danning ɗin

"Khalipha kai Khalipha ka miko min maganina nasha ba Ummi tace inna gama ka taimakan ba" jiki sanyaye ya karaso cikin room ɗin ya zauna kujerar dake kallon wacce Rubina ke zaune ya kafeta da idanu

"Khalipha Yay Uwair ne yazo wajan nan kamshinsa nake ji?" jikin Uwair ne ya ɗauki wani irin mazari jin abinda zuciyarsa ke faɗa masa

"Rubina kalle ni ki kalle ni sosai gani zaune a gabanki bakya gani na?" Rubina ta miko hannu tana laluban inda yake yai saurin kai hannunsa kan nata

"Yayanmu a sakamakon dukan dasu Hajiya sukai mata jiya ta daina gani fa" wani dummm Uwaimir yaji a kunnuwansa sakamakon maganar zuciyarsa ta tsaya cak na ɗan mintina tunaninsa suke neman gushewa yafara zaton kodai mafarki yake

"Khalipha sake faɗi dan Allah ka karyata min kace karya kake Rubinan mai Rubinan tai masu da zasuyi mata wannan illar, Rubina Rubina" kansa yadafe yama kasa cewa komai

"Uwaimir yaushe kazo?" yaji muryar Ummi ta na tambayarsa, ɗago da kansa yayi yana bin Ummi da ido yakasa cewa komai, hayaniya da hargowar Hajiya Umma yasa suka ɗago kansu suna kallon juna

"Ina kake munafuki waton ta kiraka ta guntsa maka karya da gaskiyya shine har kazo gidan ka kasa shigowa wajena kai tsaye ka tawo wajanta gata uwarka ko gata uwar data kawo ka duniya to zo ka wuce muje in kuma ita ta haifa min kai sai naji yau" Uwair bai motsa daga inda yake ba hakan yabawa Hajiya Umma damar karasowa inda suke, Ummi ta ɗaga ɗaya daga cikin kujerer danning ta bugawa Hajiya Umma a fuska nan take goshinta ya fashe yafara zubar da jini da sauri Uwair ya mike yasa hannu ya dafewa Hajiyar wajan raunin da hannunsa yana kokarin janta subar wajan taja ta tsaya tana aikawa da Ummi wani kallo

"Ni kikayiwa Rauni Fatima"

"Na maki naji maki raunin idan har baki fasa shigo min pary ba wataran saina ji maki mummunan ciwon dayafi wannan" Uwair yaja hannun Umma suka fita daga part ɗin tana aikawa da Ummi zagi itama bata kyale ba har bakin gate ta biyo su tana rama duk abinda Umman ke gaya mata, sanda ta dawo ɗakin ta tarar Rubina na kuka sosai

"Ummi mai yasa mai yasa duk gidan nan ba wanda Hajiya Umma ta tsana sai ni maina mata Ummi zuciyata ta fara ayyana min maganganun Hajiya Umma gaskiyya ne niba ƴar gidan nan bace ina iyayena suke" sak Ummi tayi tana bin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login