Showing 3001 words to 6000 words out of 42953 words
kai tsaye na wuce ɓangaran Baffa inda nake zaton zan same ta acan da asuba ta gaya min zai dawo Yah Aliyu ya tafi ɗakko sa, ina shiga Yaya Sulaiman na kokarin fitowa daga ɗakin ya wani gallamin harara yai gaba shima yana sanye cikin uniform irin nawa,
"Oyoyo Rubina Rubinan Baffanta" Baffa yafaɗa yana buɗe min hannayansa, na zube a kasa ina gaida Baffa cikin girmamawa tareda tambayarsa ya hanya
"Hanya Alhamdulillah Mamana tsarabanki na wajan Yayanku Amjad zai baki"
"Na gode Baffa Allah ya saka da alkhairi yakara arziki mai albarka"
"Ke Rubina da yallah ki fito mu tafi zaki makarar da mu da kika san baku gaisa da Baffan ba ki fito da wuri mana ko salon kija mana makara" yaya Sulaiman ya faɗi haka cikin tsawa ya juya ya fice Baffa na binsa da wani kallo
"Wai kuwa Alhaji Rubina kaɗai kayiwa tsaraba a gidan nan tun ɗazu yaranmu ke shigowa ba wanda kayiwa zancan tsaraba sai ita shafaffiya da mai" Hajiya Umma ta faɗa a hasale, kallon da Baffa yabita da shi ba tare da yace komai ba yasa tai saurin yin shuru ta kyauda fuska gefe
Ina fitowa yaya Sulaiman ya fara min masifa kamar zai kawo min duka nai shuru bance masa komai ba na shiga mota driver yaja muka soma tafiya ina jinsa yana ta mita shida su Rahama amma bance masa komai ba sai ma book ɗina danake dubawa ajinmu ɗaya da Sulaiman ss 3 sam nida shi babu wata jituwa inhar ba jin sunan mahaifinmu kayi ba bazaka taɓa gane nida shi wa da kanwa bane hakanan Sulaiman shida kanwarsa Rahama suka tsane ni bansan dalili ba ko a school bama wani shiri, dana gama duba book ɗina na ɗago na kalli Hisham yanda ya takure a kusa da ni yana jin tsoron yai wani kyakkyawan motsi Rahama ta dakesa dan sabon tane dukansa a kullum in mun ɗauki hanyar makaranta, na janyo sa jikina sosai Usham yaro ɗan shekara bakwai Rahama da Sulaiman keta hira har muka karasa school muka sauka a mota muka shiga cikin makaranta nida Khalipha muka raka Usham class ɗinsa pramary section sannan Khalipha ya shiga class js Three na wuce ajinmu ina zama malamin Math ya shigo muka fara karatu,
Yau juma'a komai cikin ɗoki nake ɗokin dawowar Yaya Uweer gida Yaya Uweer nida shi akwai shakuwa mai tsanani kusan duk gidan ba da wanda na shaku da shi kamar Yayanmu Uwaimeer duk da kasancewarsa ɗan Hajiya Umma amma ina matukar ji da shi cikin yayuna tun ina karama kusan shine komai nawa hakan ya haifar da alaka mai zafi tsakanina da shi mukanyi komai tare sanda yana jama'ar bayaro kullum muna tare shi yake kaini school daga nan ya wuce tasu ya karanci Medicine harya kammala karatu yafara aiki a asibitin malam rana ɗaya ya birkice Allah ya kashe sa soja yake son zama ba yanda Baffa da hajiyarsu batayi ba amma yaki dole Baffa ya kaisa makarantar horar da sojoji dake Abuja lokacin daya zama cikakken soja akai posting ɗinsa Kaduna da can yafara aiki daga baya kuma aka cillasa can kudu inda yanzu haka yana can calabar....✍🏿
Game bukatar cigaba da bin wannan novel zaiyi magana dani whatsapp kawai 07039793439
[7/11, 9:41 AM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹
Story and Writing by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW RASHIN MAHAIFANA
Episode two2️⃣
*Kirkirarran labari ne in wani ɓangare yai dai dai da wani ko wata ai hakuri arashi ne*
Uwaimeer karfe goma saura minti goma ya sauka a filin jirgin saman malam Aminu kano dake nan garin kano baiyi waya da wani cikin kannansa ba bare yace azo a ɗaukesa ya fito yana gyara zaman jakar dake saɓe a bayansa ya fito daga filin jirgin ya karaso bakin titi ya tsare nape ya hau bayan ya gaya masa inda zai kaisa,
Sandai mai nape ɗin ya tsaya dai dai kofar gidansu ya fito ya sallami mai nape ɗin ya tura kofa ya shiga yana sakin murmushi hakanan ya sami kansa cikin wani farin ciki baya kasa gane na maine, sai dai yaji zuciyarsa sam ba daɗi tunawa da yayi Rubina na school, kai tsaye part ɗin Hajiyarsu ya wuce yasan zuwa yanzu Baffah baya gida ya tafi masallaci tun tara na safe yake tafiya masallacin gidan sarki sai bayan anyi sallar juma'a yake dawowa, bai gayawa hajiya yau zai zo ba shi yasa sanda taga shigowarsa sam bata kawo shi bane zai shigo tadaiji murya anyi sallama kamar ta Uwaimeer amma saita bari a Yusuf ne shine mai murya ɗaya data Uwaimeer, har Uwaimeer yaiwa kansa mazauni a ɗaya daga cikin kujerun falon bataɗago ta kallesa ba hankalinta na kan wayarta
"Hajiya mun sameku lafiya"
"Lafiya kalau Yusuf yasu Amnah?" ɗan zaro idanu yayi yana murmushi
"Amnah kuma Hajiyata" da sauri ta ɗago daga danna wayar datake saura kiris wayar ta faɗi kasa ta zaro idanu tana kallon Uwaimeer dake sanye da black jeans da yellow shart
"Uwaimeer kaine da safiyar nan nifa na zata Yusuf ne"
"Gani kam bakon kano na maku shigar safe, so nake na sami sallar juma'a anan shi yasa na biyo jirgin safe"
"Jirgi kuma waya baka kuɗin jirgi Uwaimeer?"
"Daddy ne ya ce inzan tawo nadaina biyo mota na rinka gaya masa zai rinka samin kuɗin jirgi yafi sauki hanya ba kyau"
"Masha Allah ubangiji ya kara haɗa min kanku"
"Amin" Uwaimeer ya faɗa yana mikewa zai bar wajan nata ya wuce can karshan gidan inda nan ne samarin gidan ke rayuwa, tsit yaji alamar ba kowa kowa ya kama gabansa yasa key ya buɗe ɗakinsa bayan ya shiga babban falon dake ɗauke da ɗakunan nasu, ya shiga ɗakinsa da sallama ya wurga jakarsa kan karamin bed ɗinsa kafin yafara rage kayan jikinsa ya shiga wanka, sha ɗaya da rabi na safe ya fito daga ɗakin sanye cikin shaddar maganta colour kalar data matukar dacewa da fatarsa ta haska sa ya kafa hula zannah bukar ya fito yana ɗaura agogon hannu baya kallon gabansa kum yaji yai karo da mutum da sauri ya dafe goshinsa kafin ya ɗago ya kankance idanu zaiyi masifa saiya ga Amjad ne yai saurin rungumesa yana murmushi "Nai missing naka Amjad, mai kake a gida yanzu? ko dai Baffah bai fita masjid ba?"
"Ya fita fa yau lauyewa nai irin banda lafiya ɗin nan harga Allah inason hutu shi Baffa kullum yana tafe daga ya tashi fita kuma sai dai kaji yana kwala min kira Amjad kai Amjad kana ina fito mu tafi, shi yasa tun jiya muka haɗa plan da Mutuniyarka ta faɗawa Baffah bana jin daɗi, shine fa na samu yau ya fita da yaya Mahmud yanzu nasan yana masallaci yana zikiri" kwashewa Amjad da Uwaimeer sukai da dariya kafin Uwaimeer ya yi gaba ya faɗin "Bafa zaka tsare ni da abin dariyar nan naka ba kana nan yanda kake sauri nake yau so nake na ɗakko mutuniyar daga school na kashe bakin mita kullum korafin aikin nan nawa take wai yasa nai nisa ko school na daina kaita bare na ɗakko ta"
"Kunfi kusa ai" Amjad ya faɗa yana kokarin shigewa ɗakinsa, Uwaimeer yai dariya yana fitowa daga falon nasu
RUBINA
Da sauri sauri na haɗo books ɗina na saka su a jaka ganin an kaɗa kararrawar tashi tuni wasu ma sun fita daga class ɗin sai yan tsiraru irina waɗanda bamu gama kwafar home work ba daga allo na saɓa jakata na fito da sauri ina fitowa daga cikin aji kai tsaye na nufo bakin get ɗin makaranta, sai dai turus naja na tsaya ganin motar gidanmu tai kwana cak na tsaya wani takaici ya kume min zuciya, ba yau su Sulaiman suka fara tafiya suna barina ba amma na yau yamin zafi sosai sabida ban da ko naira goma a jakata gaba ɗaya na gama kashe kuɗina da muka fito break hawaye suka zubo min nasa hannu na goge ina tina irin uban tafiyar da zanci da kafata nai kamar na tare nape in gaya masa in munje gida zan karɓo masa na tare guda ɗaya ina gaya masa yai gaba abinsa baima tsaya ya gama jin abinda zance ba, na fara tafiya ina gabda barin layin makarantar naga mota tai parking gefena har tsorata nayi, na raɓa ta gefan kotar nai gaba aka kuma bina ana min horn na tsaya ina hararar motar ya sauke glass ɗin motar ya ɗan leko yana murmushi
"Yaya Meer" na faɗa da wani shauki na irin kai mamakin ganin abin da baka zata ba nai saurin buɗe motar na shiga jikina har rawa yake na rungume jakata ina kallonsa sai kuma kawai na fashe masa da kuka
"Kefa Rubie rigimarki yawa gareta maimakon ki murnar ganina saiki wani zo ki fashe min da kuka"
"To ai kukan na murnar ganinka ne nidai dana sani da banyi addu'ar samun nasararka ba dakayita saka ni a gaba kana min daɗin bakin na tayaka addu'a ka cinye jarabawa gashi nan yanzu an maida ka can nesa inda zamuna watanni bamuga juna ba, da lokacin kana kaduna ai duk weekend kake zuwa yaufa sati bakwai kenan ban ganka ba" ta karashe faɗa tana shashshekar kuka
"To ai naga ma wataran aure zakiyi ma gaba ɗaya kilama ki yi nesa da kano sannan ma saimu fi wata biyu bamuga juna ba"
"Ni bazanyi aura inda bazan rinka ganinka ba, ko kuma ka samo min wani abokinka na aura mu zauna gida ɗaya" Uwaimeer yai dariya "Har yanzu bakida hankali Rubie" yafaɗa yana tashin motar suka fara tafiya "Waima ko ki tambaye ni ya hanya"
"To ai sai munje gida" kai Uwaimeer ya gyaɗa yana murmushi yaci gaba da tukinsa, akan idanun Hajiya Umma Uwaimeer suka shigo gida shida Rubina haka nan taji bata son wannan alakar mai karfi da take tsakanin Uwaimeer da Rubina alakat da tuntuni ta kafa mata ayar tambaya saidai zancan auransa da Raihana ya goge mata duk wani zargi dake ranta amma duk da hakan bazatai sanya ba taje garin kallon ruwa kwaɗo yai mata kafa
"Assagafurullah" ta faɗa a fili jin zuciyarta na kawo mata wani tunani na daban, da sauri ta kirasa a waya lokacin yana kokarin shiga part ɗin su Rubina kiran Hajiyar ya shigo wayarsa, ya tsaya ya ɗaga kiran da sauri hanin Hajiyarsu ke kira "To" kawai yace banji abinda aka gaya masa a wayar ba ya kalleni tareda bani school bag ɗita dake hannunsa ya ce
"Hajiya na kirana bari naje na dawo"
"Tam maizan dafa maka"
"A'a kibari sai anjima in mundawo daga masallaci ki shirya muje tare" da murna ta shiga wajan Ummi dake ta yiwa Khalipha masifa danme zasu tawo su bar Rubina
"Ummi kiyi hakuri ai gani nazo ma, kuma na tabbata ba laifin khalipha bane"
"Allah Anty Rubina baba driver ma saida yayi magana yace baki fito ba shine Yaya Sulaiman yace mu tafi kawai da Baban ma yaki tada motar bakiga zagin dayai masa ba harda cewa saiya saka an koresa an kawo wani driver ɗin"
"Ke maiya zaunar dake a class ɗin har Sulaiman ya rigaki fitowa"
"Na tsaya kwafar homework ne Ummi kiyi hakuri" Ummi ta wuce bedroom ɗinta rai ɓace, ni kuma na shige ɗakina nafara cire Uniform ɗina na nufi loundry na wanke Uniform ɗina dana su Khalipha a washing machine sannan na shiga wanka, bayan na zagaya baya na shanya mana su
HAJIYA UMMA Bayan ta kira Uwaimeer a waya ta sakko daga benanta ta tsaya a a falonta na kasan tana jiran shigowar Uwaimeer ɗin
Rai ɓace ta kalli Uwaimeer daya shigo yanzu "Uwaimeer ban gane ba ban san inda kasa gaba ba akan yarinyar nan wai mai kake nufi ne nace mai kake nufi ne" da mamaki Uwaimeer ya kalli mahaifiyar tasa yana kokarin danne abin dake ransa ya basar yana faɗin
"Bana nufin komai Hajiya kin sani tun Rubina na yarinya nake kulawa da ita, kawai Allah ya sani biyayyarta a gareni yasa nake jinta ta daban a cikin kanne na,"
"Uwaimeer karnaji kar kuma na gani karka kuskura naji wata magana ba kalar wannan daka faɗa min yanzu ba"
"Hajiyata ba wata magana a yanzu ko a gaba bayan wacce na gaya maki yanzu ki rigada kin sani Rubie kanwata ce uba ɗaya kuma ba ita kaɗai ba komai naiwa Rubina ina yiwa Rahma kawai Rahama batada kunya ne shi yasa na sallamata, Rubina nada hankali sosai"
"Hmmm munafuncin banza matsa ka bani waje" yana fitowa daga part ɗin hajiya ya jingina da bango yana sauke numfashi ya ɗora hannunsa ɗaya a kirji ɗayan kuma ya soma goge hawayan daya fara zuba daga cikin idanunsa na tsananin tausayin Rubina da bakin cikin bazai iya cika burin zuciyarsa ba, xuciyarsa tai wani irin rauni raunin daya saka gaba ɗaya jikinsa yin sanyi kalau, jiki ba kwari ya wuce ɓangaransu ya buɗe dakinsa ya shiga ya cire rigarsa ya sakale ya faɗa gado, ya ɗauki wayarsa ya shiga callary ahankali yake bin hotunansa da Rubina da kallo yanayi yana goge hawayan da suka kasa daina zuba daga cikin idanunsa ya ɗakko diary ɗinsa yai rubutu ya maida inda ya ɗakko ya adana ya shiga bayi yai alwala sannan ya fito ya maida rigarsa ya feshe jikinsa da turare ya fito,
na gama shiryawa na saka babban hijab na shiga bedroom ɗin Ummi inda zan ɗakko dadduma, Ummi na gani zaune a gefan gado taja tagumi har batasan da shugowar tawa ba na zaune gefan gadon ta janye hanjunta daga tagumin da tayi ina binta da kallo
"Ummi maine?" na tambayeta
"Ba komai Rubina kaina ke ciwo" Ummi ta bani amsa tana kokarin mikewa ta shiga bayi na ce "Zamuje masallaci da Yaya Uwerr"
"Allah ya kiyaye sai kun dawo ku tafi tareda Usham Allah ya tsare" da to na amsa na fita daga ɗakin bayan na ɗauki dadduma na feshe ta da turare yana kokarin shigowa nima zan fito hannuna rikeda hannun Usham, fuskar Yaya Uweer nagani ba kalar ta ɗazu da muka rabu da shi ba, jikina nima naga yai sanyi kamar yanda nagansa a sanyaye sai da muka ɗau hanyar masjid naji Yayi shuru a motar baya cewa komai sai karatun suratul juma'a daya kunna a motar yana bi a hankali
"Yah Meer" na faɗa ina gyara zama na fuskance shi sosai shi kuma bai amsa kiran danai masa ba sai ɗagowa da yayi ya kalleni sau ɗaya ya maida ganinsa ga tuki nai rau rau kamar zanyi kuka na ce
"Wai Yah Meer maiya sameka bayan mun rabu?"
"Ya isa Rubina dan Allah ki kyale ni karki daɗa min damuwa da wannan ɗan karan surutun naki" baya na ɗanyi na jingina da seat sosai har sannan idanuna na kansa harya juyo muka haɗa idanu yaɗan saki fuska kaɗan ya ce "Yi hakuri kece zaki karamin damuwa raina a ɓace yake wallahi"
"Na sani na fahimci hakan shi yasa ma nai magana koma dai maine kayi hakuri kawai"
"Hmm Rubina bazaki gane ba na daɗe ina hakuri da abin dake damuna a zuciya saina hakurar da zuciyata sai kuma na kasa jurewa kimin addu'a dan Allah ubangiji ya warkar min mikin dake cikin zuciyata, bana zuciya tayi raunin da mikin nan zai fashe fashewarsa tamkar ɗakko dala ba gwammo nai tsakani na da hajiyata"
"To Yayana kaje hospital mana ai anayin hoton heart agani muje kawai hospital inmun dawo daga masjid saisu duba ka," Kai Uwaimeer ya girgiza yana dariya kafin ya ce "Yanzu idan nace bakida hankali sai kiji haushina ce maki akai ciwon da likita zai iya gani ne"
"Yayana wallahi fa ana hoton zuciya zasuga komai duka zasu ga mikin sai su ɗoraka akan magani" dariya sosai Uwaimir yayi harda kwarewa yana cigaba da tukinsa idan ya juyo ya kalle ni saiya kuma kwashewa da dariya zuciyata ta cika fam da bakin ciki na takure waje ɗaya har muka karasa masjid ɗin ban sake kula saba
UMMI
Bayan fitar Rubina daga ɗakin binta kawai tayi da kallo na tsananin tausayin yarinyar harta gujewa ganinta idanun Ummi nakan Rubina fashewa Ummi tayi da kuka sosai ta ɗaga hannu sama tana addu'a cikin kuka ganin lokacin sallah yayi tana nan zaune yasa ta mike tai alwala ta shimfiɗa dadduma ta kabbara sallah, tana nan zaune kan daddumar Aliyu da ɗansa suka shigo ɗakin Aliyu da ɗansa Fauzan suna sanye cikin shadda kala ɗaya hannun Fauzan na rikeda karamim carbi yana ganin Ummi ya karasa wajanta da gudu "Oyoyo mai sunan Baffah ina ka baro Ni'ima ka mata wayo ko ka biyo Abbah kunje masallaci"
"Ummi ina yini" Fauzan ya faɗa bayan ya tsugunna har kasa "Lafiya kalau masoyina ya momynku"
"Tana nan kalau tace na zauna anan zata zo da yamma inta dawo daga wajan saloon"
"To Allah ya kawota lafiya" Ummi ta faɗa tana maida ganinta ga Aliyu daya zauna kan sofa ya dafe kansa da hannu biyu "Kai fa kana lafiya kuwa naganka kamar wanda kwai yafashewa a ciki"
"Ummi tundai kan maganar da na maki jiya ne, zuciyata taki aminda da abinda kika gayamin dan Allah kimin alfarma Ummi dan Allah" yafaɗa yana sakkowa daga kan sofa ya tsugunna a gabanta ya haɗe hannuwa alamar roko Ummi ta ɓata fuska tambar bata taɓa dariya ba ta kankance idanu ta ce
"Aliyu matukar na kuma jin makamancin maganar nan ta jiya daga bakinka zan matukar saɓa maka kuma ta yaya zaka tono asirin dayake rufe taya zaka tone wannan sirrin"
"Ummi kusan kowa na gidan nan yasan da maganar nan yasan ta yanda aka sami yarinyar nan ɗai ɗaikun cikine basu sani ba yara kamar su Khalipha su Rahma amma inaga ko su Twince sun san wannan maganar,"
"To naji kowa ma ya sani amma wanne sharaɗi Baffa ya kafa akai maiya ce duka gaba ɗaya ƴaƴan kowacce a gidan nan ba wanda ya ɗaga maganar sai ta nan sai ta wajena haba Aliyu kamin adalci mana" Aliyu bai sake magana ba ya mike ya fice daga ɗakin Ummi tai tsai tanaji a zuciyarta inama inama inama ace abinda Aliyu yazo da shi zai tabbata da tabbas saita fi kowa farin ciki to amma Baffah fa da wacce fuska zai karɓi maganar Aliyun....
07039793439
[7/24, 4:18 PM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹
Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First