Showing 42001 words to 42953 words out of 42953 words

Chapter 15 - RASHIN MAHAIFANA COMPLATE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

143

na samu wannan damar yasa na kauda duka wata damuwar soyayyar Nuri nabawa karatuna mihimmanci na manta da duk wata soyayya ban bawa ko wanne namiji dama ya tunkare ni da zancan so ba naɗau zigar Yay Meer na zauna daram a kanta dayace karna sake na bawa wani dama yazo yace yana sona Baffah zai min aure batare dana cika burina na zama cikakkiyar likitar mata ba, lokacin da Yay Meer suka tafi America na wata uku da zasuyi na koma gidansa gaba ɗaya bisa umarnin Baffa, wasa wasa daga wata uku saida suka shafe shekara guda basu dawo ba sanda suka dawo naga Yayna Uwair ya zama kato abinka dama can ga kiba ga tsayi ya wani kara kyau ya zama babban mutum, karin girma aka masa tareda canjin wajan aiki ya koma Abuja gida kayatacce aka basa ba cikin barreck ba cikin manyan gidajan gwamnatin tarayya gida cikeda scurity tako ina sojoji birjik duk yanda yaso Raihana ta koma can kin yarda tayi wai ita bazata iya barin aikinta ba ta tafi wani waje daban da bata san kowa ba, yaci gaba da zamansa sai weekend yake zuwa shima ba ko yaushe ba, Uwair kuɗi sun zauna sosai yake jikani ta ko ina banda matsala a sirrince ya canza min motar hawa duk wata inada kaso cikin albashin sa nan da nan nima na canza na zama katuwa ta daman abinka da mai jikin girma cikin wannan shekaru na kammala karatuna na zama cikakkiyar likitar mata, ba karamin daɗi Uwair yaji ba sanda yaga na fito da first mukai murnar kammalawa na koma gida na zauna sai kuma Baffa ya sako ni gaba da maganar na fitar da mijin aure, iya tunani na banda kowa hakan yasa nabawa Bakon masoyi damar ya bayyana gare ni idan har da gaske sona yake zai aure ni

Hajiya Umma ba karamin haushi taji ba lokacin dataga na kammala school mai tsadar gaske haka jin datai Baffah na yawan maganar na fitar da mijin aure yasa ta kudurce a zuciyarta bazata taɓa bari Rubina tai aure ba hakan yasa tai shirin zuwa gidan Hajiya laurah suka tafi gidan bokanya, Yau ina gidan Yay meer tun sassafe muke ta shirye shiryan tarbar sa yai sati huɗu kenan bai zo kano ba yai nace muje masa Abuja nida Matarsa yai ya gama matarsa ta ce bazamu ba wajan la'asar yadawo yana sauka ni kuma na fara shirin tafiya gida yace na jira sa bayan mangariba zaije gidan sai mu tafi tare, na amince da haka suka shige ɗaki shida matarsa ni kuma na zauna nan falo, murmushi nayi ganin mini laptop ɗinsa ajje kan seater da alama manta ta yai dan baya sake da ita acewarsa sirrin sa ta aiki ce, ina karasawa kan seater ɗin na kula da jakarsa karama ta kakin soji kamar wacce akace na buɗe ta na buɗe wangale bakina nayi ganin Diary ɗinsa dana jima ina son ganinsa sau ba adadi na taɓa masa bincike a ɗakinsa na gidan amma ban gansa ba sai yau na koma gefe ina buɗewa ina bi ɗaya bayan ɗaya ina karanta rubutun dake ciki, jikina yaɗau karkarwa lokacin danai tozali da page ɗin danake son gani tun daga farko har tsakiya kalaman damuwa ne da nuna tsananin damuwar yanda zai iya sanar da wata cewar yana sonta da daɗa ɗan kalaman da suka saka jikina yin sanyi, sanda nai tozali da zanan hotona da aka zagaye da hert numfashu nane ya kusa ɗaukewa

_Kece farin cikina murmushina damuwata na rasa ta wacce hanya zan bi na bayyanawa Rubina irin ysanain son danake mata wanda na rayu da shi tsawon shekaru na rasa ta yaya zan bayyana maki cewar aure ya halarta a gare mu ina sonki Rubie ina kaunarki zanci gaba da sonki har karshen numfashi na_ wani ihu na doka tareda yin zillo banyi aune ba sai gani ɗakin Uwair da yanzu suka fito daga wanka shida Matarsa yana sanye da karamin tuwel wata shaka dana kai masa na zaro idanuna

"Gaya min ka gaya min tayaya aure ya halarta a gare mu, gaya min ta inda yaya zai iya auran kanwarsa to idanma da auran a tsakanin mu bana sonka bantaɓa kaunarka ba" nakai hannu kan dressing miror naɗau car key na Anty Raiha na fito daga ɗakin da gudu,

"Ke Rubina Rubina zo kizo nace" nai saurin datso masu kofar na kullesu ta waje na shiga mota na tashe ta, yanayin yanda mai gadi ya ga na figi motar yasa ya buɗe min gate da hanzari, ni kaina bansan iya adadin tashin hankalin danake ciki ba Ikon Allah kaɗai ya kaini gida ko motar ban tsaya rufewa ba na faɗa gidan da gudu ina wani irin kukan da sai a yanzu ya zo min na faɗo ɗakin Ummi bako sallama tana tsaye gaban danning nai wani irin juyo da ita ina zare mata idanu kamar wata sa'a ta nace

"Ummi gaya min ki gaya min ni wacece nida Yay Meer waye ba ɗanku ba ki faɗa min gaskiyya Ummi" tafi mukaji daga bayanmu tareda kyalkyalewa da wata dariya

"Fatima yau ga ranar tonon silili yazo yau ga ranar nadama tazo ga ranar sakamako yau ga illar abinda na daɗe ina nuna maku ke da Baffah kuka ki ji yanzu sai ki san yanda zaki sanar da ita ta gurɓatacciyar hanyar da aka haifo ta" Hajiya Umma ta kuma kecewa da wata dariya tana nuna Ummi da hannunta da Ummin tai sak jikinta yai wani irin sanyi......


*Alhamdulillah anan na kawo karshan Littafin Rashin mahaifana Book One ga duk wanda ke son cigaban wannan labarin zai biya kuɗin karatu 300 kacal ta wanan asusun 9014569692 Rabi'atu Yusuf Idris monay point shaidar biya ta wannan lambar 07039793439

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login