Showing 12001 words to 15000 words out of 98220 words

Chapter 5 - YAR SARKI CE HAISA NOVEL

14 Oct 2025

107

magana kema tafaɗa tana qwafa
Da sikitin colai in cokalayen qafanki seyau kike zuwa gaidani!!
Amma ai ita uwar taki Amina inaji bakya sati bakije ba dan kawai kun renani, ta faɗa tana fyace hanci, base ga stohuwa da hawaye tana share wa da bakin zanintaba, Allah Sarki me babban suna, allah de yajiqanka yaron nan duk wanda yake da sa hanu a batanka Allah kwashe masa buhun albarka kuma Insha Allahu bazega Annabi ba,
Ni da kuma kuka ɓata aka barmun miji, da shine nasan kullum ma seyazo dubani.
Jikin Ameerah ne yayi sanyi jin an ambaci yayan nata dabatama sanshi ba.


Daddyn Little ne yazo ya jata yazaunar da ita yi haquri Amaryata ta kaina ki qyalesu duka zan saɓa masu!!
Harta buɗe baki zatayi masifa daga ganin yacce ta qanqance ido mene kuma seta fasa tana washe baki ( kukan munahinci kenan kakus kaman ba ita tayiba).
Yauwa dade kaima zanmaka. Zan kwashe maka sauran albarka, amma nafasa,kasan banso suji kanmu ai, murmushi yayi yauwa amaryata hakan ma ya mun Allah barmana ke yaja kwana.Tace sannunku dazuwa yan kirki, ke takwarata zo nan abunki duk wannan qanwar taki ce tasa nai maki tijara ayoyo takwarata tafaɗa tana washe haqora, turo baki Ameera tayi aranta kuwa faɗi take "se yanzu akasan ni takwarace" halan. Zauna wa sukayi, suka gaisa da hira da dariya, kaman ba ita ta gama masu bala'e yanzu ba, Hayra takowa masu abun sha da na mosta baki. Amaryace tace yauwa nikam ina kuka baro wancan mema kuke cemasa litar ne ko me?
Aikuwa fashewa sukayi da dariya dukansu harda Daddyn Little en, Kakus little fa ba litar ba karki ɓatamun sunan yarona nikam faɗin Ameera.
An ɓata en, nace an ɓata zoki dakeni yar jakar uba.
Ammade ke takwara bakiyo halina ba wallahi kwata kwata, ai mu ana kunyan ɗan fari, amma ke ido gaste gaste kike cemun wani ɗan ki yo dama wayace ba naki ba? Daɗin abun ma sanda na haifi ubanki kamun yahaifeki harkike wani cemun ɗan ki da idanu kaman carbin malam.
Tode ina yake? Ina kuka barosa gantalallun iyayen zamani!!
Daddyn little yace'' Amarya ta yana can gidan umma.
Tace au kuce taqwace maku yaro taga sunan ɗanta garesa ko ance mata muma bamu son ɗan natane oho mata se baqin hali, tana nuna tafi kowa damuwa, kullum aiki ɗaya kuka yaronta yaronta kwa ranste Allah ba son wannan yaro muke ba, kumafa muna sonsa Ni nafita sonsa ma har shi ubanku harunan ma nafisa son yaron tafaɗa tana share guntun qwallan ta, harfa naga yaron nan a idanuna walle duk yafiku kyau da alama harda hankali yafiku.
Ni kunganni nan kullum wainar ɗari nake saya nayi sadaka inyana raye allah bayyanasa inya mutu allah masa rahama yo to akwai qaunan dayafi haka? Nasan itakama bata taɓa yiba, sekuma ta fece hanci, Allah Sarki baiwar Allah abunfa dazafi, ɗanka yabata tun yana stumma, gaskiya tayi qoqari.
Ammade matar nan akwai haquri da sinkeken qaton kanta tafaɗa tana washe baki.
Daddyn little de sunkuyar da kai yayi dan dama yasan halin kakar tasu, gashi tazaga takuma yaba masa surka, dama haka halinta yake. Ita Ameera kuwa dariya take tayi tama rasa me zata ce
Tana jinjina stufa irin na Amarya itade bazata sauyaba kullum abunta gaba yake kaman abun ba sauqi, Yau tazageka tas gobe kuwa tayabeka kaman maroqiya.
Kallonta tayi nikam kakus ya isa haka bafa mushiga gidan baba qarami mun gaidashiba daga zuwa kin cikamu da mitanki, ba muje semu dawo muhuta.


Bude baki tayi au wai dan bashi yahaifekiba? dan ubanki Haruna nace dan ubanki Haruna shine bakije kin gaida Muhammadun da matan nasaba! Ah lallai kingirma.
Tom harara kike kowa se kisan zaman dazaki da takwarata bata girmama maki iyaye kingani de ko gaidasu bataje yi ba ah to
Tashuwa sukayi basuce komiba
Suka fice a sashen kakartasu, shiga daya daga cikin manyan part en sukayi, aikuwa sunyi sa'a Baban nasu qarami yana gida.
Sosai sukayi farincikin ganinsu shida matan nasa 2
Amma diayar kana ganinta kasan ba har zuciyaba farincikin.
Gaggaisawa sukayi, Baban nasu jiyake kaman yayi yaya dan farincikin ganin ɗiyar yayan sa da mijin nata, sannunku daxuwa yaran kirki Allah maku albarka sannunku da ziyara.
Haka suka gama gaggaisawa harda ɗan hira kaɗan suka sha ruwan da Mama hafsatu takawo masu, kamun suka miqe suka masu sallama, Baba qarami ne yace zaku koma sashen kishiyar taki ko Tom sannunku da gajiya aje ahuta ko yaran kirki mungode sosai, sallama suka masu suka fice a sashen nasu suka koma sashen kakar tasu amarya.
Bayan sun koma sashen. Abinci Hayra takawo masu sukaci, dasuka gama suka wuce ɗakin dayake mallakin su, a sashen kakartasu sukayi wanka, suka huta.
Dare yafara, suka zauna Dukansu a palourn kakartasu suna ɗan hira.
Wayan Ameerah Umma ta qira gaisawa sukayi. Tamusu ya hanya? haɗata da amarya sukayi. Karban wayan amarya tayi tana washe baki!!
Yar albarka irin arziqi wacce ta iya haihuwa alllah de yamaki albarka! Da Ameen Umma ta amsa suka gaisa, Amarya taace "niko yaushe mijina soja zedawo? Umma tace Insha Allahu yakusa dawowa mama. To Allah dawo dashi lafiya! yaro me hankali da kirki da ziyara ba kaman takwarataba. Da Ameen Umma ta amsa!
Wai nikam anya ba'a sanja maki ɗiyar kin nan a asibiti ba? gaba ɗaya bata ɗauko halina ba. Murmushi kawai umma tayi batace komiba(irin kunyan surukai). Amarya tace shikkenan ke baki iya hiraba tom nagode seda safe. Tafaɗa tana miqa wa Ameera wayan, amshi abun yahudawan nan. Dan inba qaton qarya na colai colai en arna masu fitsari a tsaye ba, mutum na wata duniya ina nan ina jin muryansa fa rannan ma naga harda ganin mutum ake a ciki. Dariya Ameera tasa bayan ta karɓi wayan suka gaisa da Little sannan sukayi sallama takashe wayan tana dariyan kakanta. Kakus tace "takwarata yar albarka nana maryamu wannan suna namu na manya ne fa takwara karki zama shagiri girbau en Maryam a to dan Ni ba ruwana.
Yi haquri takwarata ɗazu na maki faɗa. Ashe bani girma na da son da kike mun ne yasa kika fara shigowa nan bakije wajan baban kuba. Allah maku albarka koh!! Suka amsa duka da Ameen stohuwa me ran qarfe.
Haka sukata hira jefi jefi da abun dariyan kakar tasu har suka yi seda safe kowa yaje dan ya kwanta.
Ɗakin dayake nasu dama suka nufa. Kasance wanta takwaran Amaryan komi nata akwai sa a sashen kakus en tasu, tun kan tayi aure harda tayi aure aka sauya mata komi na ɗakin ita da mijinta.


🄽ace safiyar alkhairy






🄼🄰🅂🄰🅁🄰🅄🅃🄰🄽
🅀🅄🄱🄰🄸🅂🄷


Yau take labara. Wacce tayi dede da ranan da baqi suka fara isowa masarautan qubaish. Ko wanne ɗan sarki, an tanada masa dama masauqin sa shida tawagarsa.
Tun safe shigowa aka wuni baqin na isowa, wasu har se dare suka samu isowa. Gari ya cika, gari yayi baqi, 𝙢𝙖𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙩𝙖𝙣 𝙦𝙪𝙗𝙖𝙞𝙨𝙝 𝙠𝙚𝙣𝙖𝙣.
Ƴaƴan sarakuna 12 ne sukazo daga masarautu daban daban. Kowa yazo da muradin ya auri wannan kyakkyawan Gimbiyan sannan yaci wannan wasa da za'a yi. Gimbiya wacce ai kon kyawunta ba wanda yataɓa kallon fuskanta bayan iyayenta.
Abu mafi ɗaukan hankali da burgewa a tattare da ita, kalan kwayan idanunta. Domin daban suke.




Muje zuwa danjin ya zasu kaya?✍️



ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️



💋💋 امى بتولة💋


𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚


💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮
𝘼𝙣𝙙
𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl✍🔥

Follow me in my page's


# WhatsApp ➡️08146292652


# facebook ➡️unique uwar batoorlerh


# instagram ➡️hareeyh-lurv


# whattpad ➡️@ourmmanbatoolerh


# TikTok ➡️uwar batoorl




اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍




__________________________________________________________________




🅿️ 21&22




💋💋 امى بتولة💋
















Ko wanne ɗan sarki, ya sauqa a masauqin da aka ta nadar don shi da jama'ar sa. Sannan an wadata ko wannen su da duk abubuwan da zasu buqata, a matsayinsu na yaran sarakuna sannan kuma manya-manyan baqi " A MASARAUTAN QUBAISH.




🅁🄰🄽🄰🅁 🄶🅄🄳🄰🄽🄰🅁 🄳🄰 🄶🄰🅂🄰
"𝙧𝙖𝙣𝙖 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙦𝙖𝙧𝙮𝙖" faɗin malam ba'haushe wai "sai dai uwar ɗiya taji kunya".
FILIN TARO
Mutane ne a cike a wannan qatoton fili, ba ko masaka stinke. Sosai filin aka qawata shi dan wannan taron(gasa) ya cika fam da jama'a, mutane da dama sun hallari wannan taro.
A gefe guda kuwa na wannan fili, ko wanne ɗan sarki, da wajan zamansa shi da tawagar sa(hadimominsa).
Taro yayi taro. Ko wa ka gani fuskan sa ɗauke da fara'a!! ko wa ya qagu yaga abun da ze wakana a wannan fili. Sannan kuma wa zata zaɓa a cikin yaran sarakunan? wane ne jarumin da zai lashe gasan? Kowa kawai zuba na mujiyarsa yake, ya ga ta inda Gimbiyar tasu zata ɓullo.
Gefe guda kuwa a munbari mai girma Sarki Qaseem ne da fadawan sa,waziri, galadima,da dai sauran dogarae da kuma ƴan fada.
Manyan ƴan kasuwan cikin Masarautan dama wasu a wajen Masarauta, manyan masu kuɗi na Masarautan da wajen Masarauta, suma wajan zaman su a qa wace. Guri yayi guri, taro yayi taro(abun se wanda ya gani kawai).
hayaniyan da ke tashi a wajen ne ya ɗauke cak!! Abun da ya ɗau hankalina na juya dan ganin ko menene?? Wajen yayi tsit, ba kajin qaran komi sai sawun takalma gami da qirarin da dogarae da kuyangu ke yi!! Wanda hakan ze tabbatar maka Gimbiyar ce ke shigowa filin taron.

***
𝙏𝙖𝙠𝙖𝙬𝙖𝙧 𝙠𝙞 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖
𝙔𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞, 𝙟𝙞𝙠𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞!!
𝙎𝙖𝙡𝙚𝙡𝙚𝙣 𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖!
𝙈𝙖𝙘𝙚 𝙙𝙖𝙮𝙖 𝙩𝙖𝙢 𝙠𝙖𝙧 𝙢𝙖𝙯𝙖 𝙙𝙪𝙗𝙪,
𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙖, 𝙮𝙖𝙧 𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙞, 𝙟𝙞𝙠𝙖𝙧 𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙞.
𝙆𝙤 𝙣𝙖𝙢𝙞𝙟𝙞 𝙗𝙖𝙮𝙖 𝙩𝙪𝙣𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣 𝙠𝙞 𝙨𝙚 𝙮𝙖 𝙨𝙝𝙞𝙧𝙮𝙖.
𝙂𝙖𝙗𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣! 𝙗𝙖𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣! 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙖𝙣𝙞𝙮𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧𝙚𝙣 𝙝𝙖𝙦𝙤𝙧𝙖,,
𝙁𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙬𝙖𝙩𝙖 𝙨𝙝𝙖 𝙠𝙖𝙡𝙡𝙤
𝙆𝙞𝙣 𝙯𝙖𝙧𝙘𝙚 𝙕𝙞𝙣𝙖𝙧𝙚 𝙠𝙤 𝙈𝙪𝙧𝙟𝙖𝙣𝙞 𝙠𝙖𝙞 𝙝𝙖𝙧𝙙𝙖 𝙢𝙖 𝙡𝙪'𝙪 𝙡𝙪'𝙪 𝙙𝙖𝙣 𝙠𝙪𝙬𝙖 𝙨𝙖𝙞 𝙢𝙖𝙞 𝙩𝙨𝙖𝙣-𝙩𝙨𝙖𝙣 𝙧𝙖𝙗𝙤 𝙙𝙖 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙢𝙩𝙖 𝙣𝙚 𝙯𝙚 𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙠𝙞, 𝙩𝙖𝙠𝙖𝙬𝙖𝙣𝙠𝙞 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙔𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞 𝙠𝙪𝙢𝙖, 𝙎𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙢𝙪 𝙩𝙖 𝙜𝙤𝙗𝙚 𝙄𝙣𝙨𝙝𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝𝙪, 𝙢𝙖𝙩𝙖𝙧 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞, 𝙮𝙖𝙧 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞, 𝙟𝙞𝙠𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙢𝙖𝙢𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞.
𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼 𝙈𝙀𝙃𝙒𝙄𝙎𝙃 𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙣 𝙢𝙪 𝙩𝙖 𝙜𝙤𝙗𝙚 𝙙𝙖 𝙖𝙢𝙞𝙣𝙘𝙚𝙬𝙖𝙣 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝.
𝙃𝙖𝙮𝙮𝙖 𝙠𝙖𝙞 𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙨𝙖𝙣 𝙠𝙖𝙞 𝙗𝙖 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙢𝙞𝙣 𝙣𝙖𝙢𝙞𝙟𝙞 𝙗𝙖 𝙣𝙚 𝙟𝙖𝙖 𝙠𝙖𝙪𝙘𝙚 𝙠𝙖 𝙗𝙖𝙬𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖 𝙛𝙞𝙡𝙞 𝙙𝙖𝙣 𝙢𝙖𝙜𝙖𝙣𝙖𝙣 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙢𝙩𝙖 𝙖𝙟𝙚.
𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙖, 𝙗𝙖𝙨𝙖𝙙𝙖𝙪𝙠𝙞𝙮𝙖, 𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙠𝙮𝙖𝙬𝙖𝙬𝙖𝙣 𝙙𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙖. 𝘼𝙣𝙮𝙞 𝙖𝙣𝙮𝙞 𝙖𝙣 𝙠𝙖𝙨𝙖 𝙠𝙞𝙣 𝙜𝙖𝙜𝙖𝙧𝙞 𝙪𝙗𝙖𝙣 𝙢𝙪𝙩𝙪𝙢 𝙗𝙖𝙡𝙡𝙚 𝙢𝙪𝙩𝙪𝙢 𝙙𝙖 𝙠𝙖𝙣𝙨𝙖, 𝙖𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙟𝙖 𝙠𝙬𝙖𝙣𝙖 𝙮𝙖 𝙗𝙖𝙠𝙞 𝙩𝙨𝙖𝙬𝙤𝙣 𝙧𝙖𝙞 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖, 𝙠𝙞 𝙩𝙖𝙠𝙖 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙮𝙖𝙧 𝙜𝙖𝙩𝙖 𝙮𝙖 𝙙𝙖𝙮𝙖 𝙩𝙞𝙡𝙤, 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 𝙝𝙖𝙬𝙖𝙮𝙚𝙣 𝙈𝘼𝙎𝘼𝙍𝘼𝙐𝙏𝘼𝙉 𝙌𝙐𝘽𝘼𝙄𝙎𝙃!!!
***

𝙌𝙞𝙧𝙖𝙧𝙞 𝙠𝙖𝙬𝙖𝙞 𝙩𝙖𝙠𝙚 𝙨𝙝𝙖 𝙩𝙪𝙣 𝙠𝙖𝙣 𝙩𝙖 ɓ𝙪𝙡𝙡𝙤 tsakiyan taron 𝙝𝙖𝙧 t𝙖 𝙞𝙨𝙤 𝙩𝙨𝙖𝙠𝙞𝙮𝙖𝙝𝙣 𝙩𝙖𝙧𝙤𝙣 jama'an.
Idanuwa ne duk suka koma kanta, kowa ka gani yana magana tom yabon kyau irin na halitta da Ubangiji SWT yayi mata ake.
Sanye take da kaya irin na jarumai mata masu zuwa yaqi, ko ina na a rufe yake baka ganin komi se qwayan idanuwan ta. Duk da kasancewan kayan yaqi ne ajikin ta kuma jikin a rufe hakan be hana bayyana kyau, jarumta, baiwa, sadaukan taka, da komi da Allah ya azurta ta dashi ba, ma bayyani.
Fara ce sol! Duk da baka ganin fatan jikin ta, Amma qwayan idanuwan ta kaɗai ka gani ze tabbatar maka da hakan, qwayan idanun da ke zautar da mai kallon su. Blue-Blue haka qwayan idon su ke, ga farin idon kuma fari tass!! ka ranste ba idon mutum ba, dan kallon su ma na ɗauke wa mutum ido.
Wu cewa tayi ta zauna wajan da aka qanwata, aka kuma masa kwalliya, dan zaman ta.
Tun shigowan ta filin taron ba iya jama'a ba har yaran sarakunan duk suka ruɗe, kowa ji yake kaman ya ɗauke ta ya gudu da ita.


Mai magana ne ya tashi, ya na jawabi da farko maraba yaiwa duk baqin da suka hallara da ma ɗauka cin jama'ar gari. Ya gaida kowa yacce ya kamata. Yama yaran Sarakunan barka da kuma addu'an nasara ga mai rabo. Sannan ya fara koro jawabi :-
"Kaman yacce aka sani ba wanda ya taɓa ganin fuskan GIMBIYA MEHWISH. To musabbabin taron nan gasa ne tsakanin yaran sarakuna masu nema da biɗar auren Gimbiya. Abu ɗaya ne duk wanda yake ganin ya shirya a yaran sarakunan tom ze iya fitowa su gwabxa. Duk wanda yayi nasaran cire abunda ke fuskanta tom shine de yaci gasa kuma Insha Allahu Shine wanda zai Aureta".
Yaran sarakunan ne suka fara mamaki!! Just simple abun fuskan ta, ta ɗauki kowa rago kenan? Kowannen su faɗi yake a ransa "zata sha mamaki".
Ku san dukkansu a tare suka tashi.
Magana mutumin ya qara yi. "Da alama de gwarazan mazaje ne suka zo neman auren Gimbiyar tamu kuma Sarauniyar gobe Insha Allahu.
" Yanxu dai za'a fara ne da na farko a jadawali, ɗan sarkin garin A𝙠𝙠𝙖𝙡. Daga jin sunan sa ya tashi ya fito, bayan ya kimtsa zan zaronsa sannan ya damqi takobin sa, cike da faɗi da tafiya cikin jarumta ya shige cikin fili da yake na buga gasan.
"Gimbiya ana buqatan ki a fili" faɗin mutumin da ke magana da abun sauti. tashuwa tayi cike da jarumta da haiba ta nufi cikin filin
"Ana mata kirari da kuma tafi".
Husur aka hura musu nan take suka fara gobzawan.
Gobzawa suke yi abun gwanin burgewa!
Tun yariman garin A𝙠𝙠𝙖𝙡 na ganin abun wasa har abu yafi qarfin sa, tun yakan iya kai hari har ya dawo kare kansa kawai yake yi. Ana hakan har Gimbiya ta kaisa qasa ko jikinta takobin sa bai taɓa ba.
Haka aka ta gobzawa tsakanin Gimbiya Mehwish da ƴaƴan Sarakunan har sai da ta gobza da yaran sarkuna huɗu (4) a ranan.
Sannan duk cikin waɗanda duka gwabza da su ba wanda ya ko taɓa jikin ta bare buɗe abun da ta rufe fuskan ta.
A haka gasan ranan ya tsaya sai zuwa gobe kuma. Mutanen masarautan se jin daɗi suke! da nishadi! da kuma qara jin jinawa jarumta irin na Gimbiyar tasu.
Sarki Qaseem kuwa ya kasa cewa komi, kuma ya rasa dalilin ƴar tasa na cewa buɗe fuskanta ne ya zamana ta zaɓe ka. Duk da ya saba da jin tace a buɗe fuskanta ta bada kaza-kaza.
Amma yau ya basa mamaki sai dai bakomi, ya nawa ƴaƴan Sarakunan fatan Sa'a ga mai rabo.
A haka taron yau ya watse sai kuma Allah ya kaimu zuwa gobe su cigaba. A ɓangaren Gimbiya kuwa ba don ta gaji ba, sai dai ganin lokaci na qurewa kuma ga salloli akawunansu( ibada).


Haka taro yawaste kowa ya kama hanyan komawa masauqin sa ƴaƴan Sarakunan, ƴan gari kowa ya koma gidan sa wasu kasuwan su. Gimbiya kuwa ta koma gida da kuyangu ta,ranta wasai!!
Ta sani in dai tayi haka ba mae samun daman kada ita.
( uwar ɗakina mehwish a rage fariya ba musan ikon allah ba).




^^^^ yarinyar da aka kawo wa maganin ta sha ta warke. Sai sam barka, da izinin Allahn da ya sauqe mana magani kamun ya sauqe cutan, duk zafin ciwo da jimawan sa gashi yarinyar ta warke! Masha Allah...


^^( Abun da wasu suka kasa fahimta, shi Allah be sauqe kowanne cuta a duniya ba sanda ya sauqe maganinta, ita ciwo kaffarane
Allah bawa marassa lafiyan mu gida da asibiti lafiya!
Masu lafiya Allah qara masu lafiya!
Wa ɗanda suka rigamu gidan gaskiya Allah masu rahama!
Allah ravamu da iyayenmu lafiya
Alfarman rasulullahi sallallahu alaihi wasallam.)^^


Abba ne zaune da Umma suna hira kasancewan A𝙢𝙟𝙖𝙙 baya nan. Yaje kawo masu magun gunan da Abbansa ke saida wa yake kuma amfani dashi
Abbane yace M𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢𝙖𝙩𝙤𝙪 𝙣𝙖 kin kuwa ga Abinda aka yi yau? Murmushi tayi ni kuwa nagani Abban jarumin Umma. Nifa ko a tarihi in ba de na manta bakam to ban taɓa gani ko jin labarin mace haka ba, in bade a mutanen da ba.
Anya ma macece? dariya Abba yasa wato de anya macece kike cewa. Ta ya za'a nemi mata aure tana ba mace ba tom? Maryama.
A haka dai suke ta hiran su, kasancewan duk suna wajen akayi gasan.




🄱🄰🅄🄲🄷🄸
^^^^ kwanan ta biyu a gidan kakar tasu, sosai take kewan mijinta!! Saka makon tun zuwan su washe gari ya koma saboda aiki.
Duk da halin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login