Showing 15001 words to 18000 words out of 98220 words

Chapter 6 - YAR SARKI CE HAISA NOVEL

14 Oct 2025

77

kakus en nata kuma takwaranta amma taji daɗin zuwan ta Bauchin, atleast wani yawa-yawan ciwon da cikin yake sa mata yaragu, da ta haɗu da dabarun stohuwa laulayin dama-dama.
Yayan hayra wanda yake ɗan baba qarami, sosai yake kula da ita shima, kasancewan su kusan age mate's sannan suna shiri sosai.
Zaune suke a palourn kakar tasu, hira suke yi. Ameera tace "yaya abdoul wai yaushe ne zakayi aure kam? Kaga fa har na haifa mana yaro sannan ga wani a ciki". Murmushi yayi!! Wato ko kunya na bakiji har ga wani a ciki lallai sister, But karki damu nima very soon zanyi auren nan de.
Dariya ta saka shikkenan Allah kawo tagari ya kuma nuna mana lokacin! ya kawo mana surkar mu lafiya. Ameen qanwa ta amma point of correctiom Auntyn ku de ba surka ba kam.
Dariya tasa tace "koma de mene ne ba case".
Sai ga muryan kakus da ke fitowa ɗaki ashe taji hiran nasu, yauwa wallahi ke dai takwara kya tambaya mun shi du besa fa, ga kyau kaman mazan qauye. Ɗan sikitin sinkin renin hankali gauro kawai qato dashi yaqi aure, Sadakar sa zan bada ko a qauye zan tura wata tayi maleji da shi, dan ya stofe a gida ba wacce zata Aure sa Qur'ani. Mai Ameera zata yi in ba dariya ba, dariya take yi har da riqe ciki!!!
Haɗa fuska abdoul ya yi "kin ga amarya ki dena ta kuramun, Ni nace da mace ɗaya zan zauna, ke kaɗai kin isheni auren zobe mukayi ba qari ba saki. Hararansa ta yi Qur'ani ni ka rufamun asiri ina zan kaika?
Dube ka fa!! Ni ban sonka ina zan kaika, ni mijina nake so kuma ya tafi ya barni, fece hanci tayi da ƴar qwallan ta!! Ni ma bin sa zan yi ɗan balarabe na ba irinka ba baqi duqu nini. Dariya suka kwashe dashi duka shi da Ameera, ai de ko gawayi nake tunda ya tafi ya barmun ke tom nine mijin ato kiyi biyayya na ɗaga qafa ki shige. Dan ubanka Muhammadu nace bazan ɗaga ba, da kasamu kyan mijina ai da mata se ka ture.
A haka de ta zauna suna hira tana sokiburutsun ta suna dariyan su, wanin ta taya su darawa.






🄺🄰🄳🅄🄽🄰
^^^^ Umma ce zaune a palour tana waya:-
"Gwaggon yara yaushe zaki leqo mu ne kam? gaba ɗaya kunyi wuyan gani, da ke da doters en nawa. Su kan ma rabon su da nan har naa mance shekaran
Umman su ke dai bari kawai ayyuka ne se a hankali gaba ɗaya.
𝙈𝘼𝙃𝙍𝙀𝙀𝙉 da 𝙈𝘼𝙃𝘼 kan ma sunfi kowa son suzo su ganku, issues ne se a hankali, Amma Insha Allahu ko ban zoba, zan sako su hanya su zo su gaida Amarya, kamun Amarya ta kunce mun notin kai. Murmushi Umma tayi!! kai Gwaggon yara, maman tamu?
Tace "ita dae ni ai ina tunanin haɗuwa na da stohuwar nan Umman yara ammade Insha allahu nima zan shigo ba da jimawa ba. Su ma yaran naki ba zai wuce nan da 1 week ba in sun samu hutu gobe, daga nan su wuce Adamawa wajan Hajiya Babba ma su gaida ta. Umma tace "shikkenan Gwaggon su Allahu ya kaimu, ta amsa da Ameen.
Sallama suka yi ta kashe wayan.
Ta qira matan baba qarami suka gaisa da su ma, ta qira su Amarya ma suka gaisa.
Ta a jiye wayan zata shiga wanka kenan sai ga qira ya shigo wayan nata dawo wa tayi taga A𝙪𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙗𝙚𝙚𝙗𝙮
Ɗauka tayi, sallaman ma da shagwaɓa aka yi! Murmushi tayi! haba de kaiko sojan Umma, Yanzu fa kai soja n bai kamata kana shagwaɓa ba. Qara narke wa yayi kaman yana gaban Umman ta sa! Umma ni dai na gaji. Au tom shikkenan daga QATAR en ka wuce JIDDAH. In yaso sai ka dawo tare da mahreen da maha, kaga kamun nan kai ma ka huta acan ɗin. Dan mun yi magana be jima ba da Gwaggon ku, wai za suzo mana hutu.
Turo baki yayi! wato Umma baki son ma gani na yanzu? wata nawa fa ban ganki ba.
Murmushi Umma tayi, ba kai kace ka gaji ba? Tura baki ya kuma yi ni umma gida zan dawo. Su zo da kansu in sun tashi zuwa kawai. Wan can fistararriyan wai me take da suna maha koh!
In naje zan iya karyata ba ruwana . Iyye sannu baban ta, nace sannu babanta,
Ashe Auta har ka girma, kai ma kasan an maka reni murmushi tayi shikkenan adawo lafiya. Turo baki yayi Umma nifa ba yaro ba yanzu. Kashe wayan Umma tayi tace "gwanda kai yaron nan".
Aranta kuwa daɗi take ji kaman ta ga gudan ɗan nata a gaban ta yanzu ta haɗiyesa dan farin ciki .







🄼🄰🅂🄰🅁🄰🅄🅃🄰🄽
🅀🅄🄱🄰🄸🅂🄷


^^Yau take rana ta biyu da za'a ɗaura daga inda aka tsaya jiya na gasan.
Yauma dai kaman jiyan ne sosai filin ya cika da dan dazon taron jama'a wanda kaman sunfi na jiyan ma yawa......






𝙔𝙖 𝙍𝙖𝙗𝙗𝙞 i𝙣𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙧𝙤𝙦𝙤 𝙖 𝙜𝙖𝙧𝙚𝙠𝙖, 𝙙𝙪𝙠 𝙖𝙗𝙪𝙣 𝙙𝙖 𝙮𝙖 𝙠𝙖𝙨𝙖𝙣𝙘𝙚 𝙢𝙪𝙣 𝙛𝙖𝙙𝙖 𝙗𝙖 𝙙𝙖𝙞 𝙙𝙖𝙞 𝙗𝙖 𝙮𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙢𝙖𝙣𝙖 𝙖𝙛𝙪𝙬𝙖 𝙠𝙖 𝙮𝙖𝙛𝙚 𝙢𝙖𝙣𝙖.
𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙨𝙖𝙣𝙮𝙖 𝙬𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙖𝙗𝙪 𝙙𝙖 𝙣𝙖𝙠𝙚 𝙖𝙡𝙗𝙖𝙧𝙠𝙖 𝙖𝙡𝙛𝙖𝙧𝙢𝙖𝙣 𝘼𝙣𝙣𝙖𝙗𝙞 𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙎𝙖𝙡𝙡𝙖𝙡𝙡𝙖𝙝𝙝 𝘼𝙡𝙖𝙞𝙝𝙞 𝙒𝙖𝙨𝙖𝙡𝙡𝙖𝙢🤲


𝙈𝙖𝙨𝙤𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙞 𝙙𝙖 𝙠𝙪..... 𝘼𝙙𝙙𝙪𝙖𝙧 𝙠𝙪 𝙖𝙠𝙤 𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙪𝙨𝙝𝙚 𝙖𝙗𝙪𝙣 𝙨𝙤 𝙣𝙚 𝙖 𝙜𝙖𝙧𝙚𝙣𝙞


𝙈𝙪𝙟𝙚 𝙯𝙪𝙬𝙖𝙖𝙖𝙖


Ba muma yi komai ba tukun yanzu labarin ya fara.




ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️



💋💋 امى بتولة💋


𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚


💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮


𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖


(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl✍🔥)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍



𝙒𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞 𝙦𝙞𝙧𝙦𝙞𝙧𝙖𝙧𝙧𝙚 𝙣𝙚, 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙖𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙜𝙖𝙧𝙚 𝙣𝙖𝙨𝙖 𝙖𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙖𝙗𝙪𝙣 𝙙𝙖𝙧𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙛𝙪𝙨𝙠𝙖𝙣 𝙖𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙖𝙗𝙪𝙣 𝙩𝙖𝙪𝙨𝙖𝙮𝙞, 𝙨𝙖𝙞 𝙙𝙖𝙞 𝙗𝙖𝙗𝙗𝙖𝙣 𝙖𝙗𝙪 𝙢𝙖𝙛𝙞 𝙧𝙞𝙣𝙟𝙖𝙮𝙚 𝙨𝙝𝙞𝙣𝙚 𝙛𝙖𝙙𝙖𝙠𝙖𝙧𝙬𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙠𝙚 𝙦𝙪𝙣𝙨𝙝𝙚 𝙖 𝙘𝙞𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙙𝙖𝙧𝙖𝙨𝙞 𝙣𝙖 𝙧𝙖𝙮𝙪𝙬𝙖.
𝙄𝙣𝙖 𝙛𝙖𝙩𝙖𝙣 𝙯𝙖𝙢𝙪 𝙦𝙖𝙧𝙪 𝙙𝙖 𝙙𝙖𝙧𝙪𝙨𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙠𝙚 𝙦𝙪𝙣𝙨𝙝𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙞𝙣𝙨𝙖. 𝙎𝙖nn𝙖𝙣 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖 𝙗𝙖𝙢𝙪 𝙙𝙖𝙢𝙖𝙣 𝙖𝙢𝙛𝙖𝙣𝙪𝙬𝙖 𝙙𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙖𝙞𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙖𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙢𝙪 𝙠𝙤𝙮𝙖 𝙖𝙘𝙞𝙠𝙞.
𝘼𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙠𝙚 𝙗𝙖 𝙙𝙖𝙞 𝙙𝙖𝙞 𝙗𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖𝙛𝙚𝙢𝙪 𝙖 𝙠𝙖𝙣𝙨𝙖.

𝙎𝙖𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙧 𝙬𝙖 𝙜𝙖𝙧𝙚𝙠𝙪 𝙢𝙖𝙨𝙤𝙮𝙖 𝙩𝙖𝙧𝙚 𝙙𝙖 𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙘𝙞𝙣 𝙢𝙚𝙢𝙗𝙚𝙧𝙨 𝙣𝙖 𝙇𝘼𝙁𝘼𝙕𝙄 GIDAN KARAMCI.

_____________________________________________________________




🅿️ 23&24




💋💋 امى بتولة💋


















^^^ jama'a ne a cike filin, dan sunfi jama'ar da suka hallara a gasan da akayi jiya yawa. Kamar yacce a kabi daki-daki jiyan da ya kasance ranar farko, haka yau inma komi daki-daki aka bisa har shigowan Gimbiya wannan qayataccen fili, ita da jama'ar ta da kuma masu mata kirari.........
Yariman da za'a fara da shi a yau da ya kasance rana ta biyu ne ya fito. Ga Yarima ga Gimbiya a fili!! An gwabza an gwabza a tsakanin wannan Yarima da kuma Gimbiya, gwabzawar da ta ja hankulan kusan dukkan jama'ar wajan domin kuwa wannan haɗadden Yarima ya gwada jarumta sosai!!
In daa wannan Yarima ya yi nasaran taɓa jikin Gimbiya Mehwish da takobin sa, har ya zama jikin su ya hadu. Wanda a sakamakon wannan haɗuwan da jikin nasu yayi, da kuma idon sa da ya samu nasaran shiga cikin na Gimbiya, shi ya kasance nakasun sa(weakness) wanda ya temaka wajan qara kashe mai jiki!! Ba tare da wannan Yarima ya fargaba ko kuwa ankara, Gimbiya ta kaisa qasa..
Gaba ɗaya ranta a jagule yake don kuwa yayi matuqar ɓaci, wanda wannan ɓacin rai har ya bayyana a qwayan idanuwan nata,wanda duk da kasancewan su blue hakan be hanasu nuna ɓacin ran da take ciki ba, domin kuwa sun sauya daga blue zuwa dark-blue. Faɗi take a ranta, "shi waye da har ya samu daman taɓa jikina?".
Yarima Ammar. Wanda ya kasance na biyu a jerin na yau, shine ya fito fili. Bayan ya shigo fili, sukayi-sukayi suka gwabza shi da Gimbiya kaman ba gobe. Sun tayar da qura har ya cika wajan, kasancewar shima ɗin jarumi ne. Amma kasancewan ran Gimbiyar na ɓace tun haɗuwan jikin ta da na Yarima Fu'ad, hakan yasa bai samu daman taɓa ko jikinta ba, koda da takobin sa ne.. Har ta kusa yankan wannan ɗan sarkin sai dai Allah ya kare kasancewan shima en ba baya ba a wajan jarumta.
A haka a ranan sanda ta gwabza da yaran sarakuna biyar, a hakan dai yau ma taron nasu yawaste zuqata wasu cike da farin ciki wasu kuma saɓanin hakan.
Kowa ya koma masauqin sa bayan wastewan taro. Yayin da yaran sarakunan da suka faɗi ko wannen su ke cike da baqin ciki. Wasun su komawa kawai suke son yi. Gashi Sarki ya basu haquri kuma an riga da an faɗa masu sai an gama komi kowa zai koma.
Sauran yaran sarakunan da basu yi ba kuwa gaba ɗaya sun sare da irin jarumtar Gimbiyar barin da suka ga yacce tayi faɗan yau ɗin. Cewa suke "anya wannan macece kuwa? Qarfi haka da jarumta ace maza tara yanzu duk ta kada su."
A haka suka kwana kusan dukkan su da suka rage basu gwabza gasan ba, tunani ɗaya suke kuma da tunanin yacce zasu kaya a goben suka kwana dashi a rayukan su.
^^ Daga qarshe taya zasu yi wanin su a cikin su da suka rage yaci?^^
In da suka yanke shawaran.....
( nima dai uwar batoorl ban jiba ni daku mu haqura gobe afilin daaga muji.. )


^^^^A ɓangaren ita Gimbiya Mehwish. Har ta koma gida ranta a matuqar bace yake, sakamakon daman taɓa mata jiki da Yarima Fu'ad ya samu. Ta so ace faɗan ba na gasa bane da tabbas in bai mutu ba se ya rasa hannayen sa dan seta cire masa su.
Amma duk da haka ranta wasa! "ba wanda ya isa ya haye wannan gasan da na sanya ko ba su ba na sani" faɗin Gimbiyar.
( Ni ko uwar batoorl nace za dai ki sani amma baki sani ba kam dan nice nan oum batoolerh nasani, ni keda wuqa da nama)
^^^ Wasta ruwa ta yi. ta gabatar da sallahn ta, shiryawa tayi cikin dogon riga maroon tai rolling da milk veil har ta rufe fuskan ta kaman ko yaushe idanuwan ta ne kawai a waje, haka kawai ta ji ta sanya alkyabba. Black alkyabba ta ɗauko a closet ɗin ta, turawa tayi tai hanyan wajen ɗakin nata dan zuwa sashen da mahaifiyarta take, ta dubo ta. Tana fitowa kuyangun ta suka durqusa suna mata sannu, hanu ta ɗaga masu. Ganin tana tafiya ya sanya sauran ta shuwa suna ɗaga mata bayan alkyabban nata! Direct hanyan sashen Sarauniya suka yi dan sun san bata wuce wajan ko kuwa garden(lambu).
Suna zuwa dai dai qofan part en Sarauniya suka ja suka staya. "𝙏𝙖𝙠𝙖𝙬𝙖𝙣 𝙠𝙞 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙐𝙬𝙖𝙧 𝙜𝙞𝙟𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙢𝙪, 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙖𝙣𝙞𝙮𝙖, 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖𝙧𝙚 𝙜𝙖𝙗𝙖𝙣𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣𝙠𝙞 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙗𝙖'𝙖𝙙𝙖𝙡𝙞𝙮𝙖, 𝙖𝙨𝙝𝙞𝙜𝙖 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙖 𝙛𝙞𝙩𝙤 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖, 𝙮𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙎𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖,𝙜𝙖𝙗𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙗𝙖𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙯𝙪𝙘𝙞𝙮𝙖, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙝𝙖𝙡𝙞, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙣𝙪𝙛𝙞, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙢𝙪'𝙖𝙢𝙖𝙡𝙖, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙖𝙙𝙖𝙡𝙘𝙞, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙣𝙢𝙩𝙖, 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖, 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙝𝙖 𝙠𝙖𝙡𝙡𝙤," qirarin da amintattun bayin da ke gadin part en suke ma Gimbiya tun kan isowanta. Ɗaga masu hanu tayi, shigewa tayi bayan sun buɗe mata qaton qofan da kaman ba'a cikin gida yake ba. Tana shigewa suka rufe qofan yayin da kuyangun kuwa suka juya, dan ba'a basu daman tsayawa a qofan ba.
Da sallama Gimbiya ta shiga ɗakin da mahaifiyar nata take ciki, "Assalamu'alaikum" jin shiru ba'a amsa ba yasa yanayin ta ya sauya dan sanin da tawa Ammaahn ta ma'abociyar amsa sallama ce in dai bakin ta nada daman furta kalma. Qara sawa bakin gadon da Ammaah ɗin ta ke kwance tayi, a yacce ta ga yanayin jikin mahaifiyar nata, shi ya qara sa mata damuwa, dan ta so bata labarin abinda ya faru tunda bata samu zuwa ba. Zauna wa tayi a gefen Ammaahn nata, tana mata addu'aoe tana tofa mata har bacci ya ɗauke ta..

Bayan juya wan kuyangun, suna isa shashin Gimbiya ɗayar su ce tace laure kinga kyawun da Gimbiya tayi kuwa da ta sanya Alkyabba? Ni ko na gani hinde ai wallahi da Gimbiya ta san kyawun da Alkyabba ke mata da da dena yawo babu shi. Tabarakhalla Masha Allah, billahillzi laure in nayi aure na haihu sai na wa Gimbiya ta kwara ko zata samu ko da kaɗan a kyawun Gimbiya ne kuma Allah yasa kan lokacin an samu wanda ya buɗe mata fuska dan ko kallo ɗaya na masa da ido na zan kafta hoto na ajiye a zuciyata in nayi ciki nata tariyowa ina kallo. Dariya laure ta saka amma hinde ke dai Allah yaye maki da surutu kinga ma ba na tashi nayi aiki na kan ace gulman Gimbiya muke kin san jakadiya yan zu ta shigo ta sa mana ido. Carab tana rufe baki wata kuyanga ta shigo( wacce farkon labarinmu ta bamu labarin Gimbiya a taqaice) kayan jikinta ba irin nasu bane, "laure wai kukam me yake damun ku ne? Meyasa kuka maida gustiri stome aikin yin ku ne?" faɗin wacce ta shigon. Wacce aka qira da lauren mae zuba ɗazun tashuwa tayi tana jakadiya a yafe mu amma dama aiki zamu tashi yi yanzun. Juya wa kuyangar da laure ta qira da jakadiya tayi ta nufi ɗakin Gimbiya. "Hmmn hinde Wallahi wannan yarinya dan tana ganin itace jakadiya tana wa mutane abinda ranta ke so". "A'a laure gyara batun ki, dan dai uwar ta bata lafiya, ta zauna a matsayin uwarta, kamun ta warke take mana rawar kai. Ai uwar tata zata warke zamu koma dai dai maga qarshen rawan kan nata" faɗin hinde. Kema dai kya faɗa, ace wai da ita kaɗai aka yarda bayan uwarta, kin ga fa har sashen Sarauniya naga ranan ta fito abinda ko masu gadin ba shiga suke ba. Hinde tace "Ke dai qyale ta maga qarshen rawan kai".
Bayan wannan kuyangar ta shige ɗakin Gimbiya gyare-gyaren ɗakin tayi ta haɗa kayakin da za'a wanke ta share ta goge ko ina tass-tass har bathroom nata, ta kunna buner ta kunna wa ɗakin turaren wuta ta, ta fito da kayan wankin ta ja qofan ɗakin ta rufe.


^^^ Sai can Sarki ya shigo ɗakin, sallaman sa ne ya farkar da Gimbiya daga baccin da takeyi. Amsawa tayi tana "Barka da shigowa papa" amsa mata yayi yana mata sannu da gajiya. Murmusawa tayi "Papa ba wani gajiya fa". ai ɗiyata jaruma ce nasan ba lallai ta gaji ba dama. "Ya jikin Ammaahn taki"? "Papa ga Ammaah kam sai dai muce Alhmamdulillah" ta faɗa idon ta na kawo qwalla. Kallon ta mai martaba yayi yace "ba'a san jaruma da kuka ba Ebnateeyh, kiyiwa mahaifiyar ki addu'a shine sonki a gare ta ko bayan ranta balle da kuma ran ta, oya karki bari hawaye ya ɓaga stadadden fuskan ɗiyar kirkin mu ƴar albarka, ƴar Papa da Ammaah". Maida hawayen tayi ta murmusa kaɗan! Insha Allahu Papa zanke mata addu'a Allah tashi kafaɗunta ya yaye mata wannan ciwo. "Ameen ya Hayyum ya Qayyum, ko kefa ƴar albarka" faɗin mai martaba.
Bayan ya zauna gefen matar tasa. Kallon Gimbiya yayi yace "Ebnateeyh meyasa wai kika sanya wan nan buɗe abun fuskan naki a mazaunin zaɓan mijinki? Sannan ba tare da shawarin mu ba. Ko dai auren ne ba kyaso? Ba kya ganin ke kaɗai Allah ya bamu! Kina da labarin mace bata mulki kuwa? In ba kiyi auren ba ya zakiyi da mulkin? Ko dai ki kinaso mulkin a ɗaura wanine, bayan kinsan banda kowa nawa! Ni ni kaɗai haka na tsinci kai na kaman ke, ko na ce gwanda ke. Tun da ni ko mahaifiya ta baxan ce ga yacce take ba, banma san tana raye ko bata raye ba har. Ki ma kanki faɗa Mehwish, yin auren ki shi ne farin cikin mu ni da Ammaahn ki."
Kanta aqasa tana sauraron mahaifin nata, duk jikinta yayi sanyi da maganganun sa. Magana mai martaba ya qara mata "Ina jinki me yasa kika ce hakan ne a mazaunin zaɓan mijin aure ki?"
"Kayi haquri Papa" haka kawai tace kanta na a qasa har yanzu bata ɗago ba.
Can nisa tace "Papa ban sa gasan dan wani abu ba. farin cikin ku kai da Ammaah ta shine nawa. Na sanya gasan ne kawai dan na tabbatar، da jarumi zan aura, kuma tsayayye wanda ba wai nice zan tare masa komai ba, shima zai taremun a matsayin sa na wanda ke sama da ni. Wanda in ma ta kama ya mulki masarautan nan, nasan ba iya qarfin mulki ba har da cancanta na qarfin jiki da na zuciya yana dashi, wanda kuma zai yi adalci da qarfin sa ba zalunci ba, wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login