Showing 51001 words to 54000 words out of 98220 words

Chapter 18 - YAR SARKI CE HAISA NOVEL

14 Oct 2025

101

gaban sa na zuwa garin da yake da tabbacin a can zai samo abun da ya kawo sa, cikin hanzari yaja jakan nasa ya na mai neman taxi.
Taxi ya samu ya tare suka shirya zai kai sa tashan da zai hau motor zuwa Bauchi. Har sun fara tafiya da mai taxi sai motorn ya tsaya cak alaman ya samu matsala, Gashi kuma sun yi nisa da airport.
Mai taxi yace sai dai ya sauqa ya nemi wani abun hawan dan gaskiya in da zai je ya taho da makanike ba kusa ba kuma ba hanyan da zai kaisa tashan motoci bane, Haka badon yaso ba ya sauqa.
Tsayawa a bakin hanya yayi ko zai samu motor sai dai ganin ta gefen da yake ba alaman motor shiru kawai sai ya shirya tsallakawa ɗayan gefen ko zai samu ko lift ne.


Daddyn little ke driving da gudun gaske yanayi yana duba agogon dake maqale a hannun sa kasancewan yau juma'a sauri yake dan ya samu ya koma gida kan lokaci ya shirya ya tafi masallaci, yau ba'a tashesu aiki da wuri ba ya kusa makara.
yasa kai zai tsallaka titi riqe da jakan sa, Motorn Daddyn little ne ya danno kai a guje ba tare da ya kula da wanda ke qoqarin tsallaka hanya ba.
Kamun mai tsallake hanya yayi qoqarin yin gaba ko baya dan kaucewa Motorn ba zato ba tsammani ji kake qiiiiiiiiiiiiiii tibbbbb
Motorn ya ɗaga mutum sama ya fado qasa Daddyn little dake tuqin sai da kan da ya garu da stairyn.
LA ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM shine abunda Daddyn little ya furta bai ko damu da buguwan da kansa yayi ba ganin abunda yake kaucewa ya faru dafe kai yayi yace "Sauri ba wajan zuwa, ya ilahi".
Fita yayi a Motorn nasa ya tsayar da wani motor dake wucewa, mai Motorn da ya tsayar ya taimaka masa suka sanya mutumin daya buge a motorn sa.
Godiya ya masa ya ja Motorn ya juya kan Motorn nasa ya nufi asibiti.


Babban asibiti ne na masu kuɗi ya kaisa, kasancewan yana da aboki a asibitin ba tare da an buqaci zuwan police ba aka amshi patient nasa.
Abokin nasa ne ya kalle sa yacce ya damu yace "freind relax bákomi insha Allahu" ajiyan zuciya Daddyn little ya sauqe plss kuyi duk abun da ya kamata zan dawo yanzu frnd ba naje mosque na dawo, likitan yace "okay freind Allah qara starewa kayi tuqi a hankali, Da damuwa ya ja Motorn nasa ya kama hanyan gida yana mai addu'an Allah yasa bai kashe ɗan mutane ba.


Yana shigowa palourn nasu da sallama Ameera ce ga miqe da mamaki tace "Husby lafiya na ganka haka jikinka da jini mai ya faru?"
Dafe kai yayi wiffey tsautayine ya sameni yau, nan ya kwashe labarin abinda ya faru ya faɗa mata.
Rikicewa tayi harda hawayen ta! Allah sarki bawan Allah, Lallashinta yayi yace in ya dawo masallaci xasu asibitin tare.
Shiryawa yayi ya tafi Masallaci, Allah ya taimake sa ya samu jam'i bayan an idar anshafa addu'a liman ya fita kamo hanyan gida yayi gaba ɗaya a rikice yake bai taɓa hatsari ba a rayuwansa yana storon ya zama sanadin da wani zai rasa rayuwan sa.




Bayan fitan Daddyn little Ameera na zaune sai ga qiran Ummanta ya shigo wayan nata,. Ɗauka tayi suka gaisa Umma tace "Ameera ya naji muryanki haka ko ba lafiya ne? ko dai jikin naki ne?"
Kaman tana gaban Umman haka take girgiza kai
Umma tace "ya naji kinyi shiru? share hawaye tayi! Umma baniba ce Daddyn little ne yayi hatsari
"Hasbunallahu wa ni'eemal wakeel" shine abunda Umma ta furta, da ban qira ba ba zaki faɗa mana ba kenan? Garin yaya yayi hastari? Ya jikin nasa?" Umma ke jero mata tambayoyi.
Umma bafa shi da kansa ba ina nufin ya buge wani ne. Ajiyan zuciya Umma ta sauqe! Amma duk da haka jikinta yayi sanyi taji kaman wani nata aka buge addu'an Allah sauwaqa ya kare na gaba tayi masu tace "Insha Allah Abbanku zai shigo Abuja dama this week in yaso sai ya iso wajan ku ya duba mai jikin nikam bazan samu zuwa ba gobe su Auta zasu Bauchi Kar abar gida ba kowa" shikkenan Umma Allah ya kaimu Allah kai su lafiya suma Mun gode Allah qara girma. Sallama suka yi tana mata faɗa ta rage yawan sa damuwa da kuma tashin hankali a zuciyarta cikine qarami da ita karya zamo mata matsala yanzu ko nan gaba "tace Insha Allah Umma zan kiyaye a gaida su M𝙖𝙝𝙧𝙚𝙚𝙣. Bayan sun gama wayan aje sa tayi dan ta gabatar da sallah kuma ta shirya ganin lokaci yayi an sauqo juma'a.
dawowan sa masallaci yayi dai dai da ta futo wanka, taya ta qarisa shiryawa yayi dan su samu suje asibitin.






---
bayan Umma ta ajiye waya Auta ne ya shigo ɗakin bakin sa ɗauke da sallama.
Umma zamu masallaci ina big broh na?
au wai bai je wajanka ba? To jeka dubosa a waje yashirya tun ɗazu yace zashi ɗakinka ku tafi, Kallonta yayi har xeyi magana sai bece komai ba ya fita.
A jikin Motorn da zasu fita ya samu little na jiran sa yasha jamfa murmushi yayi yace "looking gorgeous my son"
Tacuu Unkui.
motor suka shige sai masallacin juma'a




__
Abba ke shiryawa dan zuwa masallaci ransa a ɓace ganin ko yaushe in zai fita tana taya sa shiri amma tun jiya tafiyan yaron ta daga ta zauna sai tagumi.
Kallonta yayi yace "maryama wai yau kam baza'a taya ni shiryawa ba kuma ansani a gaba da tagumi da hawaye mai yake damunki ne?
Ko duk kewan ɗan nakine tun ba'ayi nisa ba?
Ajiyan zuciya ta sauqe, ba kewansa ba Abban jarumin Umma Kawai Inaji a jikinane kaman wani abu ya samesa, numfasawa Abba yayi yace "A matsayinki na uwa kike masa fatan alkhairy kinji koh karki biye zuciya ko sheɗan addu'a kawai ya isar maki kinji maman amadu.
Lumshe ido Umma tayi tana ajiyan zuciya Insha Allah
Kallonta yayi ya girgiza kai dan tabbas yasan **labarin gizo bai wuce na qoqi**


Allah bai manta damu ba marayamatou nah tabbas haihuwa rahamane Amma rashin haihuwa babban rahama ne ( Allah najin kunyan wanda be bawa haihuwa ba kwata-kwata ranan gobe qiyama)
Share hawayen tayi, ta tashi muje na raka ka ta amsa hulansa tana sa masa.




Hijab Ameera ta sanya ko da tagama shiryawa, Daddyn little dake jiran fitowan ta, tana shiga Motorn yaja suka kama hanyan Asibiti...








WA KUKE TUNANIN DADDYN LITTLE YA BUGE?
ME MAGANAN DA ABBA YAI WA UMMAN AMJAD YAKE NUFI?
INA LABARIN AMJAD?
duk amsoshin wannan tambayoyi namu mai sauqi ne mu dai cigaba da bibiyan wannan labari mai suna
👇
ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️



💋💋 امى بتولة💋


𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚


💦💦💦💦💦💦💦💦


𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮


𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖


(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍


_______________________________________________________________






*Godiya mutanen amana tabbas sai daku Allah saka da alkhairyh*
MATAR RASHEED marubuciyar (BAQAR IZAYA) ALLAH saka da alkhairy nagode da gudumawan ki sosai sosai
* Am speechless dear ALLAH saka ya temakemu baqi daya*
*My heartbeat( UKHTY) nagode da qwarin guiwank da kuma addu'a yar uwa rabin jiki ALLAH de ya bamu sa'a duka Fatahn alkhairy a garemu Allah albarkaci karatunmu ya albarkaci result*
SIR (ABUBAKAR SADEEQ) CEO LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION
*ina matuqar Godiya da jinjina gareka ba gudumawan da kake bayarwa a garemu Allah saka da alheri Allah qara ɗaukaka*




🅿️ 39&40

💋💋 امى بتولة💋


Maganin da Abba ya tura masu sunji daɗin aiki dashi dan kuwa Ammaan ta na samun sauqi sosai sosai ba kaman kwanaki ba
Mai martaba yasa a fara shirin bikin Gimbiya wata 3 da ƴan kai ya rage, sannan ya fara tura gayyata wa sarakunan garuruwa daban daban.





-----
bayan soja sun dawo masallaci wajan Umma ya nufa
Zaune take akan darduma tana jan carbi, ganin Autan nata sai ta shafa addu'an ta ajiye carbin. Zaunawa yayi a qasan ɗakin ya naɗe qafa ya zuba mata ido bai ce komai ba
Umma tace "ya akayi habeebyn Umma fatan an dawo lafiya?"
Lafiya lau Alhamdulillahi Umma.
Naɗe darduman tayi ta cire himar duk yana zaune awajan bai tashi ba.
Kallonsa tayi da murmushi Autan Umma yau kuma nono zakasha ne?
Yace "uhmn Umma a'a na barwa wani Autan in kin haifa yasha"
Dariya kawai Umma ta sa haba dai Auta ai an rufe qofa kuma daga kai yanzu kam sai dai ku aifamun kai da Maha
Ɗaure fuska yayi yace "Umma ni kar ma ki fara wannan magana".
Zaunawa tayi a bakin gadon ta tana murmushi tace "zo ka faɗamun wa ya taɓamun kai to"
Mastowa yayi ya ɗaura kansa a cinyan Umman sa. Yace "Ummana me ya same ki? Ɗazu na ganki wani iri Mai ya faru?"
Lumshe ido tayi! har cikin ranta tana jin qaunar yaranta sosai take son Auta shiɗin kaman a tare zuciyarsu ke bugawa duk in abu ya dameta sai yaji a jikinsa kuma masa qarya bai da amfani, shafa kansa tayi bakomi Autan Umma, kawai Daddyn little ne yayi hastari ya buge wani bawan Allah shine sosai naji wani iri kaman wani nawa aka buge.
Ayya Umma tom ayi masa addu'a Allah ya basa lafiya amma kibar sa damuwa a ranki please!
Nan dai Umma ta sake ranta ganin ɗan nata ya damu shima suka cigaba da hiran su ta ɗa da uwa




^^^ 𝘔𝘦𝘩𝘸𝘪𝘴𝘩 𝘪𝘴 𝘢 𝙥𝙚𝙧𝙨𝙞𝙖𝙣 𝘯𝘢𝘮𝘦 𝘮𝘦𝘢𝘯𝘴
𝙢𝙤𝙤𝙣 &𝙗𝙚𝙖𝙪𝙩𝙞𝙛𝙪𝙡
𝙵𝚘𝚛 𝚝𝚑𝚘𝚜𝚎 𝚝𝚑𝚊𝚝 𝚊𝚜𝚔𝚎 𝚏𝚘𝚛 𝚒𝚝 𝚖𝚎𝚊𝚗𝚒𝚗𝚐
𝘐𝘴 𝘯𝘰𝘵 𝘪𝘴𝘭𝘢𝘮𝘪𝘤 𝘯𝘢𝘮𝘦 𝘣𝘶𝘵 𝘪𝘵𝘴 𝘢 𝘱𝘦𝘳𝘴𝘪𝘢𝘯 ( 𝘱𝘢𝘬𝘪𝘴𝘵𝘢𝘯)
𝘈𝘯𝘥 Islamically 𝘺𝘰𝘶 𝘤𝘢𝘯 𝘶𝘴𝘦 𝘵𝘩𝘦 𝘯𝘢𝘮𝘦 𝘪𝘧 𝘺𝘰𝘶 𝘸𝘪𝘴𝘩 so
𝘛𝘰 𝘯𝘢𝘮𝘦𝘥 𝘶𝘳 𝘣𝘢𝘣𝘺 girl ^^^








Suna isowa asibitin direct office na abokin sa suka wuce sai suka tarar bayanan wata nurse ce tayi directing nasu zuwa ɗakin da aka kwantar da mara lafiyan, Sun same sa anmasa dreesing na ciwon da yajin yana bacci.
Zama Ameerah tayi a kujeran dake gaban gadon ta zuba tagumi, suna zaune haka sai ga likitan ya shigo.
Musabaha suka yi yace masa "freind kasame ni office" ya gaisa da Ameera ya juya yabar ɗakin.
"Ba naje na dawo" ya cewa Ameera ya fice yabi bayan likitan Ita kuwa Ameera gaba ɗaya tayi nisa wajan tunani batama san fitan mijin nata ba.
Tura qofan office en yayi ya shiga da sallama ya samu kujera ya zauna.
likitan yace masa "freind ba wani mastala sosai bane kar ka ɗaga hankalin ka stautsayi ne Allah ya riga ya aiko sai fatan Allah kiyaye na gaba kawai, ya ɗan samu rauni a qafansa sai kuma kansa daya ɗan bugu
Buguwar Insha Allahu ba komi, amma bari ya farka mugani
Magungunan da ake buqata da komi za'a yi duk abinda ya dace sannan karka damu da yawan zuwa za'a kula dashi sosai. Nauyayyar Ajiyan zuciya ya sauke ya miqe ya bawa likitan hanu suka qara musabaha yace "freind i have no word ta thanks You Allah saka da Aljanna" murmushi likitan yayi yace "you're always welcome Angon mairo" Hararan sa Daddyn little yayi ya fice a office en.
zaune ya samu Ameerah a inda ya barta, Sallama yayi ta amsa tana tambayan sa fatan lafiya ba matsalan komi?
Yace "lafiya Insha Allah"
To Allah yasa yace "Ameen".
Har yamma suna asibitin amma bai farka ba, tattarawa suka yi suka baro asibiti bayan Daddyn little ya gama settling na komai ya biya.

Abba ne zaune da Umma da Maha da Mahreen
Abba yace "nikam gobe ne tafiyan yaran nan bauchi ko?
Mahreen tayi carab tace "eh Insha Allah Abbanmu zamuje muga tsofuwan da taqi mutuwa sai masifa (dan qwalonta Abba yayi🖐)
Gidanku doter kun renamun Uwa ko tom zan saɓa maku
Dariya Maha tayi qyalesu Abba sun renamun namesy basu san albarkacinta suke ciba
"Yauwa yar kirki faɗa masu dai" inji Abba yana murmushi. Allah ya kaimu goben lafiya nima zani Abuja wani aiki in Allah ya yarda
"Allah ya yarda Abba" suka haɗa baki wajan cewa, Tashuwa kowa yayi dan yaje ya kwanta ganin dare yayi.


Soja ne da little a ɗaki da alama wani aikin yake yi a system nasa ganin yacce gaba ɗaya hankalinsa ke kan system ɗin, little keta masa qiriniya da abun ya ishesa sai ya aje system ɗin a gefe ya miqe, ɗaukansa yayi yace "muje na kaika Umma"
Ɓata fuska little yayi a'a unkui aje ba cede akaini wajan aunci ma'a
Badon yaso ba haka ya ɗaukosa suka nufi ɗakin su Maha.

Yana qwanqwasa qofan, Maha ce ta tashi ta buɗe tana waye ne kuma?
Kallonshi tayi daga sama har qasa ta murguda baki
Little ya miqo mata hanu ancii ci auken, washe baki tayi ayoyo my boy.
Karɓansa tayi bata ce komi ba ta kulle qofan juyawa yayi yana auna irin renin da Maha ke shumfiɗa masa tabbas akwai ranan da zai seta mata qwaqwalwan kanta dai-dai gwargwado.




***Bawan Allah shine bai farka ba sai wajan qarfe 2 na dare, da salati a bakin sa ya buɗe ido.
Tashuwa yayi yana dafe kansa da yaji ya masa nauyi ga kuma matsanancin ciwo da yake masa kaman zai fashe
Nurse dake tare da shi qara masa alluran bacci tayi ganin yacce yake dafe kan baya ko son mostasa, a haka baccin ya qara ɗaukansa.






^^^ 𝙈𝙖𝙝𝙧𝙚𝙚𝙣 is an arabic name means, 𝙗𝙚𝙖𝙪𝙩𝙞𝙛𝙪𝙡, 𝙧𝙖𝙙𝙞𝙖𝙣𝙩, 𝙢𝙤𝙤𝙣-𝙡𝙞𝙠𝙚
Its an arabic name that means beautiful ^^^




**Gimbiya Mehwish ce zaune suna hira da Ammaan ta kasancewan jikin nata dama-dama tun da suka fara aiki da abun da Abba ya turo masu ta farfaɗo kuma takan iya zama da kanta tayi magana sannan ciwon baya tashuwa sosai sai dai ba qafa har yanzu.
Labari Gimbiya ke bata tana bata fura mai sanyi, Ammaa har da dariyan labarin da ƴar tata ke bata, Mai martaba ne ya shigo ya same su a haka da farinciki fal ransa har fuskan sa ya qaraso cikin ɗakin
Sarauniya Meera da fara'a tace "Marhababika ya zaujee" murmushi yayi wa laki ya imra'atee
Tashuwa Mehwish tayi ta masu sai da safe
Mai martaba ne ya tsayar da ita "Gimbiya yaron nan yayi tafiya naji ko? Eh papa
Tom shikkenan in yayi inaso kisamu lokaci ki kai saqon sa gidan su
Tace "Insha Allah papa zan kai
Tom Allah maki albarka mu kwana lafiya da "Ameen" ta amsa fuskanta ta rufe as usual takama hanyan nata ɓangaren.
Bayan fitan Gimbiya, Sarauniya ta kalli mai martaba tace "zaujeee nikam ya labarin Auran ibnateey?"
Mai martaba ya kwashe labarin duk abunda akayi ya faɗa mata.
Cike da farinciki tayi hamdala ga Ubangiji kasan me zaujee wallahi tun banyi ido biyu da wannan bawan Allahn ba naji yayimun a surki ya kwanta a raina tabbas ya cancanci zama mijin ƳAR SARKI.
azamanin nan da muke ciki abawa mutum kuɗi yace a'a gaskiya da kamar wuya



To ina dalili Kuɗi abunso
Masu gidan rana
Iya kuɗin ka iya shagalinka
Barikinka aljihunka>




Sai dai bansan mai yasa kake biyewa shirmen Gimbiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login