Showing 54001 words to 57000 words out of 98220 words
ba zaujee
Cuta da Magani na Allah ne mai yasa ka goyi bayanta ta tura bawan Allah wata duniya can?
Murmushin manya mai martaba yayi yace "Sarauniya Meerah amma dai a labarin da na baki na yaronnan a faɗa mai kaman wasa ya ɗauke abun fuskan ɗiyarki na gadon nan shi kike tunanin bazai iya ba? Zai iya imra'atee na yarda da jarumtan wannan yaro sannan ɗan baiwa ne, Aure kaman yacce nace nan da wata 3 inshà Allahu".
To Allah nuna mana Mai martaba Angon Meerah.
Murmushi yayi har ransa yanajin daɗin ganin yacce masoyiyar tasa ta samu lafiya
Hira suka cigaba da yi tsakaninsu na masoya.
^^^ Tabbas soyayya baya tsufa bai bar tsohoba bare yaro inda yarda da juna da kuma haquri da juna da kuma ganin mutuncin juna, soyayyah nanan har a mutu
Shiyasa kome zaka yi ka ginashi dan Allah kayisa dan Allah bare kuma Aure
Waɗanda a cikinmu suke da Aure Allah qara haɗa kawunanmu da zaman lafiya da soyayya da zuri'a ɗayyaba tsakaninmu da mazajenmu
Waɗanda basu da Allah ya kawo nagari alfarman Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ^^^
_____
washe gari da sassafe ko wajan aiki daddyn little bai je ba, bayan Ameera ta gama haɗa masu abin kari shiryawa suka yi suka ɗau hanyan asibiti.
Sun isa asibiti lafiya, shigansu ɗakin da majinyacin yake yayi dai-dai da farkawansa, ganin ya farka Ameera farinciki kaman tayi ya!
Buɗe idon sa yayi a hankali sai dai yanzu baijin ciwon kan sosai dan haka lumshe ido yayi ya maida kansa ya kwanta.
Doctor ne ya shigo ɗakin ya dudduba abunda zai duba yayi hamdalah ganin komi yazo masu da sauqi ciwon kan nasa baija masa loosing memory ba yacce suka zata.
Duk abinda ake yana jinsu amma bai buɗe ido ba, gaba ɗaya wani iri yake ji shi da yake so a sati 1 ya gama ya koma sai kuma ga qaddara ya samesa.
Likitan ya duba komi Alhmdlh sai dai matsalan ciwan qafansa da zai iya kai kwana 10 zuwa 8 kamun ya warke yaji daɗin tafiya sosai, yana gama masu bayani yace Allah "Allah qara sauqi ya kiyaye na gaba" sai ya fice a ɗakin dan zuwa duba sauran majinyatan.
Likita na fita kusan a tare suka masto wajan gadon da yake kwance, Daddyn little yace "bawan Allah kayi haquri katashi ka wasta ruwa ka samu kaci abinci kayi sallah".
Jin an ambaci sallah sai zuciyarsa ta tsinke da ya tuna tun jiya da safe rabon sa da yayi sallah, yunqurawa yayi zai tashi sai ya kasa sakamakon qafansa da ke da rauni.
Daddyn Little hannun sa ya miqo masa ya temaka masa ya tashi, har toilet ya rakasa kamun ya fita ya tsaya a waje dan ya jira sa.
brush da maclean da suka kawo masa yayi amfani dashi ya lallaɓa ya wanke jikin sa da dabara, ledan da ya ajiye masa a toilet ɗin ya jawo ya buɗe wani milk jallabiya ne mai hula da short a ciki, cirosu yayi ya saka.
{dogon namiji shine namiji kuma mijin aure gajeren namiji kan chager ne
Bafa ni naceba nima ji nayi ana cewa shine nima nace bari na ɗan ɗana loll}
bayan ya gama sawa alwala ya ɗauro ya futo a toilet en yana ɗingisawa da sauri Daddyn Little yace "bro bazaka qirani ba nazo na taimaka ma karka fama qafan ka" murmushi kawai yayi baice wa Daddyn little komai ba.
Ameerah ta shumfiɗa masa darduma, Daddyn Little yace "bawan Allah kaci abinci sai kayi sallahn ko"
Lumshe ido kawai yayi bece komi ba yanzu ma sannan bai mosta akan darduman ba, ganin yayi shiru sai Ameera gaba ɗaya ta rikice kar dai fa kurma ne ko baya magana Allah sarki sai idonta ya tara kwalla tayi saurin gogewa tace "yayana ko zaka yi sallan kamun ka karya?
Lumshe ido yayi ya jinjina kai alamun hakan ya masa, ba musu Daddyn Little ya masa nuni da alqibla Shi kuma ya tada kabbara a zaune ya fara sallan sa.
Bayan ya idar sosai ya jima yana addu'a kamun ya shafa ya zauna awajan shiru yana tuna Umman sa
tambayansa tayi yayana ruwan zafi da mai zaka ci? Tayi maganan tana kallon sa da tunanin wataqila kurma ne baya magana kawai tana jiran ya mata sing
Lumshe ido yayi kaman bai son yin maganan (asalim halin miskilancinsa ya mosta) da qyar ya buɗe bakin sa a hankali ya mosta bakin yace "ruwan zafi kawai".
mamakine ya cika Ameera har da mijin nata wai dama yana magana caɓ.
Haɗa masa komi tayi ta ajiye a gabansa, ruwan zafin kaɗan kawai yasha bai ko kalli sauran abubuwan ba bare asa ran zai kai baki da sunan ci, gaba ɗaya abincin Ummansa yake son ci.
magani ya amsa yasha sannan ya jingina da jikin gadon.
haɗa kwanukan tayi ta maida basket ɗin da suka zo dashi ta koma ta zauna itama, Daddyn Little ne ya tambaye sa ya jikin naka bawan Allah? Kai kawai ya kaɗa fuskan sa a sake
Maida Kallonta tayi kan mijin nata, husby ko zaka samu ka wuce wajan aikin ni ka barni anan in ka taso aikin sai ka biyo muje gida na haɗo masa abincin rana ba?
Ba tare da ya Musa mata ba yace "shikkenan wiffey zan wuce in Abba ma ya shigo yau ɗin zamu taho tare You should take care, bro Allah qara sauwaqa sai na dawo" ya faɗa yana ficewa a ɗakin.
Baibi ko takan abokin nasa ba ya kama hanya dan yaje ya shirya gudun kar ya makara.
Bayan ya fita Ameera tashuwa tayi da kanta ta gyara masa gadon bata jira ma'aikatan asibitin ba, da ta gana tace masa "kana buqatan wani abune yayana? Girgiza kai kawai yayi.
murmushi tayi ita dae har ga Allah tana jin tausayinsa sannan ji take kaman ɗan uwantane sannan tunda take bata taɓa ganin mutum mai kyau irin sa ba kaman ba ɗan Nigeria ba.
Suna zaune haka shiru sai ga qiran Umma, amsa qiran tayi suka gaisa take tambayan ta ya mai jiki? Mai jiki da sauqi sosai Umma gamunan ma muna asibiti. Umma tace "Daddyn little fa? Ta amsa mata shikam ya tafi wajan aiki Umma, ba nabawa mara lafiyan waya ku gaisa Umma.
Miqa masa tayi, yayana ga Ummanmu ku gaisa, amsan wayan yayi ya kara a kunnen sa.
Assalamu'alaikum yarona ya kake?
Jin muryanta ya sanya shi jin wani sanyi na mamaye ilahirin jikin sa bai san daliliba kuma kaman ancire masa ciwon kan, Yacce ta qirasa da yarona ba qaramin daɗi yayi masa ba yaji wani nistuwa a ransa! Qara lumshe ido yayi yace "lafiya qalau Umma"
daɗi taji har da ɗan murmushinta Allah qara sauqi yarona, Allah qara afuwa, Allah maku albarka ya kiyaye na gaba Insha Allah anjuma babanku zai zo ya duba ku.
Bai qara cewa komi ba, yace nagode ya miqawa Ameerah wayan
Amsa tayi tai waje suka cigaba da waya da Umma.......
Fatahn alkhaeryh gareku kowa da kowa cikin girgin dazai zo langeria ✈️😂
ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
ourmman batoolerh ceeee✍️
Taku har kullum........
💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
*Na sadaukar da wannan shafi gareka MIJINA abun alfaharina ABU BATOORL ina godiya da gudumawanka da kuma qwarin guiwanka gareni wajan ganin labarin nan ya tafi yacce ya kamata godiya ta musamman daga matarka hareeyh- Mrs big barbieyh*
🅿️ 41&42
💋💋 امى بتولة💋
Mahreen ce ta fito sanye da riga da siket na atamfa wanda ya amshi jikin ta sai mayafin ta dake riqe a hannun ta da handbag nata, can sai ga Maha ta fito da ɗan trolleyn da za suyi tafiyan dashi itama sanye take da dark-arsh abaya wanda ya amsheta sosai.
Duk suna tsaye a palourn ko akwatin ba'a fitar ba sakamakon Little da yasasu gaba yana kuka shi sai yabi auntyn sa, Umma tace "Angon granny zaka tafi ka barni ni ɗaya? yana kuka yana magana nide gilani anbi aunci na an jauna anan ba.
Dariya Maha ta sanya yanzu Umma abarsa mu tafi mana yace baya zama dake ana soyayyan dole ne
Yanzu ke doter sai ku tafi duka ku barni ni kaɗai ga Abban ku ma tafiyan zai yi, Ummata tom kiga fa yana kuka kishirya kawai muje tare kar abarki ke ɗaya.
Hararanta Umma tayi gidan kuma abarwa waye in na biku?
Lallaɓasa da dabara aka yi suka samu yayi shiru lokacin soja ya fito shima a shiryen sa sanye da jamfa.
Umma sai binsu da ido kawai take tana hamdala a zuciyan ta ganin yacce yaran nata suka sha kyau, in ta kalli soja ta kalli Maha sai tace Ameen ya Rabbi.
Abbane ya fito shima ya gama shiryawa dan wuce wa Abuja
Gaba ɗaya suka yi waje.
Nan umma jitai kaman ta bisu su tafi duka amma ba dama dan in ba dole ba bata so abar gida ba kowa sai masu gadi da mai aiki
Duk suka shiga Motor as usual Maha ta shige gaba abinta ta zauna ko a jikinta, Mahar kuwa dama ita ba gwanar fitina bace shigewa baya tayi tana fidda wayanta tana dannawa
Umma da Auta suka raka Abba wajan nasa motor suka masa Allah tsare hanya driver yaja motorn bayan Abba ya masu bye bye shima akan su kula da hanya sosai, Kuma Insha Allah zebi wajan su Ameerah ya dubo mara lafiyan. Airport Abba suka nufa tare da wani guard nasa da zae kaisa sai ya dawo da motorn.
Auta ya shiga mazaunin driver suka ɗagawa Umma hannu yaja motorn suka ɗauki hanyan bauchi da motor zasu sakamakon Maha tacewa Abba ita bata kumason hawan girgi sai dai soja yayi driving nasu.
( *Allahu akbar kaga manya ba yan gayu yayan masu kudi har ba'a son hawan girigi*
*Rabbi yassir Allah ka yassare mana muma*
Ya Rabbi nuqud
*Kodayake ance inkana adduah da larabci dasaurankako*
*Allah ka azurtamu bijahi rasulullahi sallallahu alaihi wasallam arzuqi na duniya da lahira*)
Soja dama driving ba matsalansa bane shiyasa bai tanka mata ba, Ita kuwa Mahreen ƴar ba ruwana ce komi ma oho.
Driving yake suna hira jefi jefi da Mahreen mutuniyarsa Maha kuwa tana kallon hanya ko qala batace a hiran nasu ba
Hamnu yasa dan ya ɗau wayansa itama cikin salon neman magana tasa hannu zata ɗauki wayan dan rashin kulata da faɗan da suka saba yi kawai yasa taji ba daɗi
Ba tare da ya kula ba sai kawai yaji hanunsa ya taɓa nata, wani shock da yaji ya sanya sa saurin jan burki, tsaki yaja kekam wace kalan mara hankali ce? Dama uban me zakiman da waya? Ko wayana sa'an ki ne? wai ma yaushe muka fara wasan taɓa waya dake?
Murguɗa masa baki tayi sai kuma ta juya tana murmushi ko ba komi taji abunda take so.
Masifa ya fara wallahi Maha ki fita idona inba haka ba wannan rashin hnkln da kikace na sojojin zan sauqe maki idiot kawai
Turo baki tayi tana qunquni "bismillah" shine abun da ta faɗa.
Mahar kuwa dariya tale qasa-qasa tana danna wayanta dama tasani akwai irin waɗannan comedies a wannan tafiyan nasu ga Tom ga Jerry.
Suna tafiya shiru fuskan soja a haɗe yayi qwafa ya kuma yi, can kuwa ta qara sa hannu ta ɗau wayan bai ma kula ba hankalin sa na kan hanya.
hira suka cigaba dayi shi da Mahreen tana basa labarin yacce take tunanin haɗuwanta da Amarya da masifan tan nan. Soja yace ai duk mai irin sunan amarya ba iya masifa ma harda hauka sai yayi.
Mahreen tace "yauwa nikam ya habeeby meyasa aka samata amaryane?
Murmushi yayi ai tun sunan Aurenta da stoho mae farin gemun can ake ce mata Amarya shine fa suna kam har yanzu har jikokin ta.
Dariya ta kwashe dashi haka suke hiran su tsakanin su na dariya su dara.
Maha da ta ɗau wayan cikin sa'a babu password da murna ta nufi gallery duk inda taga hoton mace bi take ta goge ita bata ma san me yasa take hakan ba.
Ameerah duk da majinyacin baison magana sosai hakan bai hanata masa surutu ba, amma yanayin yacce yarinyar ke qiransa yaya da kuma kulawanta garesa sai yaji ta kwanta masa arai har ya kan amsa mata in tayi magana duk da ba sosai ba ( sakamakon shi cikakken miskili ne, inde kaga surutunsa shida iyayensa )
Suna zaune can around 2pm tana zaune kan darduma ta bawa qofa baya, sallaman Daddyn little da kuma Abba da taji ne ya sanya ta juyowa da fara'a ta amsa masu sallaman tana masu sannu da shigowa. shi kuma idonsa a rufe tunda yayi sallah ya koma ya kwanta.
Da Abba da Daddyn little duka suka tambayeta ya mai jiki tace "Alhmdlh da sauqi"
Abba ne yace "uwata tun safe kinanan kema yaushe kika gama samun lafiyan jikinnaki da kin koma gida ai inaga zefi ko tunda ga nurses nan karki ɓallo wani ciwon, Sunkuyar da kai tayi a'a Abba ba komi wallahi nikam ai na jima da warkewa tun jigilen da mukeyinnan.
Murmushi yayi tom uwata Allah maku albarka duka ya kare nagaba shikuma Allah basa lafiya naga kaman yana bacci ma bari na koma na samu na kammala ayyukana inson samune nakoma gida yau, tace "to Allah yasa Allah ya taemaka Abbana"
Ya amsa da Ameen
Kudi ya ajiye masu ga wannan aqara na magani ko Allah sauwaqa.
Daddyn little ne yace Abba har da ɗawainiya haka tom mungode Allah ya qara girma.
Da Ameen ya amsa ya tashi kenan sai ga qira ya shigo wayansa
Ɗaukan qiran yayi ya nufi waje, daddyn little ya bisa dan rakasa
Ummace ta qirasa, Babansu an isa lafiya? ya mai jikin ya yaran?
Duk kowa lafiya mai jiki da sauqi na isa lafiya nima, da har nafito zan koma amma bana shiga ciki na haɗaku ku gaisa, au na tunama yana bacci.
hartaji daɗi zata ji muryan wannan yaron da yake sata farinciki kuma sau murna ya koma ciki! Tace "tom Allah dawo da kai lafiya nima ai zan yi qoqari nazo gaida su in ka dawo yallaɓoi.
Murmushi yayi na manyan kaman tana gabansa bai ce komiba sallama suka yi ya kashe wayan.
Daddyn little ya rakasa har gaban motor ensa da guard's nasa ke jiransa buɗe masa qofa sojojin suka yi ya shiga suka ja sai tafiya
San da motorn su ya fice a haraban asibitin kamunnan Daddyn Little ya juya, direct office na likita ya nufa sai yayi rashin Sa'a bayanan ya ɗan fita, juyawa yayi ya koma ɗakin da majinyacin shi yake.
Bayan fitansu Ameera kuwa tana zaune sai tana kallon gefen fuskan bawan Allahn nan take gani take in ba qarya idon ta ke mata ba yana yanayi da Abban su amma wannan Balarabe mai zai haɗashi da Abba? da yake shi yana da haske sosai Abba kuma hasken ba sosai ba. Dama ance kowanne mutum yana da masu kamansa 7 a duniya wannan yana cikin masu kama da Abba
Tana cikin tunanin nan sai Daddyn little ya shigo ɗakin, ɗago kai tayi ta kallesa tace "har Abban ya tafi kenan?" Eh wiffey Abba ya tafi kema ki taso muje gida ki huta kiyi wanka in yaso da dare sai mu leqo.
Marairaice fuska tayi ta buɗe baki zata yi magana