Showing 87001 words to 90000 words out of 98220 words

Chapter 30 - YAR SARKI CE HAISA NOVEL

14 Oct 2025

94

dai-dai lokacin kuma wayan sa ya faɗo masa rai dafe kai yayi ya ciro wayan a aljihun sa da gaggawa.
Cikin gidan liman kuwa Bayan fitan wannan budurwan a ɗakin baqin bakin ta yaqi rufuwa murmushin dake fuskan ta yaqi gushe wa, zuwa tayi ta tsugunna qofan ɗakin mahaifin nata baba nakai masa ruwan nace kana zuwa,Tom ecleemat Yar baba Allah maki albarka da Ameen ta amsa tana murmushi ta tashi tayi ɗakin maman ta shigewa tayi da sallama qanwarta tasamu tana naɗin kaya,amsawa tayi ta juya ta kalleta yaya ecleemah lafiya da murmushi haka tun shigowanki? Kedai bari kawai deejah baqon baba ne tunda na kallesa nake ta murmushin da bansan dalilin yinsa ba.
kai de yaya ecleemah kode-kode? murmushin ta kuma yi bakomi fa. Can suna zaune suka jiyo muryan baba liman yana faɗin ta fito ta kaiwa baqon abinci.
Da murmushi ta tashi da sauri dan har ranta tana son qara kallon sa ficewa tayi tana faɗin "to baba" madafi taje ta haɗa masa abincin akan tray tayi hanyan ɗakin baqin, sallama tayi a qofan ɗakin ta tsaya jiran izinin shiga
Wayan ya ciro ya duba ga message na layin Ameerah ta tura masa sannan ga wani baqon number Wanda yake kyautata zaton na Umma ce dialing yayi bai shiga ba network babu "ya Rabbi" ya furta yana furzar da iska a abakin sa.
sallama yaji a bakin qofan sai ya amsa yace "shigo mana qanwata" shigowa tayi fuskanta ɗauke da fara'a kaman ɗazun kanta aqasa har ta isa gaban sa ta ajiye tray en abincin tana tsugunne kallonta yayi ki zauna mana qanwata kar ki gaji da stugunnon kinji.
Murmushi tayi ta zauna akan ledan ɗakin kanta a qasa layin da Ameera ta tura masa ya qira har kaman baza'a ɗauka ba ya kusa ending can aka yi picking, sallama yayi aka amsa a ɗayan ɓangaren suka gaisa.
Wanda ya qiran ne yace "afuwan ban gane da wa nake magana ba? Numfasawa Amjad yayi yace "Ameerah ce ta turamun layin ka"
Okay am so sorry AMJAD right? Eh shine.
Qara gaisawa suka yi ya faɗa masa nasa sunan shima.
Abdoul yace "yanzu kana inane nazo dan nasan da daren nan ba samun abun hawan da zai kawo ka gida zaka yi ba, no karka damu da safe dai in Allah ya kaimu sai na maka kwatancen inda nake in yaso mu haɗu kamun na wuce.
Har zaka koma kenan? Eh zan koma gobe in Allah yaso ya yarda.
To shikkenan Allah kaimu goben, Ameen ya Rabbi ya faɗa suka yi sallama ya kashe wayan.
Kallon ta yayi har yanzu kansa a qasa murmushi yayi yace "qanwata sorry ina wayane" kanta aqasan ba tare da ta ɗago ba tace "ba komi yaya baqo" murmushi yayi jin sunan da ta raɗa nasa "Au yaya baqo ne sunana kenan?" To yaya ko ruwan ma baka sha ba ga abinci ma na kawo maka in baba ya gani ba zaku shirya ba baison rashin cin abinci.
Karki damu zanci ko, me sunan ki qanwata? kanta aqasa har zuwa yanzun tace tace "𝗲𝗰𝗹𝗲𝗲𝘆𝗺𝗲𝗿𝗵"
Murmushi yayi wow! suna me daɗi amma kinsan me? Girgiza kai tayi a'a yaya na, sai yace "ban taɓa jin me irin sunanki ba amma sunanki yamun daɗi sannan da alama masu sunan suna da hankali" murmushi ne kwance a fuskanta har yanzun, to kaima yayana me sunan ka? Sunana "A𝗺𝗷𝗮𝗱" kaima sunanka da daɗi yayana.
Nagode qanwa ta murmusa wa tayi bata ce komi ba kanta a qasa.
Amjad yace "jeki abinki dare nayi ki kwanta ko Nagode sosai Allah maki albarka" da Ameen ta amsa ta tashi tana masa seda safe ta fice a ɗakin.
sauqa yayi yaci tuwon yasha ruwa yai hamdala, ko da ya gama cin tuwon bai kwanta ba dan tsabar farin ciki, butan da ke ajiye bakin qofan ɗakin baqin (wanda ecleemat ta kawo masa) ya ɗauka ya ɗaura alwala ya koma ɗakin sallayan dake ajiye gefe da carbi da Qur'ani megirma ya ɗauko ya shumfiɗa sannan ya tada sallah farinciki fal ran sa(zekoma yaga Umman sa).


🄺🄰🄳🅄🄽🄰
Umma qara dialing tayi amma ba'a ɗauka ba sanda ta qira yakai sau uku 3 ba'a ɗauka, fuskan ta ba walwala ta ajiye wayan Allah yasa kana halin lafiya Ameen.
Ummeyh ce ta kalle ta wai har yanzu layin be shiga ba? "A'a Gwaggon yara ya shiga ba'a ɗauka bane Allah yasa dai yana halin lafiya" faɗin Umma. Da Ameen Ummeyh, Maha da Mahreen suka amsa.
Qira ne ya shigo wayan Ummeyh, Mahreen ce ta miqa mata wayan kasancewan yana hanunta dama, amsa Ummeyhn nata tayi tana ɗaukan qiran
Wa'alaikissalam ƴar Ummeyh kuna lafiya? Tayi shiru alama ana magana a ɗayan bangare, lafiya alhamdulillahi uwata gajiya kam akwai shi fa duk da dai fushi nake dake, sai ta kuma yin shiru, to shikkenan bákomi an maki afuwa maman Gwaggon ta amma dai ba kuyi dede ba maganan baqon nan duk ke da mijinki sai dai addu'an shiriya yanzu gashi Umman ku ta qira ba'a ɗauka ba. Ameerah a ɗayan bangaren ce tace Ummeyh a tayani bawa Umma haquri Allah zamu gyara ba zamu sake ba Insha Allahu
To shikkenan maman Gwaggon ta zan bata haqurin karku qara kuma Allah ya maku albarka sai kun shigo starabanku na ajiye,
Yauwá Ummeyhn mu agaidamun ƴan qanne na seda safe, suka yi sallama ta kashe wayan.
Maha dake gefe tace "Ummeyh tunda ba zaki faɗa ana gaidamu ba muna amsawa" salati Ummeynsu tayi ni Jamila yanxu Maha har ni kin rena?
Turo baki tayi "Ummeyh nifa ba haka ba nake nufi Allah baki haquri Ummeyh na" ta faɗa tana rungume Ummeyh.
za ki tashiman a jiki ko sai na bugeki? ayya dae Ummeyh kiyi haquri bazan sake ba Allah kuwa.
Tom naji ɗagani lokacin sallah yayi, in ke ba kiyi nikam zanje nayi, bare ma inayi Ummeyh am muje muyi tare yau har goyo na za kiyi ko Ummeyh ta? Hararanta Ummey tayi ta miqe.
Umma da already ta miqe ta nufi sama hanyan nata ɗakin dan yin sallah itama cewa tayi "a'a doter ba goyo ba nono zata baki kisha", yauwa Umman yara faɗa mata dai yara gaba ɗaya basu tausayi na kofa hutawa banyi ba duk ma yaushe nazo.





Muje zuwa
Uwar Batoorl taku Ako da yaushe ✍️


ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️



💋💋 امى بتولة💋


𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚




💦💦💦💦💦💦💦


👑 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀👑


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮


𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖


(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍


_______________________________________________________________




🅿️ 63&64



💋💋 امى بتولة💋







𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!


𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.


𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢


𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄



𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄


𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎


𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.


𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......






"Sai a hankali Gwaggon yara Allah shirya mana su, ku kuma duk kutashi kuje kuyi sallah magrib yayi" Umma ta faɗa tana qarisa haura last step ɗin.
Tashuwa duka suka yi kowa yayi hanyan ɗaki dan gabatar da Sallan ganin lokaci yayi.
( Mu kula da addininmu, mu kula da ibadunmu, mu kula da i badun mu, da na iyalanmu domin amanan su Allah ya bamu. Sallah abu ne wanda be cancanci wasa ba, kada kabari abun duniya ya ruɗa ka karanta novel,chat ko wani shirmen lokacin ibada ya wuce ko da kuwa harka ne na neman kuɗi indai kana son ganin dai-dai to ka riqe addininka. Allah datar damu Ameen)
Bayan sun shigan ɗaki Maha tace "gaskiya Adda Ummeyh tazo da masifa nikam Allah yasa dai a yarda a sayamun sabuwar waya shine damuwa ta" lallai ma Maha wato ma Ummeyh ce masifa nide ba ruwa ah to kuma in waya kike so ai ga ya Habeeby ko wayar bindiga kika ce kike so zae saya maki Mahreen ta faɗa tana shigewa toilet dan yin alwala.
bakin gadon su Maha ta zauna ta ɗau wayan Mahreen kan Numbern ɗazu da suka yi waya ta shiga tana kallo wani zuciyan na cewa ta qira wanin na cewa a'a karta qira, jin qaran Mahreen ta fito toilet ɗin dole ya sanya ta fasa qiran, ajiye wayan tayi itama ta shige toilet dan yin alwalan.
Praying mat Mahreen ta shumfiɗa ta saka hijab zata tada sallah qira ya shigo wayan ta, qaramin tsaki taja kai jama'a mutum zai yi sallah ma baza'a barshi ba waye da qira haka lokacin sallah gasto-gasto kaman baya sallah nasan ba Rouheei bane kam.
Wayan ta je wajan gadon ta ɗauka, new number ta gani wanda da alama layin da aka qira Maha da shine ɗazu, hararan wayan tayi bata ɗauka ba dede kuma Maharm ta fito toilet ɗin kuma qiran ya yanke.
Maha man of your dream ya qira inaji halan shi baya sallah, a'a Addah banson cin fuska ke da namiji ɗaya ne? Me zuwa masallaci ai ya jima da sallame sallahn sa.
"Kwaji dashi" faɗin Mahreen ta wuce taje ta tada Sallahn ta, Maha ma darduman ta shumfiɗa gefen Addanta, ta sanya hijab itama ta tada Sallan sai qiran ya qara shigowa wayan.
Mahreen na sallame wa Maha ma dede ta sallame carbi suke ja atare suka yi addu'oeen su, suna shafawa Maha ta miqe tayi wajan wayan ko ɗaga darduman bata tsaya yi ba.
Mahreen ce ta miqe ta naɗe nata da na Maha ta ajiye su mazaunin su ta cire hijab ɗin jikin ta tana cewa "amma dai Maha Allah aiko da Manzon shiriya ya shiryaki.
"Adda Ni to me nayi?" Ta faɗa da shagwaɓa tana riqe da wayan a hanun ta, qiran ne ya kuma shigowa ai kuwa tana ganin numbern ne masauqi tawa kanta akan makeken gadon nasu kamun tayi picking ta kara wayan a kunne.
Mahreen tace "ta Man of dream ayi soyayyah lafiya sai kin fito" Mahreen ta faɗa tana ficewa a ɗakin nasu tayi qasa dan zuwa palour.
Maha dake kwance akan gado da waya a kunne sallama tayi da Sansanyar muryanta "Assalamualaika warahmatullahi wa barkatuhu"
Wa'alaikissalam sarauniyar mata Maryama Barka da dare,
"Barkanmu handsome"
Murmushi yayi a ɗayan bangaren kina fa sani jin ni wanine kai na na qara girma wai handsome, niko ina naga kyau?
Murmushi tayi tace "ashe dai duka mazan duniya ba mai kyau in har kaima baka dashi"
Shikenan bana ja da maganan sarauniyata fatan dai kina lafiya?
Ina lafiya Alhamdulillahi sarki fatah kaima hakan?
Murmusawa yayi daga ɗayan bangaren You are making me feeling very hungry of seeing you Queen, Yaushe za'a bani dama nazo naqara ganin kyakkyawan fuskan sarauniya ta? Murmushi tayi har sanda fararen haqoranta suka fito anytime you are welcome handsome.
Since you said anytime bana yi sallar insha'ee na shirya nazo hope am welcome even dis time? Lah lah noo not today You are not welcome today but may be any day after today.
okay madam Allah kaimu dan gaskiya am eager to see this cute face again, Ko dai ugly face ba.
Dariya yayi a ɗayan bangaren wanda ko ba'a faɗa ba kasan ya bayyana kyawun sa matuqa (me kyau sannan ya haɗa da dariya yaya kenan?). And you most be joking inde kina faɗa wa wannan kyakkyawan halittar Ubangijin ungly bari ma kiji You will make a very big sin( zunubi) sai dae kiyi istigfari ki tuba sannan kuma ki haɗa da hamdala (godiya ga Ubangiji).
Lumshe ido tayi "she's just feeling her self somewhere else not this world again( duniyar masoya kenan)".
Wayan suka ci gaba dayi cikin wasa da shauqi in ka gansu zaka ranste sun shekara da haɗuwa not even knowing is just few days relationship.
Suna waya su ne basu yi sallama ba har sai da aka qira isha'ee kamun suka yi sallama, kashe wayan tayi tana kallon silin ɗin ɗakin tana murmushi, a lokacin Mahreen ta shigo ɗakin, l kallon Maha tayi tai murmushi ta wuce ta shumfiɗa praying mat ta tada Sallah.
Maha bayan ta gama juyin ta akan gadon ajiye wayan tayi itama ta miqe dan gabatar da nata sallah.
Umma zaune da Ummeyh a palourn suna hira, Ummey tace "wai nikam Umman yara ina yarona yayi ne tun da jiya ban gansa ba? Niko ina zan sani Gwaggon yara ba muna tare ba amma baya wuce ya fice da yaron sa dai kam.
To Allah dawo dasu lafiya, Umma ta amsa da "Ameen".
ko gama rufe baki ba suyi ba sai sallaman sa suka ji shi da Little amsawa suka yi Umma na cewa "Gwaggon yara Kinga ɗanki ɗan halak yaqi ambato kina tambaya sai kuma gashinan kaman yasan Gwaggon sa na neman sa" isowa palourn yayi yana Ummeyh na gani ban ɓata ba.
Habeebyn Ummeyh ai nasan ban da ɓata kam na dai jika shiru ne. Zaunawa yayi gefen Ummeyhn tasu yana "gani tom Ummeyh na"
Maha da Mahreen ce suka shigo palourn a tare.
Mahreen tace "yaya soja sannu da dawowa" Murmushi yayi sannu auntyn soja.
Ummeyh ce ta kallesa au wai Mahreen ce aunty lallai kam gayamun yaushe ta zama auntyn ka?
Umma tace "yauwa Gwaggon yara tambaya mana shi dai" murmushi yayi bai ce komi ba.
Mahreen kuwa qasa tayi da kanta wai taji kunya. Maha taɓe baki tayi tana miqawa Little hanu my boy ayoyo I miss you, kaman dama bai ganta ba jira yake ta qirasa har da gudun sa yana faɗawa jikinta "aunci unkui afita a ni ance maca mufita da anci na yaci aunci i micc u cuu" yafaɗa cikin gwalantin sa.
Ummeyh dariya ta saka jin abinda Little ya faɗa da maganan sa da baya fita sai tace "wai dagaske Maha kin koyawa yaron nan ɗan banzan surutun kinnan lallai kaga iyaye Allah shiryaku duka ke da ɗan naki"
Soja yace "ai Ummeyh boy yayi rashin mama indai wannan ce" ya faɗa yana taɓe baki.
Tura baki tayi tana qunquni tim ina ruwan mutum ma da ni,
Umma tace "qyalesu doter kekam uwa tagari ce Allah maku albarka duka" suka amsa da Ameen duka palourn.
Abba dake shigowa ne yayi sallama, Maha ce tayi saurin amsawa tana ayoyo Abbana.
Da murmushi yace doter maman yaro sannun ku ko, Little yace "apoki annu a dawowa nima ai anbi unkui na anguwa kuma aka bimu ba" Umma da take ta murmushi bata ce komi ba bayan amsa sallaman Abban sai tace "baki abun magana angon gilani".
Abba murmushi yayi aboki sorry ko next time zaka bini in yaso sai kaima na biku ko? Ɗaga kai Little yayi yana washe qananan haqoransa.
Wucewa ɗaki Abba yayi bayan yai masu sannu dukansu, Umma ta tashi tabi bayansa.
suna shiga ɗakin ya rungume matar sa, amarya ta mai ƴaƴa da jikoki shine ake ta murmushi ko qala ba'a cemun ba ko?
Kama kunne tayi tana murmushi aimun afuwa yallaɓoi baza'a sake ba.
kallonta yayi yace "angama amarya ta". murmushi tayi bata ce komi ba ta taya sa ya rage manyan kayan jikin sa.
yallaɓoi abar wasta ruwan nan sai munci abinci kaga dama kai muke jira.
murmusawa yayi Allah maki albarka Ameenatu, da Ameen Umma ta amsa tayi gaba yabi bayanta suka komo
palourn.
Ummeyh na zaune inda suka barta da Maha da Mahreen sai Little.
kallon su Umma tayi tace "Gwaggon yara muje muci abinci ba"
tashuwa Ummeyh tayi tana faɗin "to Umman yara matar yaya.
"Doter je ki qira yayanki yazo muci abinci ko, angon granny da Mahreen mu tafi kamun su iso" Umma ta faɗa tana juyawa zuwa dinning.
Turo baki Maha tayi kaman tace ba zata ba ta nufi hanyan balconyn da zai sada ta da ɗakin soja tana qunquni.
su kuwa duka dinning area

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login