Showing 1 words to 3000 words out of 32414 words
MIJIN-TA-CE
1
NA
Haj. Hafsat C. Sodangi
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
Haqqin Mallaka (m) Haj. Hafsat Sodangi
Copyright© Haj. Hafsat Sodangi
GODIYA
Godiyata ga Allah take Subhanahu wata'ala, mai kowa mai komai, gwani kuma mai hikima wanda ya yi halitta tasa duka bibiyu, ya kuma halicci mutum da Aljan don su bautata mishi.
Tsira da Amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa, shugaban Manzanni, Manzon tsira Manzon rahama Annabin qarshe Muhammad (S.A.W) da Alayensa da Sahabbansa da waxanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar Alqiyama.
SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin ta Makarantanshi ne, na kusa da na nesa na gode qwarai da kulawarku, Ubangiji ya saka muku da alheri, amin summa amin.
TUKUICI
Tukuicin littafin na Kabiruna ne.
KABIR CHINDO SODANGI (A.T.B.U Bauchi)
Haqqin Mallaka:
Haqqin mallakar littafin
GORO
Goron naki ne Goggona
HAJIYA RAKIYA BABA SANI a Bukuru
BUGAWA A COMPUTER:
NAFI'U SALISU
08021225160, 07054584199
E-mailaddress:nafiusalisu47@yahoo.com
Litattafan Marubuciyar:
Uwar miji
Naga ta kaina
Wayyo duniya
Rabon kwaxo..
Cikar alqawari
Tabbataccen al'amari
Yi wa wani
Abu naka..
Nufin Allah
Gani gare ka..
Kifi na ganinka...
Me zamu ce da maza?
Garin banza..
Biyan buqatar rai
Hattara!
Da kamar wuya..
Daga qin gaskiya..
Mata masu duniya
Shamaki
Mai uwa...
Duk xaya
Mata da kicin xinsu
Wacece Ni?
Ayi dai mu gani..
Kyautata
Mai Uwa...
Mijin-Tace
MIJIN-TA-CE
“H
umaira! Humaira!! Humaira!!! Bata jin wannan kiran ne ko kuwa?” daga can cikin gidanmu nake jiwo waxannan maganganun.
Abinda yayi dalilin da na fasa shiga cikin gidan na qara ja da baya na tsaya ina sauraron mai maganar.
Cikin takaici da vacin rai na yanda ita kullum babu dama ta kira wani ta xan sa shi wani abu don ni ma in xan samu in huta komai sai dai ta kira Humaira.
Can cikin zuciyata na sake jan wani mummunan tsaki a daidai lokacin da haushinta ya sake kama ni a dalilin zuba wa kwanon dake hannuna ido da nayi, cikin takaici nace sai kace ba ita ta aiken ba, tun kafin in kai ga kawo mata aiken da tayi min xin har ta mance tana sake nemana don ta sake aikena tanfar dai babu kowa a gidan sai ni.
Maimakon in hanzarta shiga cikin gida in kai mata aiken nata, musamman da yake ina jin yanda ta kasa daina qwala wa sunan nawa kira, sai kawai naja na tsaya cikin zauren na maqale jikin bango ina sauraro tare da yin tsokaci kana wasu al’amura da suka addabi zuciyata.
Ko yaushe ne ni ma zan samu in xan huta in samu in rinqa watayawa irin na sauran yaran gidanmu, in mallaki ‘yancin rayuwa irin na yanda nake ganin sauran ‘yan uwana suna dashi?
A kullum zuciyata ta xan samu wani sarari ko wata dama da zata yi min wata tambaya, to ba tayi yi min tambayar da ta wuce waxannan tambayoyin, yaushe ne ni ma zan huta? Yaushe ne ni ma zan samu ‘yancin rayuwa irin wacce sauran ‘yan uwana ke da ita?
A lokacin da nake yarinya ‘yar qarama, na xauki halin da nake ciki na takura da qunci da rashin hutu tanfar hakan ya same ni ne a dalilin ni xin ni ce qarama cikin yaran da suka kai munzalin moro.
Don haka sai nayi ta fata da buri waxanda suke biye da ni su kawo sanda za su karve ni, amma daga baya sai na gane a’a ba haka ba ne tunda ai akwai wasu qannen nawa da tazarar watanni goma ne kawai a tsakanina da su.
Kamar irin su Suwaiba, kuma su xin ba ayi musu irin aiken nan da ake yi min na sayo min kuka, sayo min daddawa, sayo min kanwa, komai ma dai ba kuma wannan ne yafi komai vata min rai ba, sai irin wai ko a gida xaya abubuwan da ake buqata suke to ba za a haxa min aiken ba, sai na kawo xaya a sake maida ni.
Duk a dalilin dai wai kar a ganni a zaune ina hutawa, ko sanda nake yarinya ‘yar qarama wannan jeka-ka-dawon kan ci min rai, to balle yanzu da na soma sanin abinda ke min ciwo, ga kuma wasu qannen nawa da yawa da suka taso bayana waxanda su ba hakan ake yi musu ba, waxanda su suke ma da ‘yancin a aike su su ce ba za su ba.
Babana Malam Surajo mazaunin unguwar Jahun ne dake cikin jihar Bauchi, Jahun gaba take kaxan da Nasarawa, in har ka biyo ne ta qofar Nasarawa ne, gaba xaya ta nan kewayenmu har unguwannin dake kewaye damu mutane da yawa sun san shi, sun kuma san gidanmu.
Saboda kasancewar shi xin a shekarun da suka gabata yana cikin ‘yan kasuwar da kasuwa ke kai musu, ko a yau xin nan kuwa da ake faxin harka ta xan ja mishi baya yana cikin rufin asirinshi daidai gwargwado.
Sanda na soma wayo a gidanmu ina yarinyar qarama, na buxe ido ne na tarar da Babana da Matanshi na aure guda biyu, wato uwargida Hajiya Majadan wacce gaba xaya gidan har mutanen unguwa ake kira Mama.
Sai kuma Innata wacce akan sakaya sunanta da nayi qoqarin yi nasha tabka da bulala akan wai ni xin fi’ili ne dani da kuma sanabe iri-iri don haka nima na haqura na shiga sahu wajen gantsara mata sunanta da ake kiranta dashi Gambo.
Mama ita ce uwargida a gidanmu, auren saurayi da budurwa aka yi musu ita da Babana, tana matuqar jin d axi da kuma gadara da hakan, da kuma alfahari da uwargidancin nata.
Zan ma iya cewa a wurin Mama, gani take tanfar duk wata mata da ba auren saurayi da budurwa suka yi da mijinta ba, to gani take tanfar auren matar ba wani aure ba ne na sosai, in ma ‘ya’ya ta haifa to ‘ya’yan da ta haifan sun fi kama da gasu nan dai gasu nan, amma ba wani ‘ya’ya masu ‘yanci ba.
Wataqila hakan ne ma dalilin da yasa a lokacin da ‘ya’yanta mata suka zama ‘yanmata suka kawo munzalin aure ta kasa ta tsare, tayi qememe ta qi yarda da mutanen da Babana ya kawo su aure su.
Dalili, wai su xin masu mata ne ‘ya’yanta ba za suje suyi bau tar ‘ya’yan wasu ba, samari gal a leda zasu aura, don haka akan dole Babana ya yarda Kaza taja Zakara.
Ya xaurawa ‘ya’yanshi Anti Sha’awa da Anti Kaltume aure da samarin da uwarsu take so. A kullum Mama cewa take yi da kaje ka samu ai gara a zo a same ka, duk tsiya an zo an same ka a gidanka da ‘ya’yanka da mijinka ai babu wata tsiya da za a kawo maka, dole kuma abi tsarin da a ka zo aka same ka akai, tunda dai mijinka ne, gidanka ne, to wane fi’ili za a kawo maka?
Mama mata ce mai nuna isa da gadara ga kuma mulki, zai yi wuya qwarai rana ta fito har ta kai ga komawa ga Ubangijinta baka ji ta tana yi wa kanta kirari ba, kusan kullum sai ta faxa, “Alhaji mijina ne, auren saurayi da budurwa aka yi mana ni da shi, aurenmu aure ne na soyayya babu wani abin shi da ban sani ba, haka shima nawa.
Aurenshi nayi tun bai da ko kwabo tun ‘yan wandunan sakawanshi basu wuce guda biyu ba nake tare da abina, don haka babu wata matar da zata shigo min gida a dalilin ita da iyayenta sun hangi arziki da rufin asiri ta ce zata kawo min wani fi’ili.
Ba zai yiwu ba, ba zan yarda ba, shima maigidan ba samun shiga za’ayi ba a wurinshi, yauwa duk wacce ta hango min mijina tayi sha’awar shigowa taci arzikin da ta hanga to zata zo ne tayi zaman haquri, in har ta matsu da zaman in kuwa ba ta matsu ba sai tayi gaba kamar yanda wasu da yawa suka yi da suka gane ba za su iya ba.”
Duk waxannan kalamai na Mama da takan furta kamar wasa kamar shaqiyanci da iyakacin gaskiyarta take yin su, haka nan kuma al’amarin yake a hakan kuma ake zaune babu musu ko jayayya kan maganganun nata.
Babana ba ya iya musu da Mama, baya jayaiya da ita kullum a to yake a wurinta, gashi kuma tayi sa’a yana matuqar gudun vacin ranta kan abin da take so kuma to kullum zai iya sakin ra’ayinshi ya koma nata don neman zaman lafiya.
Xan qaramin misali kuma shi ne, yanda ya haqura da bayar da auren ‘ya’yanshi Sha’awa da Anti Kaltume ga mutanen da yake ganin sune suka dace ya bada su ga waxanda Mama take so, duk kuma da gaba xaya ‘yan uwanshi da aminanshi ba su so yayi hakan ba.
Innata dake zaune da Mama da mijinta kuwa haquri take yi, haqurin kuma ba kaxan ba, don kuwa in ban da tana da tsayayyun iyaye waxanda suke da tasiri mai qarfi a kanta da bata iya yin shi ba.
Ita Innan ‘yar gata ce ta qin qarawa a gidan su Yayu ne da ita maza da mata masu yawa, gashi kuma dukkansu ji da ita suke yi ‘yar auta ce wurin mahaifinsu Mallam mai babban allo a wurin mahaifiyarta kuwa ma ita kaxai ce mace.
Kyakkyawa ce qwarai, a lokacin da tayi ‘yanmatancinta babu wanda bai san da labarin kyanta ba, musamman ma a unguwarsu ta qofar Dumi, unguwar da a farkon auren Babana da Mama a can suka zauna da ya gina gidanshi na farko a Jahun, shi ne ya taso ya dawo nan kafin daga bisani ya gina gidan da muke ciki a yanzu, wanda manne yake da tsohon gidan namu.
Da yawan mutanen da suka san Innata da irin gatancin dake gare ta suka kuma san halin zaman da take ciki a gidan namu kan ce wai har da rabon haihuwa cikin abinda ya zaunar da ita.
Mallam mai babban allo Malami ne mai karantatarwa yara da manya suna xaukan karatu a wurin shi.
Yana da matanshi na aure guda biyu, Hajiya ‘yar dubu ita ce uwargida, ita ce kuma uwar manyan ‘ya’yan gidan gaba xaya su Alhaji Maikuxi, Alhaji Malam, Alhaji Kawu, Inna Aisha, Inna Hajara, gasu nan dai da yawa gaba xayansu sun girmi Innata nesa ba kusa ba, don ma ‘ya’yansu sune sa’o’inta wasu ma da yawa sun girme ta.
Saboda ita mahaifiyarta Hajiya Turai an bashi aurenta ne a shekarunshi na girma bayan rasuwar matarshi ta biyu ta rasu ita Hajiya Turai ‘ya’ya uku ne da ita Kawu Hassan da Husaini sai ko ita Gambonsu.
Matan Mallam mai babban allo zama suke yi na girma da mutunci ita Hajiya ‘yar Dubu ta kama girmanta itama Hajiya Turai tana kame da kanta tana kuma girmama Hajiya ‘yar Dubu saboda ta girmama kanta shima Mallam yana iya qoqarin shi wajen ganin gidanshi ya zauna lafiya.
Don haka sai komai ya tafi bai xaya gaba xaya ‘ya’yansu kuma suna girmama su saboda mahaifinsu yana da girma a wurinsu.
Tasowar da Innata tayi a cikin gidansu cikin wani yanayi na shagwava mai tsanani saboda rashin kwabo da sangarcewa yasa Alhaji Maikuxi yasa hannu ya xauke ta daga cikin gidan ya maida ita nashi gidan gaban matarshi Kubra wacce a lokacin take da ‘ya’yanta maza guda uku, wato Abdullahi da ake kira Abba sai kuma Auwal da Ahmad.
Ita kuwa Hajiya Kubra tayi mata riqo na gaskiya da amana ta hanyar bayar da ingantacciyar tarbiya tare da sauran ‘ya’yanta waxanda suka girmi Innan da wasu masu yawa da suka biyo bayanta.
Inna ta taso cikin gidan Alhaji Maikuxi tanfar ita ce babbar ‘yarshi mace, itama Baba take kiranshi tanfar dai shi ne ya haife ta, don haka daga baya ne qwarai da yawan ‘ya’yanshi dama sauran mutane suka san cewa ita xin qanwarshi ce ba ‘yarshi ba.
A lokacin da ta zamo budurwa kuwa ba zai yiwu in kwatanta yanda ta zamo ba, don kuwa ba qaramin gata Alhaji Maikuxi ya nuna mata ba.
Manema sosai tayi duk da bai yarda ya bada damar aje gare ta ba, saboda jan da yayi ya tsaya kan cewar karatu zata yi.
Sai dai Mallam mai babban allo bai goyi bayan hakan ba, hasalima shi ne ya bada umarnin bayar da auranta ga Babana saboda kamun qafar da Baban nawa yayi da Almajirin mai babban allo Alhaji Yahaya, wanda shi kuma Aminin Babana ne, tare ma suka taso tun suna ‘yan yara.
Duk da bin umarni ne yasa Alhaji Maikuxi aurar da Innata a wannan lokacin saboda kwata-kwata shekarunta goma sha biyar ne, gashi kuma gaba xaya an san Mama da irin matan da ta kora a gidanmu da ma raxe-raxen da ake yi na fin qarfin Maigidan da ake cewa tayi.
Kowa cewa yake yi zata ne kawai ta dawo ‘yar qaramar yarinya zata yi mata sanadin zawarci bai hana Alh. Maikuxi kashe dukiyarshi mai yawa wajen hidimar auren nata ba.
Inna ita kaxai a gidanmu, xakunan kwana uku ke gare ta gami da makaxexen falo mai xauke da toilet a cikin shi.
Hajiya Kubra ce taja ta tsaya kan sai an bata wannan wurin kafin ayi bikin, kasancewar gidan namu a lokacin sabo ne gashi kuma Babana yana matuqar son auren, ga kuma sulalla a hannunshi, yasa yayi musu yanda suke so xin duk da irin tashin hankalin da ya fuskanta daga wurin Mama.
Su kuma su Hajiya Kubra da mijinta ba suyi qasa a gwiwa ba, suka shaqe mata wurin nata da kayayyakin alatu gami da gadaje irin na alfarma.
Alhaji Maikuxi yana matuqar sona a dalilin tsananin son Innata da yake yi, wasa dani yake yi irin wasan Jika da Kaka, don kuwa ya dage kan cewa Innata ‘yarshi ce, don haka sai na daxe ban gane cewar ba shi ne mahaifinta ba, sai a wani lokaci da wani abu ya faru.
Rannan ne cikin dare na farka a xaya xakin Inna damu ‘ya’yanta muke kwana a ciki sai na jiwo muryar Babana yana magana cikin yanayi mai qarfi, alamar dai akwai vacin rai cikin maganar tashi.
Sannu a hankali da na saurari maganar tashi sai na gane tuhumar Innata yake yi yana tambayarta dalilin da yasa Mama tasa ta aiki bata yi ba?
Ban jin bayanin da Inna take yi mishi, don magana take yi a hankali cikin muryarta mai sanyi, sai daga baya da maganar tayi tsanani ne na jiwo ta tana cewa, to tunda kace ita bata qarya me yasa in ta gaya maka magana ba zaka yi hukunci ba kawai sai kazo kana tuhumata?
Babana ya ce, ai haka ma za ki ce? Ta ce eh, saboda in ta riga ta faxi nata zancen ko na musa baka yarda.” Ya ce, “To kar kuma kice an zalunce ki.” Ta ce, “Uhun, zalunci kam ai a cikinshi nake raye, sai dai kuma na sani da sannu mai sakayya zai saka min, don kuwa ba zan yafe ba.”
Inna tana faxin haka naji saukan dukan Babana a jikinta, wai tayi musu Allah ya isa shi da Mama. Tuni jikina ya shiga rawa ina ta karkarwa akan gado na rasa yanda zan yi in taimaki Innata, tunda bayan saukar dukan farko da naji wasu masu yawa ma sun biyo bayan shi.
Nayi kamar in miqe in fita falo don dai ya ji motsina ko zai saurara sai kuma na tuna da gaya mishin da Mama take yi wai ni xin zamana a wannan xakin lave nake yi musu, komai suke yi shi da Innata ina jin su.
Don haka ya hana ni kwana a nan ya fito dani tsakar gida saboda tana son ganin ta rage qarfin mu’amallar dake tsakanina da Mahaifiyata, wacce ta tabbatar cewar ni ce farin cikinta na wannan lokacin.
Bisa wannan dalili yasa nayi shiru, na sake komawa na qara lavewa kan gadon namu sai dai hawaye da suke ta gudu kan kumatuna.
Ban san dalili ba, Inna ta qi kuka wanda in da tayin wataqila da dukan da yayi matan bai yi tsanani haka ba, don wataqila yaso tayi kururuwa ta yanda Mama zata yi abinda ke faruwa don tasan shi xin yayi hukunci kan qarar da ta kawo mishi.
Duk da Babana ya daina dukan nata, ban kuma ji wani motsinta ba, kwana nayi idona biyu ina kuka, don haka ina jin buxe qofar