Showing 12001 words to 15000 words out of 22537 words

Chapter 5 - NAGA RAYUWA 3

02 Dec 2025

70

sauri
na,sake runtse idon don ita kanta ba na son
nagan ta Bayan gaishe da su Abba da ya yi ina
jin takunsa yakaraso bakin gadon danake anan
naji yace Bata farka ba haryanzu" Abba yace Ta
farka sai dai idan sake komawa tayi Humaira ta
karaso ta dafa kafada ta jinayi kamar namake
hannun ta amma na kyale ta sai dai zuciyata na
matukar tafarfasa har ban san sanda hawaye ya
silmiyo ta gefen kunci na ba Inajin Humaira tace
lah Abba mafarkin kuka ta ke yi? Abba yace,wane
irin mafarkin kuka kuma ke dai humaira da
shiririta kike matsa in gani Abba yasa hannu ya
shafi hawayen yace da gaskiyarki sai daiba
mafarkin kuka take ba kuka take dagaske . Wato
Aysha ba zaki cire damuwa daga ranki ba ko? Ni
banga abinda akayi miki ba da ya tsunduma ki
cikin wannan damuwar Na san kina jina Humaira
tace Abba kayi mata ahankali babu mamaki
abubuwan da suka, faru da ne suke damunta
azuciya Abba ya girgiza kai to ai shikenan Allah
yayi mana magani Amma ya kamata kicire
damuwar nan tunda komai yariga yawuce Gaba
daya haushin maganganun su nakeji Don haka da
sauri na mike namayar da gashina da ya kwanta
agefen fuskata Ustaz yana gefe ya zubomin ido
wata harara na watsa masa Madadin naga
yahade rai sai na ga ya saki murmushi yace
aysha yajiki? Banko amsa ba nashige toilet ban
san me zanyi aciki ba amma zaman toilet din yafi
min zama ina shakar kanshin Ustaz yana hadda
samin tunani iri-iri Ina shiga na saki kuka
ahankali mai tsuma.Zuciya Ba na so suji muryata
don haka natoshe bakin tsawon lokaci ina toilet
har umma tagaji ta shiga bugamin toilet din tana
fadin ke ayshatu lafiya? kifito ga mijin naki yazo"
wani bugun zuciya naji da karfi na kasa yunkurinnovels / NAGA RAYUWA book 3 part 11
NAGA RAYUWA book 3 part 11
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:17
Saboda ina tsoron ganin fuskar mijin nawa
mummuna ne? kyakkyawa ne? Allah ne masani
Banbude ba sai da naji Umma tana cewa Ba kys
jine? nace ki bude ga mijin ki da abokansa nan
Da kyar na bude nace Umma miko min hijabina
janyoshi tayi tamiko min tas na goge idona don
inason bawa Ustaz mamaki zan nuna masa ina
son mijina nima turus... . YAN UWA SORRY
WANNAN PAPER DIN COMPLETE YAYI DAMAGE
TO DAN HAKA MUN SALLAKESHI DON BAZAI
KARANTUBA . Sai naji yace Gaskiya Alhaji Amarya
tayi Allah yasanya Alheri Inaji katon banzan yana
dashe baki yana "Amin-amin Nagode yalabbai"
sannan ya mike "Bara mu tafi na, ga kamar tana
so tahuta kasan marar lapiya ba kasafai yake son
hayaniya ba . Amma yayannan naki yanada kirki
Ban ko kalle shi ba suka mike ya iso gurina ya
ajiye bandir.Din kudi na 500 yana fadin "To my
madam Allah yakaro lafiya" cikin wata
dasasshiyar murya ga kana nan ido wasu jajaye
mitsi-mitsi dasu sai fakadeden hanci baje, a
fuskar tamkar faranti Ya juya yasake dashe
gaftara- gaftaran hakoransa A zuciyata nace wai
Allah yayi halitta a nan!" . "Amarya sai gani
nabiyu" Tamkar nace amaryar ubanka sai dai na
dauke kaina Jin buga kofar ne yatabba tar min da
fitarsu Hakan yasa na fashe da kuka Har ma na
rasa wane irin zafi Zuciyata take yi Da daddare
likita ya rubuta min sallama kasancewar an fara
gudanar da hidimar bikin gidan adinke yake da
jama'a wanda suka zo daga garinmu Potiskum
Ana ta yi min sannu ni dai na samu na shiga
dakinmu Nan din ma . 'yan mata ne aciki amma
cikin tunzura nace "Da Allah ku fita waje kuba ni
waje na kwanta" Ba su musa ba suka yimin
sannu suka fice falo na kwanta Daidai lokacin
Humaira ta shigo da gudu ta fada jikina tace
"Aysha sis,oyoyo, ashe an sallamo ki? amma naji
dadi bara na kira My Ahmad na gaya masa" wata
harara na watsa mata nace "ke ba na son
munafunci na ce miki ina nemansa ne? . "Haba
Aysha sis, shifa yace idan an sallamo ki na kira
shi ya sake miki ya jiki" Girgiza kai kawai nayi
nace "Humaira fice a dakin nan tun kan cimiki
mutunci Keda Ahmad din"Ta zaro ido tace My
Ahmad din? Tsaki naja nace "Ko uban Ahmad ne
banzaye munafukai" ganin yadda na matse ina
masifa ne hakan yasa Humaira ta fice sum-Sum
jikinta asanyaye Naja tsaki nace "munafukai
kawai ko kunya ba ta ji ba wani My Ahmad ko
gidan ubanwa yazama na ta?" jinayi anturo kofa
har najuyo zan banka ashar sai naga umma
ce,hakan ya sa nawa bakina linzami Umma
tazauna agefen gado ta ce "tashi Aysha magana
za miyi " Dakyar na mike ta zubo min ido kafin
tace . "me ya farune?" Nace Name fa Umma?
"Yanzu 'yar uwarki taje,da kuka tana sanar dani
wai tafasa auren Ahmad saboda ta lura kina son
mijinki shin dagaske ne abinda ta fada?" Tamkar
nace "ba haka bane amma sai wata zuciyar ta
sanar da ni wannan ce dama ta takarshe hakan
yasa cikin matukar kunya da jin nauyi nace Eeh
Umma" Umma tazaro ido tace . "Kina son sa fa
kika ce?" Na daga kai, sai naga Umma jikinta
yayi sanyi, tace "Aysha Kirufa mana asiri don
Allah kada kisa mu abakin duniya Ace duk sanda
muka tashi sha'ani sai wani abu ya faru tunda an
gama magana har ankarbi sadakin humaira to ki
bar mata Ustaz tunda tun farko ke kika ce
bakyason shi aka kuma biye miki yanzu kice
kuma kin dawo kina sonsa . wallahi kada na sake
jin zancen nan 'yar uwarki ce don kin rasa ta
samu bai kamata yazama abinda muwaba . Ki
share hawayenki shima wannan mijin naki
maikudi ne kuma yanada kirki matarsa mutuwa
tayi wajen haihuwar dansu na takwas" Da, sauri
na zaro ido tace "takwas Umma? . wayyo na
shiga uku Abba ya rasa wanda zai ba wa aurena
sai wannan basamuden?" Umma tayi saurin cewa
"Rufemin baki kada ki tara min jama'a to sai me
don 'ya'yansa takwas ba tare dake za su
zaunaba suna wajen kakarsu, kuma ya ce ma
kuna auren Abu dhabi za ku wuce acan inda yake
gudanar da harkokinsa ba ki ga gidanki ba da
akaje gida tamfatsetse tamkar ba a duniya ba . "
Runtse idona na yi ina jin Umma ta gama surutun
ta fita. Tunani kawai na keyi ta yadda zan iya
zaman aure da wannan mutumin Ni maison miji
kyakkyawa na nunawa sa'a amma kudurar
ubangiji ta sauka akaina Kana ta ka ne Allah na
tasa kuma ayanzu na tabbatar ba duk abinda
kakeso kake samu ba sai wanda Allah yaso Ina
kallo Umma ta fice daga dakin zuciyata ina sake
tuna zancen Umma da take ta koda arzikin
mutumin wai har da cewa gida tamfatsetse
tamkar ba a duniya ba to ni ina ruwana . Da
arzikinsa? Na ja tsaki yafi a kirga. Haka aka shiga
gudanar da shagalin biki ni.Kuwa ba na shiga
kowace sabga koda yaushe ina daki akwance ina
ganin yadda wasu suke kallo na a dafe da alama
suna hasashen yadda nake yi wa 'yar'uwata
bakin ciki ne ni dai bin kowa nake da kallo
fuskata kuwa ta yi fayau ni kaina na san na rame
matuka da gaske. Ranar da ya kama za akai
amare a ranar naji labarin wai, ni ma zanbi mijina
Abu- Dhabi, Hankalina ba karamin tashi yake yi
ba idan na tuno yadda mijin nawa yake Tunda
magriba na fara jin hayaniyar motoci Humaira ce
ta shigo da gudu ta, fada jikina ta rungume ni
tana wani kuka maitsuma zuciya Hakan ya sa ni
ma na saka kuka ba tare da na shirya hakan ba. .
A marairaice kanwar umma ta shigo, ta ja hannun
Humaira tana fadin "Kuyi hakuri haka rayuwar
mace ta ke takaitacciya ce agaban iyayenta" Ina
kallo takama humaira suka fice.Nasan shi kenan
na rasa Ustaz, har'abada zuciyata ta karye na
sake fashewa da kuka Gidan yayi tsit duk an
fashe,kai amare daga ni sai Umma ji nayi anturo .
Kofa an shigo In bude ido naga Abba ne da
Umma Abba yazauna abakin gadon cikin muryar
rarrashi yake sanar dani natashi naje mijina yazo
tafiya dani "Ayshatu ina sake baki hakuri akaro
na biyu akan duk abubuwan da suka,faru a baya.
. Sannan ina miki nasiha da kibi mijinki sau da
kafa saboda ko ba komai aljannarki atafin kafarsa
take. Na sani Ayshata mai biyayyace don Allah ko
da bakya sonsa kidaure kibishi. Alhaji Danjuma
mutumin kirki ne" Da sauri na sake fashewa da
kuka jin sunan da Abba ya fa da wai Danjuma.
Kai daga ji ka san an rayu akauye. . Umma tace
"To mene ne na kukan tunda ta faru ta kare.
Ubangiji ya ba ku zaman lafiya Tashi maza ki
kintsa yana jiranki a mota airport za ku tafi."
Cikin rarrashi Umma ta tilasta ni nashirya cikin
wata rantsattsiyar laffaya, fara. Ta sha ado da
zare marun. kayan kam sun amshi jiki na caras
na fito tamkar 'yar tsana Na raya araina ina ma
gidan Ustaz za a kaini ba gidan wannan mutumin
ba." Da kyar nayi sallama da su ina kuka cikin
karaji yaya usman ya rike hannuna ya rakavels / NAGA RAYUWA book 3 part 12
NAGA RAYUWA book 3 part 12
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:19
Ni har bakin motar yana sake jaddada min na yi
hakuri duka rayuwa nawa ce. Idan dan Adam yayi
duba da abubuwan zamanin baya da suka shude
zai gane rayuwar duniya ba,komai ba ce jin Yaya
usman kawai nake har ya bude bayan motar ya
saka ni yana rufe motar na sake fashewa da
kuka. Daidai lokacin Danjummai ya juyo daga
kujerar gaban motar ta masu zaman banza sai ji
nayi ya ce "Shatu sai hakuri a,rabuwa da iyaye
akwai ciwo amma ga 'yanmata hakan yafi ciwo
ba ga ke da ba wannan ba ne aurenki
nafarko".Tsit nayi saboda jin haushin kalamansa
Ji don Allah ko hakan shine salon da ya dace
ararrashi amarya? Sam babu riba ga auren
babban mutum. Harmuka isa airport ban sake
tofa komai ba naja bakina na tsuke ina sake
taraddadin yadda zan zauna da wannan mutumin
Ina,jinsu suna ta shewa suna hirar kasuwancin su
Isarmu airport tayi dai-dai da lokacin da ake ta
kiran passenger ciki kuwa har da mu ana sanar
sauran mintoci kadan jirgi yatashi raina a bace
nake bin sahun mutuminda da za abani dama
nakashe wani shi zanfara kashewa . Muna hawa
jirgin hancina yafara shakar kamshin Ustaz Nan
take na fara waiwaye awautata wai ko zanganshi
amma sam ban ganshi ba take na amince yawan
tunanin sa da nake yine yasa nafara jiyo kamshin
sa Bat na nemi mijin nawa Na rasa hakan ya sa
na fara waiwaye- waiwaye saboda ni sam ba
taba shiga jirgi nayi ba balle nasan ka idojinsa
Tsawon mintuna ina laluben mutumin amma ban
gan shi ba hakan ya tunzira zuciyata na sami
waje kawai na zauna ina fargabar yadda jirgi zai
daga ni sama na zama tamkar tsuntsu a sama
wani mutum ne yazo ya tsaya akaina tare da
sanar dani wai wajen sane,nazauna har yana
nuna min numbersa ajikin boarding pass. Take
kwalla ta fara zubar min ganin yadda mijin nawa
kiri-Kiri zai saka adauke ni 'Yar kauye Murmushi
kawai na saki da furta kalmar"am sorry". shima
yasaki murmushi ya ce "Ba komai 'Yan mata
kiduba lambar sit dinki ajikin boarding pass dinki
Na daga kai na nawuce ina laluben lambar
kujerata Da sauri na isa wajen sai dai na tsaya
turus domin daf dawani mutum aka ajiyeni wata .
Lafiyayyiyar suit kuma daga jikinsa kamshin
turaren Ustaz yana fitowa ya rufe fuskarsa,da
wata magazine Mamaki ya kama ni nan na shiga
waiwaye ina tunanin INA MIJINA? haka na zauna
saboda ba na so adaukeni 'yar kauye Amma
kamshin da mutumin yake ya ta kura min saboda
kamshin.Turaren Ustaz Ahmad Tunda Nazauna
bai tan kamin ba Ni ma kuma ban kula shi ba Na
dai kaddara kawai barci yake ko kuma irin
miskilayen mutanen ne shi din jigum na zauna ina
ta addu'a a raina don kam a tsorace nae Dalili?
ban taba shiga jirgi ba wani sauti naji yana sanar
da mu muyi tightehing belt dinmu Gaba daya na
rikice don ban ma san inda belt din yake ba
Mutumin bai wani bude fuskarsa ba ya dana belt
dinsa alamar shidin kwararre ne Na rasa yadda
zan yi tamkar na tambaye shi amma, nafasa na
hakura kawai na cigaba da addu'a a raina Jinayi
kunnuwana sun yi dum dai-dai lokacin da jirgin
ya fincika zai daga ban san lokacin da na
kankame jikina ba ina salati jinayi wannan
mutumin kawai yayi caraf ya riko hannu na
Ahanzarce na juya zan masa . Masifa duk da
tsoron da nakeji Cab ko kunsan WA NA GANI? .
Da sauri na ware idona don natabbatar shidin ne?
tabbas shine ustazuna . ya matse cikin wasu
marun din suit sun amshe shi sosai abinka da
farin mutum cikin matukar mamaki na zame
hannu na nace Ustaz me yakawo.Ka nan? Ina
humaira? Bai min magana ba sai zallar murmushi
kafin yace "Humaira tana gidan mijinta" Na sake
waro ido nace Wanene mijinta ban da kai da na
sani? . " Ustaz ya lumshe ido kafin yace Ni ba
mijin Humaira ba ne ni mijin Ayshata ne" Wani
farin ciki ne ya,mamaye Zuciyata da sauri na ciji
kaina inaso na tabbatar ba mafarkin da na saba
ba ne Ustaz na,lura da ni ya jawo hannun ya
matse yace "Ba mafarki kike ba Aysha nine,Ustaz
dinki" Yakai min sumba a hannu sannan yace "Is
a long story bari muje gida kisha labari" . Tuni
maganar jin tsoron jirgi ya sha ruwa saboda, ga
ni ga masoyina Ustaz dan gaske,Ban sake
magana ba illa sakin murmushi Shi ma
murmushin yake ya jawo ni gefen kafadar sa ya
kwantar akan kafadarsa Akunne ya rada min
"Aysha kiyi barci . Na san kin dade baki yi barcin
farin ciki ba" Na saki murmushi don kam azahirin
gaskiya ya fada Wani annuri ne yake shiga
zuciyata na lumshe idona kamar mai barci sai dai
sam ba barcin nake ba zallar soyayyar Ustaz ce
take ratsa duk wani ilahirin jikina, . Ina kuma
sake jaddada godiyata ga jalla ta'ala buwayi
gagara misali Da son na san yadda reshe ya juye
da mujiya al'amarin Allah kenan kana taka Allah
na tasa .Ta jalla itace gaskiya Azaton Ustaz barci
nake don haka bai tashe ni ba don ko da aka
kawo abinci ma karba kawai ya yi ya ajiye min
nikuma na yi lamo sam ba na son narabu da jikin
Ustaz Ina shakar kamshin sa mai sake
tsuma,soyayyar sa azuciyata sai asubar can garin
sannan muka isa Gaba daya Ahmad ya kankame
hannuna tamkar wani zai kwace ni awajensa
Wani rantsattsen hotel ya kama mana tamkar
aljannar duniya zuciya ta fari kal nake mayar da
kafata duk inda Ustaz, ya ajiye tasa Shikuwa sai
jifa na yake da wani salon murmushi Zama,yayi
abakin gadon hade da fadin "Wash,Allah " ya
lumshe,ido ni ma bin sa nayi . Da ido lna masa
kallon zallar so Ustaz ya miko min hannu "Zo
Ayshat" Ba musu na isa,ga ustaz cikin ta kun,jan
hankali amma sam na ka sa,karasawa gareshi illa
narungume hannaye ina jifanshi da murmushi
shidin ma kashe ido yayi yace "mekenan aysha?
Ina fatan ba kunyata kike jiba? . " Na dan makale
kafada alamar ba za niba Da sauri ya mike ya,iso
gareni "Why aysha? Don Allah kada muyi haka da
ke kada ki disashe farin cikin danake shirin samu
atattare dake awannan daren Ayshata please
enough is enough komai ya wuce don
Allah"yafada yana langa be kai Ni kuwa sake
shagwabe fuska nayi nace Ustaz me ya sa kuka
wahalar dani kuka ki bayyana,gaskiya? murmushi
ya sake yi yace "Har na hango aysha a asibiti da
angonta tana muzurai" ya tuntsure da dariya
abinda ban taba ganin ustaz ya yi ba Don haka
nabishi da kallon mamaki kuma sosai dariyar ta
yi masa kyau ya sake bina da kallo "kina tuna
bama- baman hara rar da kika dunga aika min a
asibiti? . . Na kwace fuskata zan fashe da kuka
Da sauri ya kamo hannu na "Come on Aysha,yau
ba . Ranar kuka ba ce so nake kawai.na nu
namiki zallarso Aysha I am in need" ya fada yana
lumshe,ido Tare da janyo hannu na Nace "Ustaz
don Allah kabani labari" Da sauri cikin dushewar
murya yace "Ba zan iya komaiba yanzu sai na
samu,nutsuwa" Shiru nayi da ba kina don na lura
abin nasa ba sauki. . *** *** *** . WAYEWAR GARI
A ABU DHABI . Duk da sanyin asuba da yake
ratsowa ta window hakan bai sa na tashiba
Ustaz, tuni ya tashi ina ta jin motsinsa har.Bacci
ya sake dauke ni Diso-dison ruwa da yake
digomin akan fuskata, shiya sa na bude idona.
Ustaz ne tsaye akaina ya dan sunkuyo yana min
wani sihirtaccen kallo da murmushi akan lebensa
yace "Beauty a,tashi ayi wanka ayi sallah
mana"Na,dan turo baki nace "wallahi na gaji
Ustaz" Ya dafe hannu na yamikar dani yana fadin
"am very sorry beauty, laifi nane na wahalar da
ke dayawa But am very sorry Laifin so ne" ya
fada yana kashe ido daya sai da ya rakani har
kofar bandaki sannan ya ja min kofa yana fadin
"ayi wanka sosai beauty banda jika- jika" Nayi
murmushi . Na shige cikin toilet din koda na fito
tuni Ustaz ya shimfida min daddumar sallah nan
na tada sallah na dade ina gode Allah acikin
sujjada bisa ni'imar da yayimin ta dawo da Ustaz
cikin rayuwata akaro na biyu Duk da godiyar da
na yiwa ubangiji anafilar ma'aurata da mukayi
adaren jiya Ina zaune ina karatun littafi mai tsarki
Ustaz,ya turo kofa yashigo cikin wata jallabiya
light green colour yazauna agefena hade da sanya
kansa akafada ta yace "kada ki roki ubangiji ya
kara min sonki please Abar ni haka wallahi a
hakan ma wahala nake sha Tuni sonki ya
cunkushe,min zuciyata . Bana iya aikata komai
sai zallan tunanin ki Idan za ki roki Ubangiji ki ro
keshi ya rage min sonki" Wani kallo na dallare shi
dashi yayi murmushi kafin ya lumshe ido ya
kankameni cikin slow voice yace "Ya Allah ka
ragemin..." Da sauri na toshe bakinsa nace "Ba
amin ba" murmushi yayi yace zo ki sha,tea Allah
yabarmu tare forever" Na saki murmushi ni kadai
na san annurin da ya baibaye min zuciyata Zuba
min tea yake a cup amma gaba daya hankainsa .
Akaina yake Na sa hannu zan karbi tea din bayan
yagama hadawa gaba daya ya hada hannuna ya
matse "Allah yaki yaye ai inde ina raye kuma ina
kusa dake kin daina ci da sha da kanki." Yajanyo
ni gefensa yashiga san yamin cup din a baki
maza kisha gimbiyata 'yar albarka mai tarin
alheri da ni'ima Na lumshe idona ina hasashen
dalilin da ya sa Ustaz yake min wannan sumbata
tun daren jiya Bayan mun gama breakfast na
koma gado da niyyar komawa,barci don barci
nakeji har alokacin Ustaz yakawar da kayan ya
biyo ni kan gadon Barci za ki koma? Na daga kai
cikin muryar shagwaba na ce masa "wallahi
Ustaz barci nakeji" Yajawoni jikin sa yana cewa
maza kiyi bacinki dama labari zanbaki na
abubuwan da suka faru bayan kince ba kya sona
da sauri na mike nace please Ustaz gaya min Ya
lumshe ido yana murmushi . *** *** *** . Tun
Sanda kotu ta wanke ki tas daga zargin da ake
miki naga kina watsomin kallon tsana tuni
gwiwata tayi sanyi don nasan da kyar idan za ki
sake amincewa da soyayyata akaro Na biyu.AGA RAYUWA book 3 part 13
NAGA RAYUWA book 3 part 13
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:24
Bansare da al'amarin ba saida na biki gida Nan
ma naga babu wata mafita don kuwa karara kike
min kallon tsana Haka natafi gidanmu gwiwata
asanyaye mamata na zaune afalo ta dubeni itama
cike da tausayawa don tsukun wannan lokacin
sam ba ni da sukuni wallahi Aysha ko abinci ba
na iya ci sai mama ta tursasa ni. . Lauyoyi kuwa
na nemi sama da mutum ashirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login