Showing 21001 words to 22537 words out of 22537 words
shi din ma hamdala ya yi. Da Abba yadawo
ma da fara'a nayi masa Murna shima dariya
kawai yake yana fadin "aysha kenan" Sai dare
UstaZ ya zo muka koma gida zuciyata fal da farin
ciki. BAYAN WATANNI SHIDA Abubuwa da dama
sun faru sun wuce. Ciki kuwa harda
matsananciyar kulawa, kauna da tausayi da Ustaz
yake yimin ganin ina dauke da cikin dansa ko
kwakkwaran motsi Ustaz ba ya so yaga na yi. A
yanzu haka ma shirye-shiryen tafiyar mu Egypt
ake ni da mahaifiyarsa don yace ba zan haihu
anan kasar ba Har da Mami na yake shirya mana
tafiyar don ita awatan haihuwa ma take. Kwance
kawai nake kaina yana wani azabar ciwo, cikina
yayi turtsitsi a gabana. Kafafuwana sun yi luba-
luba, haka hanci na yayi muni sosai kai gaskiya
ciki ba karamin muzanta halittar mutum yakeyi ba
Ammafa wasu fes za ka gansu babu abinda ya
canja sai abinda ba za a rasa ba. Jin motsi nayi
da kyar na juya sai naga Ustaz tsaye abayana
yana doka murmushi da alamun . tsananin farin
ciki a fuskarsa "Ayshatu My Angel, albishirinki?"
Cikin kaguwa da son sanin mene ne nace "GORO
fari katoto."madadin ya fada sai ya miko min
hannu,"kama ni kitashi ki ba ni goron" Na waro
ido sosai Ya kuwa tuntsire da dariya "Ayshatu kin
yi kyau sosai da cikin nan." Harara na watsa
masa don na san tsokana ta yake yi sannan ya
cigaba da wakar da yake min "'yar beauty mai
katon hanci 'yar beauty mai katon lebe." Gaba
daya na shagwabe fuska nace "Kaga ka ga Ustaz
ba na so" Shi ma kwaikwaya ta ya yi "Kin ga -
kinga aysha ina so" Na wurge shi da pillow ya
cafe yana murmushi hade da min wani fitinannen
kallo "I LOVE YOU MY WIFE. Kin shagaltar dani
ban gaya miki albishir din ba MAMINKI TA
HAIHU" Da sauri na mike "Amma ka tsaya kana ja
min rai me ta haifa tashi ka kaini" Cikin mamaki
Ustaz yake kallona yace aysha ashe da kwarinki
kike langabewa, dubi yadda kika tashi ahanzarce
daga sanar da ke haihuwar Mami" Na kwabe
fuska nace Don Allah katashi ka kaini" Babu
musu ya mike ya zira min hijab dina . Muka fice
daga gidan sai da muka shiga mota ya ce "Ba ki
ji me ta haifa ba" Na ce metahaifa? 'yan biyu
duka mata "SHUKURAN LILLAH" Nafada afili.
Ustaz ya saki murmushi yace su aysha anyi
kanne Da hawayena na shiga gidanmu ina
tunanin ashe za mu ga wannan lokacin aduniya
Tabbas Bahaushe bai yi karya ba da yace
Mahakurci mawadaci kuma BAYAN WUYA SAI
DADI. Na zauna a gefen gadon ina kallon mamina
da fuskata cike taf da farin ciki sannan ahankali
itama hawayen ya zubo mata. Umma ma
hawayen take Tace "kukan farin ciki kam ya zama
dole. Allah kenan da ba ayi masa dole shiya ke
ba da haihuwa alokacin da yaga dama" Na dauki
'Yan biyun ina kallo kamar mu daya da su sak.
Wallahi tamkar yadda nake ina yarinya Da sauri
na dauki hotona babba da yake rataye a dakin
mami na kara a fuskarsu. Cikin dariya mami tace
"Ba saikin kara ba, kamar ku daya" Abba yace
"Kwabo da Kwabo kuwa" Aka kwashe da dariya.
Kafin a ce Mene ne wannan? tuni gidan mu
yadinke da hayaniyar jama'a 'ya'ya da surukai da
jikoki. . Kafewa na yi anan zan kwana, amma
Abba ya ce tilas na tafi gidana na dawo washe
gari. Amota Ustaz yake sanar da ni wai bizarmu
tafito jibi za atafi Ni kuwa na zabga masa harara
cikin wasa nace "Ai kai ma ka san ko birnin
Lantsandan ne ba zan tafi ba ayi suna ba." "Kada
muyi haka da,ke aysha kin ga watan haihuwarki
ya kama, tun da dai ta haihun lafiya ba shikenan
ba" Allah Ustaz kada ma ka fara don babu inda
zani sai anyi suna Shiru yayi na lura ransa ne
yabaci duk da haka bazan sauka daga kan
ra'ayina ba.Har mukaje gida bai kula ni ba illa
yadebo min abinci ya ba ni a baki harda tausar
da ya saba min magana ce dai ta fatar baki ta
gagara. ***** ***** ***** Tsakar dare naji bayana
yayi wani irin amsawa ba shiri.Na mike jin
marata ta amsa. Na daka wa Ustaz duka,shima a
razane ya farka, yana duba na yace "aysha
lafiya?Me ya faru?"Da kyar nace masa "Mutafi
asibiti yallabai, marata kamar za ta balle" Da
azama ya daukeni cak inata gumurzu Iya mai yi
mana aiki da ita muka tafi asibitin. . Tsawon awa
guda a asibiti ina abu daya kafim Allah ya yanke
min na haifo santalelen yarona jajir da shi, gashi
har gaban goshi da kibarsa dumimi tamkar diyan
indiyawa. K da idona ya haskomin yaron anfita da
shi wani farin ciki ne ya mamaye ni na tuna wai
wannan da na ne mallakina kai Allah na gode
maka "Alhamdulillah" na sake furtawa ahankali.
Ahmad na ga yaturo kofar yashigo bayan da
likitar tafita Cikin tsananin farin ciki ya dube ni
yana da fa goshina"sannu ayshata da wahala ko?
Ubangiji yasaka miki da mafificin alheri. Ayau na
sake alfahari nakasan cewar ki matata da kika
santalo min kyakkyawan da" Daidai lokacin
Umma da Mami suka shigo mamaki ya kama ni
ganin mami ita da ta haihu jiya amma tafito
yau.Lallai na amince soyayyar gaskiya ce
tsakaninmu kowa sannu yakemun, Maman Ahmad
ta zo kafin asallatu asibitin yacika dan kam da
'yan'uwa da abokan arZiki Ahmad,kuwa sam
bakinsa yaki rufuwa. Humaira ta dubeni cikin
murmushi ta ce, "Aysha sis yaron nan da Ya
ahmad yake kama ko kadan bai dauko ki ba
Lumshe idoovels / NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:35 . Kawai nayi ta sake cewa "Ya aysha haihuwar da wahala? Wata dariyace ta kufcemin ganin ta da turtsetsen cikinta nace "Ba bayani yarinya sai ranar da kikazo yin taki sannan zaki gane shayi ruwa ne." Murmushi tayi tace tana shafa cikinta "How I wish na bude ido naga babyn.Kawai akwance a gefena batare da na sha wahala ba yana inya inya." Gaba dayan dakin aka saka dariya ganin yadda Humaira ta tsorata sosai Mamina ce ta shigo bayan ta dawo daga wajen likitan mace jaruma tamkar ba ita ce ta haihu ba Ta miko min hannu hade da cewa "Mike mu tafi na amso sallama" Dakyar na mike don jikina kam bai karasa warwarewa ba, duk inda nabi idon Ahmad a kaina "sannu aysha" shine kawai Kalaman da yake jerowa "Hope dai ba inda yake miki ciwo" Na lumshe idona hade da kada kaina koda mukaje gida Hajiyar potiskum ce ta tilastawa Mami tafiya gida fada take tana sakewa "Maza yar albarka ki tafi gida kema fa danya ce sharaf." Murmushi Mami kawai takeyi ganin yadda hajiyar potiskum take nuna mata kulawa hakan ya tabbatar Mata da dinma . bacin rai.Yasanya ta wanke kafa taje har gidansu taci zarafinta. To haka dai 'yan'uwa suka dunga nunamin kulawarsu. An yanke shawarar hada sunana da taron sunan Mami za ayi.Inda za ayi ababban hall dina wato AYSHA IMAM KHALIL {A..K RESTAURANT}. Ranar sunan da safe Ahmad ya sanar da sunan mahaifinsa aka saka wato,Sulaiman, hakan ya sa Humaira ta yi masa lakabi da AKBAR. An taru sosai ashagalin taron sunan. Manyan mutane sun halarci babban shagalin inda 'Ya'yan Mami suka ci suna NILFA da NAUFA. Sunan Mamina da ummana aka saka Mun samu kyaututtuka sosai daga manyan mutane Ustazu na kuwa yana makale da ni tamkar wani zai kwace masa ni. Tsummun idanunsa suna kaina. Daren ranar sunan Ya Ahmad ya sameni adaki azaune agefen gado na jingina da gadon ina lumshe ido tsabar gajiya ce take nukurkusata Akbar nake bawa mama. Fuskarsa adaure yake dubana Yana fareti atsakar dakin hakan ya dan razana ni. Zuwa can ya zira hannu a aljihu ya miko min ambulan fara tas. Gabana ne yafadi , narintse ido na ba ta re da nakarba ba . A zuciyata nace "shikenan an kuma" karbi mana yana fada cikin dakakkiyar murya da tsawa Hannuna na rawa na karba na bude Addu'a nake kafin na karanta. Abinda na gani ne yasaka ni mikewa ba shiri "Ni kuma da gaske Ya Ahmad? Ka ba ni kamfanin sarrafa shinkafa?" Dariya ya saki yace "Da tsorata kika yi My Angel?" Na zube gwiwa ta akasa ina sake godiya. Ya dago ni "Is enough Aysha, duk abinda nayi miki kin cancan ci fiye da hakan. Da ni da dukiyata duka mallakarki ne. Na yi miki wannan kyautar ne saboda jajircewa da kike wajen yimin biyayya akan duk abinda na umarce ki. Kin cancanci sunan MACE TA GARI, MACE MUMINA mai share hawayen mijinta a kowane,yanayi wanda hakan yayi karanci awannan zamanin da mata suke daukan kansu sune a sama bayan Ubangiji yace "Arrijalu kawwamuna alannisa'u" Ya Zama dole mace tayarda itace akasan mijinta shine shugabanta, wanda matan yanzu sundauki hakan rashin wayewa da gidadanci BURIN MACE A ce ita take juya mijinta awannan zamanin babu asarar da ta wuce hakan. Ba wayewa ba ce hakan . illa dabbanci da tabewa hade da rashin zurfaffan ilimin addini. A bayyane take macen da ta ke aikata hakan tana jayayya da hukuncin Ubangiji ne da kuma koyi da yahudu da Nasara. Da suke cewa "What man can do woman can do better". Karya ce wannan da tsagwaron jahilci.shi ya sa nake godewa Allah da ya tsame min matata daga sahun wadannan mutanen. Bayan wannan, yanzu fada min abinda kikeso." Na lumshe ido nace "Babu abinda nake so ka gama yimin komai yallabi sai abu daya kayimin Alkawarin ba za ka taba yimin kishiya ba." Cikin murmushi yace "Na yi miki alkawari Aysha ke kadai kin isheni rayuwa." Hawayen dadi ya sulmiyo min don Burina yagama cika nace . "ALHAMDULILLAH"