Showing 18001 words to 21000 words out of 22537 words
Ummana Da sauri na isa
garesu ina niyyar durkusawa mama tayi saurin ka
ma ni tace "Barshi Aysha ba sai kindur
kusa,ba".Taraba ni da jikin tana sakarmin
murmushi Ta ce Ya jikin naki? Ustaz yace kinsha
jiki" Na sunkuyar da kai cikin matsanan ciyar
kunya Yaya usman ne ya karaso wajen yana
murmushi.Yace Aysha ina mijin naki? . Alhaji
maitumbin Nair? Na wurge shi da hararar wasa
duk gurin aka saki dariya Humaira Sis tace "Wai
har na hango Aysha sis lokacin da take muzurai
zan aure mata miji" Na kaimata duka da sauri ta
buya a bayan maman Ahmad tana fadin "Taimake
ni mamanmu" Duk gurin dariya ake haka muka
rankaya aka shiga motoci da niyyar raka ni gida
Tunda aka bude wawakeken gate din nake kallon
gidan nawa da na yi wa lakabi da Aljannar duniya
Titine fetal, kafin ka shiga cikin harabar gidan
Shuke- Shuken da suka kewaye gidan sun
matukar kawata shi. Kana shiga harabar gidan
daga gefen da aka yi wani hadadden parkin space
sai daya gefen da akayi wani hadadden garden da
yaji grass carpet da kujeru masu lilo kala-kala sai
fitulu daga can ciki kuwa wani babban
Swimming,pool ne sai tsuntsaye kala- kala masu
kyawun launi da suke ta yawo ciki kuwa harda
aku da dawisu Gurin ya kawatu sosai Zaka hango
wani step.Da wawakekiyar kofa sai karfe da ya
zagaye wajen nan ne harabar gidan. Kina shiga
kofa falone mai girman gaske sai kofofi guda 4 .
Duk wacce kika bude falo ne guda biyu daya cikin
daya sai bed room guda daya da kitchen, A
babban falonma akwai wata kofa idan kika bude
babban kitchen ne da ya hada kaya na al'farma
akwai kofa a kitchen din da bukkoki guda uku
masu kyawun fasali da kuma Swimming,pool
haka tsarin gidan Ustaz tabbas gidan ya yi kyau
matuka da gaske. Ina gefe jikin mamina ina
kallon Humaira da su Jamila da A.Khadija da
suke hada-hadar zuzzuba abinci suke kayatacci
yar Walima suka hada mana ta murnar
dawowa,lapiya Ni ba ta abincin nake ba so nake
kawai na kebe da Mamina don haka na ja
hannunta nace "Mami dan zo kiji" Wani
kayataccen daki muka shiga Mami fadi
take"Alhamdullahi, yanzu duk wani burina ya cika
Aysha ta yi aure a inda ba za ta wulakanta ba" Ni
dai murmushi kawai nake saki na zauna agefen
hadadden gadon Mami kuwa stool ta ja ta zauna
"mene ne wai kika rabo ni daga cikin mutane kika
kawoni nan?" Na shagwabe fuskata nace "Mami
tambarki zanyi, Inajinki sarkin shagwaba Ashe
haryanzu wannan halin naki yana nan"UWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 16
NAGA RAYUWA book 3 part 16
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:29
. Na yi murmushi nace "Mami don Allah anmayar
da aurenki ne?, Taza ro ido tace Da wa? Na kara
bata fuskata kamar karamar yarinya nace Da
Abba mana A'a tace min Hawaye ya fara zubo
min shikenan murnata ta koma ciki
Ashe,hasashena bai zama gaskiya ba sai da ta
bari na yi kukana mai isata sannan ta tuntsire da
da dariya tace BURIN AYSHA MAFARKIN AYSHA
YA CIKA NA KOMA GIDAN ABBANTA" Yeeeeh?
yeeee'" Na saki ihu harda tsalle akan gado na ce
"Alhamdulilla,mamina how comes?" Ta gyara
zamanta kafin tace "Kawai dai na gaji da zarya da
aiken da Abban-Aysha yake min hakan ya sa
babana yace lallai sai na komo gidansu Aysha
dama wani course naje na wata hudu ina
dawowa babana ya mayar da aurenmu ba tare da
sanina ko neman yardata ba. Sai bayan komai ya
daidaita Ya kira ni ya sanar dani tilas na koma
gidansu Aysha ba shawara yake ba ni ba umarni
ne amatsayinsa na babana. "Haka na hakura ba
koma bayan tarin hakuri da NADAMAR ABBAN
AYSHA" Nayi murmushi na share hawayen dake
Zubo min bayan nagama sauraren bayanin
MAMIN AYSHA . Cikin zuri'ar GIDAN SU AYSHA.
Mami.Tashare min hawaye hade da cewa Na sani
duka,zuri'ar gidanku suna so na illa shaidan da
ya so ya ruguza dukkan farin cikinmu Tun lokacin
da abin yafaru na tabbatar da cewa dole,Abbanki
ya shiga rudani har ya zartar da BAGAGON
HUKUNCI akaina Banga laifinsa ba sam don ko
waye zai iya zargin da hannuna dumu-dumu a
ciki musamman yadda al'amarin yazo da
sarkakiya, acikinsa. Tilas kowa ya jefa ayar
tambaya akaina, duk da hakan ya jefani cikin
tashin hankali ganin yadda mutane suke, kallo na
ahagunce. Hakan ya sosa zuciyata abu daya da
ya burgeni ganin yadda Ummanki sam ba ta
amince da hakan ba. Hakan ya tabbatar min da
nagartar Umma" Na ja ajiyar zuciya bayan
sauraren jawabin Mami Daidai lokacin Humira ta
shigo, da tsallenta turus tayi sai kuma ta juya ta
na dariya Mami ta kwala mata kira Ba ta dawo
ba illa amsa mata da ta yi tana cigaba da
magana "Babu maishiga tsakanin uwa da 'ya
dama Abba ne yace na kira masa amaryar sa
suci abinci" Baki Mami tabude sai kuma ta saki
murmushi . Tace "Mhn..Aysha wannan kanwar
taki, da rawar kai ta ke amma Ummace take sake
sangartata yarinya an mata aure amma koda
yaushe sai taxo gida don tabara" Nace mami ai
baki ga komaiba da bakya nan ba ki gani ba ko
da yaushe Umma nanika ta take ajikinta wai ta
sami gatan daba ta, samu ba Mami tace Umma
ba ta da zance sai na Humaira yanzu tunda ta
fuskanci ta na da ciki sai al'amarin ya bunkasa
koda yaushe bakinta ba ya gajiya da fadin Allah
sarki humaira Allah yaraba lapiya Yauwa da
gaske kema Aysha juna biyun gareki?" Wata
kunya ce talullubeni na sunne kai na ajikin mami
ina dariya Mami ta dago da kaina ta ce "ke tsaya
wani kike jin kunya.?" Idona na rufe na daga
mata kai, Mami tace, Ba shakka amma fa aiki ja
Ya sameki 'ya najin kunyar uwarta shige muje mu
ci abinci." Ustaz ya na ganin mu ya taso ya tare
mu yana kallon mami yace "Amaryar Abba tun
dazu Abba yake aikawa a kira ki" Ya fada yana
kunshe dariya Mami ta girgiza kai tace "Lallai
Ustaz har da kai kenan kun mayar da ni kakar ku"
Gabadaya aka dau dariya . Mamy ta zauna
akujerar da take kusa da Abba aka fara cin
abinci. Sai karfe 8:00 na dare kowa ya baje sai ni
kadai don Ustaz ya tafi shopping.Sai alokacin na
fara jin tsoron gidan musamman da na ji motsin
kofa aibansan sanda na kudundune jikina ba
Hankalina bai kwanta ba har sai da naji sallamar
Ustaz jikinsa asanyaye ya zube ledojin da suke
hannunsa ya zauna agefen kujera ya kuma zuba
uban tagumi da duka hannayensa idonsa a
lumshe. Da azama na mike na isa gareshi na
durkusa gabansa Dafa gwiwoyinsa na yi nace
Lafiya Ustaz.? Baibude idon ba illa ya matse
hannayena cikin nasa Tsawon lokaci kafin ya
bude idon. Araza ne,nadu be shi ganin yadda
idonsa ya,yi jajir nace "Na shiga uku Ustaz waye
ya mutu?" Ya hau girgiza kai "Ni namutu Aysha
wallahi na kashe kaina Bansan dalilin da,ya sa
mama ta tilasta min auren Hameedah ba Aysha
ba zan iya adalci tsakanin ku ba wallahi yau daya
da zanbarki ba kiji yadda zuciyata take bugu ba
ba na son nafada halakar Ubangiji don kuwa ya
umarce mu da muyi adalci atsakanin matanmu. .
Ya sanar damu idan har ba za muyi adalci ba
kada ma muyi biyun Aysha bazan iya adalci
tsakaninku da hameeda ba ya ya zanyi? ya sake
runtse ido Ni kaina hankalina yayi masifar tashi
don wallahi na manta da wata Hameeda Yanzu
kenan Ustaz raba mana kwana zai sunga yi?
Zaidunga zuwa da kin wata ba niba Zan bude ido
wata rana naga babu Ustaz agidan nan yana can
wajen wata yana nunamata soyayya kamar yadda
yake nuna min? na rintse idona kai ni ma wallahi
bazan iya ba ban san lokacin da na fara kuka
wiwi ba Ustaz ma kukan yake yi ahankali yana
kuma bubbuga bayana alamar rarrashi. Daidai
lokacin wayarsa tayi kara alamar ana kira Amma
Ustaz yayi banza da wayar sai ni nasa hannu na
dauka "MY WIFE 2" Naga an saka da sauri na
ajiye masa wayar akan cinyarsa na kuma mike
nashige daki da gudu Na fada kan gado tsawon
lokaci sannan Ustaz ya biyo ni ya tsaya abakin
gadon ban san me yake tunani ba har zuwa
lokacin da ya hawo gadon ya dago fuskata na
rintse Ido "Ta shi Aysha magana zamuyi" Na
bude idona . "Kiyi hakuri kowa da irin tasa
kaddarar mu.Tamu kaddarar kenan Zan tafi ga
wata dattijuwa nan da zata tayaki zama a falo na
miki kiyi ta jan Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
Zan leko nagan ki gobe tunda sai jibi zandawo
nan Da kudi a drawer dakina ko zaki bukaci wani
abun" Rintse ido na sake yi na fashe da kuka
hade da damke hannunsa kada katafi Ustaz
wallahi in ka tafi zuciyata zata,iya fashewa.
"Babu abinda zuciyar ki za tayi Aysha don ba
akanki aka fara kishiy ba kiyi Nazari da hakan..."
Ina kallo Ustaz yajanye hannunsa ya tafi Wani
kukan ya sake kwacemin shi kenan ya tafi
wajenta A yau ba Ustazun Aysha bane Ustazun
hameeda ne kuka yaci karfina sosai tabbas kishi
bala'i ne sai a yau na sake jaddada hakan Ni ce
har karfe ukun dare ina kwance a haka sam na
kasa rintsawa Juyi kawai nake akan gadon ina
hango fuskar Ustaz yana ta zanga wa hameeda
soyayya kamar yadda yakemin na sake rintse
idona still hakan nake,sake gani Kawai ji nayi ina
furta kalmar"Na shiga uku yanzu haka zanyi
rayuwar aure da Ahmad duk . Sanda zai tafi gurin
wata? Na ji kamar zan mutu Anya hakan zata
yiwu? Na dau wayata ina duba lokaci karfe
3:00na dare na ga ni Ban ji shakkar komai ba na
danna lambar mamina da niyyar kiranta Tsawon
lokaci tana ringin kafin Mamina ta dauka ji nayi
tace Aysha lapiya Atsahon daren nan? Cikin
shisshikar kuka nace "Mamina na kasa barci
zuciyata ciwo take ga kaina yayi nauyi Cikin
kidima itama Mamin tace "Subhanallah! Shi Ustaz
din yana ina?ya barki baku tafi asibiti ba?" Na
sake sakin kuka da karfi nace Mami ya tafi
wajenta Cikin kidima itama Mamin tace ita wa?
Na ce Mami Matarsa mana hameeda"Mami
tasaki nannauyan ajiyar zuciya tace "Wallahi
kinbani tsoro Idan na fahimci matsalarki Aysha
kishi ne ya kamata kuwa ki ajiye shi agefe duk da
ansan yana da ciwo amma yana zuwar wa
mutum a inda mutum yadau keshi idan kadau
keshi da zafi zaizo maka da Zafi, idan kuwa
kadau keshi da sauki sai ya zo maka asaukake
Don haka inaso ki dauke shi da sauki please and
please Aysha ki yi koyi dani da Ummanki, kada ki
ba mu kunya"
A novels / NAGA RAYUWA book 3 part 17
NAGA RAYUWA book 3 part 17
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:31
. Na rintse ido nace"wallahi Mamina bazan iyaba,
kowacce mace da yadda Allah yayita ni Allah
yayini acikin mata masu tsananin kishi Ba zan
Iyaba mamina"Cikin tsawa mami tace "Zaki iya
aysha kowacce mace koya take har ta saba.
Haka ke wacce irin yarinyace mata nawa aka
yiwa kishiya suka zauna lafiya..." Fashewa
dakuka nayi ganin yadda Mami ta harziko Cikin
tattausan lafazi mami tace "aysha saurare ni kiyi
shiru haka maza ki tashi kije ki yi alwala kiyi
sallah zaki samu sauki azuciyarki kinji?maza
tashi aysha." To Nace sannan nabi shawarar
mami na mike nashiga toilet cikakkiyar alwala na
daura ina fitowa na fuskanci alkibla ina sallah ina
hawaye acikin sujjada na dade ina kaiwa Allah
kukana akan ya yaye min wannan matsanan cin
kishi koda na gama agurin na kwanta ina mayar
da ajiyar zuciya Tabbas wallahi kishi ciwo ne
babu maganinsa sai addu'a bansan lokacin da
barci ya daukeni ba Karar waya ne ya farkar dani
daga nannaiyan barcin da ya dauke ni ina kai
dubana kan screeb din wayar naga sunan
REALITY ya bayyana. . Na san Ustaz ne nayi
tsaki naduba agogo karfe 5:45 yaje
yasha,soyayyarsa da barcinsa sai yanzu ya tuna
dani. idan har ya damu dani meyasa bai kirani ba
tun jiya? Gaba daya kashe wayar nayi namike
nashiga toilet Ko da na idar da sallar barci ne ya
sake yin awon gaba, dani akan sallayar. Shafar
fuskata da naji anyi shi ya sa nabude idona.
Ustaz ne zaune agabana ya zuba min ido cikin
tausayawa Ban mike daga wajen ba illa ma
dauke, kaina da nayi daga kansa na sake lumshe
idona Ji nayi yasaki ajiyar zuciya yace "Aysha kiyi
hakuri please ban san yadda zanyi ba Ni kaina sai
ajiya na sake yarda ba Zan iya adalci
atsakaninku ba Ina tare da hameeda ne kawai
amma ruhina kacokam yana kan aysha ko da na
kwanta juyi kawai nake ina tunaninki Gashi ba
damar kiranki don ina tare da ita Zai zama kamar
cin fuskane" Sake tunzira zuciyata yayi jin yace
wai yana tare da ita Wato yana sanar da ni tare
su ka kwana a daki daya. Yakamo hannuna tashi
Aysha ba dai anan kika kwanaba akasa." Na
dauke kaina cikin tsiwa nace "ina ruwanka . dani,
tunda kai kayi kwanan farin ciki ka kwana a
luntsumemen gado tare da farin cikin ranka Ajiyar
Zuciya ya saki sannan ya saki murmushi yace
kwantar da hankalinki MY ANGEL! Daga yau
Ahmad ya zama naki ke kadai banbar gidan ba
sai da NA SAKI HAMEEDA Wai don gulma kuma
sai nazaro ido nace Saki? Ustaz why? Yalakuce
min hanci "Kaji gulma Natabbatar har zuciyarki
cikin farin ciki kike" Na girgiza kai "Ko daya
Ustaz, ko ba komai Hameeda mace ce yar uwata
ba zanso abinda yafaru da ita yafaru daniba me
ya sa, ka sake ta Ustaz? Da ka barni ahankali
zan saba", Ahmad ya dangirgiza kai "Ni ba zan
saba ba Aysha, sam ba zan saba da rashin adalci
ba koda Allah yace mu auri mace sama da daya
saida ya umarce mu da muyi adalci. Idan nakasa
adalcin me kike zaton zai faru dani? tashi fa,zanyi
ranar lahira da shanyayyen barin jiki Me ya fi
hakan takaici? shiyasa na amince rabuwar mu
shine mafi alheri Tun daga mota da na fita, raina
abace yake har naje gidan babu fara'a afuskata
Hameeda na da kirki tatareni da abinci amma .
wallahi ko fuskarta ba na gani Kece kawai acikin
idona Har muka kwanta na kasa yi mata kulawa
irin ta aure duk da na lura da bukatarta kenan
"Shiyasa da safe na yanke shawarar rabuwa da
ita bayan na mallaka mata makudan dukiya da
gidaje sannan muka rabu kuma ta min
kyakkyawar fahimta haka iyayenta ni ma su
Abbana ba su yi fushi da ni ba don haka Ayshata
takwantar da hankalinta Ahmad na tane ita
kadai" Da safe na ga Mamina da ummana
mamaki ya kamani ganin, dukansu fuskarsu
ahade take gabana ya,shiga faduwa har ina hada
harshe wajen fadin "Lafiya Mam?" Ai kuwa ta
aiko min da wata harara hakan yasa na gumtse
bakina Cikin fada Umma tace "kin kyauta Ayshatu
saboda bakin kishinki shine kika sa sai da Ustaz
ya saki matarsa" Da sauri na zaro ido nace "Ni
kuma? wallahi Umma ba ruwana" Mami ciki zafin
rai tace karya kike Aysha ya mukayi dake jiya?
Babu ruwanta mami nida kaina na saki Hameeda
saboda ba na daga cikin wadanda za su iya rike
mata biyu. Bazan iya adalci atsakanin wata
macen da aysha ba dakai na nayanke . Shawarar
sakinta" Haka ya zauna ya dunga fahimtar da su
har suka fahimta Mami tace "Dama Abba ne yace
mu zo muyi mata fada, zata da hadin bakinta
amma yanzu mun fahimta, hakan shine adalci, a
wajen duk maza da zasu fahimci rashin adalci
babbar masifa da sun rabu da auren mata
matukar suka san ba za su iya adalci ba"Daga
haka suka mike Ustaz yace "Umma har zaku tafi
Tace "Dama abinda ya kawo mu kenan don
hankalin Abba ya tashi da ka sanar dashi ka rabu
Da matarka ya zata laifin Ayshatu ne" Ina kallo
suka shige motarsu suna daga min hannu sai a
lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo min
tunanin duka al'amuran duniya yanzu ni zasu
zarga Ustaz na ji ta bayana ya hada ni da jikinsa
ya ziro hannu yana share min hawaye "Mene ne
na kuka My Angel? please stop it, I hate to see
you crying." Cikin wata salon murya yasanar dani
haka sannan yaja ni cikin gida yana sake
jaddada,min zazzafar kaunar da ya sabar dani
Ranar da nayi sati biyu da tarewa agidan
gwarzon mijina Ustaz Ahmad Sulaiman da wuri na
tashi, . Na fara shiri don zaikaini ziyara.Zuciyata
cike da farin ciki don na dade ban fita ba, saboda
Ustaz ba ya son yawo don haka ya rokeni ma
nabar zancen karatu don shi sam ba ya sha'awar
koda yaushe mace tana zarya ahanya ya
mallakamin wasu manyan kamfaninsa guda biyu
da gidan mai guda daya duk ya sa aka mayar da
sunana akai. Tsaf na fito cikin wata hadaddiyar
doguwar riga zubin misra, kalarta yelo ma adon
ja. Na yi rolling da jan mayafi na yi kyau sosai,
abinka da mai shigar karamin ciki fatata ta yi
subul-subul tamkar bayan kifi don santsi Gidansu
muka fara zuwa, nan na ga soyayyar surika ashe
kawai surukai masu kirki. Mahaifiyar sa ta
rungume ni sosai ajikinta da kanwarsa Khadija ita
ma nan da sati biyu za ta amarce. Kayan motsa
baki kala-kala mama ta sa aka ajiye min.
Nakuwa ci sosai don kayan kwalama ne Sai
la'asar sannan muka bar gidan Daga nan kuwa
gidan Humaira muka wuce, don babu nisa sosai a
tsakaninsu.Humaira sarkin rawar kai sai tsalle
take da murnar ganina mahmud yana gaisheni ta
cafe da cewa . "Darling ba kace ya bebinta ba"
Da sauri na zabga mata harara "Wallahi Humaira
sam ba ki da kunya" Ta tsuke baki "To kunyar wa
zanji a nan mahmud ko Ya Ahmad?" Nayi tsaki
hade da mikewa na kalli Ahmad ya hade rai tsaf
wai shi yazo gidan kaninsa. Dariya ta so kubce
min don sam hade girar bai karbe shi ba Sai da
muka shiga mota na tuntsire da dariya nace
"Yaya babba manya, irin wannan tsare gida
haka?"Murmushi yayi yace "Usainan nan taki ce
akwai rawar kan tsiya" Duka gidan yayyena sai
da Ahmad ya kaini abinda ya ba ni mamaki bai
wuce yadda suke zaman lafiya da kishiyoyin su
ba tamkar 'YAN'UWAN JUNA. Na ayyana
azuciyata Da ni ce bazan iya ba. Daga nan sai
gidanmu karkaso kaga yadda na yi tsalle na
rukunkume Mami Umma ta dakamin Tsawa tace
"ke cikata ku har abada daga ke har uwar taki ba
za kuyi hankali ba, bayan ga yadda kuke ita ma
ba lafiyace da ita ba." Na waro ido ina kallon
umma cikin mamaki na ce "Mamin? Dubifa yadda
tayi kiba Umma, amma kice ba ta da lafiya?"
Umma ta gallan harara To uwar maganaUWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 18
NAGA RAYUWA book 3 part 18
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:32
. Kibar tata ce miki aka yi ta lafiyace? Duk da
ban so gaya mikiba..." Cikin magiya Mami tafa
rokon Umma wai kada a gayamin na kuwa zaro
ido nace "Na shiga uku me kuke boye min wane
irin ciwo ne da,Mamina?" Ni sarkin hawaye tuni
na sake su kamar famfo Umma ta saki salati tace
"Yanzu Ayshatu kuka kike ke kam zanga lokacin
da girma zaizo miki" Cikin shesshekar kuka nace
"Don Allah Umma me ya same ta?" "Cikine da ita
sai ki taya ta da addu'a."Aikuwa ban san lokacin
da na saki dariya ba kuka yakoma dariya cikin
tsananin farin ciki na sake rungume MAMINA in
cewa "Alhadulillahi Allah na gode maka,da ka
amsa min tawa addu'ar Allah ya raba su
lafiya."Umma ma cikin fara'a take cewa "To me
ye na kukan aikin gama tun da kika godewa
Allah" Nace wallahi Umma kukan tsananin farin
ciki ne ni na sani Umma yau wallahi ba zan iya
barci ba." Umma Tace "Na sani aysha Na sake
cewa "Da fa na yanke shawarar da zarar na haihu
zan dankawa mami abinda na haifa ta raine shi
kamar yadda ta yi min Allah na gode maka Umma
tace Shine abin . Godiya Sai da na bugawa Ustaz
waya atake agurin. Cikin dariya nake shaida
masa