Showing 1 words to 3000 words out of 22537 words
Home / NAGA RAYUWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 1
NAGA RAYUWA book 3 part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:53
Adakata! Adakata! mukaji wasu yansanda suna
fada daga bakin kofa,inda hankalin kowa yakai
kanasu mata suka shigo dasu su 8 fuskarsu
sanye da mask jikinsu kayane bakake daya daga
cikin sojojin yaje gaban teburin Alkali abbana
yace yamaigirma mai shariah hakika anyi kuskure
wajen tsare wannan baiwar Allah ba ita
akenemaba bawannan bace wacce ake zargi
yanunani wani farin ciki ne yaxiyarceni hade da
madaukakin mamaki daga can naji yan uwana
suna furta Alhamdulillah. . ni ma sai alokacin
nafurta Alhamdulillah cikin muryar data dashe
alamar kuka dansandan yaci gaba dabayani
hakika kamanni ne sak kwabo da kwabo da ita
wacce ake neman maitsanin kama wanda Allah
yabayyana tsantsar ikonsa akansu ayau muka yi
dacen cafkesu acameroun zasu hau jirgi sutafi
south africa yallabai ita wannan itace ainihin
wacce ake nema yafada yana nuna wata daga
cikin matan dasuka shigo dasu cikin daka tsawa
ya umar yace ke bude fuskarki! yakwada mata
kulki Araina nace karamata shegiya kinsaka ni
abala'i iri-iri dazafin nama tasaka hannu tayaye
rigar fuskar da take fuskarta kafcecen bakin gilas
ne a fuskartata amma hakan bai hana ni ganin
fuskarta ba . yadda kasan tawa fuskar aka dasa
ajikin tata tasaka zara zaran hannunta tacire
gilass din tayi wulli dashi tana ciccizon bakinta
kaidaganinta ka ga wacce bata shakka,duk abinda
zaibiyo baya bani kadaiba duk mutanen wurin
cikin matsanancin al'ajabi suke kallonmu ni kaina
nazare ido kawai nake ina nunata itama kuma
nuna ni take fuskarta dauke da tsananin mamaki
to wai yatake ne? mai shari'a alkali abbana ya
razana balle ummana data kasa zama bakinta
sosai yake bude ta ma kasa rufewa don tsananin
mamaki na raya araina "Tabbas hukumullah
la'ajaban". . Bayan tsawon mintoci da dakin
shari'ar yabakunci hayaniyar mutane alkali
Abbana yamayar da glass dinsa yakuma dakatar
da surutun ta hanyar buga gudumar kotun da
karfi nan take kowa ya,nutsu aka kuma kasa
kunne don cigaba dasauraron shari'ar kowa
yanason sanin dalilin wannan matsanan ciyar
kama tamkar irin yaran nan yan biyu masu kama
daya kamar kwabo da kwabo . da bature yake
kira IDENTICAL TWINS.Abbana ne yadubesu
dukkansu sannan yamayar da kallonsa akan
carbon copy{mai kama dani} "baiwar Allah
konace bayin Allah dagaske ne kune kuka yiwa
minister sata bayan yaudarar sa dakukayi kuka
kaishi hotel kuka bashi maganin barci bayan yayi
barcin kukayi amfani dawannan damar kuka dauki
hoton tsaraicinsa ma'ana kuka daukeshi tsirara
kuka kuma watsawa internet don ku bata masa
suna bayan kun masa awon gaba da kudadensa
dalolin amurka? kodayake kafin nan zanso nasan
sunayenku sunan uba ko wakili jiha ko unguwa?"
Abba yafada yana duban su gaba dayansu suka
shiga kallon junansu daya bayan daya sannan
suka nuna mai kama dani da alama,itace zata
wakilcesu ba tare da tsoron komaiba tawani
watsa hannayenta tayi far-far da idonta "sunana
SHANY,haka nataso agidan dana rayu naji ana
kirana Aisha ne cikakken sunana sunan uba ko
wakili kuwa bansan ko daya daga cikiba ko kuma
nace bani dashi sam..." . Gaba daya naga yan
gidanmu sunsake zaro ido sun zubamata Abbana
cikin matukar mamaki yace . "Kamarya ya?
mutuwa yayi ko kuwa sallamaki yayi kika koma
rayuwar bariki?" Tabe baki tayi tare da kada
harshe tace "lala lala,ni yar tsuntuwa ce kamar
yadda wadannan dukkansu yantsuntuwane muna
karkashin kulawar wata mata" Abbana yasake
xuba mata ido yace yar tsintuwa kamar yaya?
inakallon yarinyar sai data dan yamutsa baki da
alama ta fara kosawa datambayar sai dai inaji
kwarjini yayi mata don haka tayi kasa da idonta
tace kamar yadda kasani duk wani dan tsuntuwa
aibashi da sunan daya wuce shege. Dafarko
sunana Shany kamar yadda na sanar tun abaya
muna karkashin wata mata mai suna ATINE YAR
HARKA mutalatin da,biyar ne cif karkashin
kulawarta tunmuna yara tare da wadannan muka
taso wanda dama su sa'annina ne agidan
dukkanmu babu maicikakken asali hakan yasa sai
yadda tayi da rayuwar mu tun muna yara muka
tsinci kanmu acikin bautawa wannan mata
tamkar bayi haka muke agidan kalilan daga
cikinmu take warewa tasaka amakaranta wanda
kyansu yakai kyau ciki kuwa harda ni don tasha
fada wai ni BABBAN JARINTACE. . Nayi
makaranta tun daga nursery har primary da
secondary yanzu hakama ina jami'a tana bani ci
da sha da suturu masu kyau amma fa duk acikin
kudin damuke tara mata! shine kuma hakan baya
samuwa sai yarinya takai shekara sha uku
alokacin dazata ce wai tasan zata dawo mata da
abinda takashe bata sakamu yin karuwanci saidai
tana koyamana dabarun damfara ta yadda zamu
yaudari mutum mukwace dukiyarsa mugudu
yaudarar maza muke yi sosai ta hanyar nuna
tsiraici ma'ana shigar banza wanda da zarar
mutum yayi katarin haduwa damu sai ya fada
tarkonmu saimu yasheshi mugudu club-club
muke zuwa da inda mukasan attajirai da manyan
gwamnati suna zuwa har dai kawo wannan
lokacin da tsautsayi yakaimu muka yaudari
wannan ministan Abinda yasa muka yada
tsiraicinsa kuwa a internet yar'uwarmu yayiwa
fyade..." daga haka taja dankaramin bakinta ta
tsuke alamar bazata,sake cewa komai ba kotu
kuwa tuni takacane da hayaniya mai shari'ah
abbana yayi rubuce rubuce sannan yadago yana
kallonta yanzu ina ita uwar dakin taku take . dan
rausayar dakanta tayi kafin tace tana abuja tun
ranar da abin yafaru tace muje muyi takanmu don
minista yakai abin ga hukuma ita kuma bazata
iya shari'ah da gwamnati ba da dai wanine da ta
tsaya mana har iya inda karfinta yakare abba
yasake gyada kai yace yanzu ina kudin?"yana
wajenta dama ita ake bawa"Abba yasake yin
rubuce-rubuce sannan yadago yakalli jamian
tsaron dasuke wajen "sakamakon kotu takama
yaran da ake zargi da aikata,wannan laifi kotu
tawanke aisha daga zargin da ake mata bisa
rashin sani da akasin da akasamu na
matsananciyar kama da Ayshan take da ita wacce
ake zargin takuma yi umar nin tsare Shany da
yan uwanta tare dakawo uwar dakinsu tahanyar
bin kwatancen dasukayi kotu ta dakatar da
wannan shari'ar har zuwa 1/5/ 2016,alokacin da
muke sa ran ganin wannan uwar dakin nasu ta
bayyana kanta akotu" daga haka yabuga
gudumar kotu daukacin jama'a kuwa suka amsa
da koooootu" . Tundaga nesa nake hango fararen
hakoran ustaz tare da yan uwana da ummana da
suke fara'a saide nayi matukar mamaki danaga .
Idanun mamina jawur alamar tasha kuka Na
ayyana meyaparu kuma?itada yakamata tayi
murna kuma take kuka Nazata zangan ta tana ta
fara'a sakamakon yau mun wanku daga zargin da
akemana tas. . Yau inason ganin mutane dayawa
naga dawanne idon zasu kalleni bayan tarin
abubuwan dasuka faru abaya babu wanda
nakeson gani fiye da,ya usman masoyin gaske
yadda yan jaridu suka baibayeni da tarin
tambayoyinsu hakan yasa na saka kuka don
sanin bazan iya basu amsar komai ba fatana
kurum na hadu da mamina naji kukan me takeyi
ganin bazan basu amsaba hakan yasa suka juya
akalar tambayarsu gurin yan uwana kowa
hamdala yake koda Ahmad yaji labari. . Ni kam
duk basa gabana don dama nafada duk ranar da
gaskiya ta bayyana akwai kallo da yawa Ganin
Abbana yanufo wajenmu yana ta doka murmushi
hakan yasa na sulale na gudu akunnen .ya usman
na rada masa kaini gida.Sweet bros wallahi na
gaji da azama yaja hannuna muka fice daga
taron jama'ar bayan yashigar dani mota yana
murmushi yace Aysha kinga lamarin ubangiji ko?
dama nasanar dake kicigaba . da addu'a dasannu
gaskiya zata bayyana yafada yana jan motar
kafin mu isa gida saida yabiyadani ta shopwrite
ya saya min kayan amfani bayan yafitone
yakalleni Aysha inazan kaikine gidanki kocan gida
kike nufi? wani kallo nawatsa masa "gidana kuma
ya usman?ainagama auren ahmad ai da din ma
don ba yadda zanyine yasa nakoma gidansa
amma yanxu bamai tilastamini wallahi ya usman
dan murmishi yayi yace kibi komai asannu aysha
ta Gum nayi dabakina.Don ko kadan babu
maisakani komawa gidan ahmad yaushe? . ai
wallahi dolene yasakeni awannan karon kam ya
usman yana fakin naga dandazon motocin yan
uwana data Abbana data ahmad da alama tuni
sundawo fuskata a daure tamau nashiga gidanmu
atsaye cirko-cirko da alama suna jiran dawowata
babu wanda nakalla nayi hanyar kazamin dakina
dakin shirgi inda lokutan baya ummata,tace nan
ne makwancina tamkar ba uwata data haifeni ba.
. Inazama Abba yashigo yana dubana cike da
tausayawa,yace . Ayshatu mezakiyi a wannan
dakin dan Allah tashi maza.AGA RAYUWA book 3 part 2
NAGA RAYUWA book 3 part 2
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:55
Bani da damar yimasa musu amatsayinsa na
mahaifina amma wannan lokacin kam sai na dana
naraya azuciyata cikin taushin kalami nace Abba
ina zani ina ce nan din shine makwancina dakuka
za bamin? Abba yadurkusa gabana ya dago kaina
"Ayshatu komai yafaru abaya Inaso kidaukeshi
amatsayin kaddara ma kinki Aysha mu
mahafankine kituna kafin fara abin wanne ga tane
bamu nunamiki agidannanba? . ko wani uba ko
uwa kaiga duk wani maisonki ma dole yaji,yataba
amma ba tsanabace Ayshatu mun yine don
samun nutsuwarki Ayshatu tunda abin nan yafaru
ban taba fashin kaiwa Allah kukanaba akan
yashirya minke...." Wani kukanne ya kwace min
nace "Amma Abba kasani ankuntatamin an
wulakanta ni duk akan laipin daba nawaba Abba
baku taba tausaya minba akullum kallon tsana
nake gani muraran,a idonku babu wanda yaji
tausayina sai Ya usman da mamina da ita ma
aka dora mata laifin da batajiba bata ganiba
yanzu Abba dawane idon za ka kalli mamina?
Abba yaruntse idonsa Nasani tabbas al'amarin
yagirmama azuciyarsa ahankali ya bude idonsa .
"Ba ni da idon dazan kalli fateema Ayshatu
tabbas nayi nadamar abubuwan dasuka faru da
ina da iko dana goge duk abinda suka faru abaya
Ayshatu na zalinceku kiyi hakuri don Allah
kiyafemin duk hakan yafarune akan rashin sani
Don Allah kiyafemin..." Take naji zuciyata
takaraya mahaifina ne yazanyi dashi? tilas na
hakura,kasa nayi dakaina badon banyafe ba sai
don tsananin tausayin Abbana waiyau shine yake
kwantar da murya akaina bayan nidin.Ikonsace
yana da dama ya aikata hakan koma fiye
dahakan komafiye da hakan koda baya zargina da
aikata kowane laifi Balle akan abinda ake kyutata
zaton nice na aikatashi muryata na rawa nace
Abba kadaina rokon yafiyata nidin wacece? . Abar
ikonka cefa? kana da dama ka aikata fiye da
hakan akaina..." Abba yadaga kai yace Na sani
kedin yar albarkace ubangiji yayi miki albarka ya
mike tashi muje dakin ummanki kiyi wanka kicire
wadannan tsinannun kayan murmushi nayi
namike Har a lokacin suna nan afarfajiyar
gidanmu Ahmad sai zabga min murmishi yakeyi
niko kodigon fara'a babu atare . dani na tattare
fuskata nahade dakin umma nafada natarar da ita
a toilet fitowa tayi tana murmushi tace kinshigo
Ayshatu shigo kiyi wanka nahada miki ruwan
wankan cikin tausasawar murya takemin magana
nima tausayi tabani hakan ya sa nace to
ummana Nafada ina murmushi Tunda nashiga
toilet din nake faman dirzar fatar jikina tamkar
Allah ya aiko ni,nacuda yakai sau ashirin gashin
kaina kuwa haka nadunga dirzarshi har umma
tagaji tafara bugamin kofar sannan nabude nafito
umma tace wai! lallai kin dirzu dubi yadda fatarki
harja take murmushi nayi nace Badoleba umma
sai sati fa ake wanka wallahi nikaina har bashi-
bashin kaina nakeji Umma cikin tausayawa tace. .
Mungode Allah de dakomai yazama sai labari
zama nayi agaban dressing mirror din umma
nadau wani Nuetrogena body oil ina shafawa
kasan cewar lokacin sanyine banyi wani make-up
ba umma takawo wata riga sabuwa light Orange
colour mai kyau tabani nasa ni kaina nasan nayi
kyau gawata iska tana kada ni tanashiga kofofin
jikina da kuwa dauda ta cikasu dankwalin rigar .
nadaura akaina sannan na fito falonmu har
alokacin mutane ne dan kam agidanmu dukkansu
yan Zuwa murna Allah yakiyaye gaba ne dai dai
lokacin ya usman yashigo,yanayinsa yanuna
yanuna yana cikin matukar farin ciki yazauna
yana dubana da dan murmushin gefen kumatu
yace Aysha kije inji mijinki wani kallo na zuba
masa nace "Ya usman miji kuma?Aini banida miji
ahalin yanzu umma tadan dubeni tace banganeba
Aysha ya,usman yamike yanafadin "Rabu da ita
umarni nabaki kije yana sitroom yana jiranki
idanma zaku rabu bai kamata kurabu
tahakaba"ban mikeba sai da umma tace Aysha
usman nefa yabaki umarni idan da amana kuwa
usmanu baicancanci hakan daga wajenki ba
dasauri namike jin furucin umma nayi saurin
ficewa tamkar bazanyi sallama sai dai nadaure
nayi sallamar ya amsa idanunsa. . Acikinnawa
fuska ta daure nace masa lafiya malam gani ance
kana kira na yadago yana murmushi hade dacewa
to zauna mana my beautiful wife ba zama nazo
yiba malam inada abubuwan yi acikin gida kuma
kada kasake kirana matarka matarka tana gida .
"Aikin daki ke haryafi kiran mijinki muhimmanci
Aysha? kuma da kikace kada nakiraki matata
yaushe nacireki amatsayin matata?nawaro idona
ina harararsa ko baka cireni ba kwanan nan
zakaji sammaci don wallahi saika sakeni mikewa
yayi ya iso gabana yasunkuya yana duban
fuskata madam dina babu murmushin nan mai
sanya ni nishadi?wai me yafaru ne? yaufa ranar
murnace tsaki nayi nace kadameni madam dinka
nacan gidanka wannan dai Ayshatu ce aysha
mazinaciya,karuwa,maibin yan fashi dafatan
kagane yanzu lumshe idonsa yayi yace please
ayshata forget the past nayi danasani banyi masa
magana ba saima juyawa danayi nashige gida
don kam alokacin ba na maraba da ahmad
sulaiman . Daddare kamar kowanne lokaci muna
zaune ayadda ake zaman cin abinci Abbane
yadubi umma "ina tsammanin wani al'amari game
da yarinyar nan maikama da aysha ina hasashen
ko daga tsatsonmu tafito don tsananin kamar ta
yi yawa kinsan kuma masu kamanceceniya da ita
adangi suna dayawa kasancewar ance dama da
kakarmu suke kama toshi,ne nake hasashen ko
ita . ma jininmuce don haka nake dada tsaurara
bincike akanshari'ar umma ajiyar zuciya tayi
sosai kafin tace ashe bani kadai wannan abu
yadama ba tsananin kamar yayi yawa kamar yan
biyun da ake kira IDENTICAL TWINS sai dai kuma
ai babu wanda yataba rasa yarsa adanginmu
Abba yaja gwauron numfashi gaskiya babu
wanda yataba rasa yarsa akaf zuri'armu ta
potiskum wallahi sosai nakejin yarinyar nan acikin
zuciyata tamkar yata kuma natausaya mata da
ita da yan uwanta matukar.Tausayawa . koda
anbincika ba zuri'ata bace nizan dauketa da
sauran yan uwanta da ba asamu danginsuba
umma tace gaskiya hakan yakamata kayi tunani
mai kyau ubangiji yataya ka riko nikuwa nasan
zancensu baishigeniba haushi yaringa bani dalili?
sune silar fadawata duk wani bala'i don haka
sam banji wani ko digon tausa yinsu ba .
KASHEGARI Tun danatashi naji zuciyata
takwadaita da son ganin mamina baiwar Allah
don haka bayan dana karya naroki umma tabarni
naje umma tace . "ayshatu yar gidan mami nina
isa nahanaki zuwa gun maminki? kije amma dai
karki . dade tunda mutane suna zuwa miki murna
har namike tace aysha ki tambayi ahmad kinsan
hakkinsane yasan da fitarki gabadaya nabata
fuska nace umma wanne irin na tambayeshi
kuma? nifa umma wallahi bazan koma gidansaba
don haryanzu abinda yayi min banmanta ba
kobama hakaba nibana son zama da kishiya inje
inawani raba miji da ita baki umma tasaki tana
kallona tace tabdi bashakka aysha kanki daya
kuwa? . bazaki.Raba miji dawata ba to kinci
gidanku idanzaki sauke wannan tunanin banzan
tun wurima gwanda kisauke don ba inda zaikaiki
sai tashar wahala menene laifin ahmad dazakice
bazaki koma gidansa ba? naja kwafa nace umma
bakiji irin maganganun daya dunga dankaramin
ba duk akan laifi daba nawa ba sannan yayi min
kishiya,batare dasani naba mahaifiyarsa babu
tsanar dabata nunamin ba sannan yanzu ace
nakoma auren sa? . Allah yakiyaye umma tace
duk naji aimuma iyayenki duk munmuki laifi
meyasa mu kika yafe mana? murmushi nayi nace
kudaban shi daban bari nayi sauri natafi ina isa
gidansu mami kamar kowanne lokaci hajiyarsu .
da kallon banza tatareni ko gaisuwata ma da
kyar ta amsa tana wani cin magani bankulata ba
illa ma cewa danayi mamina ta na nan? . hajiya
tawurgeni da wani kallon banza tace aysha
fatima ba uwarki bace sau nawa zangaya miki
banason ganin sillan kafafunki agidannan? Nidin
ma kallo nawurgamata don tsohuwar tafara
kureni,naturobaki nace dadinta ba wajenki nazo
ba kuma wallahi babu wanda ya isa yace mmina
ba uwata bace,Allah ne ya hada bazamu rabuba
ehe! na mike,ina mata,dariya nahaye saman da
mamina take ina hawa na juyo ina dubanta tarike
haba tana fadin ba shakka nayi nata gwalo
nashige dakin mamina.WA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 3
NAGA RAYUWA book 3 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:58
Wannan karon tsaf na sameta azaune tana
karanta wata mujalla bataji shigowata ba
kasancewar kofar abude take sai da taji nayi
tsalle ajikinta afirgice tamike tace Ho ho ho!
aysha sam bakya girma kwabe fuska nayi kamar
zanyi kuka nace mamina mekuma nayi? tajawoni,
jikinta tana cewa babu abinda kikayi sweet
daughter me yafito dake madadin kizauna kihuta
daga fitowarki jiya shine kika debo kapa kika taho
yau?. Hawayene yazubo min daga idona mamina
tace subhanallah meya faru ayshatu? Nace mami
na wallahi gidan babu dadi tun da babu ke Don
Allah mami yaushe zaki dawo gidanmu? . Dif
naga mamina tayi da fuskarta tamkar dai ba ita
ba ce take annashuwa yanzu tace "aysha ni da
gidanku har abada babu sunan dana sakawa
gidanku illa BAKIN GIDA anyi min abinda ba ataba
yimin ba arayuwa kedin ma dandole nake kulaki
saboda kaunarki ajinina take daga Rabbil Izzati
idan ban da haka abinda akamin akanki yaci ace
tuni nayi watsi da al'amarinki tobazan iyaba
konayi kamar nafita harkarki sai naji nakasa jinki
nake tamkar kedin jini . nace wane irin cin
mutunci ne abbanki da zuri'arku basuyimin ba?
hattasu muhammad usmanu ne kawai bai zargeni
ba,kuma hargidan nan yazo yana bani hakuri don
haka babu abinda zance masa,sai kuwa
ummanku macece jaruma da ta dau duniya ba
komaiba don tabbas hakika yar uwa ta daukeni
har nan gidan tazo tana bani hakuri" shiru nayi
sosai nagaza,cewa mami komai don kam nida
kaina na sani anci zarafin,mami akan laifin da ba
nata ba Nadade sosai,don sai karfe uku natafi na
sake baiwa mami hakuri . murmushi kawai tayi ta
ce aysha ni da gidanku har abada" Banga,laifin ta
ba don kam anyi mata laifin dayaka mata tadau
kowane irin hukunci kamar.Yadda nima nasha
alwashin bazankoma gidan Ustaz ba don nima
yashaka min maganganu masu kama da kamshin
mutuwa ina isa gida natarar da galleliyar motar
Ustaz akofar gidanmu tsaki naja azuciyata nace
sarkin naci Baya cikin motar Aharabar gidan
nagansu azaune shi da ya farouk gaba daya basu
isheni kallo ba donsu kansu yayyen nawa bawani
kallon arziki nake,musu ba Adage nake kallonsu .
Dalili?lokacin da abin yafaru babu wani wanda
yabawa iyayena hakuri acikinsu sai ya usman
don haka gaisuwa ma dakyar nake gaishesu akan
tilas Har nawuce ya farouk yataso dasauri ya
biyo bayana Ahankali yakemin magana Aysha
kina kallon mijinki kika shareshi tundazu fa
wajenki yazo yana jiranki wani kallo na watsa
masa hakan yasa baici gaba da magana ba Nace
yaje yanemi matarsa amma bani ba don ni
nawuce tunaninsa daga, haka da azama najuya
zanshiga gida ji nayi an riko hannuna ko ba
afadaba nasan Ahmad ne don kuwa ga
mayataccen kamshin turarensa nan ya cika
hancina da azama nafuzge hannuna fuskata
ahade nawurga masa wani wulakantaccen kallo
nace for the last time malam kada kasake
yunkurin hakan..." mekike nufi? kina matsayin
matata kiyimin warnin akan jikinki? kada ki manta
fa mallakina ne yafada yana sake,wurgamin kallo
tsaki nayi nace kaidin wai wane irin sarkin
nacine.? Sau nawa zangaya maka kabar kiran
aysha amtsayin matarka How I wish anaganin
zuciya nabude maka kaga matsananciyar tsanar
da nayi maka" . Baki asake yadubeni da alama
yana mamakin kalamaina ne murmushi yasaka. .
Yace aysha kenan Ni kuma da ina da hali
danabude miki tawa sirrin zuciyar kin ga
soyayyarki zalla da tacika ta muryarsa atausashe
yasake cewa Allah ne yajarrabeni dasonki da ina
da iko da na rabu dake tunda hakan shi ne
burinki Ahankali yaja dabaya yafice ko kadan bai
bani tausayiba don ni din ma baitausa yamin ba
alokacin da nake neman ya a gajeni alokacin
yabude min faifan rashin kirki da wulakanci Naja
tsaki na shige gida ina guna guni . AN KOMA
KOTU . ranar da za akoma kotu da wuri muka tafi
da sam bazanje ba sai dai nashirya naje saboda
inaso ayi komai akan idona mune asahun farko
akotun kotun ta dinke da jama'a kowa nason jin
karashen shari'ar ne yakawo shi ina hango
Ahmad yana ta sakar min murmushi ni kuwa
dauke kaina nayi tamkar banganshi ba wanda
rabon da naganshi tun ranar daya ritsani
aharabar gidanmu saboda koyazo bana fita ko
umma tace nafita rokon ta nake ince tabari na
huta Abba ma kuwa bai tilas taminba tsawon
mintuna . Ashirin muka dauka akotun kafin alkali
Abbana yashigo yana, zuwa kotu ta samu
bakuncin shiru da kanshi yayi umarni afito masa
da,su